← Book details Sugar Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 43

Sashe 41

Sugar Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aharabar gidan sukayi perking dukkansu fitowa sukayi shaheed maƙale da jannat ɗin, sallama sukayi suka shiga parlor inda suka samu duk wani me alaƙa da wasu yazo daga family abbeyn dady ƙarami harna abba na gwaggo Ubaidah, dana dady, se baba malam da inna wuru,,,,da kallo duk aka bisu har suka samu wuri suka zauna fuska kowa zaka kallah babu daɗi sabida duk sunji abinda ke faruwa...bayan sun zauna ne suka shiga gaisarda iyayensu, inda sukuwa suke yiwa jannat yajikinta....baba malam kuwa da kallo kawai yake binsu har seda yaji kowa yayi shiru tukkunna ya kalli hafees yace "ina ita lubnah? Kanshi aƙasa yace jami'an tsaro suntafi da ita. Jinjina ƙanshi kana ya kalli abba yace "abbansu kaje kafito da ita kabawa jami'an haƙuri domin wannan matsalar cikin gidace. "Cikin girmamawa abba yace "to malam daga hakan ya Miƙe tareda riƙo hannun Yusuf yace suje dady ma da sauri yamiƙe yabi bayansu amma abbeyn dady ƙarami ko motsawa daga inda yake beyiba domin ji yakeyi inama ze iya tariyo baya dayasaka anzubarda cikin lubnah tun kafin ahaifeta tazamewa ahalinsu guba cikin rayuwa, to innayi ma tunanin datakeyi kenan domin kamar tahaɗiye zuciya takeji azaunen datake...ahakan kowa yayi shiru ana jiran dawowar su abba.

Kusan awa ɗaya da rabi da tafiyarsu basu dawoba har su hafees nashirin bin bayansu tukkunna suka shigo Yusuf agaba lubnah na biye dashi abaya duk tafita kamanninta sabida dukan datasha agun hafees gaya ko acan seda tasha maruka agun wani jami'in tsaro me shegiyar zuciya.

Wuri tasamu tazauna can makure nesa dasu kaɗan kowa awurin da kallo yabita amma Banda iyayenta da adda murja...shi kuwa baba malam gyaran murya yayi kana yace.

"Abubuwa marasa daɗi sunfaru acikin ahalina wanda nida iyayenku bamusan tushen faruwar abinba amma yanzu abba abinda nakeson sani akan tabbaci shine shin dagaske ne me sunana kasaki matarka kuma saki ukku? Yatambaya yana kallon shaheed..shi kuwa ƙasa yayi dakanshi dudda cewar yatsani lubnah iya tsanuwa amma bayada muradin yimata sakin tozalci irin hakan kodan darajar iyayensu dakuma amininshi kuma ɗan uwanshi hafees sedai ƙaddara tariga fata domin shi kanshi besan ya akayiba yasaketa. "Badakai ake magana bane kayiwa mutane banza? Yatsinkayo muryar dady cikin faɗa domin kowannensu yanzu ne zafin sakin kedawo musu ƙasa.

Da sauri yaɗago yana kallon mahaifin nashi cikin rawar murya yace "eh eh hakane nayi sakin...jinjina kai baba malam yayi kana yace wani laifin tayima harka yanke wannan hukuncin? Yasakejin tambayar abazata. Nisawa yayi kana yace "nima bansan abinda tayimin baba malam kawai da kallimar saki nafar lokacinda buɗe idona a asibiti. "Cikin tsawa dady yace wannan wanne irin zancen banzane shaheed? Karka maidamu ƙananun mutane mana ko akwai sa'arka acikinmu? Kokuwa kallon kakeyi wasan yara mukazoyi? "Ya isa hakan plesse kabarshi yayi bayani atsanake, cewar abba...shi kuwa baba malam cewa yayi "asibiti kuma ? Mikajeyi asibiti? Kafin wani yayi magana hafees yamiƙe cikin ƙunar rai yace "baba malam nine wanda zanbaka wannan amsar domin nasan dayawa daga cikin abinda kukeso kusani wanda wanima shi kanshi shead besanshiba. Nisawayayi kana yacigaba da faɗar "ranarda shaheed ya kwanta asibitin bazan taɓa mantawaba ina gida yakirani da sassafe akan naje school ɗin su jannat na ɗauko mishi ita, alokacin nayi mugun mamaki domin bejima da kaitaba, sedai a yadda najishi kamar wanda keshirin barin duniya yasa naje da sauri naɗauko ta ɗin kamar yadda ya buƙata, sedai bayan nakawota nayi danasani marar adadi dubada abinda yayi mata dudda cewar matsrshi ce amma ganin baya cikin hankalin kanshi kuma ga jannat ɗin karamar yarinya shine abinda yaƙara tada nawa hankalin Bashiri dole na nemi ghaisha ananne fa ku ɗauke su dashi har ita kamar gawa muka kaisu asibiti, shine lokacinda yafarka yayiwa lubnah wannan sakin,,,,nikuwa naje gun doctor ɗin daya dubashi ananne yake gayamin yasha wani abinne me mugun haɗari wanda ya haddasa masa wannan abin da ace besamu maganin matsalarba to tabbas ze iya rasa rayuwarshi....nayi mugun mamaki matuƙajin wannan bayanan hakan yasa nakoma gidanshi inda na ɗebo duk nau'in abinci dana ganin akan dining, nakawowa doctor domin abincikamin abinda ke ɗauke da wannan muguwar gubar? Cikin kuma sa'a aka samu aciki, hankalina yayi mummunan tashi amma ban gayawa kowa ba illa shi dana tambaya daga pert ɗin ghaisha aka kawo musu abinci ko matanshine suka dafa, shine yacemin lubnah ce tabashi abincin, kuma tun Kaita gidan bata taɓa dafa mishi wani abinba se a wannan ranar, wlh shine dalilin dayasa nake zarginta, segaya kuma yau ba'aje ko inaba matarda tagayawa shaheed inda jannat take muka bibiye wayarta har muka samosu, nasamu wasu mahimman bayanai akan cewar tabbas lubnah ce tasiyawa kanta saki da hannunta agun shaheed sabida mugun hali irin nata da mummunar zuciya bara kuji kuma da kunnenku, yaƙarasa zancen yana fidda wayar feenah wadda yatsinta alokacinda ze fito daga gidan. Dukkansu kallonshi kawai sukeyi anrasa wanda zece wani abun harya kunna voice ɗin feenah dakuma lubnah inda muryarta tafito ɓaro ɓaro tana faɗar....!

