← Book details Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 14

Sashe 7

Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin Wata ɗaya da zuwa ta ƙasar Amsterdam da kuma haɗuwa dashi sosai muka shaƙu da juna abin kamar almara, sai dai muna yawan samun matsala dashi akan zafin zuciyarsa, amma daga baya komai tsananin faɗan da muka yi muna dawowa mu shirya abin mu.

Sai dai har yanzu fama yake dani akan na furta masa ina san sa amma naƙi.

Yauma zaune nake saman table a cikin wani wurin shaƙatawa da kuma buga Troupe.(Wasan Tebur).

Kallon nake cikin Murmushi ina gyara riƙon da nayiwa Jakata a kafaɗa nake faɗa masa.

"Ka iya sarrafa fushin ka Aasief, hakan ba daidai bane ka dinga ɗaukar fushi akan ƙana nun Abu."

Nayi maganar ina juya fuska ta gefe tuno abin da ya faru yau da zamu shigo wurin, duka sosai yayima wani matashi akan yayimin kallon bariki.

"Nima banason wani abu ae."

Ya bani amsa yana daka tawa da abin da yake yi.

Da mamaki na saki baki ina kallon sa.

Shi kuma ya ci gaba cewa.

"Abin da kike yi ne, har yau da baki ce ki naso ba! Ah sam bana son hakan."

Murmushi nayi ina miƙe wa tsaye cikin gyara Jakata.

"Saurayi idan ya nuna ƙaunar sa a wurin Budurwa, ta ce saita tsaya tayi tunani kafin ta yanke hukunci, hakan yana nufin tuni ta amince, sai dai mu ce mun amince ne, sam bamayi."

"Me yasa?.".

Ya tambaya cikin sauri.

Murmushi na kuma yi.

"Irin daÉ—in da kuke ji idan mace ta mutu akan ku, toh muma irin daÉ—in muke ji, idan Namiji ya dinga bibiyar mu.
Humm.
Kasan irin jin kan da muke yi kuwa yayin da muka ga Namiji yana bibiyar mu, mu haka mata muke. Ka fahimta?..."

"Toh ke nan tun daÉ—e wa kika amince dani?."

Ya tambaya.

"Kana tan tama ne?."

Na basa ina juyawa zan wuce.
Fuskata É—auke murmushi na musamman cike da jindaÉ—i.

*Bayan Wani Lokaci.*

Shaƙuwa ce ta musamman mai zaman kanta ta ƙara shiga tsakanin na da Aasief Mai Waje, sai dai har lokacin bance da shi ina son sa ba, haka kuma yake haƙuri dani sosai, domin abin da nakeso yake yi komai wahalar sa kuwa.

Cikin Abokan karatu na da ma Æ´an makarantar mu sosai suka saba dashi saboda yawan zuwa makarantar wurina da yake yi.

Yau ma kamar kullum muna zaune ni da shi saman Benchi doguwa muna fira a cikin makarantar mu wurin hutawa.

Miƙe wa tsaye nayi cikin tsananin tashin hankali da tsoro, hango Tantiri a makarantar mu da nayi suna tahowa wurin da muke shi da abokan sa wajen su bakwai dukkanin su mabanbantan ƙasashe suke.
Leo Tantiri ne na ƙin ƙara wa a makarantar mu ya tara Laifuka akan sa babu adadi cikin makarantar, kuma babu abin da ake iya masa sakamakon kuɗaɗen da iyayen sa suke dashi.

Asalin sa ɗan ƙasar ne, cikin Tantiran Abokan sa akwai Rahul ɗan ƙasar India, akwai Indivisi ɗan Poland da dai sauransu, suna tsula tsiyar su yadda suke so, babu mai taka musu burki.

A haukar sa Leo ɗin wai sona yake tun ganin da yayimin na farko a makarantar yake bibiyata, ban taɓa kulasa ba, kuma ban faɗa wa Aasief ba sanin irin zuciyar sa.
Kuma duk zuwa makarantar da Aasief yake basu taɓa haɗuwa da Leo ɗin ba.

Gashi yau komai ya rincaɓe Leo ya ganni da Aasief ban san menene zai biyo gaba ba.😓

Ƙari sowa wurin sukayi ja-ja-yen idanun sa akaina, nima nawa akansa, yayin da na Aasief idanun sa suke akan mu duka cike da mamaki.

