← Book details Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 13

Sashe 11

Zainab Mai Ruwan Gaskiya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rawaya ya kwanta a kan fuskar ta, yana bayyana ƙuruciyar da lokaci bai shafe ba amma zuciya ta gaji. Ta zauna a ƙasa, ta jingina da bango, ta rufe idonta kamar tana sauraron wani murya daga nesa. "Ruwa na nan… kuma ni nan ne." Muryar Faruk tana dawowa a hankali cikin kwakwalwarta kamar ƙamshi daga wani tsohon wuri, ta murmusa, amma murmushin ya ƙunshi zafi da salo guda. "Me yasa rayuwa ke barin mu da abubuwan da ba za mu iya mantawa da su ba?" ta furta a hankali, kamar tana tambayar kanta. A lokacin, ƙwallar zinariyar da take rataye a wuyanta ta fara ɗan haske, kamar tana amsa tambayarta, wani ƙara mai laushi ya fito daga cikinta ba sauti bane, amma jininsa ya isa kai tsaye zuciyarta. Saboda gaskiya tana rayuwa ne a cikin mai ɗaukar ta." Zainab ta buɗe idonta da sauri, wani yanayi ya cika ɗakin iska da ɗan ɗumi, kuma ƙanshin ruwa mai ɗanɗanon ruwan sama ya fara bazuwa. Ta tashi, ta kalli madubin da ke gefe, a ciki ta ga fuskar ta, amma a bayan hoton nata akwai inuwa inuwa mai siffar mutum, tana kallonta da murmushi. "Faruk?" ta furta cikin tsoro da bege. Sai muryar ta dawo da wani laushi da ke sa zuciyarta bugawa da natsuwa lokaci guda: "Zainab, ruwan nan bai ƙare ba, gaskiya tana buƙatar wanda zai rike ta da tsoro da kauna tare." Ta durƙusa, tana riƙe ƙwallar zinariyar, hawaye na sauka a fuskarta. "Idan haka ne," ta ce cikin murya mai sanyi, "To bari na zama ruwa… bari na zama gaskiyar da ba ta gushewa." Ruwan a cikin kwandon ya yi ƙara, sannan haske ya lullube ɗakin gaba ɗaya. A lokacin da komai ya lafa, Zainab ta tsaya da nutsuwa, amma ba ita ɗaya ba akwai wani salo, wani natsuwa, da wani haske a idanunta da ke nuna cewa ta gane: Ba wai ruwan nan ne kawai ya bar alama ba, ita ma ta zama wani ɓangare na labarinsa. Ranar ta yi duhu kafin rana ta fadi. Wata iska mai ɗauke da ƙanshin ƙasa da ruwa ta ratsa ƙofar gidan, Zainab ta tsaya a tsakar gida tana kallon sararin sama da ke kumbura da girgije. A ƙasan zuciyarta,ta san akwai wani abu da zai faru, a duk lokacin da ruwan nan yake motsi, wani ɓangare na rayuwarta yana kira gare ta. Ta riƙe ƙwallar zinariya a wuyanta, ta runtse idonta, cikin wannan duhun, ta ji kamar tana cikin wani wuri dabam wuri mai annuri amma cike da nutsuwa. "Zainab…" Muryar ta sake dawo da sanyi, kamar tana fitowa daga zurfin ruwa. "Lokaci ya yi da za ki san asalin ruwan nan, ba a halitta shi kawai domin soyayya ba, amma domin gaskiya, gaskiyar da ta haɗa rayuka biyu kafin lokaci." Ta ji hawaye sun taru a idonta. "Wace gaskiya, Faruk? Me yasa ni?" Sai haske ya bayyana a gaban ta, yana canzawa zuwa hoton wani tsohon wuri kogi mai nisa, cikin daji, in da rana ke haskakawa ta cikin bishiyoyi, wani saurayi da mace suna tsaye a bakin ruwan, hannayensu a hade. "Kin gane su?" Zainab ta kalli su sosai zuciyarta ta fara dukan da ba ta iya fassara ba, sai ta gane fuskar matar… fuskar wata ce, Kuma fuskar saurayin Faruk. Ta ja baya da