Sashe 7
Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A can nesa, ta hango wani mutum tsaye cikin farin kaya, yana kallonta da idanun da ta sani fiye da kowanne: Faruk.
"Faruk…" ta faɗi da rawar murya.
ya yi murmushi mai raɗaɗi. "na ce miki kar ki zo, Zainab."
Ta yi tafiya zuwa gare shi, amma kowane mataki da ta ɗauka, wurin yana nisa.
"Me ya faru da kai? me yasa kake nan?"
"Na nemi gaskiya," ya ce, muryarsa tana ƙara yin ƙasa kamar ana haɗa ta da iska.
"Na nemi abin da bai kamata ɗan adam ya nema ba, na so in dawo da wanda muka rasa… amma ruwan nan bai ba da rai kyauta, Sai da ya karɓa.,
"Ya karɓa me?"
Faruk ya dubeta, ya ɗan ɗaga hannunsa, a cikin tafin hannunsa, ta ga wani haske mai launin zinariya, yana ƙonewa a hankali zuciyarta.
"Ya karɓi rabin raina, kuma yanzu, idan kin zo nemana ni, zai karɓi rabin naki."
Zainab ta girgiza kai, hawaye suna zuba.
"Ban damu ba! Zan zauna tare da kai, ko a nan, ko a wancan wuri!."
Faruk ya matso kusa da ita a hankali.
"Kin manta me tsohuwa ta faɗa?" ya tambaya.
"Gaskiya tana da fuska biyu, na farko soyayya ce, Nn biyu... hadiya ce."
Iska ta motsa, wurin ya fara dusashewa. Wani murya daga can ƙasa ta soma kiran sunanta
"Zainab! Ki dawo! Kar ki bari ruwa ya rufe ki!"
Muryar Hajiya Kubra ce.
Faruk ya kama hannunta, hannunsa sanyi amma mai daɗin taɓawa.
"Zabi ɗaya ne ke nan, Zainab, Ki tafi, ki rayu da labarina, ko ki zauna nan da ni a tsakanin gaskiya da mafarki."
Zainab ta kalli hannunsa, sannan ta kalli sama in da wani haske mai launin fari ke haskowa daga nesa.
"Faruk," ta faɗi cikin kuka, "ban iya rasa ka sau biyu ba."
Sai ta matso kusa ta rungume shi.
A lokacin, ruwa ya sake yin ƙarar girgiza, kamar ana rushe duniya, haske ya cika komai, sannan shiru.
Da ta buɗe ido, tana kwance a bakin tafki.
Hajiya Kubra tana kan kanta, tana kuka.
"Alhamdulillah... kin dawo, Zainab."
Amma Zainab ba ta ce komai ba.
Sai ta ɗauki akwatin katakon daga gefenta, ta buɗe a ciki babu takarda, babu zobba, sai ƙaramar ƙwallar haske, mai launin zinariya kamar wacce ta gani a hannun Faruk.
Ta murmusa a hankali, idonta ya cika da hawaye.
"Faruk bai ɓace ba," ta ce da ƙasa. Yana tare da ni a cikin ruwana."
Tafkin ya yi wani ɗan motsi, kamar yana amsa mata.
Zainab ta dawo cikin garin ruwa uku, amma komai bai kama da yadda ta bar shi ba, hasken rana ya fito, amma ya yi laushi kamar bai cika duniya ba.
Mutane suna motsi kamar daidai, amma idanun su sun ɗauki wani sanyi mai zurfi, kamar sun san wani abu da ba kowa ya sani ba.
A cikin jakarta, ƙwallar zinariya da Faruk ya bar mata tana haskakawa a hankali, ta sanya hannunta a kai, kuma ta ji dumin zuciyarta yana hade da dumin Faruk kamar yana nan, amma a wani wuri daban.
Hajiya Kubra ta tsaya a gefenta.
"Kin tsira, Zainab, amma kin biya farashi, ruwan nan bai bari ba tare da karɓar wani abu daga zuciya ba, Kin rasa nutsuwarki, amma kin samu gaskiya."
Zainab ta kalli ruwa, wanda yanzu ya yi shiru.
"Ni yanzu… ina da shi a kaina," ta ce cikin murmushi mai raɗaɗi.
