Sashe 13
Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba tare da ɓata lokaci ba suka ware ma ta wani ɗaki a cikin gidan sannan suka kai ma ta kayan aikin da zata buƙata.
Nan ne fa da shigarsu ta fara ƙoƙarin cire masa harsashin.
Ta sha wahala sosai sannan da kyar ta samu ta cire tana haÉ—a uban haÉ—a gumi sannan take cewa da shi ta kammala.
A hankali ya janye ƙafar tasa yana rumshe idanu saboda azaba.
"Karka damu na haÉ—a maka da Allurar kashe zafi, zuwa anjima zaka nema zafin ka rasa."
Zaynerb tayi maganar ba tare da ta kallesa ba, bayan ta buɗe idanunta sannan ta ƙari sa wurin ɗayar Budurwar da aka harba a kafaɗa.
Cikin taimakon Allah Zaynerb ta samu tayi ma ta treatment da ya kamata, sannan ta kalleta tana ƙare wa irin shigar dake jikin Budurwar kallo, ta tambaye ta
"What is your name?."
Tayi ma ta maganar da turanci ne dan ta fahimci da wuya idan tanajin Hausa
"Samiupter D'Souza..."
Budurwar ta bata amsa.
"Daga wata ƙasa kike, kuma menene ya kawoki nan ƙasar, sannan garin ya ya waɗannan mutanen suka yi Kidnapping naki?."
Zaynerb ta jero ma ta tambayar kamar wata Æ´ar jarida idanunta akan Budurwar da ta kira kanta da ' Samiupter '.
"Ƙasar Indiya nake yanki kudanci, nazo Birthday Party na Æ™awata ce, a hanyar mu na zuwa Abuja daga Kano waÉ—annan mutanen suka yi garkuwa damu, kuma sun kashe Ansha, dama tare da ita nake. Ta ce zata rakani Abuja saboda ban san kowa anan Æ™asar ba."ðŸ˜
Cikin kuka Samiupter ta ƙari sa bawa Zaynerb labarin muryarta har dashewa tayi saboda tsananin tashin hankali da wani irin hali da take ciki.
Rungumo ta Zaynerb tayi tana lallashi cike da tausayin ta.
Yayin da shi kuwa Aasief ido ya zubawa Zaynerb É—in yana kallon ta.
Neelarh kuwa tuni baccin wahala ya yi gaba da ita tana daga gefen sa ta jingina da kafaÉ—arsa.
"Zaynerb kin canza sosai kamar bake ba, kuma ban san dalili ba, kece kika yimin laifi, amma ni kika É—aura wa laifin..."
A hankali Zaynerb ta juya ta kallesa jin irin maganar rainin wayo da yake son kawo ma ta, ranta a ɓace ta basa amsa da faɗin.
"Aasief kaine ka canja ba kamar yadda na sanka ba, ka canja daga Aasief mutumin kirki dana sanka, gaba ɗaya halayyar ka basu yi ba, ban taɓa tunanin ka da irin halin da na tsinceka ciki ba a wancan lokacin, ka rasa wacce zakayi Alaƙa da ita sai wannan Arniyar Erisha haba wallahi ka bani mamaki ba kaɗan ba."
Zuwa lokacin kansa ya fara É—aurewa da kalaman Zaynerb, sam bai fahimci abin da take nufi ba kwata kwata.
"Kiyimin bayani yadda zan fahimta, nifa cikin ruÉ—ani kawai maganganun ki suke jefa ni, dan ban san inda suka dosa ba sam."
Wannan karon kallon sa tayi da kyau idanunta na cika tab da kwalla take faÉ—in.
"Haba mana Aasief ya kakeso ka mayar dani shashasha ce, ko an gaya maka wancan Ranar da kace na sameka Gidan ka banga komai bane?."
"Me kike nufi ne Zaynerb, wacce Ranar kuma?."
"Kaji ko ƙara raina min wayyo kakeyi fa, wancan Ranar mana da dare da saƙon ka ya shiga wayata kana faɗin nazo Estate naku gidan ka, ko kuwa dai ka manta Ranar?...."
