Sashe 16
Yar Gidan Tsohowa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ido biyu sukayi da Mahmud ta tsayar da idonta gareshi ta kasa d'auke idonta a kanshi gaba d'aya kyanshi da haibarshi ya tafi da imaninta."
Mahmud kuma lokaci d'aya yaji ya tsaneta, saboda daga ganinta bata da tarbiya da kamun kai a tare da ita."
Wow ta furta had'ida mik'ewa tsaye tanufi wurin mahmud tasanya hannu zata shafi gefen fuskarshi yayi saurin rik'e mata hannu had'ida had'e fuska yayi jifa da hannunta gefe d'aya saura kad'an ta fad'i k'asa"
Bata damu da abunda yyi mataba, illah tazo gabanshi daf da shi ta zauna yanda suna iya jin saukar numfashin junansu tace "kana da kyau wanda baya misaltuwa, ina sonka."
Ta juya ta dubi Alhaji Atiku tace "daddy wnn yana da kyau ina son shi zan aureshi."
Alhaji Atiku yasaki dariya, yace shalele ai yayankine Abu yazo gida kenan, ki sanyawa rayuwarki kinsameshi, harma kin aureshi."
Mahmud yayi saurin d'aga kai sama ya dube Alhaji Atiku cike da mmki."
Shalele tasaki dariyar jin dad'i, tace "nagode daddy na dan haka nake sonka fiye da momy, tana kaiwa nan tafita cike da jin ddi
Tana fita Alhaji Atiku ya maida kallonshi a kan mahmud da murmushi a kan fuskarshi yakira sunanshi.
"Mahmud wnn itace 'yata kwaya d'aya tilo a duniya sunanta *YUSRA*
A duniya babu abunda yusra ta nema ta rasa."
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_)😅
Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)
*20*
Tafe take d'auke da robar abnci, a hannunta,
tuwon masara da miyar karkashi, tafito daga danie tafe take tana 'yar wak'arta wadda taji d'alibai nayi."
.
A gefen wasu manyan 'yan mata ta wuce da alama prefet ne
Taji suna fad'in "sai munyi mgnin wann shigiyar yarinyar badai ance Aljanu garetaba,
Idan dare yayi musameta a. D'akin da take,
ai a d'akin senior Rukayyah take, musameta a can idan tayi barci muci ubnta."
Suka sanya dariya harda tab'awa."
Dijama na gefensu basu lura da itaba, amma ta fahimci da ita suke,
Ta girgiza kai, ta kuma shan jinin jikinta saida taga wuce warsu tabisu a baya
Sai da taga inda suka shiga snn ta juya ta nufi d'akinsu."
Duk d'alibai kowa yanacin abincinsa amma bnda dijama, senior rukayya ta tambayeta meyasa batacin abinci?"
Murmushi ta kakaro tace batajin yunwa ba ynzun zataciba."
Misalin k'arfe 9pm kowanne d'alibi ya kwanta indai Junior ne."
Itama dijama ta kwanta barci yak'i d'aukarta gudun kartayi barci prefet d'in d'azun sushigo suyi mata illah duk a tsorace take."
Ai kuwa a can bayan d'akinsu taji tahowarsu suna fad'in ga d'akinsu nan mushiga muci uwarta."
Ai kuwa tanajinsu tayi saurin durowa daga kan gadon ta d'auki robar miyar tuwonta tanufi bakin k'ofar d'akin,
Kasan cewa k'ofar d'akin shafe yake da siminti,
Robar miyar ta d'aga gaba d'aya ta wanke k'ofar d'akin da miyar karkashi, ta juya takoma kan gadonta ta kwanta."
Su biyar ne ko wannesu da zangareriyar bulalarshi, a hannunshi suka tunkaro d'akin gadan gad'an suna zage zage,
Suna kawo wa kan dangaramar bakin k'ofar d'akin,
dukansu suka darje k'afa suka fad'i,
had'a baki sukayi gaba d'ayansu suka saki ihu suna fad'in "wayyo Allah jama'a kukawo mana d'auki,
Wnn tace k'afarta wnn tace wyyo hannunta wata kuma tace k'ugunta."
Dijama na kan gado ta lafe kamar barci, takeyi
Dariya ce kunshe a cikinta."
Anan d'alibai suka kawo masu taimako aka tallabesu aka d'aukesu daga wurin zuwa d'akinsu."
