Sashe 23
Yar Gidan Tsohowa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dijama ta kallesa ta mere baki tace "su Ahmad mnya, yayi saurin d'ago kai ya kalleta tace
Wlh zantona idan ka kuma hararata."
Abba da mommy sukayi saurin kallonta,
Abba yace "tona mana ummie nah mekikeso ki fad'a?"
*Allah ya sadamu da Alherin dake cikin wnn safiya ta juma'a*
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_)😅
Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
*28*
Kowa ya maida hankinsa a kan dijama yana sauraren abunda zata fad'a."
Sai kallon khalil takeyi,
Tace "infad'a ko inyi shuru?"
Mammy da Abba suka had'a baki sukace fad'a mana."
Khalil sai zarar ido, yakeyi kamar Wanda yyi k'arya ya had'a gumi,
ya kuma had'e fuska ba wani alamar wasa a tare dashi."
Ta karkace kai cike da tsiwa tace "zanfa tona."
Mommy tace tona mana ummie meya faru?"
Gani yayi tana gyaran baki alamar zata fara mgna, tonawar zatayi kuwa,
Ya shiga tunanin abunda zaiyi ya fitar da kansa."
Yayi saurin ture plate d'in tuwon dake gabansa ya fad'i K'asa
Gaba d'aya abinci ya zube k'asa duk ya b'ata masa jiki,
K'afarsa ya rik'e yana fad'in wash k'afata."
Hankalin kowa ya koma kansa anayi masa sannu,
Kuma marairacewa yayi yana fad'in "wash mommy k'afata, da sauri Abba ya shiga diba masa k'afar Wanda ba wani abu da yakeji gareta."
Sai da ya ga ya d'auke hankalin su gaba d'aya zuwa gareshi.
Sun mnta da maganar dijama snn ya sauke ajiyar zuciya ya mik'e tsaye yana d'ingisa k'afa ya nufi d'akinsa."
Kallo dijama ta bishi dashi tana mmki a gaban idontafa ya ture plate d'in abinci,
kuma bbu wani Abu da yasame shi a k'afarsa,
Tab tace lallai yaya khalil babba ne."
Zaka warke ka dawo ne."
Bayan ya wuce ne ya shiga d'akinsa kai tsaye akan gado ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya. Yana murmushin samun nasara ya tserewa tarkon dijama."
*GA WNN YA TAYAKU FIRAR DARE*
🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar Gidan tsohuwa_)😅
Writteng
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)
*29*
Murmushi yakeyi idan ya tunada dijama a lokacin da take cewa
In tona."
Sai ya tsinci kansa yana mai sakin dariya,
Ya mirgina a kan gadonsa tare da rungune pillow."
Tabbas ko ba'a fad'a masa ba yasan ya kamu da son dijama,
Wanda ita kuma yake ganin matsananciyar tsanarshi a idonta."
Dogon nishi yaja ya kuma rungume pillow yace "dole ki soni dijama domin ni nakine bakida wani miji a fad'in duniyar nan Wanda ya wuce ni,
Ni nakine ke tawace."
Yana cikin wnn tunanin bacci b'arawo yyi awon gaba dashi."
Tun daga lokacin wasan b'uya ta Shiga tsakaninsa da dijama,
Koda zasu fito break fast, 9:am har ya karya yayi tafiyarsa,
Darana kuma lokacin da zaici abincinsa har suntafi makarantar islamiya, da dare sai bayan ya tabbatar da sun shige yake shigowa yaci abinsa yayi tafiyarsa."
Gudun kar su had'o da dijama ta tona masa asiri a gaban Abba da mommy, kamar ynda tace."
Hakan sukaci gaba da yi da ita har zuwa lokacin da hutyn makarantar su ya k'ara zata koma."
Duk wani shige da ficinta a kan idonsa takeyinsa yana kalllonta wani Abu idan tayi shi yayi dariya wani kuma ta yaji ta kuma Shiga ransa."
Yana lissafe da hutun makarantar ta ya k'are, lokacin da ya taso daga makaranta ya biyo ta wani katafaren store yayi mata siyayyar kayan makaranta masu yawa ya shigo dasu,
A lokacin Mahmud ya turo yaronsa da siyayyar duk wani Abun da yasan tana buk'ata ya saya mata."
