← Book details Yar Gidan Tsohowa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 26

Sashe 13

Yar Gidan Tsohowa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalil da bai lura dashiba sai ji yayi ana kwankwasa mashi glass din mota,
Idonshi ya d'aga da suka soma komawa launin ja saboda b'acin rai da takaici, ido biyu yyi da Mahmud murmushi ya sakar mashi had'ida sauke ajiyar zuciya ya
Bud'e motar ya yafito

, mahmud ya tsura mashi ido yana kallonshi had'ida tambayarshi meke faruwa?"

Meyasa yayi parking wuri d'aya kuma ya had'a kanshi da sitiyarin mota yana tunani meke damunshi?"

Khalil ya nisa yace "tayar motata CE narasa Wanda yayi mun hakan kuma lfy k'alau na d'auko FATEEMA da wnn yarinyar Wanda tazo daga k'auye na kawosu makaranta, abunda mmki daga shigata mkrantar na fito, na tarar gaba d'aya an farfasa mun tayar mota ta baya,
Ni Abun yana bani mmki."

Murmushi Mahmud yayi ya dubi khalil yace " muguntar me kayiwa dijama kafin kuzo nan?"

Khalil ya ya mutsa fuska yace "Niko meye had'ina da ita da har zanyi mta wani abun?

Kawai dai muna cikin tafiya tasaki baki tana barci na tayar da ita, had'ida zubawa mota ta turare saka makon jin da nayi motata ta canza wani wari naji yana fitowa a ciki kamar tayi mun tusa a ciki, kasan mutumin k'auye yanda yake da k'azanta, kawai shine."

Mahmud yasan za'ayi hakan domin yasan dijama bata barin bashi."

Ya dubi khalil ya yace "mundun baka daina shiga harkar dijama ba saita daza maka fitinar da bazaka mnta da itaba a rayuwarka,

domin kuwa dijama bata barin bashi kuma bata yafiya da zarar kayi mata abu komai girmanka saitabi ta wata hanya ta rama abunda kayi mata,

Dan haka KA daina tunanin Wanda ya aikata maka hakan bakowa bane face dijama ce."

Khalil ya zaro ido waje yana mmki a fusace ya juya zai shiga cikin mkrantar Dan yaci ubanta."

Mahmud yayi saurin rik'oshi ya dawo dashi yace "yi hkri KA kyaleta ai nasamo maganinta gobe gobe nan makarantar barci zan turata kowama ya huta."

Khalil ya kuma har zuk'a yace brother Dan Allah KA barni natafi naci ubnta Dan wlh nafita iya rashin kunya da tujara."
Nafita iya k'auyanci wlh zan kakkarya mata hannu idan na rik'ata."

Mahmud ya kuma rik'eshi yana fad'in " KA natso mana kayi hak'uri dibeka 'yar k'auye duk ta da kula maka lissafi."

Auwal shima ya shiga bashi hak'uri snn ya hk'ura ya bisu suka shiga motar Mahmud suka nufi gida da cewar zasu turo mai gyaran mota tare da direba idan ya gyara sai a dawo mashi da motarshi gida."

Sai da suka fara ajiye Auwal gida snn Mahmud yaja motar suka nufi gida."

Kai tsaye wurin ajiye motocin gida mahmud yayi parking da sauri khalil ya bud"e murfin mota ya fito ranshi a dagule, kai tsaye d'akinshi ya nufa batare da ya bi takan kowa ba."

Ido Mahmud yabishi dashi snn yyi murmushi a ransa yace "indai dijama ce kad'an ma kagani."

Ya duk'a ya d'auki takardun makarantarta da siyayyar da yayi mata ta makaranta yanufi ciki da ita."

Da sallama ya shiga palon gidan ya tarar da Abba da mmy zaune akan kujera suna kallon film d'in marigayi d'an ibro mai suna hajiya babba, suna dariya."

Gefen Abba ya nufa ya gaida shi tare da momy suka amsa mashi cike da kulawa."

Jim kad'an yayi shuru Dan baisan yanda Abba zai d'auki maganar da yazo da ita ba,
ta mayar da dijama boarding school."