Kowa sai mmki yakeyi meyasa suka fad'i kuma a lokaci d'aya?"
Washe gari ko waccensu tayi targad'e a hannu wasu kuma a k'afa, suka jera suna tafiya zasu nufi class d'insu."
Dijama itama cikin shirinta na makaranta, sanye take da uniform, ta gabansu ta gifta ta wuce suka bita da kallo basuyi mata maganaba, d'aya daga ciknsu ta wurga mata harara,"
Suna ganin hakan suka had'a baki sukace daina harararta karki kuma janyo mana wani sabon bala'i,
Ina ganin Aljanun wancan yarinyar manyan Aljanune ko furtawa kayi zaka daketa, sunajinka zasu rama mata."
D'aya daga cikinsu tace nidai daga yau ko kallon inda take bazan kuma yiba wlh ba yarda za'ayi akasheni a banza ni kad'ai ce iyaye na suka Haifa."
Dukansu suka had'a baki sukace muma ai mun kyaleta, ,wurin da takema baxamu kuma bi ta wurinba."
Duk abunda suke fad'i shugaban makaranta yana bayansu basu saniba, ya kuma fahimci ko a kan waye suke magana."
Mmki ya shigayi da tunanin kalaman yayanta Mahmud a lokacin da ya kawota, saida yayi ta bashi hak'uri akan duk abunda dijama zata aikata na rashin jin magana yayi hak'uri dan Allah karya kureta, amma kuma ya hukuntata,
Daga k'arshe Yayi mashi kyautar kud'i mai tsoka yatafi."
Dama yasan batajin magana kenan."
Kai tsaye class d'insu dijama ya nufa, tana zaune a kan kujera ta d'auko littafinta tana dubawa ko da dai ba komai tasani a cikin littafinba tana karanta wqni wuri wani wurin kuma bata ganewa."
Kiran sunanta shugaban karanta yayi yace tabiyoshi."
Yana tafe tana bayanshi saida ya shiga office dinshi ya zauna snn ita kuma ta duk'a
Ya dubeta da kyau yace khadija bakyajin magana, dama yayanki ya fad'a mun halinki,
Ynzun muka k'are waya dashi yace zaizo ya d'aukeki ya bar garin nan dake yakaiki wata k'asa kiyi karatu a inda bakisan kowaba, kuma ba wnda zaije wurinki."
Ido ta zaro waje ta turo baki idonta ya fara zubar da hawaye. Tana fad'in "Dan Allah malam kayi hak'uri kakirashi a waya kabashi hak'uri na tuba bazan sakeba."
Kuka takeyi Sosai snn malam yace tayi shuru,
Zai kirashi yabashi hak'uri. Amma da sharad'in bazata kuma rashin jiba,
Da Sauri ta d'aga kai tace "eh tayi mashi Alk'awari."
Anan shiga yimata nasihohi a kan ta tsaya tayi karatu da amfanin ilimi ga rayuwar d'an Adam.
Jikinta duk ya mutu Tayi mashi Alk'awarin daga yau zatayi karatu, amma kuma ya kuma jawa prefet kunne karsu daketa."
Murmurshi kawai ya d'aga kai yace xanfad'a masu, snn yabata umurnin ta tashi tawuce aji."
Tun daga ranar Dijamah tashiga karatu baji ba gani tare da taimakon senior rukayyah."
Hankinta ya kwanta karatunta kawai takeyi sai dai wani lokacin idan ta tuna da gida,
Taji kewar tsohuwa, zataja wuri d'iya inda ba mai ganinta taci kukanta har tagaji snn ta share hawayenta ta koma cikin mutane ta zauna."
Duk wani rashin jin magana ko tsiwa duk ta zubar dasu babu abunda ta Sanya agaba sai karatu,
Musamman idan ta tuna da kalaman da yaya Mahmud yake furta mata " takwala mai kwanyar kifi, bata gane karatu,
A kullum idan ta tuna da wad'an nan kalaman nashi sai ta kuma maida hankali a kan karatu domin so takeyi ta nuna mashi ba kwanyar kifin ke garetaba."
Burin ta d'aya ne a yanxun ta ganta tafarajin turanci domin wani lokacin yaya mahmud harda turanci yake zaginta amma bata sanin abunda yake cewa."
