← Book details Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 14

Sashe 9

Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kuka ba shi ne abin yi ba yanzu, hasa lima banga amfanin yin sa ba."

Cikin sauri Lailah ta katse Afeefah da tayi wannan maganar da faÉ—in

"Yanzu idan bamu yi kukan tausayawa Anty Zaynerb ba, menene kike so muyi, na'am ki faÉ—a min?."

Ko kafin Afeefah ta bawa Lailah amsa, Haleesat ta rigata da faÉ—in

"Abin yi yanzu shi ne musan yadda za'ayi soyayyar su ta dawo..."

"Ban gane abin da kike nufi ba, Humm wai so kike kice mana, kina da yadda za'ayi Anty Zaynerb su ci gaba da Soyayya da wannan mayaudarin?."

Lailah ce tayiwa Haleesat É—in wannan tambayar cikin sauri. Ko kafin Haleesat ta nema amsar da zata bata, suka jiyo Muryar da basu yi tsammani ba, ta bayan yana faÉ—in

"Qwarai kuwa, tabbas abin da ya kamata ayi ke nan yanzu, musan yadda za'ayi soyayyar Zaynerb da shi Aasief yake ko wane?, ta ci gaba da gudana, saboda kwata kwata banma yadda wai shi É—in zai iya Yaudarar ta ba, duba da yadda ya nace ma ta da farko, da'ace cin Amana ko yaudara ne a zuciyar sa tabbas ba za suyi daÉ—ewan da suka yi a tare ba."

Maleek ne duk yake wannan maganar yayin da yake saukowa daga saman Staircase's na part nasa, sannan ya ƙari sa palon ya zauna daga gefan Afeefah saman 3sieter.

Ashe tun farkon fara karanta labarin soyayyar na Zaynerb da Lailah tayi yake tsaye daga saman Bene, tabbas yaji komai, kuma sannan har zuciyar sa bai yarda cewa Aasief yaci amanar Zaynerb ba.

"Tabbas nima ban yarda ba wallahi, duba da yadda ta rubuta labarin, cewa tayi fa wannan Leo yace yana son ta, sannan ita ma Erisha ce ko, ta ce tana son Aasief, idan kukayi duba da irin Abin da Zaynerb tayiwa Leo É—in a tsakiyar makarantar, gaban dubban É—alibai, da kuma irin rashin mutuncin da ta ce tayiwa ita Erisha É—in, Tabbas a tunanina zai iya kasancewa Leo da Erisha sun haÉ—a kai ne..."

"You are right sister Haleesat ni ma haka nake tunani."

Cewar Deejarh tana yunƙurin kuma cewa wani abu suka haɗa idanu da Maleek, da sauri tayi ƙasa da kanta tana rufe bakinta, ita fa wallahi waɗannan rikitattun idanun nasa tsoro suke ba.😁

"Duka kunce wani abu amma yanzu Menene abin yi?."

Fadeelah ce tayi maganar yanzu, duk da cewa ba wani shiri ne tsakanin ta da Zaynerb ɗin na azo a gani ba, amma wallahi sosai ta tausayawa Zaynerb jin wannan labarin nata a soyayya.💓

"Abin yi ɗaya ne yanzu, shi ne mu fara sanin Wanene shi Aasief, musan ƙasar da yake, musan su waye familyn sa, da komai nasa, sannan koma menene sai ya biyo baya."

Maleek ne ya faɗa hakan, don a tunanin sa hakan ne yafi kamata ayi cikin wannan taƙin da suke ciki.

Sannu a hankali Momy Rafi'at da ita ma taji kuma ta saurari komai na abin da ya faru da Zaynerb a soyayya, ta fara ja da baya, Allah Allah take ta koma sama, don bata fata wani daga cikin su ya fahimci taji komai.

Cikin zuciyar ta kuwa faÉ—i take.

"Ohoo Very very amazing, wai dama haka labarin soyayyar Zaynerb É—in ya kasance, lallai kuwa idan haka ne, sara ne yazo ma ta daidai da bakin gatarin ta..."

