← Book details Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 13

Sashe 2

Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ƙarbawa ya fara yi yana kawowa in da Zainab sai da ya ƙalli sunan ta sannan ya haɗe ta da sauran.

Tafiya ya yi sai office ɗin shi marks ya fara yi sosai ya yi mamakin ganin Zainab kawai taci 66/70 hakan ya sa ya ce leka a window yaga wata ƴar S S 3 ya ce ta kira ma sa Zainab Hassan S S one.

Toh ta faɗa amma ranta na mata ƙuna akan mi zai aiki kiran jiniyar ta tana siniya.

Shiga ajin ta yi ta ce "Zainab Hassan ki je in ji Malam Aliyu."

Ta ce "waye malam Aliyu?."

Uwarki ce ƴar iska daga zuwan malam har kin maƙale ma sa mayya kawai.

Sai lokacin ta gane waye Sir Aliyu.

Banza ta yi mata kamar ba da ita take yi ba.

Ta shi ta yi zowa in da ake kiran nata.

"Assalamualaikum"

"Waalaikimussalam"

Sir na shigo

Sai da ya ɗau lokaci sannan ya furta cewa "Eh."

Shiga ta yi amma sai ta yi tsaye a bakin ƙofar kuma ta yi shiru sai daga baya ta faɗi

"Sir gani ance kana nema na."

Shima shirun ya yi ma ta sai da yaɗau lokaci mai tsawo dan har ta fara gajiya.

Sannan ya ce "Eh"

Shiga ta yi ta yi tsaye tana kallon shi cikin ranta ta ce ma sha Allah, Allah ya yi halitta a nan

"Kallona kike tsayawa ko neman kiran da aka yi miki."

Saurin faɗan

"A a Wallahi."

Kujera ya nuna ma ta ya miƙa ma ta ta karda yana faɗin

"ki sake rubuta test ɗin ki dan ban yarda da wannan ba."

Mamaki take wai dama Sir ya yi Hausa amma yake musu turanci.

Zama ta yi tana mamakin me ya sa zata sake rubuta test ɗin.

Takardar ta ɗauka ta fara rubutawa.

Ido ya zuba ma ta yana kallo Zainab farace sosai dan tafi shi haske, ba doguwa bace sosai amma tana da tsayi, hanci siriri sai kace bairo, tana da tattawar Allah ya gefen bakinta labɓanta jajaje kamar ta yi kwalliya, tana da dimpul ko bata yi dariya,.

"Ma sha Allah", ya faɗa bai san ya fito ba.

Jin ya yi magana ya sa ta ɗaga kanta dan ta ga me yake yi ta ji yana faɗan ma sha Allah.

Kamin ta kalloshi har ya janye idanunsa, sai ta kalle shi bata yi magana ba sai kawai ta ci gaba da rubutun ta.

"Malam nagama."

Kallon ta ya yi sai ya sake kallon takardar, ya yi mamaki sosai da ganin lallai ba copy ta yi ba.

Hmmm kawai ya ce sannan ya ɗauki paper's ya miƙa mata.

"Idan kika je ki bawa monintar ɗinku."

Ita ko har yanzun mamaki take yi sosai dan bata yi tunanin yana jin hausa har haka ba.

"Toh" kawai ta ce.

Fita ta yi daga office ɗin wani lafiyayyen ajiyar zuciya ta sauƙe sannan ta tafi ajin su.

Shiko yana kallon ta window 🪟 amma haka kawai ya tsinci kanshi da murmushi.

Zainab na shiga ajin Naja'atu da Halima suka sakar mata tambaya

"Zainab mekikawa Sir ne?, da aiko a kira ki kuma kin jima sosai."

"Ba komai fah."

"Wallahi bamu yarda ba."

"Toh sai kuje ku tambaye shi mana."

"Ke dai muke tambaya ba shi ba malama."

"Shi ke nan toh."

Ringing ta shi daga makaranta a ka yi dan haka suka tashi dan zuwa gida.

A hanyar su ta zuwa gida gaban sai bugawa yake yi saboda abin da zata tarar a gida

Haba dai Abuh meke damunki ne haka kinyi shiru ki yi hakuri wata rana sai labari .

"Ke ni kam ba abin da nake tunani kawai naga ji da surutun ne."

Hmmm Amma fa badan sun yarda ba.

"Kin san idan Sir baƙo ya ce yana sona wallahi da gudu zan amshi soyayyar shi, malamin akwai kyau ga kuɗi ga jida kai, ilimin boko ilimin addini duk ya haɗe, ni Allah ya sa idan ban zama matar sa ba, ina fatan zainab ta zama matar sa, saboda ina ganin hankalin shi sosai."

"Mtsww gaskiya Halima kin cika min kunne da surutu, toh ni ina ruwana da shi ke dai mai son shi Allah yasa ya zama mijinki." Zainab ta faɗa cikin son gajiya da surutun.
Chapter 2 · 0% Book details