Sashe 6
Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsohuwar ta ce, tana mai ɗaukar numfashi mai nauyi,
"Saboda ba kowa ke dawowa ba."
Zainab ta ji sanyi ya ratsa jikinta, amma ta karɓi akwatin da hannuwanta masu rawa, tana ji a ranta cewa tafiyar nan ba ta komai bane face farawa, farawa na gaskiyar da za ta girgiza duk abin da ta taɓa yi imani da shi.
Da daddare, tana cikin ɗakin otal ɗin ƙauyen, ta zauna tana kallon hoton Faruk. Fuskar nan mai cike da sirri, da idanun da ke kamar suna kallonta daga wani wuri mai nisa.
"Faruk," ta faɗi a hankali,
"me yasa ka ɓoye gaskiya daga gare ni?"
Sai dai abin mamaki, kamar daga cikin duhun ɗakin, wata murya mai rauni ta amsa ba daga kunne ba, amma daga cikin zuciyarta:
"Saboda gaskiyar tana da farashi, Zainab... kuma ni na biya rabin nasa."
Zainab ta zabura, ta dubi ko akwai wani a ɗakin, amma babu kowa sai iska mai sanyi da ta shigo daga taga, tana kaɗa hoton da ke kan tebur.
A lokacin ne ta lura da wani abu a bayan hoton, akwai rubutu da ba ta taɓa gani ba a baya:
"Garin Ruwa Uku in da komai ya fara, kuma in da zai ƙare."
Zainab ta zauna cak a bakin gadon, tana kallon rubutun da hannunta ke rawa.
"In da komai ya fara, kuma in da zai ƙare…"
Ta ji kalmomin suna echo a cikin zuciyarta, kamar ana karantawa daga wani nesa, wani sanyi ya ratsa ta daga ƙafafunta zuwa wuya, sai ta ɗaga kanta da sauri ta duba madubin da ke gefen ɗakin.
A cikin madubin — kamar wani ɗan lokaci ta ga wani inuwa a bayanta, mai siffar mutum, amma kafin ta juya, inuwa ta shuɗe kamar hayaƙi.
Ta tsaya, ta dafa kirjinta.
"Zuciyata ce kawai," ta faɗa a hankali. "Babu komai."
Amma daga gefe, akwatin katakon da tsohuwa ta ba ta ya fara yin ƙara ƙarar ƙaramar murya, kamar ana murmurɗa makulli daga ciki.
Zainab ta matsa kusa, tana jin bugun zuciyarta yana ƙaruwa.
"Ba yanzu ba," ta tuna da gargadin tsohuwa, "Ki buɗe kawai idan kin kai garin Ruwa Uku."
Sai dai wani abu a cikin zuciyarta ya motsa, wata ƙwaƙwalwa ko sha’awa ta haramun.
Ta ɗauki akwatin, ta girgiza shi a hankali.
Sautin ƙaramin abu ya buga daga ciki kamar zobba biyu suna haɗuwa, ko ƙaramar ƙwallon tagulla.
Ta ɗauko makullin ƙaramin siriri da ta saba ratayawa a wuyanta — mallakin Faruk tun kafin ya ɓace ta gwada buɗe akwatin.
Klik.
Akwatin ya buɗe da sauti mai laushi,
a ciki akwai ƙaramar takarda, da wani zobba da ba ta taɓa gani ba,
a cikin takardar, akwai kalmomi guda uku kawai, da rubutun da ta gane nan take rubutun Faruk:
"Ki daina nema na.”
Zainab ta saki takardar ta faɗi kasa,
Idanunta suka cika da hawaye, ba saboda tsoro ba amma saboda wannan saƙon ya tabbatar da abu ɗaya:
Faruk yana raye.
Amma me yasa yake so ta daina nemanshi?
"Me yake boyewa?
Kuma me ke da alaka da wannan garin ruwa uku?"
Haka ta ci gaba da tambayoyin da ba mai amsa mata.
Ta rufe akwatin da sauri, ta ɗauki jakar tafiya, zuciyarta cike da tambayoyi,
a lokacin da ta fita daga ɗakin, wata iska mai kauri ta biyo bayanta tana ɗauke da murya mai sanyi wacce ba ta san daga ina take ba:
"Gaskiyar ba ta so a binciketa, Zainab... amma kin riga kin fara."
