← Book details Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 14

Sashe 6

Sarauniyar Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayin da daga gefe kuma wasu samari da ƴan matan turawa suka fara sakin kiɗa da wasu ababen ƙila dake hannayen ko wannen su.

Ban gama shan wannan mamaki ba, wani abin mamakin ya kuma faruwa sakamakon Juyowar da ya yi yana fuskan tana hannayen sa riƙe da flower's ya tsuguna ƙasa kusa dani fuskar sa akaina bakinsa yana furta kalmar.

"I Love You...Do You Winning To Marry Me?..."

Hakan yake furta wa
A gareni....

Yayin da mutanen wurin cikin tafi suke faÉ—in.

"Say something for him, please say you love him please please."

Haka kawai suke faɗa suna ƙara wa, yayin da shi kuma gwanin idanunsa suke kaina yana jiran amsa na, kuma bai fasa daga miƙo min furannin da yake yi ba.

Tsaban mamaki da al'ajabi kasa magana nayi, na zama tamkar Statue ina kallon su gaba É—aya mutanen dake wurin, sannan na mayar da idanuna akan sa.

Tabbas Guy É—in Jirgi ne, toh menene yake nufi da wannan bazatar nasa.

Abin tamkar wani shirin Film, da za'a ga saurayi ya yi surprising masoyiyar sa irin wannan.

Dariya nayi dan kuwa wannan abin dariya ne a wurina, banda haka kawai daga ganin sarkin fawa a kasuwa sai Miya tayi zaƙi?.....🤔

Kallmashe ƙafa ɗaya nayi saman ɗaya ina gyara tsayuwata tare da gyara goyon da nayiwa backpack ɗi ta, na wani juya idanu fuska ta ɗaure da murmushin rainin wayo nake faɗin

"Kai! Lallai ma kai ɗin nan, toh gaya maka aka yi niɗin wata ƴar Baba nace da zaka shirya wannan ƙaramin wasan domin jan hankalina iyye, bani amsa ta."

Nayi maganar ina kallon sa sannan na ci gaba da cewa

"Toh wannan salon bai burge Zaynerb Mai Kyau ba a canza wani."

Na faɗa hakan ne dan ina da tabbacin cewa baisan sunana ba, toh na faɗa ne saboda ya riƙe aha.🤣😁

*The Next Day*

Zaune nake a palon Gidan Madam Joy wacca na sauka Gidan ta, domin bani da burin zama a É—akunan makarantar da zan fara, Shiyasa Daddy ya nema min Gidan wannan Baturiyar.

Dariya kawai nakeyi na tuna abin da ya faru jiya a Airport.

A lokacin koda na faÉ—a abin da na faÉ—a jan Akwati na nayi na nufa motar drivern Madam Joy da yazo É—auka na.

"Ke Kyakkyawa ta ki sani muddun muka kuma haɗuwa a gobe, tofa tabbas kina so da ƙauna na."

Ya yi maganar cike da Qwarin gwiwa cikin Murmushi yana bubbuga faffaɗan ƙirjin sa alamar tabbatarwa.

A lokacin Murmushi mai tsada nayi ina basa amsa da faÉ—in

"Ina maka fatan rashin sa'a."

Dariya na kuma yi tuna hakan da nayi, in banda abin sa ma, ae ba yau zan fara zuwa school ba, sai next week.

Ina cikin haka Lovely Ƴa ɗaya tilo wurin Madam Joy ta fito zata tafi company na Architecture's don zaɓar kalar gidan da zata zauna ita da Saurayin ta bayan sun yi Aure, don Auren nasu ya kusa.

A lokacin naji ina son ganin yadda birnin Amsterdam yake dan ban taɓa zuwa ba.

Saboda haka magana nayiwa Lovely akan ta jira na shirya zan karata.

Bada ɓata lokaci ba, na shirya cikin Gown doguwa har ƙasa ta Shadda galilan milk color sannan ba tare da na ɗaura kallabi ba na yafa Veil ɗina shima brown kalar aikin dake jikin Gown ɗin sannan na saka flat shoe.

Na fito Palo wurin Lovely dake jirana muka fita zuwa mota, sannan muka É—auka hanyar company.

