← Book details Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 13

Sashe 3

Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ne dai gaskiya ina son shi wai anya Zainab ke cikakkiyar mace ce, duk mace na son rayuwa da namiji, shima namiji yana son rayuwa da mace, sannan ke kizo kina mana hauka akai." Naja'atu ta faɗa suna taɓawa da Halima.
ZAINAB
Marubuciya Sha'awa Faruk diggi ✍️
WhatsApp number 080808304152
PAGE NA
5&6
Yamutsa fuska ta yi kamar zata yi kuka ta ce
"Eh ni ba mace bace dutse ne, ke ni na faɗa miki ban tashi aure ba yanzun, sai na gama school ko zan maida hankali na kan samari."
"Kan ki ake ji kar ma ki yi aure ki zauna haka nan."
Rabuwa suka yi saboda gidajen su, suna kallon juna ne, hakan yasa suka rabu.
Tana shiga gida ta tarar da wata matashiyar mata zaune wajen murhun wuta sai gumi take yi.
"Assalamualaikum"
"Waalaikimussalam"
"Mama ina wuni ya gida?."
"Lafiya ƙalau Abu Mama, ya karatun?."
"Lafiya ƙalau Alhamdulillahi."
"Toh yau kam baki makara ba ko?."
"Tabb wallahi Mama nasha bulala sosai ji hannuna fa", ta faɗa tana nunawa Mamarta ta hannun ta.
"Ayya Abuna yi hakuri je ki cire kayan jikinki ki huta."
"Mama ai Abba ba zai barni ba."
"Je ki kawai ki cire kayan jikinki ki kwanta, idan kika ji sauƙi sai ki fito kamin yadawo."
"Toh shi ke nan Mamata, na gode Allah da ya bani ke a matsayin Uwa, Allah ya kare min ke ya ƙara tsaremin ke Mamata."
Dariya Mama ke yi saboda ƴarta na bata dariya sosai.
"Toh ameen Abuna kema Allah ya tsare min ke da kullimin musulmin Allah gaba ɗaya."
"Ameen Mamata."
"Allah ya nuna min ranar bikin ki yarinyata."
Dariya Zainab ta yi sannan ta shige ɗaki.
Kayan jikin ta ta cire tasa kayan zaman gida falle da t shirt ruwa ta ɗiba a bokiti ta shiga bayan gidan.
Wanka ta yi sannan ta yi alwala, ɗakin ta shiga ta gabar da Sallar, kwanciya ta yi sai bacci.
"Wai har yanzun wannan ƴar iskar yarinyar bata dawo gidan nan ba, kuma na faɗa miki ta daina zuwa wannan karatun dan ba amfanin da zai yi mata."
"Haba Abban Abu yanzun da kan ka zaka shigo cikin gida ba tare da ka yi sallama ba, idan yaranka suka gani kuma fa suka ɗauka mai zaka ce musu?."
"Wallahi Zara'u ki fita idona ya rufe ko yanzun naci mutuncin ki anan, ta fito idan ta dawo ko naje har makarantar na dauko ta."
"Dan Allah ka bar yarinyar ta huta haba dan Allah, yarinyar ka ce dai ko baka so wallahi."
Zainab surutun ta ji ya yi yawa hakan ya sa ta fito dan jin meke faruwa ganin Abban ta ne ya sa ta ganewa abin da ke faruwa hakan ya sa ta ce
"Abba ina wuni ya kasuwa?."
"Idan ban wuni ba za ki ganni anan ne, dan uwarki wace ki ɗebo ruwa kizo ki a jiye min kayan gwari na a titi."
"Toh Abba Amma islamiyya fa da ƙarfe huɗu ake zuwa."
"Kinci ƙaniyarki wuce ki je ɗebo ruwan, kuma wallahi idan kika gama baki je in da nace ba sai kin bar gidan nan."
"Yi hakuri Abba zanje yanzun."
Harara kawai ya watsa mata ya yi tafiyar shi waje.
"Kenan yau ba zuwa islamiyya ko?."
"Toh Mama kin ji abin da Abba ya ce dole zanyi hakuri da zuwa islamiyyar."
"Shi ke nan Allah ya yi miki albarka Abuna."
"Ameen ya rabbin alamina."
Tashi ta ɗauki bokiti dan zuwa ɗiban ruwan .
Tana tafiya tana hawaye ga yunwar da take ji kuma ga rashin zuwa islamiyya, sannan ga shi tanajin zazzaɓi sakamakon dukan ɗazun.
Acikin tafiyar ta ji ana kiran
"Abur Mama dan Allah tsaya ki ji."
Tsawa ta yi dan ganin mai kiranta wani mutum ne baƙi ne sosai ga ƙaton ciki, shima kanshi ƙato ne.
"Haba Abu mama tun ɗazun na ke kiranki fa amma kin share ni."
"Ayya yi hakuri ban ji bane meke tafe da kai sauri nake zanje ɗebo ruwane."
"Ah toh muje na rakaki ko?."
"A a a na gode sosai ba na buƙatar hakan."
"Saboda mi kika ce haka babyna nifa wallahi son ki na ke da gaske idan kin yarda dan Allah karki ce min a a."
"Nima ina sonka amma irin soyayyar ɗan uwa musulmi."