Karɓar wani abu kamar gyalle kamar igiya siriri ya yi daga hannun Rahul, sannan ya miƙo min yana faɗin.

"Karɓa wannan."

Karɓa nayi da mamakin menene abin.

"Kin san wacce rana ce gobe?."
ya tambaya

A'a
Na basa amsa, ya ci gaba da cewa

"Ranar shagalin raki ce, bisa al'adar Indiyawan nan makarantar kowa a yau yake shagalin sa Saboda haka karɓi wannan ki ɗaurawa mai."

"A'a."

Na basa amsa.

"Ki É—aura mai."

Ya kuma faÉ—a
"A'a."
Nima na kuma faÉ—a in seriously

Tsawa ya buga min da faÉ—in

"Ke ba haka nace ki É—aura masa ba?."

Je far da abin da ya kira da raki ɗin nayi ƙasa ina basa amsa da faɗi cikin tsawa.

"Nima ba nace a'a ba."

Tsayawa kowa daga ɗaliban makarantar ya yi da Abin da yake yi suka mimmiƙe tsaye suna kallon mu.

Kallon kallo muke tsakanin Ni da Leo sannan na fara magana cikin É—a ga murya.

"Zan iya kiran ka da Yaya."

Na nuna sa, sannan na ci gaba.

"Na kira wannan, na kuma kira wancan, zan iya kiran ko wani Namiji da Yaya a makarantar nan, amma banda shi, saboda Ina Son Sa..."

Juyawa nayi ina kallon Aasief dake sakin ƙayataccen Murmushi na jindaɗi sannan ta ce ina kallon cikin idanun sa

"Aasief Ina Son Ka, da duka zuciya kuma zan Aure ka."

Juyawa nayi na kama hanya nabar wurin fuskata a É—aure tamau.

"Ke Kyakkyawa ta nima Ina San Ki!!."

Murmushi nayi ba tare dana juyawa ba.

Kallon gargaÉ—i kawai Aasief yake bin Leo da tawagarsa dashi yana karkaÉ—a hannu.

Sannan cikin sauri ya biyo baya na cike da jindaɗi, yau dai na faɗa Ina San sa cikin tsakiyar makaranta gaban dubbanin ɗalibai.💃💃

*Zaynerb 💓 Aasief 🤙*

Tun daga wannan Ranar wannan lokaci cikin wannan taƙin.

Salon rayuwata da na masoyina Aasief ya canza.
Dan kuwa wani irin so da ƙauna mara misaltawa muke yi wa junan mu, abin kamar almara.

*One Month Later*

Yauma tsaye nake gefan titi ina jirar ƙari sowar Bus da zata kaini zuwa paint class da yake bani lecture Ranar.

Sanye nake da Doguwar riga da kuma wando irin dai na Pakistan nayi rolling kaina da mayafin rigar, sosai nayi kyau, ina saɓe da handbag ɗi ta.

Gefana kuwa mutumin nawa ne tsaye shima sanye cikin t-shirt da wando jeans ya saka p-cap idanun sa rufe da glass hannayen sa cikin aljihun wandon sa.

"Idan kin kammala ƙare min kallon ki matsa gefe."

Saurin kawar da kaina gefe nayi jin abin da yace ashe yana lura dani.

"Gefe kuma saboda me?."

Na tambaya da mamaki.

"Ke dai ki matsa nace idan kuma ba haka ba, Karki zarge ni da koma miye ya biyo baya aha."

Dariya nayi sannan kuma ban matsa ba, don ni kaina nasan ina da mugun taurin kai.

"Tabbas idan baki matsa gefe ba zaki sumba ce ni a wannan taƙin."

Dariyar rainin wayo na kuma yi ina faÉ—in
"Lallai toh ma na karɓa Challenging ɗin sannn."

Ban rufe baki ba, na zaro manyan idanuna cike da tashin hankali ina kallon ƙaton karen turawan da ya tunkaro ni, wani ƙato dashi jikin sa gaba ɗaya gashi ne, launin Fatar sa brown, daga bayan sa mai kula da shi ne yake biye da shi cikin fella gudu a son sa na ya tsaya, sai dai ina wannan tunkaro ni kawai yake tamkar wanda ake basa umarni.

