← Book details Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 14

Sashe 13

Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hidaya kara rushewa tayi da kuka ta kashe wayar ta ajiye ta , bata taɓa tunanin hajiya zata faɗa mata haka ba kenan ma da sanin ta , za'a yi mata kishiya.

shiru tayi tana share hawaye dole tabi mommy domin tasa inhar za tayi mata abib da take so kishiyar nan da za ayi mata labari zata zama ba mamaki ma yar gidan babban mutum ce.

★★★

Talatu talatu, da sauri talatu ta fito tana cewa haba yaya hadi lafiya kake min wannan kiran ka shigo cikin gidan nan babu ko sallama.

Ke bana son rashin kunya harkar arziki ce ta , zo mana amma Umaru yana so ya saka bakar kafar sa ya ture mana arziki.

ya faɗa yana gyara malin malin din sa.

Talatu tace '' kayi min bayani yadda zan gani?.''

to yanzu nan ina zaune ƙuda nabin baki na saboda tsabar talauci da yake damuna hinin yau babu wanda yazo ya siya dabino ko sai wata bakar mota katowa fa wallahi fuskata tas sai da ta fito a jikin motar, ta tsaya wani hamshakin mutum ya zuge Glass da sauri na , nace mai alhaji kwano nawa za'a baka ? mutumin nan talatu sai yace '' gidan malam hadi yake nema.,,

nanfa jiki na ya fara zikiri nace wanne wanne hadin bashi da inkiya yace mahaifin nimrah yar gidan malam Umaru sai nace me hadin yayi nayi haka ne naji idan wani abu ne tofa nace ban san sa ba , banci nanin ba nanin zata cine ne

cikin zaƙuwa talatu tace '' kai sauri ka kara samin labarin ni dadi na da kai idan ka tashi bada labari komai sa ka faɗa.

hmmm ke waya ke harkar tsiya, ki tsaya na zube miki ita a fefe yace '' zai bani dubu hamsin nanu mai gidan.,,

sai nace to faduwa ta zo daidai da zama ni ne amma gaskiya na saka ran da dubu hamsin din nan ka bani ita tun safe babu wanda yazo ya tsaya min anan gurin da sunan yazo siyan dabino

sai yace '' alhamdulillah za mu iya magana dakai.,,

nace a'a bani kudi na sai ka faɗa min duk wata magana da zaka faɗa min mutumin nan talatu sai ya dauko rafar kudi ta yan dubu dubu guda uku ya biyu dubu dari cif na karaba ina godiya kin san wani abin takaici wai ashe auren nimrah yake nemawa ɗan sa Umaru yace a'a wai yafi karfin nimrah shi talaka ne

Salati talatu ta saki tace '' kai ashe daman bashi da hankali ga arziki yazo mana yana ƙoƙarin ya saka kafa ya ture shi bara na sako hijabi mu tafi.,,

tsaya tsaya mana dad'i na dake son kuɗin ki, yayi yawa wallahi sai nace mai ni ne wan umaru uwa daya uba daya bani sadakin ta gobe ka dawo a daura musu aure.

Kinga miliyan daya ya bani da dubu dari biyar ya bani yanzu zuwa za muyi , gidan sa mu haɗa hannu da hannu mu taushe shi gobe ayi abin da za ayi kar ma makiya suji ni wallahi ace ina da yarinya bashi zanyi matsalar, kinga rafi'atu baka ce su kuma masu kudin nan suna son farar mace shi ya saka ma bance gata nan ba.

ban da abin ka yaya hadi ga zulai nan ai da dan hasken ta.

wani kallo yayi mata, yace '' kin ga bana son shir'man banza sako hijabin ki muje dole ya amshi sadakin nan wallahi yarinyar nan idan ta auri Alhaji saheer ai sai mun gaji da keta hazo idan har ba kaza bace ci ki goge baki nama amshi number sa ma.,,

Wallahi kuwa ta faɗa tana saka hijabin ta , gaba yayi tana bin sa a baya tafiya suka yi me nisa sannan suka isa gidan su nimrah a soro suka ci karo da malam yana cin abinci washe baki yaya hadi yayi yace '' malam umaru dan uwana rabin raina abinci kake ci haka...?.,,

mamaki ne ya kama malam yace '' yau kune a gidan nan Allah ya saka lafiya.,,

haba kai ko kunya baka ji ba laifi ne dan ɗan uwa , ziyarci dan uwan'sa.,

suka faɗa suna zama a kan tabarma talatu tace '' yaya umaru magana ce ke tafe damu.,,

Ke rufe min baki ni zan fara magana ya faɗa yana zaro kudi ya zube mai gaban sa , kallon mamaki Malam yake musu yace '' yaya talatu ina kuka samu kuɗin nan haka

dariya hadi yayi ya hade gurin waje ɗaya yace '' naka ne sadakin yarinyar nan ne nimrah da Alhaji saheer dalhat ''

kai ya hadi sadaki fa ka ce ? yaya da bakai gaggawar amsar wannan kudin ba wallahi ficikar sa bata burge ni duk da a yi a bincike da nayi da kuma nazari ba na gansa da wani mugun abu ba wallahi mutuncin ya'ta yafi min wannan kudin.

kana kuwa da hankali umaru kalli gidan da kake ciki kuma gidan haya idan shekara tayi , wallahi Allah ni nasan baka da kudin da zaka biya na haya ba siyar da yarinyar ka , kayi ba aure haramun ne daman ai shi kowa yasan yana son talaka to Allah yayi daga gare mu fashewa yayi da kuka ya ci gaba da cewa mahaifiyar mu da zata mutu ni taba wa amanar ku a iya sani na , na kula daku shine yau zakai mana bakin ciki arziki ya zo kace a'a idan ka zauna da yarinyar nan Umaru ka faɗa min idan ta zauna zaman me za tayi maka ? Wallahi Allah yau dana tashi babu ko, kobo a guri na amma kanin mahaifin Alhaji dubu dari ya bani.