Ya nisa ya sunkuyar da kai yace "bansan ynda zka d'auki maganataba, Abba
Kayi hakuri Abba, rashin jin magnar dijama yana d'aga mun hnkali, musamman rashin karatun da batason yi"

Abba idan muka nuna muna tausayawa dijama muk'ak'i tilassa mata akan tayi karatu to anan gaba abun saiyafi damun rayuwarmu akan yanzun."

Abba wnn dalilin yasa na yanke shawarar gobe idan Allah ya kaimu zan mayarda dijama makarantar barci. Domin nagama shirya ko mai har uniform na d'unko mata da siyayyarta da komai yanuna wa Abba."

Abba yayi shuru nawani d'an lokaci yana tunani sann ya d'an nisa, yace "Allah yayi maka Albarka Mahmud hakan dakayi dai daine domin kuwa dijama takace duk hukuncin da kayanke a kanta dai daine."

Mahmud yayi saurin d'aga kanshi da sauri ya kalli Abba da yaji yace dijama tashishi, to meyake nufi da cewa hakan?"

Hakan dai ya barwa cikinsa maganar ya tashi yayiwa Abba sallama ya nufi d'akinshi."

Lokacin tashinsu dijama nayi, Abba ya kira wayar khalil yajita a kashe, bai kuma bi takanshiba yayi wa direba waya cewa yaje ya d'aukosu makaranta."

Dijama anci karatu muryar harta dusashe a kan d'aga murya wurin karatu."

Direba na ajiyesu ta fito da karatun da akayi masu a bakinta tanayi tundaga waje take karatun har tashigo gida."

Sautin karatunta ya tayar da mahmud daga barci, yaja dogon tsaki ya tashi zaune a kan gadonshi ya rik'e kanshi da yaji yana Sara mashi."

Wato ita wnn yarinyar rashin karatunta baka hutaba yin karatun ma baka hutaba."

Yaja dogon tsaki ya Tashi ya fad'a toilet domin yayi wanka ya fita."

Da karatu tashiga babban falon gidan, karatun shine sallamarta Abba da momy sukayi dariya, Abba yace Alhmdulillah Ashe ummie na mahaddaciya ce😊 kai Allah na gode maka
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅

Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)

*17*

_pls dan Allah readers na rok'eku da Allah duk Wanda ke karatun littafin nan idan yazo indabayaso ya k'etare kawai🙅‍♀__

Dariya tasaki ta kai zaune kusa da mmy had'ida fad'in wash mmy nagaji yau munsha karatu."

Momy tayi dariya tace "ai naga alama Ummie nah Allah yasa ki d'ore da hakan, da munfi kowa jin dad'i."

Murmushi kawai Abba keyi ya mik'e yanufi massalaci domin yin sallar magariba,

Momy ta kallesu tace "to 'yan matana kutashi kuje kuyi sallah kuyimun addu'a snn kufito muci abinci."

Da gudu suka tashi suka nufi d'akinsu domin yin sallah."

Khalil yana kwance rufda ciki sai juyi yakeyi saboda matsananciyar sha'awa dake damunsa, gashi yanxun budurwanshi d'aya ce Yasmin kuma ya d'auki Alk'awari yabarta, ba zai kuma wai waiyartaba."

Juyi kawai yakeyi yana sauke nishi sama sama,
Khalil mutum ne mai yawan sha'awa wnn dalilin yasa da momy taga take takensa, tasha kamashi yana kallon fina finan BF, ta fad'awa Abba duk abunda tagani, don hka shawararta d'ayace,
ya fitar da wacce yakeso ayi mashi aure gudun karya fad'a ga aikata zina."

Anan take ran Abba ya b'aci yashiga yin fad'a yana fad'in

khalil mai zaiyi da macce kwata kwata shekararsa Ashirin da biyar a duniya, ko Dan ta ganshi da jikin girma za'a kira mashi zancen aure yanxun."

Mahmud ma yayansa ba yanzun zaiyi aureba bare khalil jariri, da yanxun yake karatu mataki na uku, Dan haka kar a kuma yimun irin wnn zancen a kiyaye."

Momy tabashi hak'uri taja bakinta tayi shuru, amma sai dai tana sanya ido game da shiga da ficenshi."
ko da dai khalil d'in yana kiyaye duk wata hanya da zata sanya a fahimci yana neman wasu matan a waje."