Kwata kwata na kasa motsi sai faman zare ido nakeyi ina jiran tsammani don kuwa banajin karen nan idan ya ƙari so wurin bazai yi yaga yaga da nama na a ɗanye ba.

Cikin zafin nama Aasief dake gefena ya kamo hannuna da hannun sa É—aya yayin da É—ayan ya jefa wa wannan karen key's dake hannun sa.

Gaba ɗaya na binsa nayi, nauyin da nayi masa yasa gaba ɗaya mukayi ƙasa ina daga sama nayi masa rumfa.

Unfortunately lips ɗi na suka sauka cikin nasa ja-ja-yen laɓɓan.

Oh my God kasa motsi dukkanin mu mukayi, ga mutane har sun fara taruwa kanmu cike da son ganin kwakwaf.😅

Cikin yardar Allah na samu na miƙe tsaye ina kama baki cikin zare ido, tuna wai da gaske sumbatar sa nayi.😹

Cikin sauri na nufa Bus da ta ƙari so wurin ko gigin juyawa garesa banyi ba.

"Ke Kyakkyawa ta, ya ya dai baki da abin faÉ—a ne?."

Tambayar ya yi min cike da shaƙiyanci, ni kuwa ƙin juyawa nayi, da sauri na shige cikin Bus ɗin ina Dariya.🤓

_-_*-_

Rayuwar Duniya daɗi idan ka sama wanda kake so yake ƙaunar ka tsakani da Allah.

A wannan zamanin mace abar tausayi ce, tabbas wurin samun Namiji wanda yake ƙaunar ta da gaskiya.

Yawancin Mazan mu na yanzu bamu suke so ba, jikin mu kawai suke buƙata, yayin da kuma mu Matan yawanci kuɗaɗen samarin muke so.

Ni dai nayi dace na zama mai sa'a cikin masu sa'ar, na sama haɗaɗɗen lu'ulu'u na Aasief Mai Waje, kyakkyawan matashin Saurayi na.😇

Na gwadashi ta ko wani ɓangare amma halayensa masu kyau kawai nake gani, ban taɓa ganin sa da wani mummunar siffa ko hali mara kyau ba.

Aasief É—i na irin waÉ—annan samarin ne na kirki waÉ—anda kafin mace ta sama kalar su sai tasha wahala gaskiya.

Soyayya muke gudanar wa mai tsafta tsakani na da Aasief Mai Waje kyakkyawa na.

**
Murmushi nayi dai dai lokacin da na shiga Elevator da zai sadani kai tsaye izuwa Room na Saurayi na Aasief.

Jiya da dare ina kwance saman Bed saƙon sa ya shigo wayata, wai na samesa a estate nasu yau misalin 4:50pm.

Ba tare da tunanin komai ba, yau na shirya cikin kyakkyawar shiga na fito daga Gidan Madam Joy.

Kai tsaye na hau Taxi na taho zuwa Address ɗin da ya rubuta min a saƙon, koda na sauka a taxi bayan na biya sa kuɗin sa.

Sosai nasha mamaki ganin ba tare da binciken komai ba. Gate man dake tsaron Babban gate na Estate É—in ya buÉ—e min na shiga ciki, haka shima mai tsaron gate na biyu.

Ban kawo komai a raina ba, don duk tunani na, shi Aasief É—in ne ya yi musu umarni da hakan.

Hannu nakai domin knocking Room É—in nasa, ga Mamaki na a buÉ—e yake.

Saboda haka cusa kaina ciki nayi. Wannan karon shi ne farkon zuwa ta Estate da yake kuma farkon shigata Room É—in sa.

Palo ne haɗaɗɗe na gaske, wanda tsantsan kyawun palon ne ya sa na kasa gaba na tsaya ƙare wa palon kallo.

Subhanallah!

Na furta a fili sakamakon hango Boxer da nayi yashe a tsakiyar palon.

Humm wata ƙilama gajiya ya yi jiya Shiyasa bayar Boxer a ƙasa kuma a palo.
Chapter 7 · 0% Book details