Sashe 1
Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ZAINAB
https://whatsapp.com/channel/0029Vb7ASdiJ3jv1qnuWHH3U
PAGE NA 1 DANA 2
SHA'AWANATU FARUK DIGGI MARUBUCIYA
Zamu fara da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai, Allah ya sa yadda na fara wannan littafin Allah ya nuna min gama shi lafiya, Allah ka yafe min kuskure da ke cikin shi.
Banyi wannan littafin dan cin zarafin wata/wani ba ko cin fuska.
Inayin ko masoya na kuma ina godiya da haɗin kain da kuke bani Allah ya sa ka da alkairi 🙏🙏.
1&2
Wata budurwa ce ke tafiya a natse bata kallon komai face in da take sanya kafafunta, tayi nisa acikin tafiyarta kenan ta tsinkayi muryar wata budurwa na kwala kiran Abuh! Abuh! da jin wannan murya ta budurwar dake kwala kiran Sunan Abuh ko ba,a fada mata ba tasan Halima ce tsayuwar ta da minti uku sai ga Halima ta iso in da take a tsaye.
"Haba Abuh yanzun tafiyar ki kika yi bayan kin san ina jiran ki, wallahi ba ki da mutunci kuma ga shi bakida lafiya kuma kice sai kinje school."
har ta ga ma mitar ta kyakkyawar budurwar nan da aka kira da Zainab bata tanka mata ba.. Da ga ni dai yarinyar miskila ce😄 chan bayan kamar minti biyu haka ta cigaba da tafiyar ta kamar ba ta ji abunda Halima ke fada ba duk da kuwa tana jinta rass.
Da Halima ta ga alamar ba tsayawa za ta yi ba ta ga alamar yan miskillancin sun motsa dole haka ta bita suka cigaba da tafiya a tare har suka iso makarantar .
Dukan latti suka tarar a nayi aiko ido ya raina fata dan Zainab akwai tsoron duka.
"Assalamualaikum"
Malam Rabi'u ne ke dukan latti Zainab rage tsawo .
cikin Dan yin ƙasa da kai ta furta acikin zazzakar muryar kamar ana busa sarewa, ko algaitu ga ta da sanyi Wanda in tana magana zakaji har tsikar jikin ka natashi, dan Allah malam ka yi hakuri, da ta furta ne yasanya ni dawo wa da ga sumar tsayen danayi tun lokacin da ta buda baki ta yi sallama.
"Zainab kullum ma kara kike yi kuma kinfi kowa tsoron duka."
"Wallahi malam da wuri muka fito sai dai muna da nisa ne kamin mu iso."
"Toh ba sai ki riƙa hawa machin ba amma kullum sai kin zowa mutum da uzuri, jiya ma haka kika yi nayi miki uzuri toh yau kam sai na ɗiba na ga shi wallahi."
Malam dan Allah ka yi hakuri in sha Allah gobe ba zan sake latti ba.
"Ashe kina magana ƴar iska ina miki magana kina sharewa dani, ai duka yasaki magana."
"Ta romin hanunki ko ki kwanta." Malam ya faɗa
Hannunta ba shi bulala goma ya yi mata amma ko a jikinta amma fa taji zafin dukan sosai dan hannunta har kumbura ya yi.
Goma ya yiwa Halima tana ihu tana ƙari har aka gama mata.
Shigowar wata baƙar mota wulik cikin makarantar shine yaja hankalin mafi yawan ɗaliban.
Motar tatsaya daidai wata bishiyar dalbejiya,
A yanzu kallo ya koma ne akan Wanda zai fito daga cikin wannan mota mai kyau da ɗaukar hankali.
Ƙafarsa yafara zirowa ƙasa maisanye da sauciki na farin takalmi, yakuma zuro ɗayar itama, saikuma yafito gaba ɗayansa.
Ajiyar zuciya Halima ta sauke tareda faɗin ya salam!.