Dafe kansa dake mugun sara masa Aasief ya yi wani tunani tana ɗar suwa a Ransa, cikin sauri ya kalleta don ya ƙara tabbatar da tunanin sa, yake tambayarta da faɗin.
"Ina jinki a Ranar menene ya faru da ki ka zo Estate bayan kin ƙari so Room nawa, menene ya faru, please Zaynerb Tell me anything everything, please ki faɗa min duka abin ya faru da kuma wanda kika gani?."
Cikin tsorata da irin yanayin da ya fara shiga, idanun sa sun yi jajur na ɓacin rai Yayin gaba ɗaya jijiyoyin kansa suka tatashi, kai kana ganin sa kasan ransa ya yi matuƙar ɓaci.
Bai damu da kalar raɗaɗi da kuma jinin da ƙafarsa da aka harba take fitarwa ba, ya miƙe tsaye ya ƙari sa wurin ta.
Jijjiga ta yake yana roƙon ta akan ta faɗa masa abin da ya faru a lokacin, ihu da kuma maganar da yake ma ta da ƙarfi yana jijjiga kafaɗunta ne, yasa Neelarh da Samiupter suka farka daga ɗan baccin da ya fara ɗaukar su a firgice suna zazzare ido cike da tashin hankali.
Wani irin ban ko ƙofar akayi Sannan wannan ƙaton Gardin wato Gaddafi ya shigo ɗakin cikin ƙatuwar muryarsa kuma cike da bala'i yake faɗin.
"Wani mara rabon ne, yake mana ihu anan wurin, da alama ya gaji da rayuwar sa ne..."
Ya yi maganar ne yana ƙari sawa wurin da Aasief yake a durƙushe bai dena jijjiga Zaynerb yana faɗin ta faɗa masa gaskiya ba.
Cike da tsantsan mugunta ƙaton Gardin yakai hannu ya finciko Aasief ya miƙar da shi tsaye sannan ya saita bakin bindigan hannunsa a ta bayan Aasief ɗin yana ƙoƙarin juyo da shi.
Cikin Wata kalar da fusata da zafin nama Aasief ya juya gaba ɗayansa sannan ya dunƙule hannayen sa yakai ma masa wani wawan naushi a ido.
Zubewa Gaddafi ya yi ƙasa cike da azaba idanun sa na fitar da jini.
Bin sa ƙasan Aasief ya yi Dan bala'i, yana kai masa naushi a fuska ta wurin da ya tabbatar yana masa rauni, cikin wata kalar murya kakkausa yake faɗin.
"Dan uban ka ina tambayarta abin da ya faru shekaru biyar baya, shi ne zaka shigo tsakani da wannan jahilar Muryar taka, wato dama bakasan haushin ka nake ji ba, kaine ka harbeni ko zakaci uban ka yau."
Maganar Aasief yake yana kuma kai masa naushi a ta ko'ina na fuskar sa, Aasief bai dena dukan Gaddafi ba har sai da yaga ya daina motsi alamar ya suma...
Sannan ya dakata sannan cikin fitar da huci na mugun ɓacin rai ya juya kamar wani kububuwa yana kallon Zaynerb wacce ganin abin da yake yi, yasa idan banda rawa babu abin da gaba ɗaya ilahirin jikinta yake yi, tun kafin yace da ita komai ta fara masa bayani.
Cikin lokaci ƙanƙani Zaynerb ta koroma Aasief gaba ɗaya bayanin abin da ya faru lokacin da taje Room nasa, ta faɗa masa irin tashin hankalin da ta shiga da kuma irin maganar da Erisha ta faɗa ma ta.
*Aasief*
Wani wawan naushi ya kai ma bangon É—akin wanda har sai da gaba É—aya É—akin ya amsa.
Idan banda huci babu abin da Aasief yake yi tunda yake a Duniya ransa bai taɓa ɓaci ba irin na yau.
Wai ashe duk waÉ—annan shekarun da aka kwashe idan Zaynerb zata tuna sa, tuna sa take yi a matsayin Mazinaci mayaudari....
Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un
Zubewa ya yi a ƙasan idanun sa na fitar da ruwa.