"Faruk, koda bau tare da gani ba, yana tare da ni, kuma gaskiya… tana nan, amma ba a bayyane ba kamar yadda na zata."
Tun daga wannan rana, Zainab ta fara tafiya cikin duniya da sabon hangen nesa, kowa da kowa yana ganin ƴar matashiyar da ta dawo daga garin ruwa uku, amma ba wanda ya sani abin da ta gani a cikin ruwan nan.
A duk lokacin da rana ke faduwa, idan ta kalli ƙwallar zinariya a hannunta, za ta ji muryar Faruk:
"Zuciya ta kasance tare da ki, kuma yanzu ke ce mai riƙe da gaskiya."
Zainab ta rufe idanunta, ta ɗan murmusa, sannan ta matso gaba.
Rayuwarta ta cigaba, amma a cikin kowane zuciya da ta hadu da shi, a cikin kowane zabi da ta yi, akwai wani sirri mai ƙarfi: gaskiya tana da farashi, amma ba a rasa dukkan haske ba.
Ruwan ruwa uku ya tsaya a cikin ƙwaƙwalwa, kamar labari mai ƙarfi wanda ba a taɓa mantawa da shi ba.
Kuma Zainab, yanzu mai wayewa da ƙarfin zuciya, ta san cewa duk abin da ta rasa a waje, ta samu a ciki.
Hasken rana ya shuɗe a hankali, amma zuciyarta kamar tafkin nan tana cike da ƙarfi, soyayya, da gaskiya.
Shekaru biyu bayan tafiyar Zainab zuwa garin ruwa uku, ta koma birni mai cike da hayaniya, mutane suna ganin ta, amma ba su taɓa sanin abin da ta gani a cikin tafkin nan ba" Har yanzu tana ɗauke da ƙwallar zinariya a cikin jaka, mai haskakawa a hankali a kowane dare.
Amma akwai wani abu da ya canza a cikinta, a duk lokacin da ta kalli rana na faduwa, ko iska mai sanyi ta busa ta fuskarta, ta ji muryar Faruk a hankali ba kamar mafarki ba, amma kamar wani abu yana magana daga wani wuri a cikin duniya.
"Zainab…"
Ta yi ƙoƙarin juyawa, amma babu kowa a bayanta, kamar duk wani tunani, sautin yana da gaskiya, amma babu tushensa.
A lokacin da ta shiga gidanta, ta lura da wani abu a cikin madubi inuwa mai siffar Faruk, amma yana motsi daban-daban daga yadda take tsammani, ba ta tsorata ba, amma zuciyarta ta buga da sauri.
Sai wani sauti ya cika gidan:
"Ruwa na nan… kuma ni nan ne, a kowane zabi da ki yi."
Zainab ta fahimci cewa garin ruwa uku bai bar ta ba, Faruk bai bar ta ba, ko da a zahiri ta dawo, wani ɓangare na ruwan nan da sirrin da suka haɗa shi da Faruk, yana cikin rayuwarta har abada.
Ta sanya hannunta a ƙwallar zinariya, wani sanyi mai ɗumi ya ratsa hannunta, kamar ƙoƙarin tunatar da ita:
"Gaskiya ba ta barin duk wanda ya nemeta… amma wanda ya karɓa, yana rike da iko."
Ji mata da laushi, kamar yana cewa:
"Zainab… yanzu ke ce mai rike da gaskiya da ruwan nan, kuma babu wanda zai taba ɗaukar abin da ke cikin zuciyarki."
Shiru ya mamaye gidan, amma Zainab ta san, sirrin ba ya barin mutum, kuma babu wanda zai taɓa iya mantawa da shi.
ZAINAB
Sha'awa marubuciya diggi ✍️✍️
WhatsApp number 08080304152
PAGE NA
13&14
Zainab ta buɗe idanunta a hankali, hasken ƙwallar zinariya yana ci gaba da haskakawa cikin dakin, yana jefa inuwa mai laushi a bangon da ke cike da tsoffin hotuna, iskar dare ta shigo ta taga, tana ɗauke da ƙamshin ruwa da wani sanyi mai nutsar da rai.