"Ta masoya fa?" Ya tambaya.
"Gaskiya ka yi hakuri amma ni ban tashi yin aure yanzun ba."
"Toh shi ke nan zan jira ki har lokacin da kika tashi."
"No bazan yi aure ba nake nufi."
"Saboda mi a haka za ki zauna ba aure."
"Eh", ta faɗa cikin gajiya da surutun nasa.
"Amma... Bata bari yaƙara sa maganar ba da dakatar da shi.
"Ka yi hakuri ruwa zan ɗebo sai anjima.
Tafiya ta yi sai rafi wani ƙayatacce wuri ne, ruwan farare tas sai wasu tsirrai ƙanana, ƙanana gwanin kyau, sai ma ka ganshi.
Tsayawa ta yi na wasu lokuta sannan ta ɗebo ruwan ta bar rafin .
A hanyar ta zuwa gida ta ga wasu ƴan mata su biyu .
Tsayar da Zainab suka yi su na faɗan .
"Dan Allah ke yar wani unguwa ne?."
"Ga gidan mu nan."
"Ayya kice muna ku sa kenan."
"Dayar ta ce "Ga gidan mu muma
"Toh."
"Za ki biyo mu mu je gidan mu cewar", ƙaramar cikin ƴan matan nan biyu.
"A a yanzun ruwa nake jida sai na gama in sha Allah zan zo."
"Toh ba damuwa."
"Amma baki faɗa min sunan ki ba."
"Ayya na manta ban faɗa miki, sunana Khadijah wannan yayata ce, sunan ta Hafsat, saura ke ki faɗa mana sunan ki."
"Sunana Zainab." Ta faɗa .
"Toh jeki kar na tsaida ki amma anjima zan zo muyi fira."
"Toh shi ke nan sai kin zo."
Zainab sai da taga ma jidan ruwan sannan taje fitar da kayan gwarin Abba.
Tana nan har a ka kira sallar magarib, gida taje ta yi sallah sannan ta dawo, ba ita ta tafi gida ba sai isha'i kamin ta koma gida.
Khadijah taje gidan su Zainab sai ƙarfe goma sannan Zainab ta rakata har gida, da yake gida biyu ne tsakanin su.
Washe gari
Zainab ce ta yi shirin zuwa makaranta tsayawa shan koko ta yi hakan ya sa su Halima suka ri gata fita,
"Haba Abu mama yanzun baki shirya ba kike nufi."
"So take sai Malam Rabi'u ya sake zane mu."
"Gaskiya baki kyauta mana Wallahi kullum sai mun jiraki."
"Kai dan Allah ku yi mini shiru ai nima wata rana zan jiraku."
"Assalamualaikum."
"Waalaikimussalam"
"Ina kwana Mama antashi lapiya?."
"Lafiya ƙalau wallahi."
"Ke yanzun makarantar mu ɗaya kenan."
"Eh wallahi Best."
"Toh shi ke nan ga ƙawaye na."
"Allah sarki ƙawayen mu dai ko? Ya sunan su."
"Wacce sunanta Halima wannan kuma Naja'atu."
"Allah sarki toh sannun ku."
"Kema sannun ki yakike ya gida?."
"Lafiya ƙalau Halima."
"Toh mu je amma Best ai ba Class ɗinmu ɗaya ba ko?."
"Wallahi ban sani amma ni s s one zan shiga."
"Laaaa wallahi ajinmu ɗaya dake."
"Da gaske kike Halima."
"Eh mana."
Haka suka ƙarasa makarantar suka tarar da dukan latti.
Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, Zainab ta faɗa tana hawaye.
"Kai kuzo nan au har na kunsamu cikon ta uku ko?, ku zo nan wai me ya sa kullum sai kun makara ne, ke dai naga kamar ke sabuwa ce a makarantar wuce abin kawai ."
"A a malam ba in da zanje na bar Best na sai dai ka dake mu gabaki ɗaya."
Suna cikin maganar sai wata mota farace sosai mai shegen kyau.
Parking ya yi daidai wajen dalbejiya, ƙafar shi ya fara fitarwa sannan ya fito gaba ɗayan shi, wow Ma sha Allah, sanye yake da riga da wando ɗinkin zamani saddace fara sosai kamar motar shi.
Kallon makarantar ya fara yi ko mai yake kallo oho, can ya hango ana dukan mutanen wajen ya dusa, zama ya yi akan kujerar malam Rabi'u, yana kallon ƴan mata da ake duka.
"Ke saura ke kawo min hannun ki."
"Malam dan Allah ka yi hakuri wallahi bana da lafiya ne, yanzun haka hannuna ciwo yake sakamakon dukan jiya, dan Allah ka yi hakuri."
Da ido Aliyu ya bita sai kallon ta yake.
"Idan nayiwa wata layin ki ya sake daga ƙasa, kuma wallahi sai na miki bulala sha biyar."
Wasu ƴan mata ne su biyu suka shigo su na wani yanga kamar hawainiya wuce wa suka so sai jin magana suka yi.
"Kai kuzo nan kunfi ƙarfin kai da mutane, kum
"Kai kuzo nan kunfi ƙarfin kai da mutane, kuma kuzo ku tarar da dukan latti amma sai ku tafi." Yana maganar yana duban wani wajen kamar ba
ZAINAB

