Sashe 10
Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Faruk ya zauna a bakin rafi, hannunsa yana shafar ƙasan ƙwallar da yanzu ba ta haskaka kamar da ba, amma har yanzu tana da dumi, ruwa yana gudana cikin natsuwa, amma duk da shiru, tana jin kamar akwai kalmomi a cikin motsinsa kamar ana magana da shi, a hankali, cikin yaren da ba na mutane ba. Ta sunkuya, ta sanya yatsunya cikin ruwa. Nan take, yanayin ya canza. , ruwan ya daina gudu kamar yadda aka saba sai ta tsaya, tana motsawa kamar yana numfashi. Wani ƙara ya taso daga ƙasan rafi, ba ƙarar iska ba, ba kuma murya ta mutum ba, sai dai murya ce ta ƙasa da ruwa, mai cike da hikima da gargaɗi. "Mai dawowa daga hasken, kai ne ɗan farin ruwa, ka ɗauko gaskiyar da ba ta da tushe, amma har yanzu kina ƴan duniya." Zainab ta ɗaga kai cikin mamaki. "Ni ce nake magana da ku?" ta tambaya. "Ba da baki ba, amma da niyya,” ruwan ya amsa, “Mun saurari murya irin taka shekaru aru-aru, tun lokacin da mutane suka daina jinmu." Ruwan ya fara yin kwarara a hankali yana ɗaukar siffar fuska ba ta mutum ba, amma irin wadda zuciya ke gane ta: fuskarta Faruk, amma yanzu yana da nutsuwar Zahara, da hasken da bai da iyaka. "Na dawo, kamar yadda kika ce,” Faruk ya faɗa da muryar da ta shaɗe da tausayin tunawa. “Amma yanzu fa, me nake nufi da wannan hasken? Me yasa kuke bani wani abu da ba ku ga mutane da shi ba?” Murya ta ce cikin zurfi, tana haɗuwa da ƙarar ruwan da ke kwarara: "Domin ke ki saurara, mutane sun manta yadda ake jin magana ta halitta. Sun daina sauraron koguna, iska, da ƙasa, ke ce wanda gaskiyarka ta buɗe ƙofa, amma buɗe ƙofa yana nufin nauyi." Zainab ta lumshe ido. "Wane nauyi?" "Za ki zama mai ji, wacce zata ɗauki muryar abubuwan da ba su da baki, ya bayyana su ga duniya, amma ki sani, ba kowa zai yarda ba, wani zai kira ki mahaukaciya, wani kuma zai nemi karfin da ke tare da ke." A lokacin, ƙwallar ta fara ɗan haskawa, ta buga da zuciyar Zainab sai wani kallo ya shigo ma ta birane da suka lalace da fari, ruwan da ya mutu, koguna da suka dushe, mutane suna faɗa da ƙasa saboda rashin albarkarta. Zuciyarsa ta yi nauyi. "Na gane," ya ce cikin raɗa. “Ba don ni kadai bace, don duniya ne." Ruwan ya yi dariya mai sanyi, irin dariyar da take da hikima. "To, ki fara jin magana ta farko. "Ruwa ba ya bacewa sai dai ya canza hanya, ki koya hakan, kuma duniya za ta ji ta." Rafi ya koma gudu kamar da, sai Zainab ta ji iskar safe ta doke ta da sanyi mai daɗi. Ta ɗaga ƙwallar sama, haske mai launin ruwa ya dudduba cikin iska ya narke cikin rana. A wannan rana, a ƙarƙashin rana ta farko bayan dawowarta, Zainab ta zama mai jin ruwan duniya. Mutumin da zai sa halittu su sake magana da mutum. ZAINAB Sha'awa marubuciya diggi ✍️✍️ WhatsApp number 08080304152 PAGE NA 15&16 Da dare ta sauka, kogin da ta taɓa yin shiru yanzu tana rera waƙa kamar tsohon aboki, Zainab ta zauna a bakin ruwan, tana sauraron sautin da ke fitowa daga zurfin da ba ido ke gani ba, sai zuciya. "Ki dawo," wata murya ta