← Book details Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 14

Sashe 7

Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ranka ya dade idan ta barni zan cutu, zan shiga wani hali, zan fada wata rayuwa daban da ba tawa ba, na dandana aure na san yadda yake, a matsayin ka na namiji kamana zaka fahimci abinda nake nufi, zamana ba aure babbar matsala ce a gareni yanzu.

Ka dubi al'amari na da idanun dalci, ta fadi duk abinda take so na yi, na yi alkawarin kwatantawa.

Nima na san ina da wasu odd dabi'u wadanda ta kasa jurewa.

But i promised to become a changed person, a changed man for her, duk yadda take son na koma".

Da sauri Raheenah tace "saidai kai auri wata, ko dole sai ni?

Idan ma ka ki saki na bazan taba komawa gidan ka ba sai dai akai gawa ta".

Habibu yayi mata wani fitinannen kallo, kafin yace "your excellency i will do as she wish, saki nawa zan rubuta mata?"
Ambasada ya dafe kansa, bai so hakan ba, ya so su yi sulhun, couple din look perfect together, kowannen su ya san ciwon kansa.

Sannan shima yana backing aure kowanne iri ne sama da rayuwar da 'ya'yan musulmi ke yi a kasashen ketare.

Ya so ya ga laifin Habibu kan method din da ya bi ya auri Rahinah, wanda shine babban abinda ya ja masa kiyayyarta, sai ya ga cewa ko shine a matsayin Habibu bai da wata hanya banda hakan in dai yana son ta, he can relate dalilin sa na yin auren afujajan a matsayin sa na namiji, (don ya kaucewa zina ne) kuskuren sa daya gaggawa, ya aureta babu fahimtar juna.

Kafin ya samu abin ce musu su duka, Habibu ya dauki takardar dake bisa tebir, mai tambarin Nigerian Embassy Germany, ya zari biro a gaban suit din sa, ya rattaba saki a jiki, ya mikawa Raheenah.

Idanuwan su suka hadu, suka sarke na 'yan sakanni, sai ta ji hankalin ta na son barin gangar jikin ta.

Ta kasa mika hannu ta karba, because she never expects him to do it so quickly.

A wurin Habibu kuma daga yau ya gama da babin Raheenah.

Zai bude sabuwar rayuwa waadda babu mata da tunanin lamarin su cikin ta.

Ajiyewa yayi a gaban ta, ganin cewa ta gaza karba, ya nemi iznin tafiya daga Ambasada, Ambasada ya gyada kai cike da tausayin yaron, a cikin kwayar idanun sa ya gano kwantacciyar soyayyar Raheenah zallah.

Amma bravery din da yaron ya nuna ya burgeshi.

Fatan sa kada ya fada wata mummunar rayuwa bayan tasa, kamar yadda ya fada a baya.

Bayan fitar Habibu Nahuche, Ambasada Shehu ya dubi Raheenah wadda ke sharar hawaye, hawayen da bata san dalilin su ba; as she is supposed to be happy, amma sai taji wani bangare na can kasan zucciyar ta baya farin cikin, ji take kaman ta yi mistake din da bazata taba iya gyarawa ba.

Ga dai 'yancin ta samu, na yin rayuwarta freely a kasar Jamus, aunty Laura tace zata iya zama internationalprostitute, wani matsanancin tsoro da firgici ya kamata, kodai auren Habibu GARKUWA ne duk da babu irin soyayyar da take bukata a cikin sa?

"This is what you want my daughter, what is your next plan?"
Ya fada sounding fatherly, kamar shi ya haife ta, bata taba samun soyayyar uba ba, sai taji wannan kulawa ta Amabasada ta bata dan guntun hope na ta cigaba da rayuwa, zata samu mai kulawa da ita bayan Dada, zata samu kariya a karkashin kafadun sa, zata samu mafaka a karkashin alfarmar sa.

"Makaranta zan koma, karatu ya wuce ni sosai, zan dage ne in kamo abinda ya tsere min.

Amma ina tsoro, ina jin tsoron zaman hostel sabida rayuwar da ake yi acan tana tsorata ni".

"Nayi miki umarnin zama cikin iyali na, idan har zaki tsare mutuncin kanki, ki kuma maida hankali kan abinda ya kawo ki kadai.

Direban dake kai yara na makaranta zai din ga kaiki Cologne kullum yana dawo dake".

Raheenah don farin ciki sai ta fashe da kuka, ta gurfana gaban sa tana godiya, godiya mai tarin yawa, ta ji duk wata damuwa ta kare mata.

At last she will become what she want in life, Otorhinolaryngologist.
****
NEW PHASE
omai na rayuwar sa ya tsaya masa cak, ya kira wajen aikin sa ya ce bashi da lafiya, kasancewr rubutun thesis din sa na M.Sc yake yi baya halartar lectures, amma a zahiri babu inda yake ciwo a jikin sa, ciwon a cikin tsokar dake tsakiyar kirjin sa yake.

Rahinah Omar!

Rahina Omar!!

Rahinah Omar!!!

Ta shigo rayuwar sa da wani irin karfi, ta yi tasiri mai yawa a cikin ta, ta yadda har ya soma tababar hukuncinsa, anya bai yi kuskuren da bazai taba iya gyarawa ba?

Me yasa bai barta ta tafi duk inda take so da igiyar aurensa ba har zuwa ranar da Allah zai sake hada su?

A lokacin da TA HUCE take ganin zata iya zama da shi kuma goals din ta sun zama actualized?

Zuciyar sa nan da nan ta ce 'kalamanta ne".

