← Book details Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

Zaman Kanta Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wata leda ta dauka ta fara gyara zaman takardun ta..

fitowa tayi tana ƙara kallon mudubi, saka mudubin'ta tayi cikin jaka dauko wani takalmi tayi cover shoe ta saka saboda tsabar turawa, hafsatu haushi wata iriyar tafiya ta fara yi tana karairaiya tana murguda duwawu tana cewa Wallahi Allah bana son over look kin baza min eye's stop I telling me monkey.

Hafsatu takaici ne ya ishe ta domin ta tabbatar wannan turancin da take yi da ita take tasan yanzu haka, zagin ta take yi...

ganin yadda ta saki baki tana kallon ta, sai ta zage tana turanci wanda idan za'a saka kan'ta a gabas ace me take fadi bata sani ba haɗa kallomi take yi duk kalmar da tazo bakin ta faɗa take yi.

sai da ta fita soro ta saita kan'ta ta fara tafiya takardun cikin ledar nan ta fito dasu ta rike a hannu kai kace kwalin master degree ta riƙe.

tamkar me tausayin kasa haka take tafiya har ta fita bakin titi..

ita kan'ta bata san ina ya nufa ba , wani me napep ne ya tsaya ya kalle ta , yace '' yan mata ina zaki?.''

Nimrah tace '' dan Allah kasan inda ake daukar ma'aikata? neman aiki nake yi.''

matashin yace '' aikuwa akwai wata sabuwar store zan kai'ki yau abokina ya tafi Interview.''

Alhamdulillah Alhamdulillah muje ta faɗa tana shiga tada napep din'sa yayi yana Allah ya saka shi yake interview wallahi nasan kin riga kin samu aiki.''

Nimrah washe baki tayi, tayi fari ta gyara zaman glass din ta,tace '' aikuwa idan haka ta faru albashi na , na farko, kana da kaso me tsoka,,

Matashi yace '' dan girman Allah.''

cire glass din ta, tayi ta goge tace '' serious wallahi.''

Hhhh yar boko ce har da turanci?.''

Of course nan da kake gani na book book na sassauke su kuma suna kaina irin manyan book din nan su dictionary kamus duk suna kaina.

dauko kamus tayi a jakar ta duk yaji jiki wasu fefofin ma duk sun cire tace '' kaga wannan yadda kasan karatun sallah haka na iya su.''

juyowa yayi yace '' ikon Allah duk yawon littafin nan.''

Yes ta faɗa tana mayar dashi jaka, jakar jikin ta littattafan Junior dinta ne dana senior.,,

nimrah shiru tayi tana bin hanya da kallo, tunani ne kala kala a cikin ranta musamman ma , da suka ƙara sa gaban Company da sauri ta kalle sa tace '' nan ne wajen?.''

matashin nan yace '' eh wannan Company da kike gani Company matatar man fetur ne shi ne na biyu a kasar nan sabon budewa ne ina wannan dan kasuwan Saheer dalhat nasa ne.''

farin ciki ne ya kama nimrah tace '' wanda nake gani a tv..?.''

Cikin tabbatar wa , yace '' eh shi ne.''

fitowa tayi tana cewa ta ina zan shiga...?.''

Me napep yace '' bani kudina.''

Nimrah wano kallo tayi mai tace '' haba dan saurayi kasan bani dashi idan na fara daukar albashi zan baka.''

kutt me kika ce , zaki bani ko sai na kwashe ki da mari ya faɗa yana fito kamar ba shine yanzu suka gama wasa da , dariya ba.

Nimrah mamaki ne ya kama ta , tace '' sai ka dauki na annabawa bani da shi.''

ta faɗa tana kokarin shiga ganin wata katuwar mota, ta zata shiga da sauri me napep ya bi bayanta yana cewa kai wai da gaske kike ba zaki bani kudina ba...?.''

Nimrah da gudu ta shiga tana haki, me napep tsayawa yayi yana masifa.

Ƙatuwar motar nan shiga cikin Company tayi.

nimrah ganin ta shiga da sauri ta ƙarasa gurin wani tace '' sannu baba.''

Kallon ta yayi yace '' yauwa.''

Nimrah tace '' dan Allah tambaya nake yi.''

Tsohon yace '' Allah ya saka na sani.''

Nimrah tace '' dan Allah ance yau ana ɗiban sababbin ma'aikata haka ne.''

Eh ga wata hanya nan ki bi zaki ga mutane ki tsaya ga ogan nan ma ya zo shi zai muku interview.

godiya tayi mai ta fara tafiya tana kalle kalle, hanyar da ya nuna mata nan ta bi matasa ta gani da magidanta a zaune matan cikin su basu da yawa nimrah zama tayi tana bin kowa da kallo.

wani ne yace '' tashi waje nane.''

banza tayi mai , ƙara yi mata magana yayi.

tace '' kwai ka saka ne?.''

da sauri kowa ya juyo yana kallon ta.

Mutumin yace '' kut ni da waje na me makon ki ce nayi hakuri sai ki faɗa min bak'ar magana duk faɗin guri nan sai ki zauna min a guri na.''

ba wanda ya kula su, jun jima a haka a ka fara yi nimrah ita ce ta ƙarshe.

shiga ciki tayi tuntube taci da flower da sauri ta riko,ta takardun hannun ta ne suka tarwatsai.

ɗurƙusawa tayi, tana dauka.

Sadam ƙasa yayi da idon sa ,

gama haɗawa tayi ta zauna tana cewa sannun ku.