A motar muna zaune na kalla Lovely ina faÉ—in.

"Ni kuwa Lovely menene sunan mamallakin company É—in da zamuje ne, da kuma sunan É—an sa, sannan É—an nasa shekarun sa nawa?."

Na jero ma ta tambayar don ina da dalili.

Bani amsa tayi cikin turanci da faÉ—in

"Sunan sa Mr.John ɗan sa kuma Andrew yana karatun injiniyanci ɓangaren gine-gine."

"Okay..."
Na furta bayan ta faÉ—a hakan.

Da isar mu katafaren company ɗin muka fito daga motar mu, sannan muka shiga ciki, Elevator muka shiga domin ƙara sawa office na MD. Na company ɗin.

*After Some Minutes*

Zare fararen idanuna kawai nakeyi ina haɗiye yawu, tunani nake anya kuwa wannan mutumi mutum ne kuwa?.🙄

Fisabilillah nan ma sai da yasan yadda ya yi ya biyo ni?.😚

Hannu nakai zan É—auka cup of coffee da aka kawo mana ni da Lovely.

Cikin rashin sa'a kuwa muka haÉ—a idanu dashi.

Ƙayataccen Murmushi ya yi min yana mai kashemin ido ɗaya.

Da sauri na kawar da kaina gefe, ban kuma yin gigin kallon sa ba, har suka kammala maganar da suke yi.

Kallon na Lovely tayi tana faÉ—in nazo mu koma gida sun kammala.

"Am nace ba, ki É—an bani aron ta five minutes kawai?."

Ya yi maganar yana kallon Lovely É—in.

Girgiza kai tayi tana faÉ—in

"Okay.."

Sannan ta fita, da kallo na bita, Lallai ma Bature babu kai.

Yanzu daga cewa ta bashi arona ta amsa lallai.

"Toh ya ya shin yanzu zamu iya magana da kyakkyawata kuwa, nasan dai zuwa yanzu ta kware min?."

Murmushi nayi ina juya idanu sannan na juya da kujerar da nake kai ina fuskan tar sa, nake tambayar sa.

"Garin ya ya, me yasa?."

Murmushi ya yi sannan ya gyara tsayuwar sa yana bani amsa da faÉ—in

"Duka saboda ke, jiya bayan rabuwar mu a Airport ban zauna ba, har sai da nasan gidan da kika sauka, nasan matar gidan da Yarinyar ta, na kuma san dalilin da zai sa Ni Da Ke mu sake haɗu wa yau, gashi kuma mun haɗun."🥰

Ya yi maganar yana sakin kyakkyawar Smile 😎

Taɓe baki nayi sannan na miƙe na ƙari sa kusa da shi Sannan na ja tunga na tsaya.

Hannu nakai na É—an kamo Tie na shirt É—in jikin sa, ina faÉ—in

"Humm, babu laifi, You will try, sai dai fa karkayi tunanin zuciyar Zaynerb nan kusa take, um'um kaɗan hakan ya burgeni fa, ka ƙara zage damtse wata ƙila nayi tunani akan ka, Malam..."

Shiru nayi dan ban san sunan sa ba, ɗaukar handbag ɗi ta nayi, sannan na nufa ƙofa, na kama handle na ƙofar zan fita najiyo daddaɗar muryarsa yana faɗin

"Okay, babu damuwa, sannan naji daɗi da hakan ya burgeki, zan ƙara zage damtse kyakkyawata kafin nan, Aasief nake karki manta da wannan."

Murmushi nayi ba tare da na juya ba nake faÉ—in

"Ina maka fatan Alkhairi Malam Aasief, zan zuba idanu domin ganin naka salon a soyayya."💓

*Ten Days To Go*

Ƙara kallon agogon Apple dake hannuna nayi, yau tsawon kwanaki shida ke nan da fara zuwa ta University.

Kuma tun daga wancan Ranar bamu sake haÉ—u wa da shi ba.

Na ɗan shiga damuwa kaɗan, don ina tunanin wata ƙila, yaji bazai iya bane, ya kama kansa.