Ita Zainab batasan wainar da ake toya ba saboda zafin dukan har yanzun bai bar jikinta ba.
Kallon Halima ta yi dake kallon wani wajen kamar ta samu T V .
"Ke Halima lafiya kike kallon waje ɗaya ko kin samu matsala ne da dukan da malam ya yi miki ne?."
Hannu Halima ta yiwa Zainab nuna da abin da take kallo.
Kallon can Zainab ta yi wani mutum ta gani a tsaye wajen mota amma bataga komai ba.
Jijjigar Halima ta yi sannan Halima ta nuna mata wanda ke tsaye a wajen mota.
Farine sosai dogo kuma dankuwa yanada tsayi sosai, kallo ɗaya zaka masa kagane ƙaƙƙarfane saidai bashida ƙiba, ma sha Allahu akwai ƙyawun fuska, gashi kuma ya ƙawata fuskar tasa da saje baƙi siɗik, ya kwanta sai walƙiya yakeyi, sanyake da farar shadda wando da Riga ɗinkin zamani, kayan sun masa ƙyau....
"Mene ne abin kallo a nan aikin banza kawai kin ji haushi dai wallahi."
"Ai ke zancewa kinji takaici saboda ni macece dole zan yi magana idan naga abin maganar, bale wannan gaye ɗin Allah ya sa shine Sabon malamin mu."
"Ba ameen ba."
Aji kowa ya shiga sakamakon ringing da aka yi na shiga Aji.
S s one ƴan mata ne sai tsokanar juna suke yi amma mutum ɗaya ce ba ruwan ta da kowa sai karatun ta take yi.
"Malam ne ya shigo suka ce good morning Sir?."
"How are you students sit down."
"I am your new English teacher, God willing, Everyone should take out their book so that we can continue, God willing."
Kowa sai kallon shi yake komai yake nufi oho ma sa.
"Why are you (all) just looking at me mtsww?."
"Sir, please forgive me, I just want to talk (or meet) with you, please.”
Sai sannan hankalin shi ya kai kanta.
"Where did you stop?."
Faɗa ma sa tayi sannan ya ci gaba da aikin shi, har ya gama sai ya tambayi wanda bai gane ba, kowa ya ce bai gane ba harara ya banga masu sannan ya yi tafiyar shi.
"Chapp yanzun idan bake ba wallahi ba mai iya ba shi amsa."
"Kefa kika ce Allah ya sa yazama malamin ku kuma ga shi nan amma kika yi shiru."
"Ai wallahi ni kam kallon shi kawai nake yi, saboda malamin akwai kyau ga sajen nan baƙi, ga hancin nan na shi, wayyo Allah, Allah ya sa ni ce matar shi ko ke."
"Ba ameen dan Allah ki barni haka kirki sakamin ciwon kai."
Wani malami ne ya shigo daga ganin shi ba malamin kirki bane sai kallon ƴan mata yake yi Musamman Zainab.
Ta shi suka yi dan gaida shi amma ya ce su zauna kawai.
In da Zainab yazo yana faɗin wannan anyi halitta anan ba Zainab ba har sauran matan sun tsorata da malamin.
Halima suman zaune ta yi saboda tsoro sai kallon su yake yana lasan baki sai kace maye.
"Malam dan Allah ka yi mana abin da yakawo ka, saboda banga abin kallon mu kana lasan baki ba."
Idon da Halima zata ɗaga sai ganin Sir baƙo ta yi yana kallon malamin.
"Ke kinfi kowa baki ne harni za ki kalla kina gaya min abin da zanyi."
"Zoki yi kama kunnen ki a gaban allu."
"Malam ai gaskiya na faɗa kuma wallahi a makarantar nan ba a saka mata kamun kunne."
"What is happening here?"
Kowa taga ya kalla har shi malamin saboda ba wanda ya ganshi sai halima sai waɗan yake kan tagar su.
