← Book details Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba don ta yarda da maganar Sunainah ba, ta kamo hanyar gida bayan sun ɗan taɓa fira da Sunainah ɗin.

Sosai Afeefah suka sha Fira da mahaifin nata, dan sai da suka kusa one hour suna wayar, sannan suka yi sallama dashi, yana saka ma ta albarka cike da alfahari da ita.

Dan kuwa tuni labarin taimakawa mata mai juna biyu da tayi a Restaurant ya zagaye ƙasar ciki da wajen ta.

Ko minti goma basu yi da gama waya da Daddyn nasu ba, sai ga kiran Zaynerb ya shigo wayar, da sauri tayi picking, nan ma dai duk magana ɗaya ce, a kan karɓar haihuwar matar da tayi ne, sai da suka kwashe fi ye da twenty minute's suna waya da Zaynerb, sannan suka yi Sallama Zaynerb tana faɗa wa Afeefah ɗin gobe ne zata dawo nan Abujan daga Kano ɗin, sosai Afeefah tayi farin ciki da murna, dan kuwa tayi kewar Yayar nata Zaynerb sosai.

Koda gama wayarsu da Zaynerb, kiraye kiraye ne kawai suka ci gaba da shigowa wayar nata.

Duka daga na masu fatan Alkhairi a gare ta, sai masu yaba ma ta bisa taimaka wa mai juna biyu da tayi a matsayin ta na cikakkiyar SARAUNIYAR KYAU, sai kuma ƙawayenta na school a masu kiran nata, har da Ƴan uwanta na nesa da kusa, har ma da Fan's ɗin ta.

Daga ƙarshe da ta gaji palo ta fito, nan ta sama su Lailah da Fadeelah zaune harma da Haleesat wacca ba ta daɗe da dawowa gidan ba.

Yayin da Deejarh take Bedroom É—in Zaynerb tana gyara ma ta.

Deejarh

Sosai ta gyara Bedroom É—in na Zaynerb tsaf tsaf komai ya yi clear.

Tana shirin fita daga Bedroom É—in daga can gefan bed side drawer ta hango wani É—an akwati da ya tafi da tunanin ta saboda shaining da yake yi gunin ban sha'awa.

Ƙari sawa wurin tayi batare da ɓata lokaci ba, ta janyo akwatin tayo kusa da ita dashi.

Hannu takai domin taji ko'a buÉ—e yake, ga mamakin ta a buÉ—e akwatin yake.

"Oh ni Dije ta ƙauye, ko menene anan?. Wata ƙila ma Anty Zaynerb ɗin mantawa tayi tabar shi a buɗe."

Deejarh tayi maganar tana kuma kai hannu ta ciro wani É—an jotter a ciki.

An kananan naɗe saman shi da igiyoyi masu kyau ƙanana, hannu tasa ta cire igiyoyin da aka kanannan naɗe jotter ɗin dasu.

Take Manyan rubutun da aka yi da manyan baƙi saman jotter ɗin suka bayyana ɓaro ɓaro anyi rubutun ne da jan Biro.

"MY REAL LOVE STORY."

Haka Deejarh ta furta abin da aka rubuta.
BuÉ—e shafi na farko tayi nan ma anyi rubutu ne, in stylish da red Biro.

"Don't you read this book because it's secret."

Murmushi tayi bayan ta karanta haka tana faÉ—in

"Ni kuwa wallahi tunda aka rubuta haka saina karanta naga abin da za'a iya"

Tayi maganar tana buÉ—e next page.

"My Sadness Love Story😫."

Shiru Deejarh tayi bayan ta karanta hakan, tunani take ae idan ba za ta manta ba, akwai wata rana suna zauna a Palo, Lailah take cewa SOYAYYA ce silar rushewar farin ciki a rayuwar Yayarsu Zaynerb.

Tuna wannan abu da Deejarh tayi ya saka cikin sauri ta miƙe tsaye har tana kusan tuntuɓe da ƙofa wurin fita daga Bedroom ɗin.

Da gudu ta ƙari sa palon, sannan ta tsaya tsaye a tsakiya tana sauke haki faɗi take cikin nuna musu jotter dake hannunta

"Balarabiyar India, Anty Lailah, har dake Anty Haleesat wannan shi ne littafin da labarin SOYAYYAR Anty Zaynerb yake ciki, a Bedroom É—in ta na gani da ina gyarawa."