Autar alheri ✍️

*SHUGER DADY*

🥳💋💋💓💋💋🥳
Beautiful and special love💔👄

Romantic love and....🤭😚🙈

Book 4

Page 79 & 80

"Tana faɗar, nidai sokawai nakeyi arabasu yayi mata saki ukku kuma arufewa kowa baki kar wanda yayi magana akan sakin...dariyar boka sukaji yana cewa, angama da wannan babin ƙarbi wannan keji kisan yadda kikayi yasha matsananciyar sha'awa zata tasomai seya kwanta dake daga lokacinda ya kwanta dake yana tashi zemata saki ukku, wannan kuwa turaren shi zakiyi ba wanda zetaɓa ta zancen sakin shikenan angama da wannan matsalar to amma kisani idan kika kuskure duk abinda yafaru kece kikaja. "Bama abinda zefaru, cewar lubnah daganan voice ɗin yaƙare...sekuma inda feenah kecewa na'ajiye muku wannan voice ɗinne domin yazama sheda gun wanke shaheed domin yanzu daga gun bokan dayayi aikin nake nasaka yabuɗe bakin kowa kamar yadda yarufe,,,shiyasa nasanar daku inda jannat take, ni ƙawar lubnah ce ta amana dudda cewar nayimata halacci amma taci amanata ta hanyar kwacemun saurayina kuma abin sona shiyasa itama nayi mata domin taji idan da daɗi wanda kabawa amana yaci amanarka, lubnah idan kinji wannan saƙon to feenah ce karkiyi kokwanto inaso kiji yadda najine rabani da bashh dakikayi, bissalam..kit hafees yakashe wayar yana jifanta dawani wulaƙan taccen kallo me ɗauke da muguwar tsana acikin ƙwayar idonshi,,,, jannat kam kuka takeyi sosai aranta tana ayyana mitayiwa anty lubnah ta tsaneta hakan....sukuwa iyayen gabaki ɗaya kowa yayi mutuwar zaune inbanda salati babu abinda sukeyi, suna cikin wannan halinne sukaji ihun lubnah cikin tashin hankali duk suka jiyo dan ganin Mike faruwa,,,,abbeyn dady ƙarami ne ke dukanta ta ƙarfinshi yanayi yana huci kamar wani zaki jiyakeyi inama ze iya kisan kai Allah da yau ya kashe lubnah har lahira...abba ne yamiƙe cikin tsawa yake faɗar "miye hakan bakada hankaline kasheta kakesonyine kome? Da sauri innayi tace "wlh garama yakasheta dan Allah yaya kabarshi yarage mugun iri ko da kowa ze huta da baƙin cikinta...abba ko sauraren ta beyiba yaƙaɓe lubnah daga hannunshi wadda saura kaɗan ta suma, da kyar abbey ya haƙura yabarta amma da zimmar idan suka koma gida zata sani...gyaran murya baba malam yayi kana yace "lubnah kinji duk bayanan da ɗan uwanki yayi inaso ki tabbatarmin da gaskiyar abinda yake faɗa da bakinki.

Lubnah kam izuwa yanzu tagama sadaƙarwa babu wurin kariya hakan yasa doli tafara basu labarin duk abinda yafaru da kanta kana taƙara dacewa amma wlh duk abinda ta aikata yaya shaheed ne sila domin betaɓa sauke hakkinta na aure dake kanshi ba ita kuwa shiyasa har take aminta dasu Dr bilal da aurenta. Wani irin mari innayi ta tsunka mata seda bakinta yafashe dajini, cikin takaici tace kin cuci kanki lubnah domin bawani kika cuta wlh nibazan yimiki baki ba domin ko wannan bala'in dakike ɗauke dashi ya isheki...da sauri dady yace karki ƙara dukanta plesse aiga wanda yadace adakanan, domin minene hujjarshi daza'akai mishi mata yazuba mata ido kallonta muka kaima kayi wlh danasan abinda ke tsakaninka da matarka kenan dabazan aurama jannat ba. Abba ne ya zaunarda dady daya muƙe tsaye yana kora bayanai,,,kana ya kalli shaheed ɗin yace "miyasa ka aikata hakan babana? Ƙasa shaheed yayi da kanshi kana yace "bazan iya faɗa ba abba domin nayiwa kaina alƙawarin bawanda zeji zancen abakina, amma itada tace nayi mata hakan sitasan dalili tafaɗa mana domin ɓoye nata laifinne tayi tafaɗa muku nawa kawai.
Chapter 41 · 0% Book details