Babu namijin da zai iya jure kalmar rashin 'so' babu sakayawa na fita daga bakin matar sa a bainar jama'a.

To idan so cuta ne, to hakuri ma magani ne, daga yau zai koyawa rayuwar sa juriyar rashin mace kowacce iri, koda kuwa ace da gold aka kera ta.

Ya soma tunanin watannin da suka rage masa ya bar kasar Jamus ba masu yawa bane, zai yi kokari ya kammala thesis din sa ya koma gida, ya fara maida kobo ya koma dari, watakila mata mai kudi suke so, watakila don bata gan shi da mota bane, watakila don bai da gidan kansa, ko kuma watakila don abinda yake ciyar da ita da shi bai isar ta, tunda in dai akan maganar soyayya ne ai yayi alkawarin canzawa, meyasa bata bashi dama ba?

An taba soyayya rana daya ne?

Wasu ma'auratan har su haihu basu gama fahimtar juna ba, ya kamata Rahina ta yi masa uzuri, uzurin da addini yayi wa musulmi umarnin sa har guda saba'in kafin su kama shi da laifin da suke tuhumar sa. kasancewar dukkan su bakin haure ne auren su ba zai zama kamar suna kasar su cikin iyayen su ba.

Yes, yayi gaggawa, but he has no option banda ya mallakawa ruhin sa abinda yake so don ya zauna lafiya.

Ya kamata ta duba lamarin sa, ta kuma gane gangar jikin sa ce a bukace da aure a lokacin ba soyayya ce priority ba.

In da ta yi hakuri, along the way soyayyar na zuwa kamar yadda ta zo ta lullube shi a halin yanzu.

Kwanan sa bakwai bai fita koina ba, yana jinyar da bata ciwon jiki ba a'ah, jinyar zuciyar da soyayya ta riga ta yiwa illah, amma ya yi alkawarin overcoming din ta da addu'a da jajircewa by been stronger, ba don kudin rent da yake biya ba barin aikin zai yi, ya dukufa wajen karasa proposal din sa.

Ya alkawartawa ran sa ba shi ba Raheenah, koda ita ce autar mata, ba zai kara zuwa inda ta ke ba, ko a hanya ya ganta zai dauke kai, ta je ta yi rayuwar ta yadda ta zabeta.

Wani sako na zuciyar sa na tabbatar masa da cewa watarana in ta gama bokon nata, when her dreams are born alive, she will surely come to sanin cewa ta yi sake da damar ta a baya, she will come searching for love wanda a lokacin zai yi mata wuyar samu.

Yes he accepted the fact cewa bai kyautawa Raheenah Omar ba, a takaitaccen zaman auren su, amma kuma wanene yake sama da kuskure?

Sai aka yi mana umarni da in mun zo gyara kuskuren mu a bamu dama, koda itace one last chance in the whole world.

Allah da Manzon sa sune kadai suke perfect a komai, shi dan adam ne, he must have his own flaws.

A yayin ne kuma wani tunani ya darsu masa, ko dai Rahinah bata da lafiya irin ta 'ya'ya mata ne?

She never appreciates auratayya.

Kuma kamar ma shine abinda tafi tsana a rayuwar ta.

Akwai mata masu irin wannan halittar sosai, wanda ba ciwo bane halitta ce, only caring husbands can understand and go along with them as such.

In ba haka ba ina dan adam zai zabi boko akan sunnar Annabi?

Koma dai menene shi an yi ta ta kare tare da shi, taje ta ji da bokon ta, in ta so ta zamo farfesa.

A dare na uku, ya soma samun sassaucin zuciyar sa, ya cire tunanin sake aure daga ran sa.

Ya soma haka wani wawakeken rami domin binne Raheenah a ciki ba don ta mutu ba, sai don ya samu sa'ida wajen gudanar da al'amuran cigaban rayuwar sa.

Sai a washegari ya samu kiran Hajiyar sa, Haj.

Kaltume Nahuche.

Bai san dalili ba yana jin kamilalliyar muryar ta cikin kunnuwan sa sai ya samu kansa da saka kuka.

Shi autan ta ne, ita kadai yake sakewa da, amma ko ita bai gaya mata auren da yayi ba, ba don komi ba sai don ya san bazata amince ba, kuma bazata taba bari ya auri yarinyar da basu san asalinta ba, besides, ta dade da kama mishi mata a cikin dangi.

"Hajiya kiyi min addu'a, ina cikin wani hali"
"Ko minene Allah ya sawwaka shi, ya zaba abinda yafi zama alkhairi, saura wata nawa ka dawo?

Don asa bikin ka da Shafa'atu kurkusa.

Kana dawowa sai ta tare, in ya so daurin auren sai a yi ba sai ka dawo ba".

"Hajiya ayi hakuri kawai, in ta samu miji ta yi aure.

I've nofeelings akan diya mace yanzu, an sha ni na warke, sai fatan cikawa da imani".

Zuciyarta ta narke, jin yadda yake magana in despair, la shakka wata ta karya zuciyar autan ta.

"Wacece ita?

Kuma a ina take?

Su waye iyayen ta?"
Ta jero mai tambayoyin guda uku a jere kuma a tsanake, Habib ya kwantar da kai akan masangalin kujerar falon sa, bai taba boyewa mahaifiyar sa komai na rayuwar sa ba, sai auren sa da Raheenah, kuma fada matan a yanzu bashi da wani amfani tunda auren ya riga ya narke, with no any form of bright memories.

"Sunan ta Rahinah".
Chapter 7 · 0% Book details