Tsaye nake ina jiran taxi domin Drivern Madam Joy da yake zuwa ɗaukata bai sama damar zuwa yau ba, sakamakon matar sa dake naƙuda, ita kuma Lovely bata state ɗin ma gaba ɗaya, yayin da Madam Joy aiki ya yi ma ta yawa a office saboda haka ba za ta sama damar zuwa ɗaukata ba.

Ba tare da tunanin komai ba, na shiga cikin taxi É—in da tayi parking a gaba na, ina faÉ—in Address da za'a kaini tare da tambayar kuÉ—in

"Okay...Madam babu damuwa ae ba saikin biya komai ba, kyauta zan kai ki."

Da sauri na dakata daga É—auko kuÉ—i da nakeyi a handbag É—i na, cikin firgici na juya ina kallon sa.

Ba kaɗan ba naji daɗin ganin sa, sai dai ban nuna masa ba, saima kyaɓe fuska da nayi ina faɗin

"Har yanzu Ban san komai akan ka ba, gashi kanata bibiyata."

Nayi maganar ina kallon gefen titi dan kuwa so nake nasan wani abu a kansa, shin kuwa shiÉ—in Balarabe ne ko kuma Bature?.

"Firstly Sunana Mohammed Aasief Yaro wajen Hasheem Mai Waje!."

Ni da Ahalina gaba ɗaya muna zaune ne a ƙasar America. Ina karatun Injiniyanci ɓangaren gine-gine sannan ina matakin ƙarshe. Hakan ya isa ko kina son sanin wani abun?."

Ya yi min maganar yana kallona ta madubin motar.

Fuska ɗauke da murmushin dana kasa ɓoyewa nake cewa

"A'a hakan ma ya isa."

"Uhum bani labari mana?."

"Labari kuma akan ne?."

Na tambaye shi

"Akan ki mana da kuma Ahalin ki."

Ya bani amsa.

Shiru nayi dan ban san ta yadda zan fara basa labari akan kaina ba wallahi.

Wawan burki yaja da ƙarfi wanda sanadiyyar hakan sai da nayi gaba na bugu da kujera sannan na dawo baya kaina ya bugu.

Cikin zafin rai ya ɓalle murfin motar ya fita, ƙari sawa wurin Baturen da motar sa ta bugi namu muka kusa hatsari ya yi.

Cikin zafin rai da ɓacin sa ya shiga bawa wannan Baturen mari yana ƙara wa.
FaÉ—i yake.
"Baka da hankali ko wato kasha giya kazo kana tuki salon kaja mana hatsari."

Bugun sa yake yana ƙara wa haɗe da Ball da shi, a titin.

Cikin sauri na buɗe motar na fito sannan na ƙari sa wurin ina jansa baya cikin basa haƙuri ganin yadda yake dukan Baturen babu ji babu gani, kuma nasan duka akaina ne, sakamakon buguwar da nayi ne ransa ya ɓaci, jansa baya nake ina basa haƙuri cikin faɗin

"Ya isa Aasief ya isa haka baka ganin jini kake fitar masa ya isa mana."

Bai kulani ba sai ma ƙara kaimi wurin ball da Baturen da ya yi.

*Tashin Sence*

Zuwa lokacin fa na fara tsorata da irin zuciyar da yake da shi.
Baya nayi ina kallon ikon Allah cikin rashin abin yi.

*A Taƙaice*
Bamu muka bar titin nan ba har sai da police suka zo suka É—auka report.

Da kyar suka barmu muka tafi wai dan ma an gwada Baturen ne an tabbatar giya yasha kuma yake tuƙi.

Fushi nayi sosai da abin da ya faru domin kuwa ko na gansa bana masa magana domin tsoron irin zuciyar sa nake.

Tsawon Sati guda muna hakan Kullum sai mun haɗu, takai har makarantar mu ya fara zuwa domin na kulasa, amma naƙi.

Daga ƙarshe da takurar sa ya isheni haƙura nayi.
Muka ci gaba da mu'amula kullum kafin ya tafi nasa makarantar sai ya fara zuwa ya kaini nawa sannan ya wuce.
Chapter 6 · 0% Book details