← Book details Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 13

Sashe 13

Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

suka ce: "Wannan yarinyar ta musamman ce, an haife ta da alamar ruwa." Sunan da aka ba ta shi ne Zainab, don girmama wadda ta kafa ruwan gaskiya tun farko. Shekaru suka wuce. Ƙaramar Zainab ta taso da halayen da suka banbanta da sauran yara, tana jin muryar ruwa, tana ganin haske a cikin madubi. Idan ta shiga kusa da rijiya, tana jin kamar ana kiranta da murya mai laushi da soyayya. Wata rana, yayin da take wasa a bakin rafi, ta ji murya daga bayan ta: "Ruwa na kiranki, Zainab." Ta juyo da mamaki. A gabanta, wani mutum tsaye cikin suturar fari, idonsa kamar kogin da ya san hanyar gida, fuskar sa cike da natsuwa, amma cikin idanunsa akwai wani abu mai zurfi kamar yana tuna wani abu da bai taɓa manta ba. "Ni kake nema?" ta tambaya cikin rawar murya. Mutumin ya yi murmushi, ya durƙusa, ya ce cikin sanni. "Ba ni ne nake nemanki ba, Zainab Ruhi na ne." Zainab ta kalle shi sosai, zuciyarta tana bugawa cikin nutsuwa. "Na san wannan murya…" Ya ce: "Da domin ruhinki ya taɓa kirana a da, ni ne ruwa da ya riƙe gaskiyarki, kuma yanzu, na dawo ba a matsayin saurayi ba, amma a matsayin wanda zai kare ki mahaifinki." Hawayen da ba ta san daga ina suka fito suka zubo a idonta. "Mahaifina?" Ya ɗaga kai, yana kallonta da murmushi mai taushi. Zamani ya juya, amma gaskiya ta dawo da mu cikin sabon jiki, a wannan lokaci, ba don soyayya irin ta masoya ba, amma don soyayya irin ta rai da asalinsa. Ruwan kogin ya fara motsi, yana yi musu kida mai laushi. A lokacin da ta kalli ruwan, ta ga hoton mace a cikin sa, fuskar da ta yi kama da tata, amma da shekaru da hikima. tsohuwar Zainab. Hoton ya yi murmushi, ya ce: "Zagaye ya cika, gaskiya ta dawo gida." Sabon Faruk ya ɗauki jarumar Zainab yanzu ƴarsa ya riƙe hannunta yana kallon ruwan da ke gudana. "Daga yau, za mu kare wannan ruwa tare, domin gaskiya ba ta ƙarewa, tana canzawa ne kawai." Rana ta fadi cikin hasken shuɗi da zinariya. Ruwan rijiya ya yi ƙara kamar murmushi, iska ta busa ta ɗauke ƙamshin soyayya da haihuwa, da sabon rai. A wannan rana, ƙauyen ya sake zama cikin albarka domin Faruk ya dawo gida, kuma Zainab ta dawo cikin sabon siffa. Rai da mahaifi ruhu guda biyu cikin jini da gaskiya ɗaya. Gaskiya ba ta mutuwa, tana sake dawowa cikin waɗanda suka amince da ita. Lokacin da ruwan gaskiya ya sake walƙiya a rijiya, mutane sun yi mamaki amma wannan karon, ba sihiri ba ne, ba haske ba ne kawai. A safiyar ranar, lokacin da rana ta fara fitowa, aka ga wani mutum tsaye a bakin rijiya. Faruk ne. Babu haske a jikinsa kamar da, amma idanunsa suna ɗauke da nutsuwa da hikima, kamar wanda ya ga duniya daga sama. Mutanen ƙauye suka taru, suka yi masa sannu da zuwa. "Na dawo," ya ce cikin murmushi, domin wannan gari ne na gaskiya, kuma akwai wanda na bari a nan." Zainab wadda yanzu ta girma, tana koyarwa a makarantar ƙauye, ta fito da sauri. Idonta ya sauka kansa lokaci ya tsaya. "Faruk…" Ya yi murmushi cikin natsuwa, ya ce: "Eh Zainab wannan karon ba don ruwa ba, amma don