Sashe 5
Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari a makaranta, Malam Sir ya kirata zuwa ofishinsa. Da fara’a a fuskarsa, ya dubeta yace:
"Zainab, na san cewa wannan nasarar taki ba ta zo ne kawai saboda kin yi karatu sosai ba, amma saboda yadda kika sarrafa lokacinki da tunaninki, wannan ita ce hanyar da ake gina shugabanni.”
Zainab ta sunkuyar da kai cikin kunya amma zuciyarta cike take da godiya,
"Na gode Malam," ta ce cikin nutsuwa.
"Abin da kuka koya mana game da natsuwa da gaskiya shi ne ya taimake ni.
Malam Sir ya murmusa, ya daga hannu kamar yana son ya nuna mata wani abu mai muhimmanci.
"Ki tuna wannan, Zainab: nasara tana fara ne daga cikin zuciya, Idan zuciyarki ta yarda da abin da kike yi, duniya za ta yarda da ke."
A lokacin ne Zainab ta yanke shawara wannan nasarar ba ta ƙarshe ba ce, ita ce farkon sabon babi a rayuwarta, za ta ci gaba da ƙoƙari, ba don kyauta ko yabo ba, amma don ta zama mafi kyawun sigar kanta.
Bayan nasarar gasar ta wuce, makaranta ta ci gaba da tafiya kamar yadda aka saba, amma rayuwar Zainab ta fara ɗaukar sabon salo, Mutane da yawa suna kallonta da wani sabon kallo wasu suna yaba mata, wasu kuma suna ganin tana jin kai.
A cikin ajin su, akwai wata sabuwar daliba da aka canja daga wata makaranta, sunanta Maryam, Maryam tana da hazaka, mai magana, kuma tana da halin da ke sa mutane son zama tare da ita. La, kowa yana son ta, har ma da malamai, A hankali, mutane suka fara daina ambaton Zainab sosai sun fara kallon Maryam a matsayin "sabuwar tauraruwa."
A farkon makonni, Zainab ta yi kamar ba ta damu ba, amma daga baya ta fara jin wani sanyi a zuciyarta. "Ko dai suna mantawa da ni ne?” ta kan tambayi kanta a lokacin da take zaune ita kaɗai bayan ajin.
Rana guda, Malam Sir ya shigo ajin yana sanar da wani sabon shiri:
"Za mu shirya wata gasa ta hadin kai kungiyoyi biyu za su hada kai su tsara wani aikin kimiyya, Kowane rukuni zai zabi shugaba."
Da zarar aka raba rukuni-rukuni, Zainab da Maryam suka fada cikin rukuni guda, dukan su biyu an fi ganin su da cancantar jagoranci, kowa yana jira ganin wace za a zaba shugaba.
Sai ɗaliban suka fara tattaunawa wasu suna cewa Zainab ta cancanta saboda ta riga ta nuna bajinta, wasu kuma suna cewa Maryam ta fi iya magana da jawo mutane.
Zainab ta zauna shiru, tana jin maganganun a zuciyarta kamar iska mai sanyi, Amma a wannan lokacin, ta tuna da abin da Malam Sir ya faɗa mata:
"Nasara tana fara ne daga cikin zuciya."
Ta numfasa a hankali, sannan ta miƙe ta ce da tawagarsu:
"Ba lallai ne ni in zama shugaba ba, Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu haɗa kai mu yi abin da zai burge duniya."
Maryam ta kalleta, ta ɗan yi mamaki, a karon farko, ta ga irin natsuwar da ke cikin Zainab ba ta fito daga girman kai ba, sai gaskiya.
Daga wannan rana, suka fara aiki tare kuma duk da bambancin halayensu, suka fara fahimtar juna, a hankali, soyayya ta abota ta fara girma tsakanin su.
Wai ina Halima da Naja'atu ne kubibiye ni dan jin sona ina ne.
"Hali me kin san meke damuna a yanzun?."
"A a sai kin faɗa."
"Abba yasaka ni a gaba wai aure zai min da wani yaron abokin shi, amma ni kam yaron bai min gaskiya, kuma bana son shi."
"Ki yi hakuri, ki yiwa iyayen ki biyayya karki saɓa ma sa, ki barshi ya yi duk yanda zai yi da ke kin ji Abu mama."
