Sashe 8
Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Matar na sanye da farin zani mai launin ƙyalli, gashinta yana tafiya kamar ruwa, a fuskarta akwai nutsuwa, amma idanunta — suna da wani irin hasken da ƙwallar Zainab take yi.
"Ke ce?" Zainab ta tambaya, muryarta tana girgiza.
Matar ta yi murmushi.
"Ni ce abin da kika boye, ni ce ƙwaƙwalwar da aka ɗaure a cikin ruwa saboda ki rayu ba tare da nauyin asali ba."
Zainab ta matsa baya.
"Ban gane ba ni fa ba ruhi ba ce mutum ce."
"Mutum?" ta ce cikin dariyar da ta yi kamar amo daga nesa.
"Eh, amma kin zo ne daga ruwa.
Lokacin da aka haife ki, an ɗebo ki daga ruwan nan da hannun mahaifiyarki, an rufe asirinki domin kada kowa ya san yadda kike da alaƙa da shi."
Zainab ta lumshe ido, hawaye suna taruwa.
"Me yasa yanzu? Me yasa yanzu yake kirana?"
Matar ta ɗaga hannunta ta taɓa goshinta.
"Saboda lokaci ya kusa, garuruwan uku da ruwan nan ke bin su suna dushewa, Idan ba ki dawo ba, zasu shuɗe, kuma muryar ki muryar mu zata ɓace har abada."
Zainab ta ji zuciyarta tana bugawa da karfi.
"To me kuke so in yi?"
"Ki dawo ki haɗa ruwan da jinin ki, ki tuna da kalmar farko da kika taɓa ji kafin ki iya magana."
A wannan lokacin, hasken ya sake raguwa.
Faruk ya bayyana a gefe amma fuskarsa cike da duhu, kamar yana daga tsakanin duniya biyu.
"Zainab, ki tsaya! Kada ki saurari ta wannan ba ita bace!"
Matar ta kalli shi da murmushi mai sanyi.
"Shi ba zai iya fahimtar menene dawo ba, amma ke, Zainab… ke za ki iya dawo da mu duka."
A nan ne ruwan ya fara juyawa, yana ɗauke da su biyu cikin ƙara mai kama da gurnanin duniya da take buɗewa dgurnanin duniya da take buɗewa daga ciki.
Ruwan yana juyawa kamar guguwa mai sanyi, yana ɗauke da su cikin sararin da ba shi da sama ko ƙasa, Zainab ta kasa bambance in da rana take ko dare.
Kowane haske yana zama inuwa, kuma kowace inuwa tana magana da muryarta.
Faruk yana ƙoƙarin kusantarta, amma kowane motsinsa yana narkewa cikin ruwa.
"Zainab!" ya kira, muryarsa tana yi mata kama da ƙarar ƙarfe a karkashin teku.
"Ki saurare ni wannan matar ba ta fito daga gare ki ba, ita ce ke ta biyu, wadda aka ɓoye domin kar ta mallake ki gaba ɗaya!"
Matar cikin ruwa ta yi murmushi mai nutsuwa, ta ɗaga hannunta, ruwan da ke kewaye da su ya daina motsi, kamar yana jiran umarni daga gare ta.
Faruk yana tsoro, ta ce.
"Tsoron gaskiya, ya san idan kika gane wacece ke gaske, ba zai sake iya kiran sunanki da wannan natsuwar ba."
Zainab ta ji zuciyarta tana bugawa sosai. A lokacin da ta dubi Faruk, idonta ya ga abin da ba ta taɓa gani ba wani zobe mai haske a wuyansa, kamar alamar da ta saba gani a cikin mafarkinta.
"Faruk…" ta furta cikin rawar murya.
"Wane ne kai a cikin wannan?"
Ya tsaya, numfashinsa yana fita da sauri.
"Ni ne mai tsaron sirrinki, na rantse da ruwanki tun kafin ki zo duniya, cewa ba zan bari ruwan nan ya sake ɗaukarki ba, amma yanzu… yana kiran ki da sunan da ban taɓa faɗi ba."
Matar cikin ruwa ta yi gaba, ta ɗora hannunta a kirjinta.