Tafiyar ta fara da safe, lokacin da hasken rana bai gama wayewa ba. gajimare ya lullube hanya, kamar sararin samaniya ma bai yarda da tafiyar Zainab ba.
Motar su Khadijah da yake ta saba tuƙa motar wani maƙo cin su, tana tuki cikin shiru, ta bi hanyar ƙauyuka da ke shiru fiye da yadda ta taɓa gani, lokaci zuwa lokaci, sai ta hangi tsofaffin alamu na hanyoyi da aka bar su shekaru da dama alamun da suka dusashe kamar tarihin da ake ƙoƙarin manta da shi.
Wayarta babu sadarwa.
GPS ya kasa gano hanyar.
Sai kawai titin da yake ta ja a gaba, kamar yana jagorantar ta zuwa in da bai kamata ta je ba.
Bayan awanni biyu, ta iso wani wuri da ake rubuce a jikin wata tsohuwar farar duwatsu:
"Ruwa Uku ku Shigo da nutsuwa."
Amma babu nutsuwa a ranta.
a ƙofar garin, ta ga wani mutum ɗaya tsaye dattijo mai ɗan gajeren hula, yana sanye da riga mai ɗan duhu, Idonsa yana bin ta da wani irin kallon da ke haɗa mamaki da tausayi.
"Assalamu alaikum," Zainab ta faɗi, ta sauka daga mota.
Dattijon ya ɗaga kai a hankali.
"Wa alaikumus salam… kin shigo?"
Ta ɗan yi murmushi. "Eh. Ina neman wani mutum... sunansa Faruk."
Mutumin ya tsaya, yana kallonta kamar ya ji sunan da bai kamata a ambata ba.
"Faruk?" ya maimaita, kamar suna ne da ke da nauyi. "Kin tabbata za ki iya ɗaukar abin da ke biye da wannan suna?"
Zainab ta ɗauki numfashi mai zurfi.
"Ba zan dawo baya ba."
Dattijon ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya juya ya nuna mata wata hanya mai cike da bishiyoyi.
"Ki bi hanyar nan," ya ce da murya mai rauni.
"Za ki ga tsohuwar masallaci, a can ne ki tambayi Hajiya Kubra, ita ce ta san in da komai ya fara."
Ta gode, ta shiga cikin garin" amma yayin da take tafiya, ta lura da abu mai ban mamaki garin ya yi kamar baya cikin lokaci guda.
Mutane suna motsi a hankali, kamar hotuna masu rai da ba su san suna rayuwa ba.
Wani yaro ya tsaya yana kallonta, idonsa a buɗe, amma ba ya magana.
Kamar duk wanda ke garin yana jiran wani abu... ko wata.
Lokacin da ta ƙarasa bakin masallaci, ta ga wata mata zaune a ƙarƙashin bishiya, tana saka tabarma da hannunta mai rawar sanyi.
"Ina neman Hajiya Kubra," Zainab ta ce.
Matar ta ɗaga kai, idonta suka haɗu kuma Zainab ta ji sanyi mai kaifi ya ratsa ta.
"Ni ce," matar ta ce a hankali. "Ke ce ƴar’uwarsa… ko?"
Ƴar’uwarsa?" Zainab ta tambaya. "Na Faruk?"
Hajiya Kubra ta ɗan murmusa, amma murmushin ba shi da daɗi.
"Eh. Amma Faruk ba ya nan, a gaskiya, bai taɓa barin garin nan ba."
Zainab ta ɗauki numfashi a hankali, zuciyarta ta bugawa.
"Ba kin ce yana ɓoye ba… amma kina nufin"
"Kin makara, Zainab," Hajiya Kubra ta katse ta, tana dubanta da ido mai cike da alhini.
"Gaskiyar da kike nema, tana ƙarƙashin ruwa. Kuma Faruk… shi ne ruwan nan."
"Faruk… shi ne ruwan nan?"
Zainab ta maimaita tambayar, kamar kalmomin sun fito daga wani mafarki,
Hajiya Kubra ta dubeta na dogon lokaci kafin ta tashi a hankali, ta yi nuni da tafkin da ke bayan masallaci.
"Ki bi ni," ta ce kawai.
