← Book details Sugar Daddy Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 43

Sashe 39

Sugar Daddy Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gudu sosai shaheed Allah ne kawai yakawosu gidan lafiya, kallon Habib, shiko yaɗaga mishi kai alamar nanne inda wayar dasuke bibiya take...ɓalle marfin motar yayi yafice izuwa cikin gidan dasauri Habib yamara mishi baya, tura ƙofar parlor yayi yashiga daƙarfi, Hakan yasa lubnah dake jikin bashh daga ita harshi suka ɗago dasauri suna duban ƙofar, "innalillahi wa'innailaihiraji'un shine abinda yafito daga bakin Habib yana kauce idonshi domin dukkansu bakomai ajikinsu ga hannayenshi akan breast ɗinta ita kuwa hannunta akan hajiyarshi... shaheed kuwa tunda ya ɗauke kanshi bekoma kallon inda sukeba yashiga buɗe dakunan dake cikin parlor.....arazane lubnah tamiƙe tsaye jikina rawa take faɗar "yaya Habib. Shidai kanshi na ƙasa bece komaiba. "Suwaye ku? Miyasa zaku shigomin gida babu neman izini? Cewar bashh cikin fishi yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, wani mugun naushi Habib yakai mishi cikin ƙunar rai ganinshi tareda ƙanwarsu kuma a irin wannan yanayin kuma yazo yana musu wasu tambayoyin iskanci...ƙasa yasaki yana duƙewa kafin Shima yaɗago danufin ramawa nanfa dambe yaraure tsakaninsu, akuma dede wannan lokaci hafees yaƙaraso gidan tareda motar Police. Kaitsaye parlor gidan suka nufa ganin yadda Habib kedambe da bashh duk ya canza mishi kamanni kuma gashi tsirara yasa yansanda sauri rabasu, wani daga ciki yajefawa bashh boxes ɗin dayagani tsakiyar parlor. Wani irin ihu lubnah tasaki me masifar razanarwa saka makom dukan da hafees kemata kamar yasamu tsaranshi cikin mugun baƙin ciki, gata tsirara agaban manyan ƙarti maza kumawai ƙanwarshi uwa ɗaya uba ɗaya jiyakeyi kamar yakasheta Dan baƙin ciki...domin tunda tayi ido huɗu da Habib tadiririce shiyasa takasa suturta kanta har hafees yasameta ahakan.

Sam babu wanda yayi Yunƙurin hanashi dukanta domin tuni police sun tasa ƙeyar bashh agaba, Habib kuwa yana tsaye kawai yaduƙarda kanshi aƙasa.... shaheed kuwa tunda yaduba dakunan dake parlor bega jannat ɗinshi ba ya dawo yayi tsaye tareda haɗe hannayenshi a ƙirji yana kallon yadda hafees ke kirɓarta kamar Allah ya aikoshi, ganin tana neman mutuwane yasashi ƙarasawa tareda riƙe hafees ɗin yana girgiza mai kanshi, cikin dasasshiyar murya yace "barta Hakan bro karta mutu bata fitomin da matataba, yayi maganar idonshi na cikowa da ƙwallah. Wani mugun kallo hafees watsa mata Shima idonshi tab da hawaye yace "ai gara tamutu bro domin koba komai zamu rage bara gurbi acikin zuri'armu wlh natsaneki lubnah nayi baƙin cikin kasancewarki ƙanwa agareni, kuma nayi baƙin cikin fitowarki a tsatso mekyau domin idan mukayi wasa kece Zaki zamo ajalin Abbey da innayi, da sauri Habib yarufe mishi baki....shikuwa shaheed rantse idonshi yayi da azabar ƙarfi kafin yakoma buɗesu akanta, cikin tsana yace "tambaya ɗaya zammiki karki bari na maimaita Miki ita? Ina matata? Yafaɗa babu wasu ataredashi,,,,Dasauri tashiga nuna mishi wata ƙofar dake cikin wani lungu bayan TV, ƙofar yanufa tareda murza key ɗin dake jikin ƙofar aiko seta buɗe, ɗakin dulun yake babu haske dalalabe yakunna hasken ɗakin inda ya hankota jan jikin gadon andaureta da igiya tareda kan gadon...wani irin kukane yazo mishi dasauri yaƙarasa gunta yana faɗar Sunanta hankali atashe? "My jannahh my jannah kitashi uncle shead ɗinkine kitashi jannah ta nine nazo gareki please karki barni dan Allah my jannah tashi kigayamin misuka Miki? Yafaɗa lokacinda yagama banyeta yana tallabota jikinshi... ahankali taware dara daran idanuwanta akanshi, dishi dishi take ganinshi Hakan yasa tabuɗe baki ahankali tace "uncle shead naa sekuma tayi baya luuu tasome ajikinshi...wata irin zabura yayi tareda fitowa dagudu yana kiran sunanta, ganin yadda yafito ɗauke da itane yasa su hafees duka mara mishi baya mota yasakata kana yayiwa motar key, dasauri Habib yariƙe hannunshi tareda ciwa koma baya kazauna da ita bro bara nayi driving ɗin, domin ganin yayi sam shaheed ɗin baya cikin nutsuwarshi....beyi musuba yafito dasauri yakoma bayan, Hakan suka nufi hospital kamar zasu tashi sama, motar hafees nabiye dasu abaya..... lubnah kuwa wata police ce mace tasakata agaba seda tasuturta jikinta tukkunna itama suka tasa ƙeyarta agaba zuwa office ɗinsu......a hospital kuwa Habib nayin Perkin shaheed yaɓalle marfin motar yafito ɗauke da ita da gudu yayi cikin asibitin suka maramai baya,,,wasu doctor's naganinsu sukayi saurin karɓarta tareda nufar emergency room da ita cikin sauri suka shiga bata temakon gaggawa...!

