Sashe 4
Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga wannan rana, kalmar “ILIMI + TARBIYYA = NASARA" ta zama tamkar tambari a cikin zuciyoyin su, kalmar da za ta jagorance su har zuwa gobe.
Tun daga ranar da Sir ya faɗi kalmar ILIMI + TARBIYYA = NASARA, a cikin zuciyar Sagir, wani sabon abu ya taso.
Ba ya gane shi sosai, amma yana jin kamar an kunna wata ƙaramar fitila a cikin zuciyarsa, fitila mai sanyi, amma cike da ƙarfi.
Sagir ɗalibi ne mai wayo, amma ya saba yin wasa da malamai, yana da saurin ba’a, yana yin dariya da ƙasƙantar da waɗanda ba su iya kamar shi,
Sai dai tun ranar, kowanne lokaci da zai yi irin waɗannan abubuwan, sai maganar malam ta dawo masa a kunne:
Duk wanda yake son a girmama shi gobe, ya koyi girmama kansa da malaminsa yau..."
Ranar Juma’a bayan sallah, ya tsaya a bakin ɗakin karatu, Malam Haruna yana share tebur, yana shirin rufewa Sagir ya tsaya gefe, yana kallon shi cikin shiru.
A da, da ya gan shi haka, sai ya yi wasa da shi, ko ya yi dariya da muryarsa,
amma wannan karon, sai kawai ya ce da nutsuwa:
"Malam ina iya taimaka maka?."
Malam Haruna ya ɗaga kai cikin mamaki.
"Ka taimake ni?, in ji shi da murmushi. toh Sagir ka ban mamaki ne yau."
Sagir ya yi dariya kaɗan, yana shafa kai
"A’a malam kawai… ina so in koyi yadda ake girmama, da farko zan fara da kai."
Malam Haruna ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ɗan dafa kafaɗarsa
"Ka fara hanya, Sagir idan ka ci gaba da haka, ka riga ka zama abin koyi."
Daga wannan rana, Sagir ya canza
Ya fara zuwa makaranta da wuri, yana gaishe da malamai da ladabi, yana taimaka wa ƙanana.
A hankali, sauran ɗalibai suka fara lura da shi.
Wasu suna mamaki, wasu suna dariya, amma daga baya, wasu suka fara koyi da shi.
Malam Haruna kuwa, a kowane lokaci da yake kallon Sagir, sai yake murmushi, murmushin wanda yake ganin amsar addu’arsa a zahiri.
Zainab ta ƙara natsuwa sosai, dama can ma tana da hankali da miskilanci, yanzu kam wannan halin nata ya ƙara fitowa fili, idan tana cikin mutane, bata yin yawan magana sai dai idan ta ga ya zama dole, amma duk lokacin da ta buɗe baki, mutane sai su tsaya suna sauraro, saboda kalamanta na cike da hikima da hankali.
A makaranta, malamai sun fara ɗaukar ta a matsayin abin koyi ga sauran ɗalibai, ko da wani abu ya faru da zai sa wasu su rikice, Zainab takan tsaya da kwanciyar hankali ta yi magana da natsuwa har kowa ya nutsu.
Abokanta kuwa suna son zama da ita saboda tana ba su kwarin gwiwa, amma kuma suna jin wani irin girman hali a tare da ita ba girman kai ba, amma irin wanda ke nuna cewa tana da tarbiyya da wayewa.
Wata rana a lokacin da ake shirin gasar ilimi ta makaranta, malamai suka zaɓi Zainab ta wakilci aji, duk da cewa ta yi mamaki, ta karɓa cikin tawali’u, tana jin tsoro a ranta, amma ta ce a zuciyarta:
"Idan na yi natsuwa, zan iya Allah zai taimake ni."
A ranar gasar, duk makarantu sun hallara, Zainab ta tsaya a gaban mutane da kwanciyar hankali, tana amsa tambayoyi cikin hikima da karimci, mutane suka yi mamakin yadda yarinya mai natsuwa haka take da basira sosai.
Bayan gasar, sir ne malamanta ya ce:
"Zainab natsuwarki ita ce makamin nasararki."