D'an Aiken yana fita kenan,
Khalil ya tsaya da motarsa ya shiga jido kaya yana shigowa dasu."
Ido Abba da mommy suka bishi dashi cike da mmki basuyi masa maganaba sai da ya gama shigowa da kayan gaba d'aya snn ya nemi wuri ya zauna a kusa da mommy yana fad'in wash nagaji da yawa."
Suka bishi da ido cike da a yar tambaya???"
Sai da ya natsu snn Abba ya kalleshi ya nuna kayan da ya ajiye tsibi guda, yace "wa d'an nan kayan fa na meye?"
Khalil yayi murmushi yace "Abba Nana khadija. na sayomawa." kasan cewar hakan yake kiranta yanxun ya tsani a kirata da dijamar nan,
Yaci gaba da cewa domin ina lissafe da gobe ne suke komawa makaranta."
Abba ya kalleshi da kyau yace Ummie ta gode amma sai dai kayi hak'uri anrigaka."
"Meye aka rigani Abba?"
Ina nufin ka kwashi kayanka kaje ka mayar dasu a inda kasawosu domin kuwa Mahmud ya rigaka, babu abunda bai sawo ya turo akawo mata taba kamar yanda ya saba a koda yaushe.
Ba kamar kai daka tsira ynxun da rana tsaka."
Khalil bazan gaji da fad'a maka a kan kacire Abunda kakeso ka fito dashi a rana tsakar nan ba."
Dan haka ka kwashi kayanka ka mayar dasu a inda kafito dasu,
Ya fahimci inda maganar Abba ta nufa. Ransa ya b'aci amma kuma ya danne yace "Abba wai menayi?" Naga kamar duk an tsaneni a gidan nan?"
Sai a lokacin mommy tayi magana tace "khalil kazo ka dakemu kawai ka huta."
Tunda har tambayar abunda kayi kakeyi, ai ina ganin kafi kowa sanin Abunda ke cikin ranka Wanda bazai tab'a yiyuwaba,
Dan Allah malam tashi ka kwashe mana kayan nan naka wad'anda suka tare mana filin wuri kasan inda dare yayi maka dasu."
Jiki ba kwari ya mik'e tsaye cike da b'acin rai idonshi ya rikid'e zuwa launin ja."
Yashiga kwasar kayansa yana xubawa a mota."
Washe gari, dijama ta kammala shirinta cikin uniform ta fito sukayi sallama da mommy, da fateema."
Abba da kansa ya d'auketa ya nufi mkranta da ita."
Bayan sun wuce ne khalil ya fito cikin da kakkiyar shadda 'yar ubansu sai k'amshi yake zubawa, ya durk'usa har k'asa ya gaida mommy, snn yace "Nana khadija tafito muwuce kawai na shirya."
Mommy ta kallesa da kyau tayi murmushi irin nasu na manya tace " ai tuni Abbanku ya tafi wurin kaita."
Saurin d'aga kai yyi ka kalli mommy Wanda itama shi take kallo, ganin b'acin rai a fuskarsa ta zaro ido tace "meyafaru ne Khalil?"
"Ba komai yace had'ida mik'ewa tsaye jiki ba kwari yace "natafi makaranta."
Mommy tace break fast d'inkafa?"
D'an juyowa yyi yace "banajin yunwa idan naje can zansamu wani Abun da zanci."
"To Allah ya bada sa'a inji mommy ta bishi da kallo tana tausayin d'an nata."
**************
A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah. Yau ne ake bikin rantsar dasu mahmud a aikin soja."
In da sun kammala trening d'insu cikin nasara da taimakon Allah tare da sanya hannun Alhaji Atiku Mahmud ya fito da babban muk'ami."
Bikin rantsar dasu akeyi a garin Abuja inda aka tara manya mutane shuwa gabanni da 'yan siyasa domin shaidarwa."
Abba da mommy da khalil da fateema duk Suna wurin a zazzaune inda suke hango Mahmud zaune cikin uniform d'in soja wad'anda suka yi mashi masifar kyau sai kallonsu yakeyi yana murmushi farin ciki."