Yanzun ba laifi ta fara ganewa,
Dama dijama tana da k'ok'ari da saurin gane karatu, rashin jine yayi mata yawa, bata Samun lokacin zama tayi karatun."
D'aliban makarantar kuma tun daga lokacin da suka ganta tayiwa prefet dukan tsiya kamar mai Aljanu kowannensu ya shiga tsoronta, yana taka tsantsan da ita, ko aikin house akeyi bnda dijama domin kuwa gaba d'aya makarantar shakkarta sukeyi."
A cewarsu Aljanu ke gareta masuyiwa mutum shegen duka."
Wnn dalilin yasa tasamu sauki takeyin abunda takeso ba wanda zai hanata."
Hatta da shugaban makaranta lallab'ata yakeyi baya son ganin b'acin ranta. duk abunda take buk'ata zaiyi mata, domin kawai a zauna lafiya."
***************
5:30 Mahmud ya tashi yyi sallah yayi wanka snn ya sanya k'ananun kayanshi wad'anda suka kuma fito mashi da mazan takarshi ta d'a namiji."
Yana cikin shirinsa saiga wayar Alhaji Atiku yakirashi a kan yayi sauri yafito shi kad'ai ake jira, zasu wuce ibadan wurin trening,
yana kashe wayar mahmud ya kira number Abba ya shaida mashi yanzun zasu wuce, Abba da momy suka yimashi Addu'a sosai snn ya kashe wayar cike da jin dad'i yafito janye da akwatin kayanshi ya nufi harabar gidan inda yakejin hayaniyar mutane da alamar abokanan tafiyarsu ne."
Koda yafito an kammala shirya komai shi kad'ai ake jira, ya bud'e murfin mota ya shiga tareda addu'a a bakinshi."
Anan suka tayar da mota suka d'auki hanyar Ibadan."
Cikin Amincin Allah da yardarsa suka isa garin Ibadan lafiya, a barikin sojoji suka sauka
aka basu masauki cike da girmamawa da karamci."
Shalele na farkawa daga barci misalin k'arfe 10:30am hankalinta na wurin Mahmud domin a daren jiya tayi mafarkinshi suna cikin wani lambu suna shanawa cike da so da k'aunan junansu."
Toilet ta fad'a tayi wanka tafito ta tsantsara kwanliya ta Jan hankali, batare da tayi sallah ba, domin yusra sallah bata dametaba saitaga dama takeyi."
Tana fitowa kai tsaye d'akin Mahmud ta nufa, tana tura k'ofa, taga baya nan babu alamun kayanshi."
Cike da tashin hankali da firgici tashiga diba ko INA a d'akin amma bbu alamarshi,
Ta koma da baya da baya idonta yana zubar da hawaye kai tsaye ta nufi d'akin daddy a lokacin yana tare da mmy mahaifiyarta suna hutawa."
Kai tsaye tashiga d'akin batare da tayi tunanin wani abuba, ko sallama babu,kai tsaye ta fad'a d'akin, ta Tarar da momy kwance a kan jikin daddy tana shafarshi."
Ganinsu hakan bai dametaba, kai tsaye ta fad'a kan gadon tayi wurin Daddy da yana ganin shugowarta yayi saurin janye momy daga kan jikinshi, Ya janyo rigarsa ya sanya yana kallonta yayi mata nuni taxo gareshi."
Tana hawa kan gadon momy ta dubeta cike da takaici da jin haushi domin ita kanta rashin tarbiyar yusra yana damunta, gaba d'aya Alhaji Atiku ya sakantata,
bata da tarbiya ko kad'an,
Mik'ewa tayi tsaye ta kai masu harara snn ta fita ta bar masu d'akin."
Tana ganin fitar momy ta fad'a kan jikinshi ta fashe da kuka mai sauti. Tana fad'in "daddy yayi tafiyarshi dama yana fad'amun baya sona wai ni nakasasshiyace, daddy meye aibuna wanda Mahmud baya sona?
, mena rasa Wanda bn caccaci so a wurin Mahmud ba?""
Pls daddy Dan Allah ka taimakamun Mahmud ya zama nawa mallakina ni kad'ai."
Bubbuga bayanta daddy yakeyi cikin sigar lallashi da kwantar da hankali, yace "daina kuka shalele,
"Mahmud ba tafiyarshi yayiba suntafi wurin trening,
So nawa kikeso na fad'a maki cewa mahmud ya zama naki."