← Book details Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 14

Sashe 12

Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da takaici Afeefah ta kwashe duka abin da ya faru tsakanin ta da Official ta faɗa wa Jiddarh ta ƙara da cewa

"Kuma fa yanzu nasan kallon wata Fan's É—in sa ko kuma wata muguwar masoyiyar sa yake yimin fa."

Afeefah ta ƙari sa maganar tana kyaɓe fuska cike da takaici Jiddarh ta cuceta

Jiddarh tsaban dariya batasan lokacin da ta faɗo ƙasa daga saman kujerar da take ba, faɗi take

"Aikuwa Queen Of Beauty Wannan Drama naki ya kusa kala guda da nawa, sai dai nawa akwai takaici ciki bisa naki fa."

"Okay, ke Menene ya faru dake ɗin Afeefah ta tambaya cike da qwulewa na dariyar da Jiddarh take ma ta, ga kuma Deejarh kamar wata mahaukaciya ita ma daga ɓangaren ta tana dariya na jin labarin da Afeefah ta bawa Jiddarh, ita ma Lailah duk da bata cikin yanayi na nishaɗi sai da abin da Afeefah tayi ya bata dariya.

Sai da Jiddarh ta saita nutsuwarta sannan ta koma ta zauna sannan ta fara cewa

"Queen Of Beauty Ina baki Story mun iso nan Kano lafiya mun sauka a Jirgi ni da Humaira da tayimin Rakiya, anan Airport naga wani haɗaɗɗen Guy ina baki labari kyakkyawa da shi, ƙarshe a kyau Guy nan yake.
Kin sanni bana gani na gyale, ganin yadda gaba ɗaya Ƴan matan Airport suke binsa da wani mayen kallo ne, yasa ba tare da shawara ko tunanin komai ba, na cire facemask dake rufe da fuskata sannan na cire After Dress dake saman kayana, nan fa na bayyana cikakkiyar SARAUNIYAR KYAU na, nan hankalin mutanen Airport ya dawo kaina waɗanda suka gane ni suka ƙari so wurin da muke nida Humaira cikin tafiya na gayu, gaba ɗaya suka rufe ni daga masu roƙo akan na tsaya muyi pictures, sai masu bani Biro da takarda wai nayi musu sa hannun ƙauna.

Abin takaici wanda nayi hakan danna na burgesa ya bar wurin, amma waÉ—annan mutanen basu gyaleni ba sai da kyar fa nake gaya miki.."

Dariya Afeefah tayi tana tambayarta da faÉ—in

"Ke nan dai idan na fahimta kinyi abin da kika yi ne, saboda ki burge wannan Guy sai kuma aka yi rashin Nasara mutane suka shiga tsakani ko?."

"Yes of course haka fa nake nufi."

Jiddarh ta bata amsa. Nan dai suka ci gaba da shan fira ko wacce tana bada labarin abin dariya tamkar waɗanda suka yi one Year ko fiye da haka da haɗu wa, bacin sau biyu kawai suka taɓa haɗu wa.

Sai da Afeefah ta kammala waya da Jiddarh sannan ta kuma dan nawa Daddyn ta Mister Mai Kyau dake Jamus kira dan tayi kewar sa sosai.

"Assalamu Alaikum Daddy wato shi ne koka kirani ko?. Ae nayi fushi ma."😩

Afeefah tayi maganar cike da tsantsan shagwaɓa ga Daddyn nata.

Ƙayataccen Murmushi Mister Mai Kyau ya yi daga yadda yake zaune a hamshaƙe saman kujerar sa ta alfarma cikin haɗaɗɗen ofishin sa dake hawa na ƙarshe cikin katafaren company nasa dake can Germany (Jamus).

"Wa'alaiki Salam WarahamatuLlahi Wabarakatuhu. Kaina bisa wuya Shalele uzurori ne suka yiwa Daddyn ki yawa sosai, shiyasa ban samu na kiraki ba, sannan ae nayi tunanin Zaynerb ta dawo ne, kodai ba yau ne zata dawo daga Kano State ba?."

Wani irin bugu na tashin hankali kuma mara dalili zuciyar Afeefah tayi jin Daddy ya ambaci Zaynerb, ita fa wallahi shaf ta manta yau Zaynerb zata dawo Abuja, cikin sauri ta ciro wayar daga kunnenta ta duba Time 4:50pm hankali a tashe ta mayar da wayar kunnen ta tana faÉ—in.

