← Book details Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 14

Sashe 3

Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abu na biyu da ya kuma É—aure ma ta kai game da Auntie shi ne hana su zuwa Gidan su Juwairiya Jabir Bici da tayi.

Gefe É—aya kuma ga Budurwar da suka haÉ—u da ita acan gidan su Juwairiya É—in bayan sun je ba tare da sanin ita Auntie É—in ba.
Tabbas idan idanunta daidai suka gani a lokacin bala'in kamani taga suke yi ita da budurwar da aka ce ita ce*SARAUNIYAR KYAU* ta Abuja.

Gaba É—aya ta shiga cikin damuwa tarin tambayoyi ne masu yawa a tare da ita, sai dai bata san wurin waye zataje ya bata amsoshin su ba.

Yanzu haka tafiya take yi izuwa garden wurin Heesham.

So take idan taje taji dalilin sa da ya sa yace Humaira ta kira masa ita.

"A gaskiya ina cikin damuwa sosai, sai naji ina kewar iyayena, Allah Sarki ni gaskiya kawai zan je wurin Auntie ita da Abba nace su bani lambar Mahaifiyata indai tana raye ina so na ganta face to face, na tambaye ta dalilin da ya sa tunda ta tafi ta barni a tsumma na haihuwa bata kuma wai waya ta ba."

Da ire iren waɗanda tunane tunanen Jiddarh ta ƙari sa garden ɗin wurin Heesham.

*AFEEFAH*

Basu bar gidan Yaya Shahid ba har sai da taga ta É—an daidai tsakanin Aeezath da Mah'eesha, duk da dai ita Mah'eesha É—in ce sai a hankali, amma ita Afeefah É—in tayi abin da zata iya.

Around 4:10pm_-_

"Kaka ta tohm saduwar Alkhairi mu dai zamu yi gaba izuwa garin Abuja sai kun sake ganin mu idan akwai rabo."

Afeefah ta kammala faÉ—a wa Amma kakar tasu hakan a lokacin da take daga tsaye cikin palon kakar tasu.

"Afeefah dawo ki zauna ina da magana dake kafin ki fita."

Juyowa Afeefah tayi tana kallon kakar tasu da tayi maganar in seriously daga inda take zaune kamar kullum litattafan Addini gabanta tana dubawa, ba tare da musu ba Afeefah É—in ta koma ta zauna, yayin da Mah'eesha dake zaune saman 2sieter ta zuba musu ido tana kallo dan jin abin da ita Amma É—in zata faÉ—a wa Afeefahr.

"FaÉ—a min gaskiya kina cikin damuwa ko?."
Amma ta tambaye ta.
Da mamaki Afeefah ta kalla Amma É—in jin irin tambayar da tayi ma ta.

"Amma wai ni damuwa kuma tona menene ke nan?."

Ita ma Afeefah ta tambaya.

"Kalle ni nan da gaske nake tambayar ki bada wasa ba, ki faɗa min iyakar gaskiya kina da wani abu da kike ɓoyewa wanda yake sakaki a damuwa?."

Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke wasu siraran hawaye suna zubo ma ta, wai ashe duk ɓoye damuwar ta da take yi saboda kar a gane, sai da wannan Kakar tasu ta an kara.

Tana share hawaye wasu suna kuma biyo baya ta fara magana.

"Tabbas haka ne, Amma ina cikin damuwa sosai, kuma ina da wasu tambayoyi da nakeso a amsa min sai dai ban san waye zan tun kara da tambayoyin nawa ba."

Shiru tayi tana nazarin ta ci gaba da magana ko kuwa ta tsaya.

Tsawon mintuna biyu sannan ta ci gaba da cewa.