"Sunanki na gaskiya," ta faɗa cikin sanyi, "ba Zainab ba ne" Zahara, wacce ke rayuwa tsakanin ruwa da iska, ki kira sunanki, kuma za ki tuna da komai."
Zainab ta rufe idonta, a zuciyarta, ta ji kamar ana ja da jikinta biyu daban ɗaya yana neman komawa cikin ruwa, ɗaya kuma yana neman tsayawa da Faruk.
Ruwan ya fara ɗaukar launin ja mai laushi.
"Zainab!" Faruk ya sake kira.
“Ki tuna abin da kika ji lokacin da kika fara ganin ƙwallar ki tuna da bugun zuciyarki, ba da muryarta ba!"
Amma muryar matar ta ratsa zuciyarta, mai taushi, mai nutsuwa, mai ɗauke da wani irin tabbaci.
"Zahara… lokaci ya yi."
A cikin wannan ɗan lokaci, duniya ta tsaya, ruwan ya tsaya, hasken ya tsaya, numfashi ya tsaya.
Zainab ko Zahara ta buɗe ido.
"Idan zan zabi," ta ce cikin murya mai cike da ƙarfi, “zan zabi gaskiya, komai take nufi."
Ruwan ya fashe da haske.
Haske mai tsanani ya mamaye komai, yana cike da sautin bugun zuciya ɗaya, biyu, uku sannan komai ya shuɗe.
Faruk ya farka da ƙarar iska mai sanyi.
Ƙwallar na hannunsa tana haskawa da launin zinariya, amma yanzu tana da zafi kamar tana numfashi.
Dakin da yake ya canza ba dakin da suka yi gwaji ba ne, wannan wurin ya yi kama da tsohon haikalin ruwa, bango da aka goge da shekaru, ƙasa mai laushi, da wasu zane-zane da ke motsi a hankali kamar suna numfashi.
Ya tsaya a hankali, yana sauraron sautin da ke fitowa daga cikin ƙwallar.
Muryarta ce, muryar Zainab, amma mai zurfi, kamar tana magana daga can karkashin teku.
"Faruk… ka bi hasken, amma kar ka yi saurin shiga, kogin Kariya ba ya gafarta kuskure."
Ya ƙara riƙe ƙwallar, zuciyarsa na bugawa.
"Zainab ko Zahara, duk wacece ke zan same ki."
Ya fara tafiya cikin hasken da ke fitowa daga ƙwallar, wanda ke nuna ma sa hanya ta cikin duhu, a kowane mataki, yana jin kamar ruwa yana magana a ƙasa kamar yana tambaya.
"Shin kai mai gaskiya ne?"
A gaban sa, wani ƙofa mai ɗauke da ruwa ya bayyana, ba ta ƙasa ko sama ba, amma tana raye, tana karkarwa da numfashi, a saman ta, akwai rubutu da ya ɓata da tsufa, amma har yanzu ana iya karantawa.
"Wanda ya shige ba tare da gaskiya ba zai manta da sunansa."
Faruk ya tsaya, ya san wannan ƙofa ce da masu ruwa ke bi don shiga cikin asalin su, amma shi fa mutum ne, mai tsoron irin waɗannan wurare, duk da haka, zuciyarsa ta ce masa Zainab tana ciki.
Ya ɗaga ƙwallar, hasken ya ƙara ƙarfi har ya cika wurin, sai muryarta ta sake fitowa:
"Ka tuna abin da na koya maka lokacin farko, Faruk ruwa ba ya cinye wanda zuciyarsa ta tsaya a kan gaskiya."
Ya lumshe ido, ya shige cikin ƙofar.
Da zarar ya tsallaka, ba ruwa ba ne ya same shi haske ne, hasken nan ya ɗauke shi kamar guguwa mai sanyi, yana ɗauke shi cikin sarari in da babu ƙasa, babu sama, sai ƙarar zuciyoyi da suka dade suna jira.
A tsakiyar wannan haske, ya ganta Zahara tana tsaye a kan tabarma ta haske, gashinta yana yawo kamar ruwan teku, idanunta cike da ƙarfi da nutsuwa.
"Faruk," ta ce a hankali, "ka zo, amma ka bar sunanka a baya."
Ya dubeta da murmushi mai ɗaci.