Autar alheri ✍️
*SHUGER DADY*

🥳💋💋💓💋💋🥳
Beautiful and special love💔👄

Romantic love and....🤭😚🙈

Book 4

Page 75 & 76

"Dukkan tsaye suke bakin emergency ɗin suna Safa da marwa yayinda shaheed yagame kanshi da guywarshi yana fitarda wani irin iska me zafin gaske...Sunanan zaune kamar haɗin baki sega dady da ghaisha Anty Habibah, harun, Yusif, sun iso sabida kiranda hafees yayiwa dady yasanar dashi anga jannat, kozama basuyuba Sega abbeyn dady ƙarami da innayi, zainab, Rukayya da dady ƙarami, gidan abba ma hakan suka garzayo dukkansu harma da gwaggo Ubaidah, abban jannat ma yazo amma adda murja batazoba, kafin kace me, a asibitin tacika da family, duk wanda yazo abu ɗaya yake tambaya ina jannat ɗin ta kuma a ina suka sameta? Amma ba mebasu amsa, daga hafees har Habib, domin shi shaheed ko ɗagoda kanshi beyiba haryanzu, kuma babu wani labari daga likitocin.

Abba ne yazo wurinda yake yazauna kusanshi tareda ɗagowa dashi yana faɗar "babana, tashi mana kaida yadace kayi murna matarka ta bayyana shine kuma kake ƙunci...kasa ƙarasawa yayi sabida ganin yadda idon shaheed ɗin sukayi jajir kamar wuta bakinshi se rawa yakeyi kamar mejin ɗari. "Lafiya babana? Wai ko wani mummunan abu yasamu jannat ɗinne? Tambaya cikin tashin hankali. Kukanda kecinshine tunɗazu besamu yayiba yazo mishi aiko yafashe da kukanda duk wanda ke wurin seda hankalinshi yatashi, kafin yafara magana cikin muryar kuka yake faɗar "sun kashe mun mata abba sun kasheta, abba miye laifin jannat dasu yimata wannan mummunan hukuncin ɗauke da tsohon ciki ko tausayin lalurarta babu? Abba mita aikata agaresu? Dan kawai tace tana sona shine tazama abin tsana da ƙiyayar da harzata saka anemi rayuwarta? Yafaɗa muryar shi na dishewa, kafin yaja nunfashi da ƙarfi yace "narantse da ismul'a a zamu abba duk narasa matata kowani mummunan abun yasameta wlh itama sena kasheta senasaka tayi nadamar rayuwarta sena zame mata darasin daseta tsani rayuwa da mutuwa, wlh abba setayi danasanin haɗa jini dani balle tayi tunanin akwai wata alaƙar data shiga tsakaninmu, yaƙarasa zancen cikin wani irin matsanancin kuka....innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shine kawai abinda duk wanda ke wurin ke maimaitawa domin dayawansu sun fara hasashen wayake duni sabida sanin halinta mummunan iyayenta dayawa kuma kansu ya ƙulle.

"Wai miyake faruwa ne? Habib kuyimana bayani mana kunbarmu acin duhu, cewar dady cikin hasala domin shine kawai yasamu zarafin yin magana acikinsu....dady nizangayama abinda yafaru, hafees yafaɗa tareda share ƙwallar idonshi....da sauri Habib yace "no bro kabar wannan zancen plesse anyishi yawuce...cikin tsawa hafees yace "yawuce aina bayan kana ganin halinda ɗan uwanmu keciki shida matarsa, ai wlh kowa seyaji mummunan abinda ta aikata koda zasu bamu damar hukuntata yadda yadace, daga nan yashiga bawasu labarin abinda yafaru tun lokacinda aka turowa shaheed text harkawo yanzu dasuke asibitin batareda yajira komaiba, seda yadasa aya shima yashiga rera nashi kukan cikin baƙin cikin abinda ƴar uwar shi kuma jininshi ta aikata.

