Sashe 2
Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike jindaÉ—i Afeefah ta amsa masa tana haÉ—awa da masa tambayar.
"Muna lafiya lau, Yaya Shahid hala dai Anty Aeezath É—in ba nan ne?."
"Masha Allah, wai Darling tana kitchen qiwa ne ya hanata tashi tun safe sai yanzu wuraren ƙarfe sha biyu take haɗa mana breakfast, duk ta bar muku ni da yunwa."
"Lallai anty Aeezath ta cancanci tuhuma tunda har tabar mana Yaya Shahid guda da yunwa har sha biyu, bari na bita kitchen É—in sai naji dalili."
Afeefah tayi maganar cikin dariya sannan ta miƙe tsaye bayan ta a je mayafin kanta a saman kujera ta nufa kitchen ɗin.
Murmushi Yaya Shahid É—in ya yi yana bin bayan Afeefah da kallo, Yarinyar tana burgesa tun daga kan nutsuwar da take dashi, kyawunta, da sauran su, shiyasa ko cikin yaran dangi yafi shiri da ita, daga ita sai Husnee da kuma Zaynerb yake sakarwa fuska, wani lokacin harda Lailah.
"Lailah yakike?, wai da gaske Maleek ya dawo, na fa kasa yarda."
Yaya Shahid ya yi maganar bayan ya mayar da kallon sa akan Lailah da take zaune gefan, Mah'eesha da tayi tsit a palon dan kuwa ba kaÉ—an ba take tsoron Yayan nasu, domin babu wasa.
"Eh wallahi Yaya Shahid ashe ka sama labari yau ina ga kwanan sa uku ke nan da dawowa fa."
Lailah ta basa amsa tana gyara zamanta cike da son suyi fira dashi.
"ÆŠan kwal uba yaji wuya ya dawo, ae naso ace ina nan lokacin da ya dawo da bazan bari Uncle Mai Kyau ya yafe masa da wuri ba Allah kuwa."
Dariya Lailah tayi jin abin da Yaya Shahid É—in yake faÉ—a, dama sun saba irin haka da Maleek É—in domin sa'annin junane su É—in, duk da dai Yaya Shahid É—in ya bawa shi Maleek kusan shekara, Yayin da shi kuma Maleek yaba mah'fuz da Yasir shekara da watanni shiyasa duka suke kansu É—aya, kuma abokai, domin kuwa idan Maleek da Shahid suka haÉ—u wuri É—aya rantse wa zaka yi abokan wasa ne, saboda yadda suke abu kamar wasu abokan wasa.
"Huh Yaya Shahid ke nan, ina baka labari sai ma lokacin da Daddy yake cewa bai yadda Yaya Maleek da ya zauna masa a gida ba, har sai ya fito da mata, a lokacin kwatsam yace Husnee yake so, ita kuma tsaban gulma harda wani faɗin zata je tayi shawara, ina faɗa maka ta shige Bedroom ɗina ta sha rawa da waƙa ta fito, tana wani kyaɓe fuska na wai ta ce amince."🤣
Dariya Yaya Shahid yana a je cup of coffee dake hannun sa yace.
"Kaji Æ´an rainin hankali dukansu son junan su su ke yi, dama tun kafin yanzu na daÉ—e da sanin cewa Maleek yana son Husnee, dan haka amfani ya yi da damar sa kawai a ranar ya jefa tsuntsaye biyu da dutse É—aya, babu komai zai gamu dani, zamu haÉ—e, Allah ya kaimu nazo Abujan."
Dariya Lailah keyi nan dai suka ci gaba da fira dashi, Mah'eesha tana daga gefe tana ɗan tsoma baki idan an sakata a wani abin.😉
Da sallama ta shiga kitchen É—in yayin da take hangen matar da ta juya baya tana aiki cikin kitchen É—in.
"Wa alaikumus-salam WarahamatuLlahi Wabarakatuhu."
"Barka dai Matar Babban dama nazo tayaki aiki ne, Yaya Shahid yace qiwa ya hanaki tashi sai yanzu kike masa breakfast."
Cewar Afeefah bayan Aeezath É—in ta amsa ma ta sallamar da tayi.
