Sashe 12
Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin zuciyarta: "Na gaya miki, ruwa ba ya barin wanda ya karɓe shi, kuma gaskiya tana raye cikin ke." Ta kan murmusa, ta ce cikin zuciyarta: "Faruk, ba zan bar ruwan nan ba. Amma yanzu na fahimci abin da ba na ganewa da farko, gaskiya ba ta nemi mutum ɗaya ba tana so ta haskaka duniya." Sai ta ɗaga ƙwallar zinariyar da ke wuyanta, ta riƙe ta a hankali. A ciki, haske ya yi walƙiya, sannan ya koma sanyi, kamar zuciya mai bugawa cikin natsuwa. A wancan dare, ruwan sama ya sake sauka, amma wannan karon, ba kamar da ba saboda kowanne digo da ya faɗo, yana ɗauke da haske. Mutanen ƙauye suka fito suna kallo, suna tambaya cikin mamaki: "Wane irin ruwa ne wannan?" Zainab ta kalli sama, tana murmushi cikin hawaye. "Ruwan gaskiya ne," ta ce cikin sanyi. "Ya dawo gida." Zuwa nan, ruwan gaskiya ya cika zagayensa daga sirri zuwa gaskiya, daga zuciya ɗaya zuwa duniya. Amma labarin bai ƙare ba domin gaskiya tana tafiya kamar ruwa, tana neman sabon tafarki. Shekaru sun ja bayan dawowar Zainab daga dajin asali. Ƙauyen ya canza mutane sun koyi natsuwa, sun koyi magana cikin gaskiya, sun daina ɓoye zuciya kamar da. Ruwan da suke sha daga rijiyoyin gari yana da ɗanɗano mai daɗi, kuma a duk lokacin da aka yi ruwan sama, ƙasa tana sheƙi kamar zinariya. A cikin wannan canji, Zainab ta ci gaba da zama cikin natsuwa, ba tare da neman yabo ko daukaka ba. Yara kan zauna kusa da ita suna sauraron labarai, mata su nemi shawara, maza su tambayi mafita. Amma duk lokacin da suke tambayarta yadda ta samu wannan hikima, sai ta ce da murmushi: "Ni ba ta ruwan gaskiya ba ce, ni dai na zama hanyarsa." Da dare ɗaya, ta zauna a bakin rijiya tana kallon taurari. Iska ta busa cikin laushi, sannan ta ji muryar da ta daɗe ba ta ji ba: "Zainab…" Ta runtse idonta, murmushi ya bayyana a fuskarta. "Na san za ka dawo, Faruk." "Ba domin ni ba ne, Zainab," muryar ta ce cikin annuri, amma domin ruwan nan, lokaci ya yi da zai ci gaba da tafiyarsa. Ta kalli ƙwallar zinariyar a wuyanta yanzu hasken ta ya fara raguwa, amma a maimakon duhu, tana zamewa kamar ruwa mai haske. "Ina nufin tafiyarsa ta ƙarshe?" ta tambaya. "A’a" muryar ta ce, "Tafiyarsa ta gaba, gaskiya ba ta ƙarewa tana komawa wurin da ake buƙatarta." Zainab ta ɗaga ƙwallar da hannunta biyu, ta ɗaga sama. A lokacin, wata annuri mai sanyi ta rufe ta gaba ɗaya, ta bayyana a cikin hasken wata, sannan ƙwallar ta narke ta zama ruwan haske mai fita kamar zuma. Ruwan ya tashi sama, ya watse cikin iska, yana yin ƙarar kamar waka mai taushi. Yaran ƙauye da ke barci suka ji iska mai sanyi ta ratsa su. Mutanen gari suka farka suka fito suka ga abin mamaki taurari suna walƙiya fiye da yadda suka saba, kuma ruwan sama yana sauka cikin haske. A tsakiyar tsakar gari, in da rijiya take, suka tarar da Zainab tana zaune cikin nutsuwa, fuskarta cike da natsuwa da murmushi, idanunta rufe. A jikinta babu ƙwallar zinariya amma a ƙasan ƙafafunta, ƙaramin rafi ya fara fitowa, yana gudana da sanyi cikin ƙasa, yana tafiya zuwa kowanne gida. Tsohon da