"Wallahi hali ba ki fahimci ni ba ne ina son yin karatu sosai amma ina ga kamar ba zai yiwu ba."
"Karki sare Abu Mama in sha Allah za ki yi karatu sosai."
"Ke Naja, ba za ki ce komai ba ne, kin bar mu sai zuba muke kina kallon bakin mu." Zainab ta faɗa tana kai mata duka.
"Yi hakuri Abu Mama wallahi abin ne ke bani mamaki sai ka ce ba shi ya haife ki ba."
Abu Mama ta kalli Naja, da idanu cike da mamaki.
"Zainab! Me ya sa za ki faɗi haka? Kin san kalmar da kika faɗa kuwa?"
Naja ta ja bakinta, ta yi kamar za ta ce wani abu amma ta kasa, Sai ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta.
Halima kuwa ta tsaya tana kallon su biyu, zuciyarta na bugawa da ƙarfi, "Sai ka ce ba shi ya haife ki ba...
” kalmar Zainab tana maimaituwa a cikin kunnuwanta kamar amo.
Halima ta share hancinta da ɗan ragi, ta ja numfashi,
“Ku daina wannan maganar, Kowa ya ta shi muje Class ni ban so fitina a wannan makarantar."
Tafiya ta fara yi, da ƙafafunta da suka yi nauyi, Naja ta bi bayanta da ido, sai ta ɗago kai ta dubi Zainab, wadda har yanzu ke tsaye tana murza hannayenta.
"Naja, me kike nufi da maganar da kika faɗa?" ta tambaya a hankali, muryarta na rawa.
Naja ta ɗaga kai, ta dubeta kai tsaye,
"Ni ma ban sani ba Zainab, na ji ne kawai ana cewa... ai ke ba ‘yar Abba bace, amma ban san gaskiyar maganar ba, wallahi."
Zuciyar Zainab ta yi wani irin tsalle, Tuni ta ji wani abu ya tsaya a maƙogwaro,
"Waye ya faɗa miki haka?" ta tambaya, murya na rawa sosai.
Naja ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce,
“Na ji Baba Lawan yana faɗawa uwata da dare. Amma suka ce kar in faɗa miki."
Zainab ta ji kamar ƙasa ta buɗe ta shige, Idanuwanta suka cika da hawaye, amma ta daure, ta miƙe, ta ɗauki jakarta ta tafi Class cikin sauri.
Naja ta bita da ido, ta furta a hankali, "Allah ya kyauta..."
A waje, iska tana kadawa, rana ta dushe, Zainab ta tsaya a bakin ƙofar gida, ta kalli sama. "Allah ka nuna min gaskiya, ko ni ce ba ‘yar gidan nan ba, ka bani ikon sanin wacece ni."
Ta share hawaye, ta nufi in da ta san zata samu amsar tambayoyinta gidan tsohuwa Hajiya Lantana, uwa ga mahaifin da ake kira Abba. Ita ce kawai mai riƙe da sirrin da babu wanda ke iya faɗa.
Tafiyarta daga wannan rana ta buɗe mata ƙofa zuwa wani ɓangare na rayuwa da bata taɓa tsammani ba ɓangaren da zai nuna mata wacece ita a gaske, da kuma dalilin da yasa ake son a rufe gaskiyar.
Yamma ta yi, rana ta fāɗi, Iskar ƙasar Arewa tana kadawa a hankali, tana ɗauke da ƙanshin ƙasa bayan ruwa, Zainab ta yi tafiya cikin nutsuwa tana nufar gidan tsohuwa Hajiya Lantana.
Gidan tsohuwar yana bakin unguwa, tsohon gida ne da katanga mai tsawo da ƙofar ƙarfe wadda ake buɗewa da ƙara, Ta turo ƙofar a hankali, tana cewa:
"Assalamu alaikum..."
Muryar tsohuwa ta ji daga ciki, mai rauni amma cike da nutsuwa,
"Wa alaikumus salam, ke ce Zainab? Zo ciki "yata."
