← Book details Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 14

Sashe 4

Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

baki daya bata cikin nutsuwar'ta haka take tafiya har ta ƙarasa kofar gidan su, shiga tayi tana cire mayafin ta , ta rataye a kafaɗa cikin Sa'a ta , tarar hafsatu, ta ajiye abincin ta fara da mai yaji salak da tumatur har da kokomba da sauri ta dauki buta ta wanke hannun ta , ta zauna ta fara ci cikin kwanciyar hankali.

Kan uba kin ajiye ne kike cimin abinci na .

Fatima kanwar, ta faɗa tana kallon ta .

Nimrah tace '' idan kin isa zo ki kwata wallahi ki ga yadda ake soya fuskar mutum sai na dilmiya fuskar ki a cikin wutar nan.,,

To yar ta'adda kin dawo na sha faɗa miki ba ruwan ki da ya'ya na amma kin ki ji duk ranar da kika sake na kama ki wallahi Allah na lahira sai yafi jin dad'i shegiya zaki ci uban ki ne indai ina raye bake ba ganin ci gaba a rayuwar ki.''

wallahi Allah ke baki isa ki yi min abin da Ubangiji be min ba.

wata dariya hafsatu tayi.

Nimrah ci gaba da cin abincin ta , tayi cikin kwanciyar hankali aikuwa hafsatu kamar ta ari baki haka ta dinga faɗa ta inda take shiga ba tanan take fita ba.

nimrah gama ci tayi ta , tashi ta wanke hannun ta, ta saki gatsa tace '' to yanzu tun da cikina ya dauka sai na tafi nayi sallah na kwanta kafin yamma tayi naga ina kuma zan nufa .''

Malam ne ya shigo yana cewa sai da kika fita kenan?.''

juyowa tayi tace '' wallahi Allah neman aiki na fita malam na gaji da suyar awaran nan , kullum ina gaban kasƙon suya kuma har yau kudin jarabawar tawa yaki haduwa , to har yanzu ban samu ba yau ma da naje wani Company wallahi dakyar na fito saita ni sukai da bindiga ,

dariya fatima da hafsatu, suka saka.

nimrah bin su tayi da kallo ta share kwalla tana kaunar tayi karatu me zurfi amma abin yaci tura kullum idan ta nemo ci suke yi malam direba ne to a yanzu yafi shekara uku bashi da mota sai dai ya karɓi haya yaje ya dan nemi na abinci kwana biyu ma abin yaci tura baya samun motar hayar shi ya saka lamarin gidan ya ƙara tabarbarewa.

Malam yace '' nimrah yawon nan da kike yi duk bashi bane mafita, ke yanzu kin gwammace adin ga nuna ki da baki? Sa'anin ki wasu na dakin mijin su wasu wata me kamawa bikin su wasu sun haihuwa, amma ke babu lissafin aure a gaban ki.,,

Nimrah tace '' malam kenan abin da ba sauri nake na ni wallahi rayuwar talauci ce bana so bawai samarin ne ba ni da su ba ka naga yar kazar nan ma cinta gagarar yake yi a cikin gidan nan idan na auri talaka haka rayuwar zata dinga tafiya kai dai kai addu'a Allah ya kawo na gari.''

girgiza kai yayi duk sanda yayi mata wannan maganar, wannan lissafin take mai bata san wani kudin ba hatsari ne a wani gidan me kudin ga kudin nan amma ba kwanciyar hankali.''

nimrah daukan buta, tayi, ta shiga bayan gida.

Fatima tace '' wallahi Allah mama nimrah tana abin da ta ga dama gashi malam baya son yi mata fada.''

Uban'ki zai min bayan wanda ya yi min okay wallahi i well slap you now now stupid daman ba tun yau ba nasan ke cream (criminal) ce wallahi.''

Fatima tace '' aikin kawai daga anyi magana sai ki dinga yiwa mutane turanci Allah ya saka ma dai-dai kike yi yanzu da wasu malaman Turanci za su ji cewa za su yi kina yiwa Turanci fyade wallahi sai sun hukunta ki.''

hhhhh in fitsari banza ne kaza tayi mu gani yau da naje gurin neman aikin nan suna yi min na fara yi musu tsuru tsuru suka yi da wani ya kawo min maganar banza nace shut up gerewe (get way) tuni kowa ya kama kan'sa Ni nan wallahi ko queen Elizabeth karya take ya nuna min turanc balle ke kina tundun dan bala tantagaryar talaka.

Yauwa mama dan Allah an buɗe wata makaranta nan bayan mu ta yaki da jahilci ki daure ki shiga kema ki dinga turo dauri gaban goshi kina riƙe book a hannun ki.

Nimrah idan kina haukan ki karki ƙara saka ni a ciki cewar hafsatu.

Nimrah tace '' hmmm mama kenan to nidai ina tunanin film zan shiga saboda abin mamaki lokaci ɗaya mutum yake shiga yake arziki sai ki ganni da ƙatuwar mota ana yimin jiniya.''

kaf cikin su ba wanda ya kula ta har ta idar da alwalar ta , ta shiga daki shinfida da'duma tayi, ta tada sallah.

wannan kenan.

