← Book details Yar Gidan Tsohowa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 26

Sashe 26

Yar Gidan Tsohowa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Abba yana ganin wayar Alhaji Atiku tunkafin ya d'auka sai da yasaki dariya snn ya daga wayar had'ida sallama,
Alhaji Atiku ya amsa masa yana mai sakin fara'a a fuskarsa."

Bayan sun kammala gaisuwar ne Alhaji Atiku yake shaida masa gobe yyi sauri yazo garin Abuja akwai meeting da zasuyi game da harkokin siyasa."

To Abba yace yana mai d'auke da fara'a da jin dad'i a fuskarsa, snn sukayi sallama ko wanne ya kashe wayarsa."

Ya juya ya kalli yusra yasaki dariya mai sauti yace "nayi mki Alk'awarin bazaki tab'a Neman wani Abu kirasaba, ki sanyawa rayuwarki a gobe za'a tsayar da ranar aurenki da Mahmud ko yaso ko baya so wnn matsalarsa ce."

Washe gari bayan Abba ya sauka garin Abuja sunshiga meeting da manya yan siyasa, anan take da San hannun Alhaji Atiku aka tsayar da Abba a matsayin d'an takarar gwamna. Kasan cewar Alhaji Atiku shikeda jama'a dan haka ko wanne d'an takara yakeyi masa biyayya."

Sauran mutunen wurin sun Amince da zab'en Alhaji Atiku anan aka umurce Abba da ya biya kud'in k'ungiya naira milyan talatin."

Abba yayi shuru domin baya da miliyan talatin, ganin shurun da yayi yasa Alhaji Atiku ya fahimce cewa baya dasu, yasaki murmushi a ransa domin hakan yakeso ya gani."

Anan take Alhaji Atiku ya cika cak d'in kud'in ya bayar."

Zaro ido Abba YAYi cike da mmki zaiyi magana Alhaji Atiku ya dakatar dashi alamar yayi shuru idan aka tashi akwai maganar da zasuyi."

Bayan kowa ya watse daga meeting d'in akabar Alhaki Atiku da Abba a office d'in Abba sai godiya yake zuba masa wanda har yarasa abunda zai fad'a."

Alhaji Atiku ya dafa kafad'arsa yace dainayi mun godiya hakan ta isheni, kasani duk abinda nayi maka ban fad'i ba saboda kai abokinane kuma aminina na gaskya. Komai nawa ina iya mallaka maka shi a kyauta"

Wnn dalilin yasa saboda mu kuma dank'on zumunci mu ya d'ore har d'iya da jikoki na yanke shawarar mu had'a 'ya'yanmu Aure mahmud da yusra."
Chapter 26 · 0% Book details