Ta shiga, ta tarar da tsohuwa tana zaune a tabarma, tana ɗinke wani zani, fuskar Hajiya Lantana ta cika da annuri amma akwai wani abu a idanunta, kamar sirrin da ke neman ɓoye gaskiya.
Zainab ta durƙusa, ta gaisheta da ladabi. Bayan gaisuwa, ta ce da ƙasa-ƙasa:
"Hajiya, akwai magana da nake son tambayarki, amma don Allah ki faɗa min gaskiya, na yi alƙawari ba zan faɗa wa kowa ba."
Tsohuwa ta tsaya cak, allura ta faɗi daga hannunta,
"Magana kuma? Wacce iri ce, Zainab?
Naja ta ja numfashi mai nauyi,
"Hajiya... gaskiya ne ni ba ƴar Abba bace?"
Hajiya Lantana ta ɗago kai a hankali, ta kalleta da ido mai zurfi, a cikin idonta akwai rudani, tsoro, da alhini,
"Waye ya faɗa miki haka?"
"Naja ce ta faɗa, Ta ce ta ji ana magana da dare..."
Hajiya ta sauke numfashi, ta jingina da bango, tsawon lokaci babu wanda ya ce komai, sai ƙarar ƙudan zuma daga waje, Daga baya ta furta da muryar da ta yi rauni sosai:
"Zainab... gaskiya tana da nauyi, kuma ba kowa ne yake iya ɗauka ba."
Zainab ta matsa kusa da ita.
"Don Allah ki faɗa min, Hajiya Zan iya jure komai."
Tsohuwa ta rufe fuskarta da tafin hannunta, hawaye suka fara fita a hankali.
"Kin tabbata kina son ji?"
"Eh, Hajiya zan jure."
Hajiya ta ɗago kai, ta ce da murya mai sanyi:
"Abbanki... ba shi ne mahaifinki ba, amma ba laifinsa bane, Ki sani, ya yi miki alheri da kauna fiye da yadda mahaifinki na gaskiya zai iya yi."
Zainab ta ji jikinta ya yi sanyi.
"To... waye mahaifina, Hajiya?"
Hajiya ta girgiza kai, tana share hawaye.
"Wannan labari ne mai tsawo, Zainab amma zan faɗa miki a hankali... Mahaifinki yana da alaƙa da sirrin da iyayenki suka daɗe suna ɓoyewa,Kuma akwai wanda zai iya yin komai don wannan gaskiyar ta ƙara ɓoye."
Zainab ta durƙusa gaba ɗaya, zuciyarta na tsalle.
"Don Allah Hajiya, kar ki ɓoye min, Ina so in san wacece ni a gaske."
Tsohuwa ta kalleta, sannan ta furta suna da ya ɗauki hankalin Zainab gaba ɗaya...
"Sunan mahaifinki... Malam Faruk Abdulrahman."
Zainab ta ɗaga kai da mamaki.
"Faruk? Wane Faruk?"
Tsohuwa ta ɗauki hoton da ke gefenta hoton saurayi cikin farin kaya, yana murmushi ta mika mata.
"Wannan ne... shi ne wanda duniya ta ɗauka ya mutu shekaru goma da suka wuce."
Ta ɗauki hoton da hannunta ke rawa. "Mutuwa?"
Tsohuwa ta gyada kai.
"Amma gaskiyar ba haka ba ne, Ya ɓace ne saboda wani abu da Abbanki da wasu mutane suka ɓoye."
Shikenan. A nan labarin ya fara shiga cikin asirin gaskiya wanda zai bayyana dangantaka mai rikitarwa tsakanin Abba, Faruk, da Zainab.
I'm
"Ni ba na jin tsoro," Zainab ta faɗi da murya mai ƙarfi, ko da kuwa zuciyarta na dukan kamar ƙarar gangar yaƙi,
"Na daɗe ina gudu daga tambayoyi, amma yanzu... yanzu zan fuskance su."
Tsohuwa ta miƙa mata wata ƙaramar akwatin katako.
"Ki buɗe wannan kawai idan kin kai garin Ruwa Uku, a can ne za ki fara samun amsoshin da kike nema."
"Garin Ruwa Uku?"
Zainab ta maimaita, tana jin sunan yana ɗauke da wani nauyi,
"Ba wanda ke zuwa can.”
"Eh,"