Murmushi tayi tana faɗin "Lallai ma wannan mutumin sai kace bashi ne ya hana ni motsawa ko nan da can ba, shi ne zai wani ce qiwa ya hana ni yi masa breakfast Aikuwa zai gamu dani tabbas."😚
Dariya kawai Afeefah ta kuma yi tana faÉ—in
"Yaya Shahid ke nan, wato shi ne yazo qiwa ya hanaki ko Humm. Ni bama wannan ba, Matar Yaya ni fa kama kike min da wata ƙawata da muka yi school tare a Jamus gaskiya kuna kama sosai."
"Allah Sarki shin ko dai Adivat kike nufi?." Aeezath ta tambaya tana kallon Afeefah É—in.
Cike da farin ciki Afeefah ta amsa ma ta da "Eh wallahi sunan ta Adivat school É—aya muka yi da ita a Jamus, tunda muka rabu, ban sake haÉ—u wa da ita ba."
"Ayya Aikuwa ta kwana gidan sauƙi domin ƙanwa ta ce uwa ɗaya uba ɗaya muke da ita."
Zaro ido Afeefah tayi tana kuma kallon ta ciki gyaÉ—a kai take faÉ—in
"Babu shakka domin kuwa ga alamu nan ya bayyana ɓaro ɓaro kuna kama sosai ita, Allah Sarki ko yanzu tana ina oho."
Afeefah ta ƙarisa maganar nata da alamun tayi kewar ƙawar karatun nata Adivat.
Aeezath tana É—auraye plate's dake hannunta ta amsa ma ta cewa.
"Ai Adivat yanzu tana can U.s tana karatun ta a can tama kusa kammala, domin ina ga a wannan shekarar zata kammala, kin san karatun likitanci take shiyasa ma ta daÉ—e bata kammala ba."
Karɓar plate's ɗin Afeefah tayi tana faɗin
"Allah Sarki kice abu ɗaya muke karanta da ita, aikuwa Insha Allah kafin mu koma Abuja zan karɓa lambarta a Wurin ki."
Afeefah tayi maganar tana jere plate's É—in a wurin da ya kamata sannan ta ci gaba da taya Aeezath É—in.
"Okay babu damuwa, in ce dai ba yau ne zaku koma na ko?."
Aeezath ta tambaya
"Yau ne anjima ma kuwa, Around 4:30pm Insha Allah mun sauka a Abuja ma."
Afeefah ta bata amsa tana ci gaba da cewa
"Amma Please na tambaye ki mana, wai menene a tsakanin ki dasu Mah'eesha ne haka, na lura sam bakwa shiri fa, ko zan iya sani Please?."
Afeefah ta ƙari sa maganar ne a daidai lokacin da Mah'eesha ta shigo kitchen ɗin, batare da kallon su ba, don taji Abin da Afeefah ta faɗa, ta wuce can ta ɗauki ruwa a fridge sannan ta buɗe gorar ruwan tana sha.
A daidai lokacin kuma Aeezath take bawa Afeefah amsa da cewa
"Kin san a rayuwar nan kowa abin da yaga zai iya yake yi. Ni a tsarina indai mutum ya nuna baya yi na, to nima fita harkar sa nakeyi, na sani ana cewa bani da kirki, sai dai rashin kirki na akan wanda ya gwadamin rashin kyautawa nakeyi, sun nuna ban musu ba, shiyasa na fita harkar su gaba É—aya, yanzu idan aka min magana ae zan kula Mutum, bazan sha re shi ba, wasu kawai suna wahal da kansu ne akan ga ba dani wallahi."
Gaza haƙuri Mah'eesha tayi sai da ta juya ta kalla Aeezath sannan tayi ma ta tambayar da ta daɗe a zuciyarta tana so tayi ma ta bata sama dama ba, sai wannan lokacin.
"To idan maganar ki haka ne, me saya ranar da muka fara zuwa gidan nan wurin ki ni da Haseeya da Hameeda kika kulasu baki kulani ba?."