"Idan hakan ne farashin ganin ki, to ina bayar da shi."
Sai ruwan ya rufe su, hasken ya narke kuma daga nesa, an ji ƙarar zuciyoyi biyu da suka yi daidai bugun lokaci ɗaya.
Faruk ya buɗe idonsa cikin haske mai sanyi, amma wannan ba hasken duniya ba ne hasken nan yana da launi na rai, mai kama da kukan rana a ƙarƙashin teku.
A gefensa, Zahara na tsaye ba kamar yadda yake ganinta a duniya ba, wannan karon, jikinta yana ɗauke da alamar ruwa a fatar sa, kamar ta kunshi teku a cikin zuciyarta.
"Ka tsallaka, Faruk," ta ce, muryarta tana ratsa cikin iska kamar sautin ƙaho mai nisa.
"Amma yanzu kai ba mutum kawai ba ne, ka shiga cikin jinin masu ruwa kuma hakan yana nufin kai ɗaya daga cikin su ne."
Faruk ya kalli hannayensa haske yana fitowa daga jijiyoyinsa kamar ruwa mai motsi.
"Ba zan fahimci wannan ba," ya ce cikin murya mai sanyi.
"Me yasa ni? me yasa ke? me yasa ruwan nan yake kiranmu?"
Zahara ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta juya ta nuna wani haske a cikin sarari.
Hasken ya bayyana a matsayin tsohuwar murya, wacce take magana kamar daga cikin ƙarni da suka wuce.
"Lokacin da duniya ta rabu da ruwa, an bar mana wasu guda bakwai masu riƙe da murya da zuciya, daga cikin su, Zahara ce ta biyu, amma lokacin ta ƙi bin hanyar da aka ware mata, ta zaɓi mutum mai suna Faruk ta yi ma sa alkawarin ba zata dawo cikin ruwa ba."
Faruk ya ji jikinsa ya tsaya.
"Kin… zaɓi ni?"
Zahara ta ɗan yi murmushi, idanunta cike da wani irin ƙauna mai haɗe da nadama.
"Na zaɓi ka lokacin da bai kamata ba, kuma don haka ne aka ɗaure ruhina cikin ƙwallar, ruwan bai yarda da ƙauna mai karya dokarsa ba."
"Saboda haka," ta ci gaba,
"lokacin da ka kunna ƙwallar, ruwan ya gane murya ta ya tashi daga barci, ya kira ni, amma ya
Zahara ta kalle shi da idanu masu cike da labarai kamar kowace ƙwayar ido ɗaya na ɗauke da duniyar da ta wuce, da wata da ba ta zo ba, ta motsa hannunta, haske mai launin shuɗi ya fito daga yatsunta ya zagaye Faruk, kamar yana tantance shi, yana karanta shi daga ciki.
"Ke yi tafiya mai nisa, Zainab," ta ce da murya mai laushi amma mai nauyi kamar ana karanta ƙa’ida daga littafin da aka manta,
"Kogin Kariya bai karɓi mutum ba tun shekaru ɗari biyu da suka wuce, me ya sa ke.?
Faruk ya yi shiru na ɗan lokaci, hasken da ke kewaye da shi yana motsawa kamar yana numfashi tare da ita, a ƙarshe ya ce:
"Saboda kai da ita na san akwai abin da ke haɗa ku biyu, Zahara da Zainab, ban zo don in kwace ba, na zo don in gane."
Zahara ta yi murmushi, ba irin murmushin farin ciki ba, amma irin wanda ke ɓoye gaskiya mai raɗaɗi.
"Idan ka san abin da ke haɗa mu, to kai ma za ka zama ɗaya daga cikinmu, amma idan har zuciyarka ba ta shirya ba, hasken da ke riƙe da kai zai koma duhu."
Sai ta miƙa hannunta, hasken ya koma kamar kogi yana gudana tsakanin su, a cikin kogin, Faruk ya ga hotuna ƙananan tunaninsa da rayuwarsa, lokacin da yake ƙarami, lokacin da margaji ta koyar da shi yadda ake sauraron ruwa, lokacin da ta ɓace, da lokacin da ya yi rantsuwa zai same ta ko da ya shiga duniya ta biyu.