Mahmud ɗago idon sa yayi ya kalli sadam domin shi tunani ya fara yi anya kuwa tana da hankali.

sadam ne yace '' yauwa ina CB ɗin ki?.''

kululu cikin nimrah ya bada wani sauti dakewa tayi, ta ciro takardun da suke jakar ta , tas dana hannun ta , ta ajiye musu.

Mahmud kallon table din yayi tun da ogan nasa yake buɗe Company be taɓa tsayawa yayi interview sai yau,yau din ma cewa yayi shi zai shi, shi ya saka ya tsaya zai yi.

abin da ya saka ya tsaya ance ana yiwa wasu alfarma yafi so ya bawa wanda suka cancanta ashe rabon ran'sa ya ɓaci ne dunkule hannun sa waje ɗaya yayi yace '' Are you even thinking straight? What did you just pour on the table?.''

rasa ina zata saka kan'ta tayi sadam ne yace '' waya baki damar shigowa nan..?.''

nimrah shiru tayi ba karamin tsoro suka bata ba , kallon wanda yayi mata turanci tayi tace '' idon'ta wayarin english.''

da sauri ya kalle ta , sai yanzu ya ƙara tabbatar wa , bata da hankali sadam dariya yayi yace '' ina takardun makarantar ki?.''

da sauri ta kwashe takardun nan ta saka su a kan cinyar'ta nemo takardar primary din'ta, tayi da ta Junior dinta sai takardar admission da aka bata , ta senior ta miƙa musu.

amsa sadam yayi yana juyawa kallon ta , yayi yace '' ungo bama neman masu shara.''

domin shi a tunanin sa neman aikin shara da yan goge goge take.

da sauri ta ɗago amsa tayi tana cewa ai idan ba zaka dauke ni na be kamata ka ci fuska'ta ba kace min bakwa neman masu shara nayi maka kama da wacce za tayi shara wallahi ko sharar gidan Gwamna a albarka bazan yi ba , balle sharar Company nan naku me kama da zuciyar talaka.

a fusace Mahmud ya tashi yana cewa zaki fita ko sai na saka an fitar dake

Nimrah wani kallo tayi mai ta murguda mai baki tana cewa aikin banza duk inda aka yi bakai ne me Company nan ba , wallahi yadda kake baki nasan haka zuciyar'ka take.

daga hannu yayi zai mare ta lokacin Saheer ya shigo da sauri yace '' Mahmud .''

A sauke hannun sa yayi nimrah tace '' barshi barshi da wallahi ya aikata kuskure mafi girma a rayuwar ka kudin mota ta kuma Allah ya isa ni ce maka nayi aikin share share nake nema ka kalle ni da kyau nayi maka kama da wacce za tayi wannan aikin wallahi ko giwa ta rame tafi ƙarfin rami wallahi allah.''

kowa kan'sa ya sunkuyar ƙasa Saheer kallon ta yayi tun daga sama har kasa dauke kan'sa yayi ya huce cikin office din da yake part part ne a wajen.

da sauri nimrah tabi bayan sa tana cewa alhaji dan Allah ka dauke ni aiki wallahi Allah nafi wata ina neman aiki ban samu ba kuma takardu na sun yi kyau kalli assignment ɗin da nayi duk very good malamai su ke saka min.

ZAMAN KAN'TA TAKE

Episode 2

Alhaji dan Allah ka , karɓa ka gani. tuntube tayi glass ɗin ta , ya faɗi fashewa yayi nimrah da sauri ta durkusa ta dauka takaici ne ya kama ta tace '' shege me katon kai, saboda kaga kana kuɗi shi ne kake hulakan'ta, talaka.

Saheer sarai ya jita amma sai yayi banza da ita da sauri security ya buɗe mai kofa shiga cikin office din yayi bismillah yayi ya zauna a kan kujera yana kallon ƙatuwar plasma da take nunawa komai na cikin Company.

sadam ne ya shigo riƙe da wasu file bakin sa dauke da sallama yace '' ni wallahi Allah ba san ya a kai ba wannan yarinyar ta shigo ba anya kuwa tana da hankali taki tafiya.''

Saheer kallon sa yayi ya miƙa masa hannun sa alamar baya son magana ya ba shi file ɗin.

miƙa mai yayi yana cewa sorry sir.

domin dukkan alamu ran Saheer a ɓace yake, duk irin kokarin da yake gurin danne ɓacin ran'sa amma sai da ya fito.

Saheer ɗaga mai hannu yayi alamar ya tafi.

fita yayi yana ja mai kofa nimrah ya kalle da take zaune tana gyara glass din ta da ido daya ya fashe yace '' wallahi idan baki tafi ba yau sai kin gane ke mahaukaciyar karya ce.''

ɗago manya manyan idanuwan'ta tayi, bata ce mai komai ba ta murguda mai baki cikin office kuwa Saheer zubawa tv ido yayi baya jin abin da sadam ya faɗa amma duk yadda akai kalmar tayiwa yarinyar zafi, kan'sa ne ya kulle to tana mace , kuma me ƙananan shekara me zai saka ta , tawo neman aiki da alama ko secondary bata karasa ba , kuma ta ,tawo Company irin wannan neman aiki bata gudun rayuwar ta , ta lalace tsaki yaja ya dauki telephone ya dandanna wasu numbobi ya ƙara a kunne yace '' ka ce mata , ta shigo.''

yana kai wa nan ya ajiye wayar sa.

ba jimawa sai ga nimrah nan da jakar ta ,irin ta wanzamai jan kujera tayi ta zauna tana cewa yallaɓai wallahi na sha wahala sosai na dade ina neman aiki..

muga takardun ki ya faɗa yana mai da hankali kan laptop ɗin sa.
Chapter 2 · 0% Book details