Miƙe wa ya yi a fusace ya fara zagaye ɗakin faɗi kawai yake.
"Saina kashe Leo, Tabbas da hannuna zan kashe Leo da wancan kafirar Erisha ko tabbas sai nayi musu KISAN GILLA."
Tabbas indai lissafin sa ya tafi dai dai yadda tunanin sa ya basa ke nan dai Leo da Erisha su ne suka shirya komai na abin da ya faru tsakanin sa da Zaynerb...
"A wancan Ranar ba Ni ne na turo Miki da wannan saƙon ba, domin kuwa sace wayata akayi a Ranar, nasha wahala sosai wurin neman ta amma ban gani ba, haka na haƙura na nufi hanyar komawa gida cikin motata a hanyar ne na haɗu da Accident, ban farka ba sai washe gari na ganni a Room na ga Leo a gefe na, yana faɗa min wai a Hanyar sa na komawa gida ne, ya ganni nayi Accident shi ne kawoni gida..."
Shiru Zaynerb tayi tana sauraren abin da yake faÉ—a ma ta kuma yana ma ta maganar bada kakkaurar murya ba, cikin murya ma dai dai ciya yake ma ta bayanin.
"Dama Leo yasan Estate naka ne?."
Zaynerb ta tambaya har lokacin jikinta bai bar rawa ba, ga kuma siraran hawaye da suke bin fuskarta.
"No bai sani ba, kuma a lokacin ban tambaye sa ta ya akai ya sani ba."
Da bata amsar, miƙe wa ya yi tsaye yana gogen jinin dake fita a ƙafarsa.
"Ku taho muje..."
"Ina ke nan?."
Zaynerb ta tambaya tana kallon sa cikin faÉ—uwar gaba.
"Barin nan zamuyi, ada banyi niyyar guduwa ba, amma wannan labarin da kika bani yasa na yanke shawarar mu gudu saboda banaso Leo yakai Yammacin yau bai mutu ba."
Zaro ido Zaynerb tayi cikin tashin hankali bakin ta na rawa take faÉ—in
"Mu-mummtuwa fa kake faÉ—a....."
*ABUJA*
*Haleesat*
Baya tayi ta jingina kanta da kujerar motar ta, idanunta akan Babban Ofishin bincike reshen manyan laifuka dake Abuja. C.I.D.
Sosai ta shiga matsanancin tashin hankali da kuma damuwa na sace Zaynerb da kuma rashin lafiyar Afeefah.
Wanda sanadin haka ne koda University bata samu taje, cikin haka ne wata ƙawarta ta bata shawarar zuwa ofishin c.i.d. domin basu report duk da cewa shima Daddy yana iyakar bakin ƙoƙarin sa haka ma Maleek.
Ranar ta fito daga bathroom ta duba wayarta nan ne taga message da Maryam ta turo ma ta, cikin hanzari ta buÉ—e ta fara karantawa.
"Sunan sa Suhais Sulaiman Interval, just 'Interval' aka fi sanin sa da shi.
Rank Officer.
Batch Number T3,783 :: D8... Specialization.
Shekarun sa Twenty something.....
D.O.B......
Iya kar abin da na sani akan sa na faÉ—a miki, kije wurin sa Insha Allah zai taimaka da nasa binciken domin shi É—in qwararren Jami'i ne wanda yasan makamar aikin sa, sannan bayada wata matsala."
Ajiyar zuciya Haleesat ta sauke a lokacin bayan gama karanta saƙon.
Nan ba tare da ɓata lokaci ba tana gama shiryawa ta ɗauki mota ta tuƙa har zuwa Babban Ofishin.
Koda isarta ofishin ta nema a haÉ—a ta da shi.
Da farko Jami'in ƙi ya yi, amma tana faɗa masa Wanene mahaifinta a ƙasar, cikin rawar jiki ba tare ɓata lokaci ba, shi da kansa Jami'in ya kaita har gaban Yallaɓan Officer Interval, sai dai kuma menene zai faru bayan ganin sa da Haleesat tayi?.....
*What Next*
_______💓💓💓
The Nainarh Kd
💓💓💓_________