"Subhanallah, Daddy Anty Zaynerb fa bata dawo ba, nifa gaba ɗaya na manta yau zata dawo, kuma tun jiya da muka yi waya da ita ta ce Yau zata dawo bamu ƙara waya ba fa, wayyo Daddy tsoro nakeji kar wani abu ya sama Anty Zaynerb na..."

Jin yadda Afeefah take maganar hankalin ta a mugun tashe ne.

Yasa Daddy saurin tarar ta da faÉ—in.

"Ki kwantar da hankalin ki wata ƙilama Zaynerb ɗin ta fasa dawowa Abuja yau ɗin ne fa, amma dai gudun zargi riƙe waya, barina tuntuɓi Uncle Sagir naku muji."

Da "Toh." Kawai Afeefah ta amsa masa amma bata tunanin zata iya kwantar da hankalin ta, bacin batasan halin da Zaynerb Yayarta take ciki ba.

Tsuru tsuru Lailah da Deejarh harma da Haleesat wacca tashin ta daga Bacci ke nan ta fito palon a gaɓar da Afeefah take faɗin Zaynerb bata dawo ba.

"Assalamu Alaikum Babban Yaya. Yau Harkokin Kasuwanci sun bari an tuna damu ke nan, tun da naga kira da Yamma nan."

Uncle Sagir ne duk yake waÉ—annan maganganun cike da farin ciki na ganin kiran da ÆŠan uwan na sa ya yi masa.

"Sagir ba wawan ne a gabana yanzu ba, wai nace Zaynerb ta fasa dawowa Abuja ne, sai ta ƙara kwanaki ko kuwa, Afeefah ta kirani tana faɗin Zaynerb bata ƙari so ba har yanzu."

Cikin sauri Uncle Sagir ya katse Daddy da faÉ—in.

"Zaynerb kuma wata Zaynerb ke nan, wai dama ba tun jiya Zaynerb kuka ce ta koma Abuja ba?."

Ya yi tambayar yana kallon Mah'fuz dake zaune gefansa yana jin abin da ke faruwa.

"Zaynerb kuma Abhu anya kuwa, ae Zaynerb tun jiya tabar nan, ta ce zata koma Abuja, babu yadda bamu yi da ita ba, akan ta tsaya gari ya waye saboda a jiyan babu Flight, amma Zaynerb taƙi ji saboda taurin kai da Yammacin ta ɗauki Driver da mota suka nufa Abuja, gashi kuma har yanzu Drivern bai dawo ba..."

Duk wannan maganar Mah'eesha ce take zubosu a lokacin da ta ƙari sa shiga cikin palon mahaifin nasu sannan ta a je masa kayan maƙulashe da ta kawo masa saman center table.

"Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un, na shiga ukuna Daddy kanaji fa wai cewa suke Anty Zaynerb É—ita tun jiya ta kamo hanyar zuwa nan, gashi kuma har yanzu batazo ba, Daddy tsoro nakeji kar'a cutar min da Yayata Daddy please kayi wani abu kaji Daddy i'm begging you please Dad say something to me pleased......"

Ƙari sa maganar Afeefah tayi cikin tsananin kuka muryarta na fita da kyar kuma cikin wahalar fitar numfashi.

"Subhanallah Afeefah menene nakeji kike faÉ—a ne, wai kina nufin Zaynerb bata dawo ba, inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un menene ke nan yake faruwa i'm so confusing fa."

Uncle Sagir ne yanzu ya yi maganar jin muryar Afeefah da kuma irin abin da take faÉ—a.

"Afeefah! Afeefah!! Kina jina kuwa, please kiyi magana mana?...."

"Na'am Daddy ina jinka domin ban mutu ba, tukunna amma muddun ba'a nemo min Ƴar uwata Zaynerb ba. Tabbas Daddy zan iya mutuwa a kowane irin lokaci...."

"Subhanallah Afeefah kina da hankali kuwa kin san menene kike faɗa, nace ki kwantar da hankalin ki Zaynerb ba ɓata tayi ba Insha Allah za'a ganta kinji Shalele ta!?...."

Tanaso tayi magana sai dai abin da ya tokare ta a maƙushi shi ne ya hanata yi magana.