Sai zuciyarta ta fara bugawa da sauri domin ta ji shi.
Muryar da ta fi kowace irin murya ta sani.
"Zainab…"
Muryar Faruk ce, amma ba kamar yadda ta saba ji ba, wannan karon, muryar tana fitowa ne daga cikin ruwa ba daga nesa ba, kamu ba daga mafarki ba daga cikin ƙwallar zinariya kanta.
Ta tsaya cak, hannunta na rawa.
"Faruk?" ta furta da rauni.
Sai ƙwallar ta ɗan yi wani motsi, kamar kumfa ta tashi a cikinta, sannan haske mai shuɗi ya bayyana, a cikin wannan haske, ta hango fuskar Faruk, sai dai idanunsa sun cika da wani launin ruwa, kamar yana kallonta daga ƙarƙashin teku.
"Ba ki kamata ki kunna ta yau ba," ya faɗi, muryarsa mai taushi amma cike da damuwa.
"Ruwan nan bai gama shirye ba, zai ji ƙamshin zuciyarki, Zainab kuma idan ya ji, zai nemi abin da kike ɓoyewa."
Zainab ta matso da ƙwallar kusa da kirjinta.
"Ban iya jira ba, Faruk Ina jin kamar sirrin nan yana canzawa a kowace rana, kamar yana kiran wani wanda ba mu sani ba."
Shiru ya sake mamaye dakin, sai daga baya Faruk ya ce:
"Wannan sirri ba na mu kadai ba ne yanzu, ruwan nan ya fara tashi daga garuruwan uku… kuma duk in da yake, ana jin muryarki, ana kiran sunanki."
Wani ƙanƙanin sanyi ya ratsa ta.
"Me kake nufi?"
Faruk ya dubeta daga cikin haske
Faruk ya dubeta daga cikin haske, idonsa na ɗauke da wata irin natsuwa mai haɗe da tsoro.
"Ina nufin," ya ce a hankali,
"ba mu da iko da abin da muka fara.
Ruwan nan yana ɗauke da tarihin da ba mu rubuta ba kuma yana tunawa da duk wanda ya taba shi."
Zainab ta girgiza kai, murya na rawa.
"Amma ni dai ban yi ma sa komai ba, na dai kunna shi, kamar yadda kake koyar da ni."
Faruk ya janyo numfashi mai nauyi.
"Kin kunna shi da zuciya mai tambaya. Kin shiga da fargaba, kuma ruwan nan yana jin fargaba kamar yadda yake jin ƙauna, a yanzu… yana neman amsa daga gare ki."
Kafin ta samu ta amsa, ƙarar ruwa mai laushi ta cika dakin ba daga injin ba, amma daga cikin ƙwallar da ke hannunta, ta fara haskawa da launin shuɗi mai sanyi, kamar hancin iska a cikin dare.
Zainab ta matso da ita, numfashinta na daskarewa.
"Faruk… yana motsi."
"Ki ajiye ta!" ya yi ƙara, amma kafin ta iya, hasken ya bazu ya mamaye dakin, yana cike da murya murya guda ɗaya da aka haɗa da nata.
"Zainab," muryar ta faɗa daga cikin ruwa, "kin dawo."
Ruwan ya tsaya, hasken ya ragu, amma a yanzu, babu shakka ba ta cikin ɗaki kawai, tana cikin wani wuri da ya san sunanta tun kafin ta haifuwa.
Ruwan ya ɗauke ta ba tare da an motsa jikinta ba, idanunta a buɗe suke, amma duk abin da take gani ya koma kamar mafarki, inuwa, launuka, da muryoyi ma su jituwa da zuciya.
Ba ta cikin daki, kuma ba ta cikin duniya kamar yadda ta sani, wurin da take yanzu yana cike da haske mai laushi, yana ɗauke da ƙamshin ruwa da ƙasa mai sabo.
Ta ji muryar Faruk a hankali, daga nesa kamar ana kiransa daga ƙarƙashin kogin lokaci.
"Zainab… kada ki yarda da komai da kika gani, ki tuna da bugun zuciyarki shi ne jagoranki."
Ta lumshe ido, amma a lokacin da ta buɗe su, ta ga wata mata tana tsaye a gabanta.