Haba yaya mene na kuka ni da nimrah duk kana da iko da mu Amma ka duba abin da nake son ka gane wannan kudin kamar mun siyar da yar mu ne shi ya saka ma da yazo nace mai a'a

Salati talatu ta saki tace '' yaya umaru kayi wa Allah da manzon sa ka amince da auren nan mu bishi da addu'a Allah ya saka ayi a saka Ubangiji ya kade fitina dan girman Allah ka amince.,,

Malam shiru yayi yana sauraran su yace '' bawai ina ja da ku bane amma ni gaskiya ba zan siyar da ya'ta ba.,,

Hadi yace '' to shikkenan ka zaɓi yar'ka akan mu ko ba komai Umaru ya faɗa yana dafa saitin zuciyar sa yana cewa talatu ki sheda idan na mutu dan uwana ne ya kashe ni.

kuka ta saki jikin Malam ne yayi sanyi ganin halin da ya'ya hadi yake ciki bashi da sama dasu, su uku mahaifiyar su ta haifa sai kuma yan uban su , su wa'yannan zaman gaba suke yi tun da ran mahaifin su yaso ya sasanta abin Amma suka ki , da yake matsalar agurin su take mahaifiyar su fita tayi mahaifiyar su malam ta shigo shine suke ganin ita ta kore mahaifiyar su.

zai yi addu'a inshallah komai zai zamo da sauki yace '' to shikkenan na amince amma kace wannan kudin yayi yawa.,,

tsayawa hadi yayi ya a '' ban gane yayi yawa ba ? Kana da kudin da zakai mata kayan daki ne ? ..''

a'a ya faɗa yana kallon kudin.

Hadi yace '' to kaga ke talatu ungo dubu daya ladan ganin ido kai kuma Umaru dauki wannan kudi ka ajiye duk abin da ya kamata sai ka dauka kayi dashi ka bar mata wani abu kar mu cinye mata sadakin mata duk ka .''

ba dan ransa ya so ma haka ya amsa Hadi lalubo wayar sa yayi ya dannawa saddam kira domin shi a tunaninsa kahun saheer ne yana dagawa yace '' kira ni bani da kudi.,,

Malam girgiza kai kurum yayi domin shi be so suka ji wannan maganar ba Allah yayi musu son zuciya ga wauta yana tunanin NIMRAH su ta gado domin kusan halin su ɗaya.

aikuwa ba jimawa ya kira Hadi yace '' to alhamdulillah komai ya tafi yadda ake so na bawa ma mahaifinta kudin gobe sai ku zo ayi abin da ya dace kar kaga ina yin magana da sauri kasan halin garin nan katin naira dari dakyar zai iya yi maka magana me yawa.,,

Saddam yace '' to Allah ya kai mu baba zan fadawa ogan nawa yace ma wannan kudi a bar shi a matsayin kudin nagani ina so sa rana .,,

To to masha Allah amma ina da tambaya Alhaji.

saddam yace ''' to baba Allah ya saka na sani.,,

amin ya Allah da man na ganka ba wani babba ba naji kuma kana cewa zaka fadawa ogan naka ka bani labarin abin da ya faru da farko kai ne wan mahaifin sa ko wani ne ko kai wakili ne...?.''

gaban malam ne ya faɗi jin maganar da wan nasa yake ki yi malam yace '' yaya kai da baka ai be ƙara sa ba ya rufe mai baki yana cewa kai shiru mana idan ana magana da me kuɗi ba'a magana sai ya gama.

ya faɗa yana sakin speaker wayar da yake dan newa yayi yace '' Alhaji ina jin ka.,,

saddam yace '' ni yaron nasa to inshallahu gobe yan uwansa za su zo dashi sai ayi abin da ya dace.,,

to to dan samari ni daman wallahi kai na ya kalle nace kaga tsoho da jikin yara.

dariya saddam yayi sukai sallama.

talatu tace '' ni fa ban gane ba ya naga ana ƙoƙarin gama komai ban ga nawa kason ba wannan dubu dayar daka miko min ita almajiri zan bawa ko wa...?.''

sakar baki Hadi yayi yace '' a'a uban almajiri zaki bawa talatu ki, kiyaye ni wallahi idan bakya so bani ai naga ni ne babba kuma ba karan ki ne ya kama ba da kin san da wannan din da zan baki, ki rai na...? karki nemi ki batan rai Alhaji umaru kana ji na ko.

ya faɗa yana wata iriyar dariya.

Malam yace '' yaya kar fa muzo muna dana sani...?''
Chapter 13 · 0% Book details