← Book details Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 14

Sashe 9

Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nene tayi mata kallon tausayi, sannan ta ce yanzu idan ramar ta kare ya za'ayi?"
"Nima ban sani ba Mami,na dai san in ina so ban samu ba mutuwa zan yi, yanzu kam na koshi sai kuma gobe in Allah ya kaimu".

Mami ta juya ta fita tana fadin "on weekends zaki raka ni asibiti, mutum baya period ai gara a duba shi a san dalili".

Cikin damuwa tace "Nene, is there any problen with that?" Nene ta dafa kafadarta tace "don't worry".

Sannan ta fita.

Nene ta ce kar ta damu, amma sai ta ji ta damun, ko wata cuta ce rashin yin period din?

Nene na fita dakin Yafendo ta nufa, ta samu kujera ta zauna, tace "Yafendo ko kin lura da abinda na lura da shi game da yarinyar nan?"
Yafendo ta ce "kwarai kuwa, kallon ta kawai nake, in kuma jira in ga ko zaki kula da kiwon da Allah ya baki.

Shi aure dama in Allah bai nufi karewar sa ba wa ya isa ya karar da shi?

Da zata ji shawara ta gara mata ta koma gidan mijin ta ta cigaba da hakuri irin wanda kowacce mace ke yi a gidan auren ta, ba namijin da yake cikakke a komai dukkan su suna da gibi, amma yadda na lura tafi jin dadin rayuwar ta da mu a haka bata ko so a dago mata zancen sa".

"Kwarai wannan haka ne, bari in je in samu Daddy muyi magana a kan ta".

Yana sauraron radio Jamus a 'yar karamar rediyon sa lokacin da Nene tayi sallama ta shiga.

Ya amsa mata, sannan ta samu gefensa ta zauna.

"Ranka ya dade magana ce ta kawo ni, akan yarinyar nan Rahinah".

Ya rage sautin rediyon sa ya bata hankalin sa.

"Ina zargin ciki ke gareta".

Radeyon hannun Ambasada ce ta subuce kasa, tace "wallahi alamu sun gama nunawa, amma duk da haka ban tabbatar ba""kuje asibiti a tabbatar pls" Mami tace "insha Allahu, amma in ya tabbata cikin ne yaya zamu yi da ita ga karatun ta mai tsayi?" Ambasada ya nisa yace "yadda zamu yi da Safeenah, idan irin haka ta same ta".
****
Rahinah bata san me ta rako Nene yi a asibiti ba, amma tunda suka zauna a gaban likita ya kuma ce ta bashi fitsarin ta komai ya fara kwance mata.

As a medical student ta san awon fitsari na nufin abubuwa da yawa.....awon cuta ko awon ciki!

Don haka kafin sakamako ya taddasu, ta yi ligib cikin tashin hankali da tararradi.

"She's two months pregnant".

Likita ta fadawa Nene ita kadai, bayan ta ce Raheenah ta je reception ta jira ta.

Sannan ya bata shaidar hakan a rubuce.

Nene ta yi masa godiya, sannan ta fito ta tadda ita suka tafi, a hanya take gaya mata an ga shawara (jaundice) cikin fitsarin ta.

Raheenah tayi wani ajiyar zuciya, feeling relieved.

Har suka zo gida zancen rama take wa Nene, wai yanzu idan ranar Yafendo ta kare ina zata sa kanta?

Nene tace "sai ki ci salad, ai shima ganye ne""amma bai da dan tsami-tsaminnan kamar na rama" murmushi Nene tayi, tace "sai a masa vineger".

Suna sauka a mota kuwa ta tafi dakin Nene cin rama.

Kwana bakwai kenan bata iya cin komai banda ramar, har yau gashi rama ta kare, babu kuma inda za'a sameta a Jamus.

Don haka tun safe take cikin kunci, haushin kowa ta ke ji, da Ahlan ya shigo yana mata surutu sai ta shige toilet ta rufe kanta don bazata iya korar sa ba.

Nene ta shigo dauke da plate a rufe ta sameta, "Rahinah yau bazaki makaranta bane?

Yara duk sun fita sun barki, ga wannan ko a mota sai ki ci kada ki tsaya ci ki makara, kin dai san kina da nisa".

"Nene yau ban iya zuwa makaranta" ta fada hawaye na ciko idon ta.

"Sabida me?""I'm not feeling well, sabida tun jiya ban ci rama ba, Yafendo ta ce ta kare""try this" ta fada tana mika mata plate din hannun ta.

Bata yi musu ba ta karba ta bude, salad ne Nenen ta hada mata da kanta, yaji kuli da vinegar da tumatur, cocumbrr da albasa.

Wani mugun yawu ya gudana a bakin ta, ta karba tun daga tsayen ta soma ci kafin ta zauna.

Amma ko loma hudu bata yi ba ta dinga kwaro amai kamar zata amayar da hanjin ta.

Tun daga ranar komai ta ci sai ya dawo, ta galabaita matuka, karfin jikin ta ya yi kasa sosai.

Ambasada yace da Nene ta kaita asibiti, koda taimakon da zasu yi mata abinci ya dinga zama a cikin ta.

Suna asibitin likita ya riketa, domin yace she's 60% dehydrated.

Aka sa mata drip nan take.

A ranar ne Ambasada ya kira Habib a waya.

"In ka samu lokaci kazo 'Sachsenhausen Hospital' da daddare ina son ganin ka".

"Insha Allah i will".

Ya fada cike da girmamawa.

Karfe takwas na dare a Sachsenhausen ta yi wa Habibu Nahuche.