Shiru ya yi sai daga baya yake cewa
"Karatu ne nake masu shine yarinyar nan ke raina min da hankali."
"I don’t understand Hausa., speak to me in English."
Shiru malamin ya yi ba amsa.
Ajin ya shigo ya kalli Zainab yana faɗin
"What is your name?."
"My name is Zainab Hassan."
Faɗa ma sa komai ta yi har kallon ta yake mata da lashe lashen da yake.
ZAINAB PAGE 📄 📃
Na
Sha'awa marubuciya diggi
WhatsApp number 08080304152
3&4
Ringing ɗin cin abinci aka yi dan haka ga baki ɗaya suka fita dan zuwa cin abinci.
Zainab.. Zainab dan Allah ki tsaya kiji Please my friend.
Tsayawa ta yi amma bata yi magana ba kuma bata juyo ba sai ci gaba da tafiyar ta da ta yi.
"Zainab wai me ya sa ba kyada tsoro ne ni wallahi ina tsoron abin da malamin zai miki."
"Uhmm komai zai yi bai daman ba kuma Allah yana tare dani."
"Wallahi nima Naja'atu shinake tunani dan da gani malamin ɗan iska ne wallahi."
Wajen wata dalbejiya suka zauna sai buga zance suke.
Shiko yana cikin motar shi yana kallon ɗaliban sai wucewa suke yi.
"Zainab ki riƙa saka tsoro a ranki saboda kina da rauni fa, ke macece ba namiji ina jin tsoron ranar da wani zai cutar da ke."
"hmmm karki damu da rayuwata saboda bata da amfani, ki damu da rayuwarki kawai, kuma duk abin da Allah bai nufeni da shi ba toh ba wanda ya isa ya sakar min shi."
"Haka ne Allah ya sa mu dace ."
"Ameen."
Duk abin da suke faɗa duk a kunnen shi sosai Zainab ta birge shi saboda jajircewar ta.
Ta shi suka yi zuwa Class bin bayan su da kallo ya yi sai da suka ɓacewa ganin shi, sannan ya fito zuwa office.
Zainab sai karatu take yi saboda haka duk ta watsar da su Halima da Naja'atu.
Wani yazo yana yamutsan fuska shi ala dole mai kuɗi .
Gai da shi suka yi sannan kowa ya zauna ya cigaba da abin da zai yi, sai kallon matan ajin yake yi.
Haka kawai ya cika allo kuma bai yi bayani ba kawai ya yi tafiyar shi.
"Dariya ƴan ajin suka fara yi, su na faɗin waye zai mana bayani.
Wani ɗan ajinne ya tashi yana faɗin,
"Ke Zainab tashi ki yi mana bayani."
"Hahaha rufamin asiri dan Allah ai wannan sai kai ke iya bayanin shi."
"Haba Abuh karki ba dani mana, idan ba za ta yi ba ke Halima yi mana bayani ."
Toh shi ke nan fita ta yi tana dariya tana faɗin.
"Kowa ya fitar da littafin shi test zamu yi dan naga kuna raina min hankali."
Wani daga cikin mazan ne ke faɗin.
"Hahaha wallahi kin iya maganar shi sosai."
"When everyone has published their book, we'll take the test —it's not that you wanted it, right."
Aiko kowa kallon window yake yi saboda basu san da mutum a nan ba.
"Sorry Sir wallahi bamu shiryawa test Yanzun ba," wani ɗaya daga cikin su ya faɗa.
"Okay, please tell me, Sir, when are we going to do it?"
"Yi hakuri malam."
Ƴan ajin ga baki ɗaya
Kowa littafin shi ya fitar a gaban aji suka raga daga su sai takardar su
"Zainab, Halima, Naja'atu, da sauran ƴan ajin duk sun tsorata da test ɗinnan da ba shiri
Haka kuwa kowa ya yi test ɗinnan amma hannu a gaba dan basu san ko ya yi daidai ba.