Baby badai tafiya za kiyi ba cewar Hidaya.

amrah zama tayi, tana shafa maman Hidaya da yake shimi ce a jikin ta.

wata malalaciyar kara ta saki tana gantsarewa tace '' gaskiya ke ta dabam ce.''

murmushi tayi tace '' hajiya ta.''

riƙe hannun ta , tayi tace '' tun da nake wannan harkar ban taɓa haduwa da wacce tasan sirrin gigita mace sama dake ba .''

haɗe baƙin su amrah tayi tana aika mata da wani mugun wasa.

a hankali ta saki bakin hidaya,

Hidaya girgiza kai tayi tace '' Please kar ki tafi.''

Amrah tace '' gaskiya Hajiya tafiya zanyi ai na faɗa miki dakyar aka bar ni, na kwana karya nayi a gidan mu.''

limshe ido Hidaya tayi tace '' okay amma zanyi missing din ki wallahi.''

Nima haka mommy na komai naki me kyau ne , amma kin haɗu da miji dutsai baya more wa dad'i.

Dariya Hidaya tayi tace '' dazu ya fita yana wani kumbure kumbure kallon inda yake ban yi ba wallahi ni fa ATM na mayar da saheer lokacin da nake tsananin bukata na nemo shi ya biya min baka ta, ta wai yana ganin ya samu lafiya yana ai.....tun kafin ya karasa na gane ina zancen sa ya dosa nuna mai nayi sam ni ban san zancen ba komai sa an shirya ake yin sa , amma ni yanzu bani da time din da zan bude mai ya shiga.''

Amrah tace '' Allah sarki Allah Hajiya ki dena yi mai haka kar wata ran reshe ya juye ga mujiya nima wannan abin da kike gani wallahi dole ta saka ni yi da kuma ƙaddara.''

ZAMAN KAN'TA TAKE

EPISODE 3

Hidaya tace '' hmmmm ba zaki fahimta ba ke yarinya ce .''

murmushi tayi, ta , tashi rataya jaka tayi rungume Hidaya ta ƙara yi ta yi mata kiss a gefen kumatun ta , tace '' bye.''

ta kara she maganar tana sakin ta tare da , daga mata hannu.

Hidaya hannu ta daga mata tace '' bye ,

fita tayi tana murmushi Hidaya zama ta gyara wayar ta, ta dauka ta kunna datar ta messages ɗin Whatsapp ne suka ɗinga shigowa musamman ma na group din su na matan manya shiga tayi ganin message din yayi yawa da alama an saki sabon update ne.

a hankali ta fara bin hirar su murmushi tayi ta buɗe DP din wacce taji tayi wani voice to voice din ya dauki hankalin ta musamman ma muryar ta , sai ta haifar mata da wata kalasa babu picture din'ta sai picture din kyakkyawar kafa anyi mata kunshin nan na yan sudan ga sarkar kafa sosai ta shagala da kallon kafar to ina ga ta'ga me kafar .

shiga ciki tayi kamar za tayi mata magana sai ta fasa, domin bata son disgi da girman ta , tana matar babban mutum kamar Saheer ta tsaya wata mace na hulakan'ta ta..

contact din admin din group din ta shiga ta fara yi mata voice tana cewa hy bestie yakike ya harkoki am naga wata so ban san ko new comer bace Please connect me with her urgently Amrah has left, and I really need this as soon as possible ...

tura mata , tayi ta she datar ta ganin bata online.

tashi tayi ta fara tafiya , handle din kofar dakin ta , ta murɗa ta shiga wayar tace tayi ringing ganin sunan kanwar ta da sauri ta dauka tana cewa sai yau kika tuna dani.

ta faɗa tana murmushi.

daga can bangaren samha tace '' aunty kin san me yake faruwa kuwa? mommy ce tace sai na buga miki waya baki sanar da ita ba , wai mijin ki yayi aure labari ya karade social media ga wani picture dai babu fuskar matar sai dai bayan ta amma shi dai wallahi Allah ba Al bane shi ne zance dai kala kala wasu sunce karuwar sa ce ko fa minti talatin ba ayi ba da ɗora labarin amma ke kin ga uban liking da comments.''

Hidaya , tace '' aure fa kika ce ? hhhh wallahi karya ne, ni kai na be iya dani ba ɓalle yake ya dauko wata kin ga , ku kwantar da hankalin ku, saheer ba zai taɓa yin aure ba.''

Samha tace '' aunty bafa a shedar na miji.''

zama Hidaya tayi ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya daukan lemo tayi ta sha ta ajiye ta saki wata uwar gyatsa tace '' nasan saheer sarai tun kafin na shigo cikin wannan gidan na gama karantar halin sa , bashi da burin aure aure mace ɗaya ta ishe shi tun kafin A'isha ta haihu be karo mata kishiya ba haka yayi hakuri har Allah ya basu da ta mutu ya dade be yi aure ba sannan ya aure ni abu biyu zuwa uku saheer ya saka a gaba ci gaban kasuwancin sa mahaifiyar sa ya'yan sa da yan uwan sa , Saheer wallahi ba irin mazan da kika sani bane yana da hakuri da kawaici amma baya daukar raini, ko ni da kika ga ina abin da nake so to akwai wani sirri a tsakanin mu.'''

dan Allah aunty faɗa min na dinga yiwa abban eman shi kinsan fa wallahi ba tun yau na san yana bin mata ba kawai hakuri nake , nake zaune dashi Allah aunty samin irin mijin ki sai an tona.
Chapter 4 · 0% Book details