rayuwa, ruwan gaskiya ya nuna min cewa gaskiya ta fi kowane sihiri kuma gaskiya tana cikin neman ilimi, aiki, da kyautatawa. Hawayen farin ciki suka zubo mata. Ta ce cikin sanyi. "Na jira wannan rana, amma na yi alkawari ban tsaya ba na ci gaba da karatu, saboda na gane gaskiya tana cikin ilimi." Faruk ya kalli makarantar da ke gefe, in da yara ke karatu da dariya. "Wannan ne ruwan gaskiya na yanzu," ya ce. "Ruwa da ke tsarkake zukata ta hanyar ilimi." Daga wannan rana, Zainab ta ci gaba da karatunta, ta tafi jami’a a babban birni. Ta karanci kimiyyar ruwa da ruwa da muhalli, saboda ta san ruwan gaskiya bai zo don soyayya kawai ba, amma don ya faɗakar da mutane su kula da albarkar ruwa da gaskiya a duniya. Faruk kuwa, ya zauna a ƙauye, yana kula da rijiya da makaranta. Ya zama kamar uba ga yara yana koya musu yadda za su girmama ruwa, su riƙe gaskiya, da yin aiki da amana. Idan Zainab ta dawo hutu, sukan zauna tare a bakin rijiya da daddare. Ta kan ba shi labarin abubuwan da ta koya, shi kuma yana gaya mata hikimomin da ya samo daga ruhi da tafiyarsa. Wata rana, Zainab ta ce: "Na gane, Faruk, au na manta Babana ruwan gaskiya bai zo don ya sa mu ɓace cikin sihiri ba ya zo don ya koya mana mu zama mutane masu gaskiya." Faruk ya yi murmushi, ya ce: "Da gaske ne, gaskiya ita ce ilimi, Ilimi kuma shi ne hasken da ba ya ƙarewa." Mutanen ƙauye suka ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya da nishaɗi. Ruwan rijiya bai bushe ba, makaranta ta faɗaɗa, yara suna karatu cikin farin ciki. A kowanne bangare, ana jin labarin Zainab da Faruk ba kamar tatsuniya ba, amma a matsayin darasi. Soyayya tana wucewa, gaskiya tana rayuwa, amma ilimi shi ne hanyar da gaskiya ke tafiya. A ƙarshen shekara, lokacin da Zainab ta kammala karatu, ta dawo gida ta buɗe makarantar ruwa, ta koyar da yara yadda ruwa ke rayar da ƙasa, yadda gaskiya ke rayar da zuciya. Mutanen ƙauye suka taru suka yi shagali. Faruk ya kalli Zainab ya ce cikin murmushi. "Kin ga, ruwan gaskiya ya dawo gida da gaske a cikin zuciyar ki, da a cikin ilimin ki." Zainab ta ce: "Ilimi shi ne ruwa, gaskiya ita ce tafarkinsa." Rana ta faɗi cikin walƙiya, yara suna dariya, ruwa yana gudana. Ba a ji sautin sihiri ba, amma an ji sautin farin ciki domin wannan karon, ruwan gaskiya ya zama ilimi da rayuwa. Ƙarshe: Gaskiya Ta Zama Ilimi Faruk ya dawo gida, Zainab ta ci gaba da karatu, ruwan gaskiya ya koma zuciyar mutane. Alhamdulillah Alhamdulillahi Alhamdulillahi Allah na gode maka da ka nuna min gama wannan littafin lafiya Duk mai son littafina ya yi min magana da wannan number 08080304152 Mai son kirana dan kulla alaƙa ya kira ni wannan number Amma dan Allah kar namiji ya kira ni saboda ina da jarumin jarumai Allah ya sa kun fahimta. 08084277827 Ina godiya sosai Allah barmu tare Nice taku har kullum sha'awa marubuciya diggi ✍️ ✍️ Kar wanda ya kirani idan yasan ba data zai turamin ko kati ko kyautar kuɗi zai ban ba atoh🤪🤪 Mu kasance a cikin littafin mu na gaba. Mai chakwakiya rikitarwa da ilmantar kai har da faɗa karwa Littafi mu nagaba shine AMRAAH in sha Allah.
Chapter 13 · 0% Book details