mamaki. "Amma wannan, wannan aii Mama ta ce, wannan kafin ku haifeni ne." Muryar ta dawo cikin sanyi, tana cika kunnenta: "Rayuka suna haɗuwa fiye da lokaci, ruwan gaskiya shi ne hanyar da Allah ya sa don tunatar da waɗanda suka manta abin da suka yi alkawari tun kafin duniya ta fara." Zainab ta durƙusa, ta riƙe ƙwallar zinariya tana jin zafi da sanyi lokaci guda, a lokacin, hasken ya zame mata hawaye, hawaye suka zubo cikin hannunta, suka koma ƙwayar ruwa ɗaya tsantsar haske. "Yanzu kin fahimta," muryar ta ci gaba, "Ba a ba ki ruwan nan don soyayya kawai ba, an ba ki shi domin ki riƙe gaskiya domin ki tuna cewa komai da ke cikin rayuwa yana da asali, kuma gaskiya ba ta mutuwa." Zainab ta buɗe idonta, ruwan sama ya fara sauka a zahiri, yana dukan saman rufin da ƙara mai laushi, amma wannan karon, ba ta ji sanyi ba, ta ji kamar ruwan yana shigowa zuciyarta, yana wanke komai da ta riƙe tsawon shekaru. Ta tashi, ta ɗaga kai sama cikin ruwan sama, ta ce: "Faruk… na gane, kuma zan kare gaskiyar nan, har abada." A cikin nisan sararin sama, wata annuri ta haska, kamar murmushi daga wani wuri dabam. Washegari kafin alfijir, Zainab ta tashi da wata nutsuwa mai nauyi kamar mafarki, amma zuciyarta ta san wannan ba mafarki ba ne kira ne, Ruwan sama da ya zuba daren jiya ya bar ƙasa cikin danshi, ƙamshin sabuwar rana yana cike da iska. Ta ɗauki ƙwallar zinariya ta saka a wuyanta, sannan ta rufe ƙofar gidan a hankali kamar tana barin wani ɓangaren kanta a baya. Babu in da ta nufa sai gabas in da hasken rana ke fitowa, kuma in da kogin da ta gani cikin hangen jiya yake. Da ta isa bakin ƙauyen ƙarshe, wani tsoho ya tsayar da ita, fuskar sa cike da layukan shekaru, amma idanunsa suna da wani haske mai zurfi. "Ƴar nan," ya ce cikin murya mai sanyi, "kina nufin Dajin Asali ne?” Zainab ta kalle shi da mamaki, "Ya ya ka san haka?” Tsohon ya yi murmushi mai kama da sanin da ta rasa: "Dajin ba ya kira kowa sai wanda ruwan gaskiya ya zaɓa, an riga an faɗi zuwanki tun kafin ki zo duniya." Ta ji jikinta ya yi sanyi. "Me yake cikin dajin?" ta tambaya da rawar murya. Tsohon ya kalli sararin sama, ya ce: "Gaskiyar da ta ɓoye shekaru dari da dama, amma ki sani, duk wanda ya nemi gaskiya, dole ya shirya da fansarta." Sai ya ba ta ƙaramin kwalba mai cikewa da ruwa mai santsi. "Wannan ruwan ne daga tushen kogin farko, idan kin shiga dajin, kar ki sha shi sai lokacin da zuciyarki ta kasa fassara abin da idonki ya gani." Zainab ta karɓa da girmamawa, sannan ta yi masa godiya. Ta ci gaba da tafiya. Lokacin da ta shiga cikin dajin, hasken rana ya fara dusashewa, amma ba saboda dare ba bishiyoyi masu tsawo suna rufe sama da ganyayyaki masu sheƙi. Iska ta cika da ƙanshin ruwa da ƙamshin ganye, kowane motsi yana da ma’ana, kamar dajin yana numfashi. Ta ji muryar Faruk ba daga waje ba, daga cikin zuciyarta: "A nan ne komai ya fara, Zainab, ki bi ruwan… kada ki ji tsoro." Ta bi ƙarar ruwa, har ta iso bakin wani rafi mai haske kamar azurfa. A tsakiyar rafin akwai dutse, kuma a saman dutsen ƙwallar zinariya iri ɗaya da wadda take wuyanta, tana walƙiya da haske