"Abu na farko shi ne, ina yawan yin mafarki a waÉ—annan kwanaki, mafarki ma munana waÉ—anda basu da daÉ—in faÉ—a.
Abu na biyu, gaba na yana yawan faɗuwa kuma ban san dalilin hakan ba, ji nake kamar zan rasa wani abu wanda yake da matuƙar muhimmanci a gare ni.
Abu na uku, jiya da muka tafi wani gida naga wata yarinya wacca muke matuƙar kamanni da ita sosai, kuma tanamin kama da Mahaifiyata da na sani a hoto, yarinyar an ce ita ce *SARAUNIYAR KYAU* ta nan Kano.
Abu na huɗu, munyi wani Challenge dasu Lailah akan za'a haɗa lambobi a kira waya, duk wanda ya ɗauka zan faɗa sunan sa da address nasa, kuma zamu ƙulla abota dashi ko wanene.
Toh anyi hakan komai ya wuce su Lailah suna takuramin akan saina kirasa.
Sannan tunda nake kiran sa sau uku kawai ya taɓa ɗauka, sauran kiran sai dai ace switch off, ko kuma layin baya tafiya.
Kuma ina yawan mafarki da muryarsa yana roƙona wai naso shi.🥺
Amma tsoro nakeji kar yaje da Aljani nake waya na rasa yadda zanyi da kaina ga gaba na da yake yawan faÉ—uwa na rashin dalili ki bani shawara kaka ta."

Ƙarishe maganar Afeefah tayi cikin zubda hawaye har tana shiɗewa.

Tsuru tsuru Amma da Mah'eesha dake gefe suka yi suna kallon Afeefah da tayi maganar, sannan Amma ta nisa tana mai girgiza kai tare faÉ—in

"Ayya, yanzu Afeefah waɗannan tarin damuwowin suna damunki amma babu wanda kika faɗa ma, kina da hankali kuwa, yanzu idan wani abu ya faru dake fa, ya ya kike so Mahaifin ku da ya ɗauki son duniya ya ɗaura miki uhum, yanzu abu na farko da zaki fara shi ne Addu'a ki riƙe Addu'a ƙam da azkhar na safe da marece, kana ki dinga yawaita karatun Alkur'ani mai girma, sannan ki rage yawan zama ke ɗaya, duk da dai nasan ba haka kike ba, ki riƙe Addu'a sosai kamar yadda na faɗa miki domin ita addu'a takobin Muminine.

Sannan da kika yi maganar Yarinyar, kika ce kuna kama, wannan abu mai sauƙi ne a wannan zamanin, domin ana samun irin haka, ga Misali nan ma da Doppelganger's ae kinga mutane ne ma banbanta masu matuƙar kama fiye ƴan biyu, koma waɗanda suka fito ciki ɗaya, saboda haka zai iya yiwuwa kamanni irin na doppelganger's ɗin kawai kuke yi ke da ita.
Sai maganar saurayi da kika yi, wannan zai iya yiwuwa son sa ne kawai ya kamaki shiyasa.😯
Sai Abu na ƙarshe da kika ce kina yawaita faɗuwar gaba, da kuma mafarkai marasa kyau, duk sharrin zuciya ce da kuma shaiɗan ki riƙe Allah kawai, sannan ki dage da Addu'o'i wannan shi ne, nima kuma zan tayaki kuma nasa ka a dingayi harda saukan Alkur'ani domin Allah ya kawo sauƙi a lamarin."🙏

Shiru Afeefah tayi tana sauraren Kakar tasu Amma, har sai da taji takai aya, sannan ta sauke ajiyar zuciya.

"Amma na gode sosai da nunatar wa kuma Insha Allah, zan kiyaye kuma na ci gaba da ƙara kaimi wurin yawaita Addu'o'i da kuma azkhar."

"Masha Allah, ae haka ake so, sai dai gaskiya Afeefah da'ace zaki bi shawarata da kin haƙura da shiga Gasar SARAUNIYAR KYAU na ƙasa da za'ayi, saboda Inajin tsoro sosai, cuz of kyawunki ya yi yawa sosai, zaki iya samun maƙiya ta ko'ina wallahi."