fito daga cikin iska, kamar ta haɗu da ƙamshin ganyen tsamiya da ɗanɗanon ruwan gishiri. Zainab ta runtse idanu, bata ji tsoro ba, tsoron ta bar shi tun lokacin da ta gane cewa ruwa ba ya bace sai dai ya canza hanya. "Na dawo," ta amsa cikin sanyi. "Amma ban dawo ni kaɗai ba, na dawo da murya." A lokacin, ƙasa ta yi ɗan karkarwa. Ganyayyaki suka yi kara, kamar suna dariya, wani ɗan ƙaramin ƙwaro ya hau kan yatsunta, ruwan da ke jikinya yana kyalli kamar madubi. "Muryar halittu ta sake buɗewa," murya ya ce. "Zai zama da wahala, Zainab Mutane sun manta yadda ake sauraro." Zainab ta miƙe, ta kalli kogin da ke yawo da hasken wata a saman sa. "Idan sun manta, zan koya musu, saboda duniya ba ta yi shiru ba mutum ne ya daina sauraro." Wata iska mai ɗauke da ƙamshin ruwan sama ta buso, ta nannade ta kamar tsohon alƙawari, a cikin kunnenta, ta ji kalmar da ta tabbata kamar alama: "Duniya za ta ji ta, idan mai ruwa ya yi magana." Zainab ta ɗaga hannunta cikin iska. Ruwan kogin ya motsa, ya zana alamu a saman ruwa kamar haruffa da aka rubuta da haske, kuma daga nesa, wata yarinya ta fito daga inuwa, tana kallonsa da mamaki. "Wace ce ke?" ta tambaya. Zainab ta yi murmushi mai nauyin asiri. "Ni ne wacce ruwa ke kira, amma mutane ba su gane ba tukuna." Yarinyar ta tsaya a bakin kogin, idanuwanta suna kyalli kamar taurari da aka nutse cikin ruwa, sunan ta Amina, amma ta ji kamar ruwan ya riga ya san ta fiye da kanta. "Ni… ban taba ganin irin wannan ba," ta ce, tana matse hannayenta. “Ruwa… yana magana?" Zainab ta yi murmushi, amma ba ta yi magana da sauri ba, tana jin ruwan yana motsawa a gefenta, tana fassara ma ta yadda zai amsa: "Ee, amma ba kowanne zai iya jin ta ba. "Ruwan yana neman wanda zai saurare shi da zuciya, ba kawai da kunne ba." Amina ta matso kusa da ruwan, ta yi ƙoƙarin jin abin da take cewa, sai a nan ta ji kalmomi masu laushi, kamar tsuntsaye da ke tsalle-tsalle a saman ruwa: "Kin zama mai sauraro, ki fahimci, ki ba da… saboda idan ki tsaya, duniya za ta fara sake magana." Zuciyarta ta yi sanyi, kamar wata alƙawari mai ɗorewa ta shige cikin ranta, ta kalli , Zainab tana tambaya cikin shiru: "Zan iya koya? Zan iya sauraron sa kamar ke?" Zainab ta yi ta murmushi mai nauyi: "Idan ka bar zuciyarka ta buɗe, ko da abin da ka ji ya kasance ƙaramar magana, za ka iya fara, amma ka sani, Amina… ba koyon jin ruwa kawai ba ne, zai koya maka yadda za ka saurari duniya baki ɗaya." Ruwan ya yi wani tsalle mai laushi, ya busa ƙamshin tsire-tsire da ƙanƙara mai sanyi a kan fuskar su. Amina ta ji kamar an haɗa ta da dukan kogin, dukan ruwan da ya taɓa gudana a wannan duniya, har ma da asirin tsuntsaye da kowane ganye mai rawaya a wuri mai nisa. A cikin zuciyarta ta fara samun wani wuri na sirri, wani wurin da kawai ruwa zai iya magana, kuma kawai masu sauraro za su iya fahimtar ta. Zainab ta ɗaga hannu, tana nuna hanyar da kogin take tafiya zuwa cikin daji mai cike da haske: "Za mu fara tafiya, duniya tana jiran masu sauraro, kuma lokacin