Ta saki murmushi, tana mai jin daɗin kalaman malaminta, ta ji kamar kalmarsa ta buɗe wani sabon shafi a rayuwarta, tun daga wannan rana, ta ɗauki kalmar a zuciyarta kamar alamar tunawa duk lokacin da ta fuskanci wata ƙalubale, sai ta tuna da ita: "Natsuwarki ita ce makamin nasararki."
A kwanaki masu zuwa, makarantar su ta cika da labarin yadda Zainab ta yi fice a gasar, wasu dalibai suka fara neman shawarar ta, wasu kuma suka fara kallonta da sabon girmamawa amma ba ta bari wannan ya girgiza ta ba, har yanzu tana tafiya a hankali, tana yin komai da tunani da nutsuwa.
Wata rana, ana shirin gasar jihohi, malaminta ya kira ta ofis dinsa,
"Zainab," in ji shi, yana dubanta da murmushi mai cike da alfahari, "muna son ki wakilci makarantar mu a gasar jihohi, na san ba zai zama sauƙi ba, amma na yarda da ke."
Zainab ta ɗaga kai cikin ladabi.
"In sha Allah, malam zan yi ƙoƙari ba don in burge kowa ba, sai don in nuna cewa ilimi da natsuwa suna da ƙima."
Malam ya gyada kai.
"Haka nake so in ji, kada ki manta, nasara ba kawai samun lambar yabo ba ce, nasara ita ce yadda mutum yake tafiya da kima har zuwa ƙarshe."
Daga wannan lokaci, Zainab ta fara shirye-shiryen gasar jihohi da ƙwazo, ta rika tashi da safe, tana nazari, tana karatu da kulawa duk da cewa wasu lokuta tana gajiya, amma kullum kalmar malaminta tana maimaituwa a zuciyarta.
"Natsuwarki ita ce makamin nasararki."
Ta ci gaba da tashi da wuri kowace safiya, tana tsara jadawalin karatunta da kyau, duk da gajiyar da take ji a wasu lokuta, zuciyarta ta kasance cike da kwarin gwiwa, kalmar malaminta, "Natsuwarki ita ce makamin nasararki,” tana ta buga a zuciyarta kamar wani ƙararrawa, tana tunatar da ita cewa duk wani ƙoƙari da za ta yi cikin nutsuwa da hankali zai kai ta ga burinta.
Rana ta zo da gasar jihohi ta fara, Zainab ta shiga cikin ɗakin gasar da fuska mai nutsuwa da tsari yayin da ake rabon takardu da tambayoyi, duk wani sautin damuwa ya kau daga zuciyarta; ta mayar da hankali ga kowace tambaya, tana amfani da ilimin da ta tara da kuma dabarun da ta koya wajen tsara amsoshi cikin hankali.
Bayan wasu mintuna da suka yi tsawo, lokacin amsa tambayoyi ya wuce, Zainab ta fita daga ɗakin da zuciyarta tana ta bugawa da jin dadi, ba tare da sanin sakamakon ba, amma tana da tabbacin cewa ta yi iya ƙoƙarinta, abokanta sun lura da bambanci a gareta kwanciyar hankali da tsari sun bayyana a dukkan matakan da ta ɗauka.
Da safe na gaba, lokacin da sakamakon ya fito, sun bayyana cewa Zainab ta yi fice a gasar, ta samu matsayi mai girma a tsakanin ɗaliban jihohi, amma mafi muhimmanci ga Zainab, ba wai nasara ce kawai ba, har ma da yadda ta koyi muhimmancin natsuwa, jajircewa, da tsarin rayuwa ta fahimci cewa nasara ba ta tsaya kawai a ga sakamako ba, amma a cikin yadda mutum ya shirya kansa da yadda yake tunkarar kalubale cikin nutsuwa.
Daga wannan rana, Zainab ta ƙara ƙwazo wajen ilimi, amma yanzu ta fahimci cewa natsuwa ita ce ainihin makamin da zai jagorance ta ga duk wani buri da take so ta cimma.