ya taɓa ba ta ruwan farko ya zo, ya tsaya yana kallo. Sai ya ce da murya mai rauni amma cike da girmamawa: "Ruwan gaskiya ya samo tushe. Zainab ta zama hanya." Tun daga wannan rana, ruwan da ke fitowa daga rijiyar nan bai taɓa ƙarewa ba. Ko da lokacin fari, ko da lokacin tsananin rani ruwan yana nan. Mutanen ƙauye sun kira shi ruwan Zainab, amma tsofaffi suna kiran sa da sunan da ya dace: Ruwan Gaskiya. Kuma a duk lokacin da ruwa ya zubo cikin ƙasa, ana jin wata murya mai laushi daga cikin iska tana cewa: "Gaskiya tana tafiya kamar ruwa tana zuwa in da ake buƙata." Ranar da ruwan haske ya watse cikin sama, duniya ta canza da shiru mai daɗi. Zainab ta ji jikinta ya yi sanyi, amma zuciyarta ta cika da natsuwa, ta san ba ita kadai ba ruwan gaskiya yana nan cikin kowanne digo da ke sauka daga sama. Ta rufe idonta, ta furta cikin sanyi: "Faruk… gaskiya ta koma in da ya kamata, amma zuciyata ba ta son duniya ba tare da kai ba." "Naso nadawo tare kai saboda ina son nasan daɗin mahaifi." A lokacin, iska ta motsa da wani irin sauti kamar bugun zuciyar ruwa. Kogin da ke gefen ƙauyen ya fara walƙiya da haske mai shuɗi, sai ruwan ya fara tashi sama, yana jujjuyawa kamar gajimare. Zainab ta miƙe, idonta cike da mamaki da hawaye. A tsakiyar ruwan, ta ga siffa tana bayyana siffar da ta fi kowacce ta sani, ta fi kowacce ta jira. Faruk. Ba cikin haske kawai ba, ba cikin ruwa kawai ba amma cikin jikinsa na gaskiya. Ya takowa cikin shiru, ruwan yana bin sawunsa kamar yana girmamawa. Idonsa ya haɗu da nata, sannan ya ce cikin muryar da ta daɗe tana mafarki da ita: "Na dawo, Zainab, domin gaskiya ta gama aikinta, kuma lokacin soyayya ya dawo cikin zahiri." Zainab ta kalli sama, hawaye suka zubo mata, sannan ta yi murmushi mai kama da fitar rai amma cike da farin ciki. "Na jira wannan rana fiye da duk wata rana." Ta gudu zuwa gare shi, ta faɗa ma sa a jiki, kuma lokacin da hannuwansu suka haɗu, ruwan da ke kewaye da su ya tsaya. Haske ya zubo daga ƙwallar zinariyar da ke gefenta amma wannan karon, ta rabu biyu, ta ɗaya ta rataye a wuyanta, ta ɗaya kuma a wuyan Faruk. "Yanzu gaskiya ta sami gida biyu," Faruk ya ce cikin murmushi. "Tana tsakanin mu." Mutanen ƙauye suka farka da safe suka ga abin ban mamaki, Zainab da wani saurayi mai annuri suna tsaye a bakin rijiya, suna kallon rana tana fito da walƙiya. Babu wanda ya tambaya ko daga ina ya fito saboda a idanunsu, sun ga amsar tambayoyin da ba su taɓa faɗa ba. Daga wannan rana, Zainab da Faruk suka ci gaba da rayuwa a ƙauyen, ba kamar mutane na yau ba, amma kamar ruwan da yake saman hanya. Suna kula da ruwa, suna koyar da mutane cewa gaskiya tana rayuwa ne idan ana raba ta cikin soyayya. Idan dare ya yi, sukan zauna kusa da juna a bakin rijiya, suna kallon taurari cikin shiru. A wani lokaci, Zainab za ta ce: "Ka tuna lokacin da na ce na zama ruwa?" Faruk ya murmusa ya amsa: "Eh amma yanzu mun zama kogin gaskiya tare da ƴata." Sannan iska ta busa cikin sanyi, ruwa ya yi ƙara mai daɗi, kamar duniya tana yi musu addu’a. Shekaru da yawa sun wuce. Ƙauyen ya girma, yara