Sun yi tafiya cikin shiru har suka iso bakin tafki mai zurfi, ruwa mai sanyi yana motsi a hankali, yana ɗauke da wani ƙamshi da ba na ruwa ba kamar ƙamshin turaren mutum da ya ɓace shekaru da dama amma har yanzu yana da tasiri.
"Garin ruwa uku," Hajiya Kubra ta fara bayani, "ana kiransa haka ne saboda akwai tafkuna uku a nan ruwa na Farko, na biyu, da na uku, amma wannan na uku… ba ruwa bane kawai. Wannan wurin yana rike da rai da kuma ajali."
Zainab ta kasa magana. Idonta ya makale kan tafkin.
"Me kike nufi?" ta tambaya a hankali.
"Faruk," Hajiya Kubra ta ce, tana kallonta kai tsaye, ya yi ƙoƙarin yin abin da ba a taɓa yi ba ya nemi ya mayar da rai da ya ɓace, Ya shiga cikin ruwa nan shekaru huɗu da suka wuce... kuma bai sake fitowa ba."
"Amma na ji muryarsa!" Zainab ta faɗa cikin firgici.
"Na ji yana magana da ni! ya bar min saƙo, da rubutu"
Hajiya Kubra ta girgiza kai.
"Eh saboda ransa bai bar duniya gaba ɗaya ba, ruwan nan yana riƙe da shi. duk wanda yake da alaƙa da shi zai ji shi, zai gan shi a mafarki, zai ji numfashinsa a iska, amma ka da ki kuskura ki kira sunansa da niyyar neman amsa… domin zai amsa."
Iska ta fara kaɗawa ruwa ya fara motsawa da ƙara, kamar ana jefa duwatsu a ciki.
Zainab ta ja baya.
"Me yake nufi da gaskiyar tana da farashi? Me yasa yake hana ni neman shi?
Hajiya Kubra ta matso kusa da ita, ta kama hannunta da sanyi mai ban mamaki.
"Domin idan kika nemi Faruk gaba ɗaya," ta ce da murya mai laushi, "ruwan zai buƙaci maye gurbin da ya ɓace, kuma wannan maye gurbin… ke ce."
Zainab ta ji numfashinta ya tsaya.
a lokacin ne ruwa ya yi wani ƙara kamar ana kiran sunanta daga zurfin ƙasa.
"Zainab…"
Ta zabura, ta waigo, amma babu kowa,
Sai tafkin, da iska, da sautin muryar da ta fi kowacce daɗewa a zuciyarta.
"Na gaya miki… ki daina nemana."
Sai ruwa ya fara ɗaukar hoto a saman sa fuskar Faruk, mai cike da ciwo da gajiya.
"Faruk!" Zainab ta kira, hawaye na zubo da hawaye.
"Ka dawo! Zan taimaka maka!"
Hajiya Kubra ta yi ƙoƙarin riƙe ta, amma Zainab ta sulale daga hannunta ta nufi bakin tafkin.
"Zainab, ki tsaya!"
Amma lokaci ya makara.
Ta saka ƙafarta cikin ruwan, kuma a lokacin da ta yi hakan, duk garin ya yi shiru, wani sanyi ya ratsa duniya, kuma hasken rana ya shuɗe.
Tafkin ya fara janyo ta a hankali, kamar yana maraba da ita gida.
"Gaskiya tana da farashi…"
Muryar Faruk ta sake maimaituwa daga cikin ruwa.
kuma yanzu, ke ce za ki biya rabin da ya rage."
Da zarar ƙafarta ta nutse cikin tafkin, Zainab ta ji kamar ana janye ta daga duniya.
Iska ta tsaya.
Ƙarar tsuntsaye ta ɓace.
sai shiru mai nauyi mirin shiru da ke cike da murya.
Ruwan bai yi sanyi kamar yadda ta zata ba.
A maimakon haka, yana da ɗan dumi, kamar jinin da ke gudana cikin mutum,
ta ji yana zagaye da ita, yana rufe kunnuwanta, hancinta, idanunta sannan komai ya shuɗe.
Da ta buɗe ido, ba cikin ruwa take ba, amma a wani wuri mai launin toka sarari mai yalwa, ba sama, ba ƙasa.
Tana tsaye a kan abin da ya yi kama da ruwa amma ba ya motsi.