Gefensa d'aya kuma sulaiman ne, shima zaune yana hango matarsa da d'ansa yana aika masu da murmushi."
Kiran sunansu akeyi d'aya bayan d'aya, ana rantsar dasu tare da fad'in muk'amin su a kuma basu ta kardar shaida."
Abba yana tare da Abokinsa Alhaji Atiku suna fira sai godiya yake masa."
Shuru Abba yayi saka makon sunan Mahumd da yaji ana kiran tare da muk'amin da yaji ba'a kira kowa dashiba,
Ya kuma kashe kunne domin ya k'arajin abunda ake fad'i."
_"CAPTAIN MAHMUD HASSAN TOFA_ yaji ana fad'i, sai ganin Mahmud yayi ya taso yana murmushi aka Shiga rantsar dashi."
Abba bai San lokacin da ya rungume Alhaji Atiku ba sai godiya yake masa, domin duk matakin da yaga Mahmud ya taka dasa hannun Shi a ciki."
Alhaji Atiku yace "ka daina yimun godiya mahmud d'ana ne. Babu abunda bazan iya yimasa a rayuwa ba"
Idan ina da rai da lafiya mahmud sai ya hau kujerar da nake kai a yanxun ta commondent general."
Abba yaji dd'i sosai har yakejin a rayuwa babu abunda ba zai iya yiwa Alhaji Atiku ba."
Hkan dai akayita rantsar dasu, d'aya bayan d'aya, snn daga k'arshe aka sallamesu da cewa kowa yatafi gida sai nan da wata d'aya idan kud'insu suka fito za'ayi posting d'insu wurin da zasu fara aiki, domin su fara yiwa k'asa aikinta."
Gidan Alhaji Atiku su Abba suka nufa, gaba d'ayansu,
A inda aka shirya masu liyafa kala kala, cikin karamci."
hakan suka taru gaba d'aya har Alhaji Atiku da matarsa suka shiga cin abincin."
Abba ya duba baiga yusra ba ya dubi Alhaji Atiku yace "Alhaji Atiku wai ni ina 'yata ne yusra bngantaba?"
tun a can nakeson na tambayeka hankalina ne ya d'auku."
Dariya Alhaji Atiku yyi yace 'ai Shalele ta tafi England wurin hutawa, .d'azun da muke waya da ita nake gaya mata yau ne ake bikin rantsar da yayanta Mahmud rigima ta sanyamun tana kuka wai meyasa ban fad'a mata ba, domin ta shiryawa mahmud kyautar da zata bashi domin tayashi murna."
Abba yace "gskya ba'a kyautawa yusra ba mutum da yayanshi."
Suka Sanya dariya gaba d'ayansu."
Mahmud bai kulasu ba sai cin abincinsa yakeyi Wanda yakejinsa kamar yana cin magani."
Domin gaba d'aya ya tsani Alhaji Atiku da duk wani Abu da yafito daga gareshi sboda yafiya son kansa da yawa."
Hakan suka kammala cin abincin ko wannensu ya mik'e tsaye had'ida yi masu sallama, Abba sai godiya kawai yake tare da mommy suka fito."
Motar Khalil Abba yashiga tare da mommy,
Khalil kuma ya shiga motar mahmud tare da fateema da mahmud d'in gaba d'aya suka d'auki hanyar kano."
K'arfe goman dare suka sauka garin kano,
Gaba d'ayansu ko wannensu a gajiye yake."
Suna sauka kai tsaye ko wanensu ya nufi b'angarensa domin ya watsa ruwa ya huta."
Mahmud yana shiga d'akinsa kai tsaye toilet yashiga yayi wanka yafito ya shinfid'a abar sallah yayi sallah sann ya fad'a kan gadonsa ya kwanta tare da sauke ajiyar zuciya, babu abunda ya fad'o masa a rai a dai dai wnn lokacin sai dijamah."
Murmushi yayi domin shi kansa ya so ya ganta, yga ynda ta koma Allah yasa dai tayi hankali ta kuma daina rashin ji."
Da tunani gobe idan Allah ya tashesu lfy zaije har mkrantar ya kaimata ziyara."