Tun daga wannan rana, Zainab ta fara tsara rayuwarta cikin tsari da hankali, Kowace rana, tana ware lokaci don karatu, nazari, da kuma tunani mai zurfi ta fahimci cewa ba kawai ƙwazo kadai yake kawo nasara ba, har ma da hakuri da daidaito a cikin dukkan ayyukanta.
A lokacin da take fuskantar ƙalubale, maimakon ta yi saurin firgita ko jin haushi, sai ta ɗauki lokaci tana nazarin yadda zata magance matsalar da hikima, wannan sabon fahimta ya sa ta fara samun sakamako mai kyau a makaranta, har ma wasu malamanta suka fara lura da bambancinta.
Zainab ta kuma gane cewa natsuwa ba wai kawai tana taimaka mata wajen cimma burinta bane, har ma tana kawo mata kwanciyar hankali a zuciyarta duk lokacin da ta ji damuwa ko fargaba, sai ta ɗauki numfashi a hankali, ta tuna cewa komai yana da lokacin sa, kuma duk abin da ta sanya a ranka da zuciya mai tsabta zai kai ta ga nasara.
A hankali, rayuwarta ta fara canzawa daga tsoro da rashin tabbas zuwa kwarin gwiwa da kwanciyar hankali. Kuma a cikin wannan sabon yanayi, Zainab ta fara ganin burinta na dogon lokaci a matsayin abu mai yiwuwa, wanda kawai natsuwa da jajircewa zasu iya kai ta wurin.
Bayan wasu watanni na aiki tukuru da natsuwa, Zainab ta samu damar shiga gasar ƙasa-ƙasa ta ilimi wadda za ta tantance ilimi da basira a tsakanin ɗalibai masu hazaka daga ko’ina, a lokacin da ta fara shirye-shiryen gasar, zuciyarta ta ɗan firgita tun tana da ra’ayin cewa wannan gasar zata zama babban gwaji na ƙarfin zuciya da hankalinta.
Amma yanzu, tare da fahimtar cewa natsuwa ita ce makamin da zai jagorance ta, Zainab ta fara tsara shirin ta cikin hankali a raba karatun ta zuwa ka shi-ka shi, tana nazarin kowanne fanni cikin zurfi, amma kuma tana ɗaukar lokaci don hutu da tunani mai zurfi, ta koya yadda za ta sarrafa damuwa yayin gasa, da yadda za ta mayar da hankali a lokacin da matsaloli suka taso.
Ranar gasar ta zo, kuma Zainab ta shiga dakin gasa da zuciya mai kwanciyar hankali, duk da cewa wasu ‘yan takara sun yi saurin firgita, Zainab ta tsaya a kan dabarunta: natsuwa, tsari, da tunani mai zurfi, lokacin da aka fara tambayoyi masu wahala, ta yi amfani da duk abin da ta koya, tana mai da hankali kan kowanne bayani.
A ƙarshe, sakamakon gasar ya bayyana: Zainab ta yi fice sosai, har ta lashe kyautar farko a fannin da ta fi kwarewa. Amma abin da ya fi muhimmanci ga ita shi ne: ta gane cewa nasara ba kawai sakamakon ƙwazo bane, har ma sakamakon natsuwa, hakuri, da daidaito a cikin kowanne mataki na rayuwa.
Kuyi hakuri zakuga na juye Sir a matsayin malam ai duk ɗaya ne kun sani.
ZAINAB
Sha'awa marubuciya diggi ✍️
WhatsApp number 08080304152
PAGE NA
9&10
Bayan gasar, Zainab ta zauna a bakin taga tana kallon yadda rana ke faduwa a hankali. Iskar sanyi ta taso tana kadawa cikin gashin kanta, tana tunanin duk abin da ya faru, ba don kyautar ba take farin ciki sosai, sai don yadda ta samu nutsuwa da kwarin gwiwa a kanta.
A baya, ta kan ji tsoro idan aka ambaci kalmar gasa tsoron kuskure, tsoron faduwa, da tsoron a raina abin da take yi. Amma yanzu ta gane cewa tsoro ba abokin gaba bane, sai dai jarabawa ce da ke nuna irin ƙarfin zuciya da mutum yake da shi.