Tunda hafees yafara magana jikin inayi kerawa kamar mazari seda su ghaisha suka zaunar da ita,,,,wani irin tashin hankali ne yamamaye dukkan iyayen nasu, kowa ka kallah kasan yana cikin mugun tashin hankali...dady ne yayi ƙarfin halin cewa komami lubnah tayi shaheed tafika gaskiya domin kuwa kaima da naka kaifin narasa mima yarufe mana ido muka kasa hukuntaka akan zaluncin dakayi mata sabida hakan dukkanmu munada hannu akan abinda lubnah tayi dudda bata kyautaba. "Wacce irin magana ce kakeyi yaya? Wani zaluncin aka mata dazata koma ƴar ta addar ƙarfi dayaji? Haba karka danne laifin mai laifi kaɗorawa wanda aka zalunta dan kawai ɓoye laifin wancan plesse. Abbeyn dady ƙarami yafaɗa cikin takaici....da sauri dady yace "anzalubceta mana kar ɓacin rai yasa kakasa ganin rashin adilcin damuka mata dukkanmu fa agabanmu yayi mata saki ukku ko kunyar idanunmu bejiba kuma bebar wata kafa daza'a iya gyara aurenba hakama dukkanmu ba wanda yace komai balle yayi yunƙurin bimata hakkinta, tayaya yanzu za'ace ahukuntata bayan shi ba'ayimasa hukunciba....jin abinda dady ke faɗa ne yasa hafees saurin bashi amsa cikin kuka yake faɗar "wlh Allah dady kowannan sakin da bro yayi mata danine najima dayimata gomanshi domin wlh batada mutunci babu abinda bata mishi har agabana nagani, kuma wannan sakin dayayi mata nasan baze wuce nasaba da maganin data bashi yashaba wanda yasa yatashi kashe jannat dakanshi Allah ne kawai yakawo sauƙin abin...dady zekomayin magana sukaji muryar baba malam abayansu domin tunda aka fara wannan bayanan yashigo mugun shuck ɗin daya shiga ne yahanashi cewa kasa magana seyanzu yace "ya isa zayyan kudena wannan zantuka hakan yanzu kubinciki lafiyar yarinyar da abinda ke cikinta, idan ta warke kuwa dukkanku kuda yaranku kusameni gida amma kufara tabbatar da tafiyarta tukkunna..."toh malam in sha Allah yadda kace hakan za'ayi, cewar abba da seyanzu yasamu zarafin yin magana....shikam baba malam juyawa yayi kawai yakoma yanajin kamar ze faɗi sabida tashin hankali, wannan bala'in acikin ahalinshi, Allah yakawo sauƙin abin.

Dukkansu Sunanan zaune yakkwat babu wanda keda sukunin taɓuka wani abun,,, Yusif kuwa jiyakeyi inama zasu bashi lubnah, da babu abinda ze hana saɓa mata kamanni wlh domin shi dama mugun haushi take bashi, sallah ce kawai tafitar dasu daga abitin koda suka dawo sunsamu wani Dr yana nemansu,,,,da hanzarin su suka same shi. Cikin sakin fuska yace "jannat tafarka har sister maryam ta temaka mata tayi wanka dudda jikinta ba kwari tayi brush kuma har ankai mata abinci,,,sedai kuma firr yaƙici se famar kiran uncle shead takeyi, shine muke nemanshi domin Asamu taci wani abun. Ai beko ƙarasa faɗar abinda yake faɗa ba shaheed yafice daga office ɗin tareda nufar room ɗin datake...da kallo duk suka bishi kafin hafees yayi murmushi yana cewa doctor "koban gayama ba yanzu kaga waye uncle shead dan bema jira kagama zancenka yaje gun zuciyarshi,,,aiko duk sukayi murmushi tareda yiwa doctor godiya suka fito sedai babu wanda yayi yunƙurin binshi gun jannat ɗin.

Tura ƙofar yayi yashiga, zaune ya hangota atsakiyar godon tasaka kanta tsakanin cinyoyinta kobe tambayaba yansan kuka takeyi,,,,ƙarasa shiga yayi ciki sedai haryanzu bata ɗagoba sabida taɗauka ma aikatan asibitinne
Chapter 39 · 0% Book details