Sha'awa marubuciya diggi ✍️
WhatsApp number 0808304152.

PAGE NA

7&8

Hankali malam ya kalli ɗaliban, yana ɗan murmushi, amma idonsa na nuna wata irin damuwa da kuma fatan alheri a gare su.

Ku sani, ya ci gaba da cewa,

"ilimi ba kawai karatu da rubutu ba ne, ilimi haske ne, amma tarbiyya ita ce fitilar da ke kare wancan hasken daga shuɗewa, idan kana da ilimi ba tare da tarbiyya ba, kamar kana da wuta ne a cikin iska; duk da hasken ta, sai ta ɓace."

Wani ɗalibi daga baya ya ɗan ɗaga hannu, cikin nutsuwa

"Sir in ji shi, amma me yasa wasu masu ilimi suke yin abubuwan da ba su dace ba?."

Sir ya ɗan yi shiru na ɗan lokaci,
yana kallon ɗalibin da murmushi mai cike da tausayi.

Domin sun manta da rabin hanya, ya ce.

"Sun dauka ilimi kaɗai zai ishe su, suka bar tarbiyya a baya, amma babu nasara sai an haɗa biyun, kamar yadda na ce: ILIMI + TARBIYYA = NASARA.

Ya juya zuwa allo ya rubuta wannan " jimla da manyan haruffa, sannan ya ce:

"Wannan ba kawai magana ba ce

"Wannan hanya ce ta rayuwa, duk wanda yake son a girmama shi, ya fara da girmama kansa, iyayensa, malamansa, da gaskiya, domin girmamawa tana komawa ga wanda yake bayar da ita."

Sai aka sake samun shiru a cikin aji, Amma wannan karon, ba shiru na nadama kawai ba ne, shiru ne na canji
a zuciyun wasu, an fara sake tunani,
a zuciyar wasu kuma, an fara sabon alƙawari.
Chapter 3 · 0% Book details