Za'a iya cewa tsakanin Lailah da Haleesat ba'a san wacece ta riga tashi tsaye ba, ta ƙari sa wurin Deejarh ta karɓa jotter ɗin.

Sai dai kawai ganin jotter É—in suka yi gaba É—aya hannun Lailah.

Komawa Haleesat tayi ta zauna taso ace ita ce ta fara sanin ya ya labarin soyayyar Zaynerb yake, wani irin ƙalu bale ta fuskan ta a ciki da har takai ga dawowa Nigeria, sannan kuma da halin shaya shaye?.

"Tunda haka ne ki karanta mana a fili kawai musan abin da yake ciki."

Afeefah tayi maganar tana tashi daga inda take ta koma kusa da Lailah É—in ta zauna a saman tattausar carpet na palon, dan kuwa ita ma a mugun matse take da jin labarin soyayyar Zaynerb É—in.

BuÉ—e shafi na biyu na littafin Lailah tayi bayan ta karanta abin da aka rubuta a bango na jotter É—in da kuma shafi na farko.

Karantawa ta fara a fili kamar haka....

Mgnr Payment fa

*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*

~Karku bari a baku labari fa🤩~

~*SARAUNIYAR KYAU*~🔥🔥Takun Tsakiya_-_
*Iya kuÉ—in ki iya shagalin ki Hajiya*

*🔥 SARAUNIYAR KYAU 🔥*
_-_👑ƚαƙυɳ ƚʂαƙιყα👑_-_

ɯ&ʂ_-_📖🖋️📲
💓 The Nainarh Kd 💓

_-_ҽρ.6_10

*Last of free page's idan kinsan bakiyi payment ba, ki gaggauta yi domin ki ci gaba da samu Update's da zafi zafi akan lokaci 💃💃💃💃*

💞💞ƚԋҽ ҽxƚɾασԃιɳαɾყ ρҽɾϝҽƈƚ ʅσʋҽ ʂƚσɾყ Ⴆιƚɯҽҽɳ ρҽɾϝҽƈƚҽԃ ʅσʋҽɾʂ💞💞

*Zaynerb Mai Kyau*:

"Shi ne sunan a kafi sani na dashi, sannan ake kira na Especially ma ƙawayena da ƴan school namu.

Yammacin wata Ranar Lahadi ne, nayi sallama da Ahalina da suka rakoni har filin jirgi na ƙasar Jamus.

Cike da farin ciki, wani ɓangaren kuma da tunanin kewar mahaifina da kuma ƙanwata Afeefah nake a Ranar, harna shiga jirgi na saita zama na.

Karon shi ne farkon shigata public jet.

Sam ban wani iya É—aura belt na jirgi ba, domin kuwa ko da zamuyi wata tafiya, ko zuwa wani wuri da Ahalina, tofa sai dai Daddyn mu ko kuma Afeefah, tofa É—aya cikin su ne yake É—auramin, suyi ta min dariya. Ni kuwa babu ruwa na.

Yanzu haka ma ƙoƙarin da nakeyi ke nan, na ganin na ɗaura belt ɗin dai dai, sai dai kasawa nayi, don ban sakawa raina dama zan iya ba.

Tsaki kawai nake faman ja, ganin ƙiri ƙiri na kasa ɗaura belt na jirgi.

A ba za ta naga fararen hannayen sa biyu ya saƙalo ɗaya ta ƙugu na, sannan ya dai dai, cikin ƙanƙanin lokaci ya gama ɗauramin belt ɗin.

Galala nayi da baki ina kallon sa, yayin da idanuna suke lumshewa a hankali, ina kuma buÉ—e su saman kyakkyawar fuskar sa mai cike da kwarjini da haiba, sam na kasa masa magana, sai idanu dana zuba masa ina kallo.

"Hello Miss do you hearing, move on this side."

Ƙara lumshe ido nayi jin daddaɗar muryarsa tana ratsa dukkanin magudanar jini da jijiyoyin kaina kai tsaye izuwa ƙwaƙwalwa ta.

Ban matsa gefe kamar yadda ya so ba sai da ya kuma magana, sannan na dawo hayyacina.

Da sauri na matsa gefe ina zare ido, sam naƙi bari mu haɗa koda idanu dashi.