Murmushi Aeezath tayi sannan ta bata amsa da faÉ—in
"Saboda a lokacin na sama labarin kece wacca bakya so na cikin familyn Shahid saboda ya aure ni, bai aura ƙawar ki ba, ko ba haka bane?. Wannan ne yasa bana shiga harkar ki ba komai ba."
Shiru Mah'eesha tayi ba ta ce komai ba, sai zare ido.🙄
*Mrs Mai Kyau*
"Sailuba ke fa nake jira baki ce komai ba tunda na faÉ—a miki maganar da ta kawoni wurin ki fa?."
Momy Rafi'at tayi maganar tana kallon Ƙanwar nata Hajiya Sailuba domin jin amsar da zata bata akan maganar da tazo ma ta da'ita.
Dogon numfashi Hajiya Sailuba taja tana kallon Yayarnata cikin nazarin maganar da ta faÉ—a ma ta tun shigowar su Bedroom É—in.
Sannan ta ce
"Yanzu idan na bari Fadeelah ta aura Maleek kamar yadda ki ka so shin bakya ganin hakan zai iya kawo matsala tsakanin, Yaranki da dangin Mahaifin su, kuma naji kince Maleek ɗin ya riga ya zaɓa wacca zai aura cikin yaran dangi, to menene manufar ki akan cewa kina so ya aura Fadeelah, ni fa gaba ɗaya ban gane inda kika dosa ba Wallahi sam."
Ƙayataccen Murmushi Hajiya Rafi'at tayi tana juya idanunta akan ƙanwar nata Sailuba sannan ta ce
"Ina da dalilai da yawa da yasa nace miki ina so Fadeelah ta aura Maleek, biyu daga ciki kawai zaki iya sani, sune na farko, idan Fadeelah ta aura Maleek Yarona zumuncin mu zai ƙara haɓaka sosai, na biyu kuma saboda dama can inada burin haɗa auren Maleek da ita Fadeelah ɗin, kuma lokaci ɗaya sannan rana ɗaya nakeso ayi dana wacca zai aura ɗin, domin kuwa bazai yiwu ya aura dangin ubansa yabar na uwansa ba, bani da yadda zanyi a fasa wancan shiyasa nace a haɗa duka."
*Turƙashi*
Hajiya Sailuba ta faɗa hakan ƙasa ƙasa tana kallon Yayarnata.
"To amma bakya ganin cewa Maleek É—in ba zai so hakan ba?."
Ajiye spoon dake hannunta Momy Rafi'at tayi tana faÉ—in
"A'a sam bazai ƙi ba, saboda Yarona yana yimin biyayya, ga duk abin da naso ya yi, sannan kuma a halin yanzu idan nace masa ya aura Fadeelah bazai min musu ba, sakamakon jiya sosai na nuna masa ɓacin rai na akan abin da ya yi mana sai yanzu ya tuna dani da ƙannin sa ya dawo gida. Saboda haka bana nada matsala dashi, sai dai ita Fadeelah ɗin ban sani ba ko tana da ra'ayi a kansa, shiyasa tun farko nace miki ita Fadeelah ɗin ta biyo ni zuwa Gidan ta ɗan yi kwanaki, nasan zan fahimci komai idan tana da ra'ayi akan Maleek."😒
*A TAƘAI CE DAI*
Momy Rafi'at bata bar gidan ƙanwarta Sailuba ba, har sai da Sailuba ta amince da maganar da taje ma ta da ita, sannan kuma tare da Fadeelah suka bar gidan, dama ita Fadeelah sara ne yazo ma ta daidai da bakin gatarin ta, domin tanada burin bin Momy Rafi'at ɗin, sai kuma ita Momy Rafi'at ɗin da kanta ta nema su tafi gida tare tayi ma ta kwanaki a cewar ta, Aikuwa babu musu Fadeelah ta amince.
*JIDDARH*
Har wa yau mamakin Abin da taji Auntie tana faÉ—a wa Heesham bai gama barin ta ba, "*KA NEMA SOYAYYAR JIDDARH*."
Wannan magana idan Jiddarh ta tuna tana ƙara mamaki, tunaninta menene abin da ya sa Auntie take so Heesham ya Aureta tunda har ta ce ya nema soyayyar ta.