sun zama manya, manya sun zama labarai. Amma gidansu Zainab da Faruk yana nan a bakin rijiya mai haske da ba ta taɓa bushewa ba. Da yake Zainab tana tare da Faruk ne bata koma cikin gidan su ba. Kowane dare, haske mai launin shuɗi yana bayyana daga saman rijiya, yana walƙiya kamar tauraro da ke cikin ƙasa. Mutanen ƙauye sun saba da shi, suna kiran sa "Numfashin Ruwan Gaskiya." Ba wanda ya san ko Faruk ne saboda yana nan kamar saurayi. A wancan shekara, lokacin da ruwan sama ya fi daɗi, aka lura cewa Faruk da Zainab sun fara yin shiru sosai. Ba kamar da ba, babu maganganu da yawa, babu tafiya zuwa kasuwa. Suna zaune tare a gefen ruwa, hannunsu a haɗe, suna kallon kogin da ke tafiya cikin natsuwa. ZAINAB Sha'awa marubuciya diggi ✍️ ✍️ WhatsApp number 08080304152 PAGE NA 19&20 Da yamma ɗaya, lokacin da rana ke faɗuwa ta bar sararin sama cikin zinariya da shuɗi, suka zauna kamar yadda suka saba. Iska mai sanyi ta busa, ta ɗauke ƙamshin ruwa, da ƙamshin furanni. Zainab ta kalli Faruk ta ce: "Na ji ruwan yana kiran, yana son komawa in da ya fito." Faruk ya murmusa, idonsa yana cike da haske. "To mu koma tare, ba a raba ruwa da gaskiya." Suka miƙe, suka ƙarasa bakin rijiya, suka jingina da juna. Sannan suka kallon sama kamar rana da wata suka haɗu a wuri ɗaya. A lokacin, ƙasa ta yi shiru. Rijiya ta fara walƙiya da haske mai ƙarfi, ruwa ya motsa da ƙarar da ta yi kama da kida. Mutanen ƙauye da suka fito suka tsaya a nesa suka ga abin mamaki haske mai launin shuɗi yana lullube su biyun, sannan sannu a hankali suka zama ruwa. Babu faduwa, babu ƙara kawai ruwa ne da haske suka haɗu, suka nutse cikin rijiya mai walƙiya. A cikin wannan haske, an ji muryar su cikin iska: "Gaskiya ba ta mutuwa… tana tafiya cikin kowane ruwa, cikin kowane zuciya da ta taɓa gaskiya." Da hasken ya lafa, mutanen suka ga cewa rijiya ta zama tamkar madubi tana nuna fuskar mutum da ke kallonta, amma da walƙiya a idanunsa. Tun daga wannan rana, duk wanda ya sha daga wannan ruwa, sai ya ji sanyi mai taushi a zuciyarsa da ƙarfi na faɗar gaskiya, da natsuwar soyayya mai tsarki. Yara suka koya cewa idan suka yi magana da gaskiya, ruwa zai yi musu murmushi. Kuma a kowace shekara, a ranar da rana ta fadi da launin zinariya, ruwan rijiya yana walƙiya fiye da yadda aka saba. Mutanen ƙauye suna cewa: "Zainab da Faruk sun dawo suna ziyartar mu, domin gaskiya tana tafiya, amma ba ta barin gida." Bayan shekaru masu tsawo bayan ruwan gaskiya ya ɗauki Zainab da Faruk, ƙauyen ya canza zuwa gari mai cike da albarka. Ruwan da suka bari yana nan ba ya bushewa, ba ya dushewa. Mutane sun koyi rayuwa cikin gaskiya, suna yin addu’a duk lokacin da suka sha daga rijiya. Amma wata rana, a lokacin da ƙasa ke amsar ruwan farko na damina, aka haifi wata jaririya. Uwarta ta haifi ta a cikin gida kusa da rijiya, kuma lokacin da jaririyar ta fito duniya, aka ji ƙarar ruwa daga cikin rijiya kamar ta yi murna. Jaririyar na da idanu masu launin shuɗi mai zurfi kamar kogin da ke cikin rana, kuma lokacin da ta yi kuka, sautin ya yi kama da ruɗin ruwa. Malamai suka zo,