Juyi kawai yakeyi a kan gado, Jiyayi baya iya hak'ura, kuma gashi ba mota a hannunshi, tashi yayi ya fad'a toilet ya sakarwa kanshi ruwan sanyi,
Sanyin ruwan na ratsashi ta ko ina ajikinsa yana sauke ajiyar xuciya sannu a hankali."

Bayan ya k'are wankan ne yayi arwala yafito ya shinfid'a abar sallah yayi sallarshi a d'aki,
wasu k'ananan kaya ya d'auko ya sanya wad'anda suka amshi jikinshi suka fito mashi da mazantakar shi, idan ka ganshi sai kace ya shekara talatin a duniya.'

Fitowa yayi daga d'akinshi kai tsaye d'akin mahmud yanufa domin ya ara mashi key d'in motarshi, yana murd'a k'ofar d'akin yajita a rufe ya tabbatarwa kanshi da baya nan."

Palon cikin gidan ya nufa da sallamarshi, a can ya hangosu gaba d'ayansu harda mahmud zaune a tsakar falo suna cin abinci."

A hankali yake tafiya ya nufi wurinsu,

Abba ya kalleshi cike da kulawa yace "dama kana ciki ne baka fito mukaci abinciba, ko ciwon kanne ke damunka?"

Runsunawa yayi ya rage tsawonshi yace "eh Abba Amma naji sauki sosai."

Ya Kalli mahmud yace brother aro mun key d'in motarka zanje gidan abokina zan amso littafaina ynzun zan dawo."

Momy tace "amma ya kamata ka tsaya kaci abinci ko kad'an ne."

Ya ya mutsa fuska domin matsanan ciyar sha'awar da yakeji komai na iya faruwa dashi."

Ya danne ya k'ak'aro murmushi yace "yanxun zandawo mmy ba dad'ewa zanyiba."

Bai rufe bakin saba dijama dake zaune gefe d'aya kusa da momy tayi ale ale tana cin tuwon shinkafa,da miyar agushi
ta d'auko lemon kwakwa Wanda momy ta had'a ta d'aga kofin sama ta kai bakinta, saida tasha ta k'oshi sann ta ajiye k'ofin k'asa,
Snn tasaki baki tasaki wani irin kyatsa jikakeyi kyrrrrrr."

Da sauri khalil ya waigo cike da jin haushi
da takaici, dama yanada haushinta,
Yanufeta gadan gadan ya kwad'a mata mari, yace "banza 'yar k'auye kinzo kinsaki baki kina yiwa mutane k'auyanci."

Rik'e baki tayi ta kurma ihu tana fad'in "wayyo Allah Abba bakina, ya fasamun baki."

Mahmud ya doka mata tsawa yace "Dan Allah malama ki rufe mana baki duk kin rud'a mana kunne."

Kafin Abba da momy suyi magana tuni khalil ya bar falon domin yasan za'ayi hakan."

Abba ya juya wurin mahmud yace "wai meyasa kukeyiwa yarinyar nan hkn ne? To tashi kafita, karna sab'a mka."

Mahmud yana murmushi ya tashi,ya fita."

Khalil yana shiga mota ya figeta da gudu bai zame ko inaba sai ciki makarantarsu a lokacin ana kiran sallar isha'i."

Inda yasaba ajiye motarsa a nan yayi parking
yafito, ya haye kan matar yana kallon 'yan mata wayayu masu aji suna wucewa, duk Wanda tayi tozali dashi saita canxa tafiya domin kawai ya ganta yaji ta burgeshi."

Kowace macce mai wucewa k'ok'arin takeyi taga ta burgeshi ya tayata, kasancewar khalil kyskkyawane bafulatani d'an gaye mai ji da kansa."

Wasu 'yan mata ne su biyu 'yan gaye suna sanye da riga da wando wad'anda suka kama jikinsu idan kika gansu saiki rantse da Allah kice ba 'ya'yan musulmaiba ne."

K'irjinsu ya cika da Brest har rawa yakeyi haka bayansu mazaune sun zauna masu Masha Allah,

Tun daga nesa da khalil ya hangosu sai da yaji tsikar jikinshi ta tashi. Wata matsananciyar sha'awa ta tasoma shi."
Chapter 13 · 0% Book details