Da isar ta Bedroom bata tsaya jiran komai ba, ta lalubo lambar sa cikin sauri sauri ta danna masa kira, domin ya faÉ—a ma ta abin da ya kamata tayi, don kuwa kanta ya É—aure, ba za ta iya komai ba, sai da shawaran mutane ukun nan da ta yarda dasu sama da komai a duniyar ta.

A palo kuwa ci gaba suka yi da tattaunawa akan yadda zasu ɓullo wa al'amarin, sai dai sun yanke iya su zasuyi, Daddy ko Momy Rafi'at koma ita kanta Zaynerb ɗin, babu wanda a cikin su zai san da wannan nufi nasu.

Sosai suka tattauna da Yayan nasu Maleek akan al'amarin soyayyar na Zaynerb. Da yadda zasuyi komai ya koma daidai.

*KANO*
*STATE*

*Jiddarh Komai Naga*💃
💋*Sarauniyar kyau ta Kanawa*💋

Daga zaunen da take saman Dressing Mirror tana fesa daddaÉ—an turaren ta mai tsadar gaske, ta jiyo Muryar Auntie (Mrs Komai Naka) tana kwala ma ta kira ita da Humaira.

Cikin sauri ta mayar da kwalbar turaren ma'ajiyar sa, sannan ta fito daga Bedroom nata da sauri, saukowa Down tayi, kana ta ƙari sa wurin Auntie tana faɗin.

"Gani Auntie wannan kira haka, Allah ya sa dai lafiya?..."

Kallon Jiddarh Hajiya Jamila (Mrs Komai Naka) wato Auntie takeyi daga sama har ƙasa, dan da nan wani takaici ya ziyarci zuciyar ta, ƙiyayyar da take yiwa mahaifiyar Jiddarh ɗin ya dawo sabo fil cikin zuciyar ta. Ita fa ta tsani wannan Yarinya Jiddarh sama da komai a Duniyar ta, ace Yarinya sai shegen kyau kamar wata huru'in.

Dan ne abin da take ji, tayi kamar yadda ta saba a kullum.

Sai da ta saita nutsuwar ta, sannan ta fara magana cikin sakin fuska da dariya, nuna musu Magazine na Daily Just dake hannunta ta yi tana faÉ—in.

"Yarana Jiddarh da Humaira ku duba wannan abin farin ciki da ya samemu haka, wai fa Abban ku ne (Alhaji Jafar Komai Naka) shi ne Mai Arziƙi na Bakwai a Nijeriya, shi ne ya fito cikin jerin mutanen da sukafi kowa kuɗi a ƙasar nan fa..."

Cike da mamaki game da farin ciki Jiddarh ta washe baki kamar gonar auduga faÉ—i take.

"Lah lah Auntie wai da gaske kike Abba ne ya fito cikin jerin mutanen da suka fi kowa kuɗi a ƙasar nan, lallai dole yau musha shagali a gidan nan."

Tayi maganar tana karɓar magazine ɗin daga hannun Auntie ɗin don sake tabbatarwa.

Ita kuwa Humaira tsaban farin ciki kasa magana tayi, sai mamaki, huh Allah mai iko, mamaki take yaushe Abbansu ya yi dukiya haka?.

*Zaynerb Mai Kyau*🥰
💓*Queen Of Love*💓

Da sauri taja wani wannan burki sakamakon buguwar da motar su tayi da motar dake gaban su, kuma ita ce da laifi, dan kuwa juyawar da tayi tana yima su Mah'eesha da Haseeya da suke back seat zazzaune magana ne, yasa ta bugi motar gaban su ba tare da ta sani ba.

Ƙasa tayi da kanta gaban ta mugun bugu, Addu'a take Allah ya sa bata kaɓe kowa ba.

Sannu a hankali ta É—ago da kanta tana kallon titin.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buÉ—e murfin motar ta fito.

"Kuyi haƙuri Dan Allah ina mai baku haƙuri, akasi aka samu, na kusa buge motarrr...."

Kasa ƙari sa maganar tayi zuciyar ta na mugun bugu da sauri sauri sakamakon ganin mutumin da ya fito daga motar da tayiwa ɓanar tare da wasu Ƴan Mata biyu.