Yana sanye da Native Hausa Attire dinsa na shadda sharaton ruwan makuba, ya kafa hula a gaban goshin sa ruwan toka mai turuwa sosai (deep grey), yayi kyau kamar koyaushe amma kallo daya Ambasada yayi masa ya gane muguwar ramar da yayi cikin watanni biyu da yayi bai ganshi ba.

A wajen parking motoci suka hadu, direba ya sauke ambasada, shikuma taxi ta sauke shi.

Ambasada ya bashi hannu sannan tare suka taka zuwa dakin da aka kwantar da Rahinah.

Daga ita sai Nene a dakin.

Kamshin turaren sa ne ya fara shiga hancin Raheenah, wani kamshi mai tasirin da bazata taba mantawa ba....da sauri ta juya kai zuwa bakin kofar shigowa.

Idanun su suka hadu, wanda hakan ya haifar da wani irin shock ga Rahinah dake kwance, domin ta ganshi ne ba zato ba tsammani.

Yayin da Habibu Nahuche ya tsura mata ido, gabadaya ta zabge ta lalace, maimakon ya zo ya ganta very healthy and jovial tunda ta samu rayuwa yadda take so?

Ta karbi 'yancin ta da take ikirarin ya danne mata?

Banda girman idanun ambasada da yake gani babu abinda zai sa shi amsa wannan kiran, don bai ga dalilin sa ba.

Tunda komai ya kare a tsakanin su.

"To zauna mana kun tsaya kuna kallon-kallo kamar zakaru" Ambasada ya furta masa sounding fatherly.

Ya nemi guri can nesa da gadon da take kwance ya zauna.

Wani irin abu na hankoro a zuciyar sa, ta shiga bugawa fat-fat-fat, bai san idanunsa sun yi kewar ta ba, sai yanzu da suka ganta kwance a gaban su, hatta zuciyar sa neman fitowa take daga tsakiyar kirjin sa....shikadai ya san halin ragaitar da ya samu kansa cikin wadannan watannin biyu masu kama da jiran tashin alkiyama a gare shi.

Rahinah ta dauke kai daga kallon sa, ta mayar wani gefen daban, tunda suka rabu ko sau daya bata ji kewar sa ba.

Bai bar mata wani abun tunawa a zaman da tayi da shi ba na kwanaki bakwai, banda kyakkyawar fuskarsa ta Rumawa data zauna a zuciyarta ta ki fita.

"Na kira ka ne Habib, don in sanar da kai Raheenah na da ciki na watanni biyu".

Daga Habib har Raheenah, a tare zuciyarsu tayi wani irin dokawa, ta doka ta sake dokawa ta ci karo da bango.

Idanuwan Rahinah kamar zasu fado kasa.....jin maganar tayi tamkar saukar aradu a kunnuwan ta, zata rantse ko mutuwar Dada da aka gaya mata a waya bata firgitata ta ruda ta kamar abinda Ambasada Shehu ya fada yanzu ba...

Yayin da Habib, Mustapha Nahuche ya wani irin lumshe idanunsa.

Wani albishir ne zai ce ko bushara da ba'a taba yi masa kwatankwacin sa ba.

Wani irin maganadisu ya ji yana fizgar zuciyar sa akan Raheenah da abinda ke cikin ta..

The feeling is so sweet da bai taba jin mai dadi a zuciyar sa kamar sa ba...nitsatstsen SO!

A hankali ya bude idanun sa akan Raheenah, wadda ta tamke nata idanun tamau, hawaye na zirara ta gefe da gefen su.

Which means she's not happy at all, she's mourning kaddar da ta afka mata rana daya.......ta tabbata ta rasa farin cikin ta daga yau, bata ga amfanin sauran rayuwar ta ba..

Ashe dai ta yi gudun gara ne ta tadda zago.....

Habib Nahuche bai shigo rayuwarta don ya fita a lokacin da take so ko yake so ba.

Kaddara bata kare tsakanin su ba, mai hada eternal dangantaka ya riga ya hada wato gamayyar jiki, wadda a yau ta maida ita matar Habib a karo na biyu har sai ta haife masa dan sa ko 'yar sa wanda take jin ba abinda ta tsana a duniya sama da kawo shi duniya...

A fili ta fada ".......bai yi sa'ar mahaifi ba, he's but selfish by nature wato mutum ne mai son kan sa da yawa (tana nufin Habib din).

Muryar Ambasada Shehu ta cigaba da ratsa mugun shirun da ya ratsa kamar daukewar ruwan sama.

"My dear Son and Daughter isn't it high time you reconcile?

Tunda kun ga yadda kaddara tayi daku, kowanne Da yana burin ya tashi tsakanin iyayensa biyu, broken home shine babbar matsala ga tarbiyya da rayuwar kowanne yaro, rayuwa duka 'yar afuwa ce, in kuka afuwantawa juna kuka kuma zauna kuka gano matsalolin ku i'm sure zakuji dadin zama da juna tunda har ga rabo a tsakani...".

Habibu yasa hanky dinsa ya goge gumin fuskarsa da hawayen da suka cika masa ido, wadanda yake da tabbacin na farin ciki ne.

Ya dubi Raheenah wadda ta kautar da kai gefe tana jin tamkar Daddy na diga mata narkakkiyar dalma a kirjin ta da ya ce wai ta komawa auren Habibu.

Ya ce "ranka ya dade ni bani da matsala da hakan in har ta amince, abinda ba zanyi ba shine sake zaman aure da ita ba tare da amincewar ta 100% ba".

Rahinah ta juyo a hankali zuwa side din da yake, a hankali ta ce "to in dai ko amincewata kake bukata to har abada bazamu koma ba, once beaten twice shy.
Chapter 9 · 0% Book details