Mah'eesha ce tayi wannan maganar fuskarta ɗauke da damuwa, domin ita ma tuntuni taji faɗuwar gaba mara wanda hakan ke nufi da wani mummunar abu zai faru.👹

"hahahaha Mah'eesha ke nan. Ni na yarda da Allah, kuma na yarda da ƙaddara ko wata kala ce, saboda haka shiga gasar babj fashi, domin Zama SARAUNIYAR KYAU ta duniya burin mahaifina ne sannan kuma Mafarki na ne zama hakan."💃💃

"Saboda haka ki kwantar da hankali ki kawai Insha Allah babu abin da zai faru sai Alkhairi."🙏

*Ten Days To Go*
*Kwanaki Goma Gaba*

"Yauwa Saira wannan Chinese recipes ɗin muke buƙata yanzu yanzu domin kuwa Afeefah tasa mun kwaso yunwa wannan uban yawo Restaurant Restaurant da muka sha."

Lailah ta faɗa hakan yayin da take miƙa wa Ma'aikaciyar Restaurant na mahaifin nasu book da jadawalin recipes na Restaurant ɗin suke ciki bayan ta kammala duba abin da suke buƙata ita dasu Afeefah ɗin sai kuma Deejarh da tayi musu rakiya.

Ɗan murmushi Afeefah tayi tana gyara zamanta saman kujerar da take a kai, su uku ne ta ɓangaren su na musamman cikin Restaurant ɗin, ita da Lailah da Deejarh da suke zazzaune.

Sun sha yawo sosai domin kuwa Restaurant biyar suka je suka duba yadda komai yake tafiya, bisa umarnin Mahaifin su Mister Mai Kyau, da yake ƙasar Jamus bai dawo ba, abin da yasa sai sune suka je Ma'aikacin da yake kula da ɓangarorin baya ƙasar shiyasa Afeefah kawai ta ce zatae shi ne Lailah da Deejarh suka ma ta rakiya.

Zuwa halin yanzu sosai faÉ—uwar gaban da take fama dashi ya ragu sosai, dalilin dage wa da tayi wurin yawaita Addu'o'i da azkhar da kuma sallolin dare babu fashi, sannan wannan munanan mafarkan da take yi, ta rage yi sosai, Abin sai godiyar Allah.

"Kai kai kai gaskiya abincin Chinese duniya, kinji irin daÉ—in da nakeji kuwa Lailah?."

Deejarh ce take zubo wannan maganar yayin da take yagar wawukekan cinyar namar kaza da aka yi ma girki irin na Chinese da kayan haÉ—in su.

Lumshe ido Lailah tayi ita ma dai dai lokacin da takai loman spaghetti irin na Chinese da irin tsinken su baki, sannan bayan ta lamushe, take faÉ—in.

"Kedai Deejarh bari kawai ae ina faÉ—a miki abincin Chinese ya yi ba'a Magana koba haka ba Afeefah?."

Tayi maganar tana mayar da kallon ta akan Afeefah da tayi shiru tanaso ta tabbata tarwa da kanta sautin da take ji yana fitowa daga ina ne kuma na menene?.

Juyawa tayi sai tin hagun ta nan ta hangowa idanunta abin da take so tabbatarwa.

Matashiyar mata ce wacce ba za ta haura 27years ba, da tsohon ciki tare da ita, tana zaune daga gefan su, nishi kawai matar take fitarwa na wahala da alamu haihuwa ce tazo ma ta.😓

Cike da azama Afeefah ta miƙe tsaye da sauri ta ƙari sa wurin ta, sannan ta kamo matar, riƙe ta tayi ƙam, tana ƙwalawa su Lailah kira hardama Saira.

"Saira na ce akwai wani spare room ne wanda za'a iya haihuwa a ciki?. Na lura ta galaɓaita sosai bazai yiwu a kaita hospital a halin da take ciki yanzu ba."

"Eh Miss akwai wani, bari na taimaka Miki a kaita ciki."

Saira tayi maganar tana ƙari sawa sannan suka kama matar ita Afeefah suka shiga da ita cikin wani spare room dake can gefe cikin Restaurant ɗin.
Chapter 3 · 0% Book details