A yadda ya fito daga motar ransa a mugun ɓace, niyyar sa ya yi wa koma uban waye ya bugi motar sa, dukkan mutuwa.

Sai dai mai?....

Cak ya dakata daga ƙoƙarin ƙari sawa wurin da ya yi niyya.

Kamar ta tsaya cak tana bin sa da Kallon mamaki.

Toh shima Aasief a nasa ɓangaren haka abin yake.

Da farko kwata kwata bai gane wacece ba, har sai da ya kusa ƙari sawa dab da ita.

Sannan ne ya fahimci wacece, kuma ya gane ta.

Duk da cewa ta ƙara girma, tsayi, haske,da kyau, sai dai tana nan a yadda ya santa babu ƙiba.🙃

*After One Hour*

"Zaynerb! Zaynerb!! Wai bada ke nake magana ba, menene haka kike ƙoƙarin yi ne, Kawai tashi guda kice zaki koma Abuja da yamma nan, wai menene abin da ya faru, kuma Wanene wannan Mutumin ki faɗa min?."

Dakata wa Zaynerb tayi daga ƙoƙarin ta na cusa kayan ta cikin Akwati, sannan ta juyo tana kallon Mah'eesha da take ma ta tambayoyi, tana mai bata amsa da faɗin

"Eh tabbas Abuja zan koma, saboda bazan iya kwana da gari É—aya da wancan mayaudarin ba wallahi."

"Me kike nufi da mayaudari, kina nufin kice shi ne wanda kuka taɓa Soyayya da shi a ƙasar Amsterdam?."

"Yes, of course, shi fa."

Zaynab ta bata amsa, tana ci gaba da cusa kayan cikin Akwatin ta.

"Okay, Toh Menene da hakan dan ya kasance kun taɓa samun matsala da shi?."

Haseeya ce tayi maganar a yanzu.

"Oh ni Zaynerba wai bakuji menene abin da yake faÉ—a min ba, cewa fa yake ni ce da laifi bawai shi ba.... Kai!! wai mutumin da na ga mace a Room nasa, shi yake faÉ—a min baya da laifi. kuma kuna goyon bayan sa kukeyi ke nan?, lallai ma."

Maganar take cikin huci da ɓacin rai, sannan ta ci gaba da cewa

"Kuna dai gani É—azun a gaban ku komai ya faru, har wani Challenging yake bani kuji fa.
Wai sai dai dama can Burin Yaudarar sa nake, wai wata ƙila ni ce na shirya komai, kuji fa Mah'eesha... Na rantse yau babu mai hanani konawa Abuja da daren nan."

Ta ƙari sa maganar tana jan ƙaramin Akwatin ta sannan ta fito daga Bedroom ɗin, kai tsaye parking lot ta nufa, da yake Momy Suwaiba ba ta nan, shi ma Uncle Sagir bashi.

Biyo bayan ta Mah'eesha da Haseeya É—in sukayi, Haseeya tana faÉ—in

"Tun da kin matsa zaki koma, kiyi haƙuri mana kibi jirgi, kinsan tafiyar mota ba zai yiwu ba, saboda hanyar bata da kyau, baya da hakan Yamma ya yi sosai, yanzu fa 5:55pm kiyi haƙuri Zaynerb ki dawo."

Haseeya ta ƙarishe maganar cikin lallashi da son Zaynerb ɗin ta fahimce ta.

Duk yadda Haseeya da Mah'eesha harma da Mah'fuz da ya dawo gidan, ya tarar da abin da yake faruwa, duk yadda suka so Zaynerb tayi haƙuri ta bari, zuwa washe gari ta koma Abuja, ƙi tayi.

Zaynerb tana da mugun taurin kai sosai, ba'a sakata, ba'a hanata, duk lallashin da aka ma ta akan ta haƙura ƙi tayi.

Daga ƙarshe haka suna ji suna gani Zaynerb ta shiga Mota Driver yaja suka nufa hanyar Abuja da wannan Yammacin.

*Aasief Pov*

"Neelarh! Neelarh. Kina ina ne, ma za ki shirya yanzu yanzu zamu koma Abuja bazamu ƙara kwana a garin nan ba."
Chapter 9 · 0% Book details