da muka isa wurin farko… za kia gane abin da ruwa yake nufi da ‘sake magana’.” Amina ta miƙe tsaye, ta ɗaga kai, idanuwanta suna kyalli da irin na wanda ya fara fahimtar wani sirri mai zurfi, ruwan kogin ya yi wata rawa, ya yi kamar yana amincewa da zaben ta. Sai suka fara tafiya, ƙasa da rana suna yi wa ruwa busa mai laushi, kuma cikin zuciyarsu, sun ji cewa wannan tafiya ba ƙarshen ta ba ce amma farkon wani abu mai ban mamaki. Sun bi hanyar kogin, daji ya yi duhu amma akwai haske mai laushi daga ganye da ke motsi kamar suna numfashi, ruwan kogin ya yi ta busa cikin iska, yana ƙirƙirar sautukan da suke kama da kalmomi. Zainab ya kalli Amina: "Ke ji?” ta tambaya. "Na ji… amma ban gane ba," Amina ta amsa cikin shiru. Zainab ta yi murmushi: "Ba kowanne mutum ne zai iya fahimtar ki kai tsaye ba, Ki fara jin, amma ki koya yadda za ki fassara." A nan, daga cikin ƙasa, wani tsuntsu mai launi mai ban mamaki ya tashi, amma ba ya ƙara fida baki, ruwan ya yi wani tsalle mai santsi, kamar yana fadin: "Wannan tsuntsu ya daina magana saboda mutane sun daina sauraro." Amina ta yi shiru, ta fahimci cewa kogin ba kawai ruwa ba ne, amma mai magana da dukkan halittu da aka manta da su, Zainab ta nuna wata hanya da ke cikin daji: "Za mu kai su wurin su, wurin da ruwan ke tarawa, anan ne za mu iya sauraron halittu su fara magana da mutane idan kin shirya." Ta hanyar daji, sun ga ƙananan halittu da ba a taɓa ganin su ba, wasu suna kallon su da idanuwa masu ɗaukar haske, wasu suna motsi a hankali, kamar suna jiran wani abu, ruwan kogin ya yi tsalle cikin iska, ya busa fuskar Amina: "Ki sani, kowanne daga cikin su yana da labari, amma sun daina magana saboda mutum bai saurara ba, idan kin saurare su, za ku fara gane yadda duniya ke magana." Amina ta ji wani zafi mai laushi a cikin zuciyarta, kamar zuciyarta ce take bayyana, ta ɗaga hannu, ta matsa kusa da ƙanaan halittun, suna fara motsi da murmushi. Zainab ta yi murmushi: Yanzu kin fara, Amina, wannan shi ne farkon abin da za ki koya, ba wai jin ruwa kawai ba, amma jin dukan abin da duniya ke ƙoƙarin faɗi." Ruwan kogin ya yi tsalle mai ƙarfi, ya bayyana wata hanya ta haske a cikin duhun daji, wannan hanya ce za ta kai su zuwa wurin babban sirrin kogin, in da za su iya farfado da halittu da suka daina magana shekaru aru-aru. Amina ta kalli Zainab, idanuwanta cike da sha’awa da tsoro. "Shin… mun shirya?" ta tambaya. Zainab ta yi murmushi mai nauyi, amma cike da haske: "Mun riga mun fara, amma abin da za mu gani zai canza yadda ka ke kallon duniya… har abada." Ruwan kogin ya yi ƙarshe mai laushi kamar yana kiran su su ci gaba, a cikin zuciyarta, Amina ta ji alƙawari mai ɗorewa, zuciyarta za ta zama murya ga waɗanda suka daina magana. ZAINAB Sha'awa marubuciya diggi ✍️ WhatsApp number 08080304152 PAGE NA 17&18 Ruwan da ke cikin kwandon gilashi a gefen tagar ya yi wani irin motsi kamar iska ta shafi saman sa, sai Zainab ta kalli wajen da ido cike da mamaki, hasken rana da ke shiga ta cikin labulen