Ji take a maqwoqwaronta tamkar ana jajjagen yaji a ciki duk yadda taso tayi magana abin cutura ya yi.

Zubewa tayi a ƙasa sumammiya yayin da bakinta yake fitar da wani irin kumfa tamkar wacca tasha poison.

Da gudun tsiya gaba ɗayan su tun daga Haleesat da Lailah har da Deejarh suka ƙari sa kanta suna kiran sunan ta cikin tsananin tashin hankali.

Sai dai ina Afeefah ba jinsu takeyi ba domin kuwa tashin hankalin da ta shiga ne yasa ciwon ta yake ƙoƙarin tashi.

*TASHIN HANKALI*
*WANDA BA'A SAKA MASA RANA*

Tofa fi ye da haka gaba É—aya Ahalin Mai Kyau suka shiga domin kuwa Afeefah ciwo ya tashi kuma yazo da mugun gardama.

Yayin da ita kuma Zaynerb an tabbatar da saceta akayi. Sai dai a yadda labarin yaje musu bawai ita kaÉ—ai kidnapper's É—in suka sace ba harda wasu mutanen.

A Ranar da abin ya faru M.MK ya dawo ya biyo ta private jet. Nasa ya dawo ƙasa Nigeria cikin tsananin tashin hankali domin kuwa abin haɗe masa biyu ya yi ga ciwon Afeefah wanda baya jin magani ga kuma ɓatar da Zaynerb tayi. gaba ɗaya yabi ya fita hayyacin sa, danma wani abun Maleek ne yake yi da kansa musamman akan binciken nemo inda Zaynerb take.

Gaba É—aya Ahalin sam basa cikin kwanciyar hankali na abin da yake faruwa, tsawon kwanaki uku ke nan da sace Zaynerb kuma babu ita babu labarin ta, sannan kidnapper's basu kira sun faÉ—a adadin kuÉ—aÉ—en da suke so a basu ba.

Wanda hakan yasa aka fara zargin da wuya idan saboda kuÉ—i suka yi Kidnapping nata.

Babu shiri gaba É—aya Ahalin Uncle Yusuf suka tattaro suka dawo Abuja Gidan Mister Mai Kyau da zama har zuwa Ranar da kidnapper's É—in zasu kira su faÉ—in Abin da suke so.

A 6angaren Momy Rafi'at kuwa za'a iya cewa tafi kowa shiga tsananin damuwa na sace Zaynerb da aka yi da kuma ciwon Afeefah.

Sai dai na ciki na ciki, Dan ita kaÉ—ai tasan Gadar Zaren da take shiryawa

*WANNAN KE NAN*
*KAÆŠAN DAGA CIKIN IRIN HALIN DA AHALIN MAI KYAU SUKA SHIGA SAKAMAKON KIDNAPPING ZAYNERB DA AKAYI*

*ZAYNERB*😣

"Na kammala fa."

Tayi maganar tana kawar da idanunta da kallon sa, sai dai cikin rashin sa'a suka shiga cikin na Yarinyar da yake tare da ita kuma ta ambaci kanta da matar sa.

Rumtse idanun nata tayi ƙam tana nuna kalar baƙar wahalar da suka sha hannun waɗannan kidnapper's.

A lokacin da ɗaya daga cikin su ya sanar police sun sama labarin wurin suke, cikin gaggawa gaba ɗaya kidnapper's ɗin, suka tattara mutanen da suka yi Kidnapping, cikin wasu motoci tamkar awaki haka suke zuba mutane a motocin. Sannan suka bar wurin dasu, tsawon kwanaki biyu suna tafiya dasu suna shiga dasu cikin tantagaryar daji, sannan bayan shafe kwanaki biyu da sa'o'i suka ƙari so da su wani ƙurman gida ƙaton gaske cikin dajin.

Sosai mutum zai yi mamakin ganin irin wannan gida a daji.
Cikin gidan suka shishshiga dasu Zaynerb kamar wasu awakai, sannan ne aka fara neman wanda zai cire wa Aasief harsashin dake ƙafarsa, da muka wata Budurwa ita ma da alama tayi musu taurin kai ne, suka harbeta a kafaɗa.

A lokacin cike da Qwarin gwiwa Zaynerb ta ce dasu ita likita ce saboda haka zata iya kula da masu raunuka.
Chapter 12 · 0% Book details