mai launin shuɗi. Zainab ta tsaya, zuciyarta na bugawa. "To me ya sa akwai biyu?" Sai ƙwallar da ke wuyanta ta fara ɗan motsi da zafi, kamar tana amsawa. Ta ɗaga kai, ta ga wani haske yana fitowa daga cikin ruwa sannu a hankali, siffar mutum ta bayyana. Faruk ne. Amma ba irin yadda ta saba gani ba hasken jikinsa yana walƙiya kamar rana ta nutse a cikin sa. "Zainab" ya ce, muryarsa kamar iska mai magana, "Na dawo ne saboda wannan rana, dukkanmu mun kasance ruwan gaskiya ne, amma an raba mu shekaru da yawa don mu koyi ma’anar gaskiya daban-daban." Zainab ta ji hawaye a idonta. "Me zan yi yanzu?" Faruk ya miƙa hannu zuwa gare ta. "Haɗa ruwan nan biyu ki haɗa su da zuciya ɗaya, idan kika yi haka, gaskiya za ta bayyana gaba ɗaya." Ta ɗauki ƙwallar zinariyar daga wuyanta, ta kusantar da ita ga wadda ke kan dutse. Da zarar suka taɓa juna, haske mai ƙarfi ya lullube dajin, bishiyoyi suka yi tsit, ruwa ya tsaya, iska ta tsaya kamar lokaci ya tsaya. A cikin hasken, ta ji muryar da ba ta san tawa ce ko ta Faruk ba tana faɗin: "Gaskiya ba ta ɓoyewa, tana jiran wanda ya shirya ya ɗauke ta." Lokacin da hasken ya lafa, ta ga kanta tsaye a bakin rafi, amma yanzu kogin yana da sabon launi shuɗi mai kama da gilashi. A hannunta, ƙwallar zinariya ɗaya ce kawai amma tana da walƙiya mai rai. Ta murmusa, ta ɗaga kai sama: "Na gane, ba ni da ruwan gaskiya kawai ni ce ruwan gaskiya." Zainab ta tashi daga bakin rafin cikin shiru, wani sanyi mai taushi ya ratsa jikinta, amma ba irin sanyi na ruwa ba sanyi na natsuwa. Babu Faruk, babu hasken dajin da ya cika zuciyarta da mamaki, sai shiru mai ɗauke da nutsuwa, kamar duniya ta tsaya tana sauraron abin da zai biyo baya. Ta kalli hannunta ƙwallar zinariyar da ke cikinsa ta zama tamkar ƙaramin zuciya mai walƙiya da haske, a cikinta, tana iya ganin zaren ruwa yana yawo kamar rai. "Wannan gaskiyar… tana da rai," ta furta cikin rawar murya. Ko da babu wanda ya gani, tana saurare. Ta juya ta bar dajin. Kowane mataki da ta ɗauka, ƙasa tana amsawa da laushi, kamar tana godiya. Iska ta busa a gefenta, tana ɗauke da ƙamshin Faruk ƙamshin ruwa da ƙamshin soyayyar mahaifi. A lokacin da ta fita daga dajin, rana ta fito, duniya ta dawo kamar yadda ta saba, amma zuciyarta ba ta daɗe da zama iri ɗaya. Tana jin kamar duk in da ta kalli ruwa a rijiya, a tabki, ko a cikin idon mutum akwai wani ɓangare na labarinta a ciki. Da ta koma ƙauyensu, mutane suka lura da canji. Zainab ta yi shiru sosai, amma idan ta kalli mutum, kamar tana karanta zuciyarsa. Ranar farko da ta shiga kasuwa, wata tsohuwa ta tsayar da ita. "Ƴata" tsohuwar ta ce, "Me kika gani cikin dajin?" Zainab ta yi murmushi mai sanyi, ta ce: "Na ga cewa gaskiya ba ruwa ba ce kawai, ita ce abin da ke tafiya daga zuciya zuwa zuciya, ba tare da ta tsaya ba." Mutanen suka fara kiran ta "Zainab mai Ruwan Gaskiya." Wasu suna zuwa domin shawara, wasu domin neman waraka, wasu kuma kawai domin kallon idanunta da ke da hasken da ba na duniya ba. Amma a duk lokacin da ta zauna cikin shiru da daddare, ta kan ji muryar Faruk tana
Chapter 11 · 0% Book details