Har jirgin mu ya tashi sararin samaniya, yana daga zaune gefena.

Tabbas a jikina Inajin ana kallo na, sai dai da na juya sai naga bani yake kallo ba, idanun sa suna kan littafin dake hannun sa.

Haka har tafiyar mu tayi nisa dan kuwa mun kusa kai mintuna talatin da tashi a lissafina.

Wani irin jijjiga jirgin da muke ciki ya yi sannan wani irin ƙara ya ziyarci dukkan wani fil_adam dake cikin wannan jirgin, ga wani irin jijjiga na tashin hankali da jirgin yake damu yana gefe da gefe tamkar zamuyi ƙasa.

A mugun firgice ina zare fararen idanuna nake kwalla ihun neman taimako kamar yadda sauran mutanen dake cikin jirgin suke yi.

Sam ban san lokaci ba, sai ganina nayi ɗare ɗare saman jikin mutumin dake gefena, na ƙanƙameshi ƙam ina fitar da ihun wahala da tsoro.

Idanuna a lumshe wasu hawaye suna biyo wa, ganin cewa gaba ɗaya mutuwa zamuyi, gani da burika kala kala a duniya ban gama cika su ba, gashi zan mutu sanadiyar hatsarin jirgin sama, dan kuwa a wannan taƙin babu wanda ya yi tunanin zamu tsira.

Cike da firgici da tashin hankali nake faÉ—in

"Wayyo! Wayyo! Wayyo ni Zaynerb Ɗiyar Mai Kyau jikar ƴar mutan sudan... Shikenan kwana na ya ƙare zan mutu, shikenan, wayyo ni Afeefah Daddy Yaya Maleek zan mutu na barku, shikenan wayyo."

Ban ma san iya adadin abin da nake faÉ—a ba, kawai sambatu nake yi cike da tsananin tsoro, na kasa addu'a sai shirme.

Sannan ƙam na riƙe shi ina wannan zare ido da sambatu.

"Hey, Miss relax mana just relax, baki iya Addu'a bane sai ihu da sambatu ki nutsu mana."

Haka kawai yake faɗi yana kamoni a ƙoƙarin sa na ganin na kwantar da hankalina.

Ina jinsa ban kulashi ba, sai dai ina mamaki ganin babu tashin hankali ko tsoro tare da shi.

*After Twenty Four Hours*

Lumshe kyawawan idanuna nayi ina ƙare wa haɗaɗɗen filin sauka da hawan jirgin sama dame ƙasar Amsterdam nayi.

Awanni ashirin da wani abu baya, banyi tunanin zan rayu ba.

Sai dai cikin ikon Allah, jirgin aka samu ya tsaya da jijjgan da yake yi, sannan aka saukemu a wata ƙaramar ƙasa dake tsakanin Jamus da Amsterdam.

A wurin muka kwana domin kuwa dare ya yi sai washe gari wani jirgin ya kwashe mu ya iso damu Amsterdam É—in.

Wai ashe dalilin hatsarin da muka kusa samu da jirgin mu shi ne, shashashan Driver na jirgin bai duba lafiyar jirgin yadda ya kamata ba, ya tashi damu ya kusa jama na mu mutu.
Aikuwa yasha tsinuwa da zaki kala kala daga wurina dan kuwa bayan samun labarin da muka yi, ya sama rabon zagi da tsinuwa wurina, bama ni kaÉ—ai ba harda sauran jama'an jirgin.

Sai dai nasha mamaki kuma na shiga tunani, na rashin ganin wannan haÉ—aÉ—É—en saurayi da muka haÉ—u da shi a jirgin farko, da banyi ba wannan karon har muka sauka yanzu.

"Wata ƙila ma ya canza jirgi ne tun jiyan."

Haka kawai zuciya ta bani.

Ci gaba da tafiya nayi ina gurgura É—an keken da wasu abubuwa nawa suke ciki, ina kuma jan akwati na.

A ba za ta naji saukar wasu kyawawan furanni masu fidda ƙamshi na musamman da kuma wasu ƙa na nan balloon's saman kaina.

Washe baki nayi ina tarosu da hannayena.

Ban gama shan mamaki ba gaba É—aya mutanen dake zagaye dani a wurin suka fara tafi raf raf suna dariya.
Chapter 5 · 0% Book details