Sashe 12
Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A take ta kira ta jikin ta har rawa yake, ji take kamar Nene ta ga komai da ya faru, ita da Habibu a mota suna kissing.
Wani hawayen bakin ciki ya zubo mata, ta ji ta tsani kan ta, ta tsani karatun da ya fiddo ta daga gidan Ambasada, in bata yi wasa ba Habibu na gab da sake rusa mata rayuwa.
"Nene wallahi ina cikin library ne wayar kuma na barta a mota"
"Meyasa kika je makaranta baki jira ni na dawo mun je tare ba idan zuwan ya zama dole?
Kinsan Dr.
Yace ki daina zirga-zirga" ta share wani uban gumi daga kan goshin ta, tace "Nene i'm sorry littafai na je amsow na clinical assignment dina, kinga ma ban samo su ba, bazan ma kara zuwa ba har sai na haihu.
Zan gayawa Daddy a nemomin na saya kawai" Nane tace "better, me zan dafa miki kan ki iso?" Tayi murmushin samun relief tace "anything traditional""to shikenan zan miki tuwon alabo miyar ugu leaf da alayyahu da ganda da busashshen kifi, yayi miki?"
Wani hawaye ya bullo mata, ashe haka soyayyar UWA ke da dadi?
Allah ya barta da danta itama ta bashi kauna irin wannan.
Allah yasa kuma kada mutuwa ta raba su yana karami sai ya mallaki hankalin kansa ko da zata mutu.
Ya zamo cewa ta gama bashi duk wata kulawa da tarbiyyar da ya kamata ya samu daga gareta.
A wannan daren, daga Habibu Nahuche har Rahina Omar, babu wanda ya iya ya runtsa.
Dare ne mai matsanancin hazo, cikin watan Nuwamba, Habibu na nannade cikin bargo sanyin kasar Jamus na shigar sa, ba abinda yake so yake bukata a lokacin sai dumin matar sa Rahinah.
Amma ta wace hanya zai bi ya dawo da damar da ya samu a baya?
Masu iya magana dama sun ce opportunity comes only once in life!
Ya bata komai, ya dade da bata komai, ya riga ya bata rawar sa da tsalle.
Haduwar su a yau ta maida masa komai sabo in itsown special unique way..... girman Rahinah da soyayyar ta sun karu sun ninku sun hauhawa a zuciyar sa, ya fahimci abubuwa da dama wadanda a baya bai sani ba; Rahinah na daga cikin kasaitattun mata da samun kamar su sai an tona.
Irin matan nan ne one in million wadanda duk namijin da Allah yayiwa baiwar mallakar su ya gama bashi rabin addini sa, ya gama bashi farin cikin rayuwa, da duk wani jin dadi dake cikin ta.
A yau ya amince da abinda a baya ya ki believing da gangan.
Cewa zai iya rayuwa babu Rahinah, zai iya hakuri da rayuwar sa single ba tare da Rahinah cikin ta ba.
A yau ya yarda ya amince rayuwar sa bazata taba zama straight ba ba tareda Rahinah a gefen sa ba.
Ko zata yarda ta saurareshi idan ta haihun kamar yadda ta yi alkawari?
Shi kuma zai yi komai don dawo da ita cikin rayuwar sa cikin martaba da mutuntawa, dadin dadawa soyayya mara yankewa har fiye da wadda bata tsammani.
Daga wannan ranar yake bincike, wani irin bincike na yadda ake tafiyar da soyayyar mata.
A rubuce-rubuce na masana ilmin psychology (self-help books and self-reflection).
Ya samo wasu tips guda goma wadanda suka ce (How to keep your woman and make her love you forever).
Marubucin ya ce; cikin abubuwanda zasu rike maka soyayyar matar ka sun hada da;
-work on yourself ; ka yiwa kanka self-evaluation; ka cancanci ta so ka ko a'ah?
-listen to her (and i mean really-really listen); ka saurareta akan duk abinda ta zo da shi da cikakken attention ka bata hankalin ka a lokacin da take bukatar hakan.
-learn how she prefers to be loved; ka duba abinda tafi so ka nuna mata soyayyar ka da shi.
-give her gifts (ka kasance mai yawan yi mata kyauta, kyauta tana kara dankon kauna).
-be honest with her (ka zamo mai gaskiya da kyakkyawar manufa akan ta).
-respect her (ka girmamata) and treat her with this respect.
-find creative ways to tell her that you love her (ka zama mai iya kirkirar hanyoyin gaya mata yadda kake son ta in your own special way).
-allow yourself to be vulnerable; wato ka dinga nuna mata raunin ka. (Allow yourself to make mistakes and admit to them.
Allow yourself to be real and true and not hide any of yourself from her.
Don't be afraid to cry in front of her.
And don't be afraid to let her cry, too.
Vulnerability allows for deep connection and bonding
in a relationship.
If you can't be yourselves
in your most raw forms, how are you supposed to feel safe building a whole life together?"
Habeeb Nahuche sai ya ga cewa duka wadannan tips din da wannan masanin ya zano duk zurfin ilmin sa shi bai mallaki ko daya ba!
Bai taba nuna wa Rahinah dayan su ba, yet yana blaming din ta da kasa son shi duk cancantar sa.
Ita soyayya ta gaskiya ba ta ta'allaka da appearance din mutum, but the way he demonstrates himself.
Ya yarda duk ilmin ka ilmi baya taba karewa a duniya, saidai ka dauki iya wanda zaka iya ka bar ragowar.
Inama!
Inama!
Inama Rahinah ta yarda ta sake bashi dama koda sau daya ne a rayuwar su???
****
A nata bangaren, Rahinah Omar, kwana tayi tunanin abinda ya faru a yau, tana mai tariyo komai dalla-dalla.
Idan zuciyar jin tausayi ta kutso, sai zuciyar neman kwatar 'yanci ta hambare ta.
Mutumin da bai ji tausayinta ba, ita akan me zata ji tausayin sa?
Yana son ta koma ne don bukatun kansa amma bai taba tunanin ya tambayeta asalin ta ko na iyayen ta ba.
Wanda ke kara tabbatar da cewa ba damuwar sa bace personal life din ta, abinda yake yimawa kawai shine a gaban sa.
Ita wannan soyayya ta Habibu ta kasa ganeta, domin ta hada biyu da uku bata bata ma'ana ba.
Tana burin auren mijin da ke matukar son ta, wanda zai rungumi maraicin ta kada yayi amfani da shi ya cutar da ita, wanda zai so ta da dukkan zuciyar sa.
Amma Habibu fa?
Ta tabbata ba don cikin nan ba da daga ranar da ya sake ta bazai kara waiwayota ba tunda duk abinda yake so daga gareta ya riga ya same shi.
Tsaki tayi ta juya a hankali don taji dadin kwanciyar ta, sai taji gefen wuyan ta na kamshin Carolina Herrera (men) har zuwa lokacin.
Abinda ya tuna mata da incidence din.
Is what happened Haraam?
Bata sani ba, in haramun ne tana neman gafarar Allah, domin kuwa bata da laifi, laifin ta shine kasa yi masa gardama wajen binsa tamkar rakumi da akala.
"Ya salamu sallim".
Ta fada a fili.
Amma wani sako na zuciyar ta na gaya mata it's not haram din, tunda har yanzu cikin iddah take.
Kuma abinda addini ke so a wannan tsakanin shine su yi sulhu.
Sulhun da bata jin har abada zata yarda da shi.
Washegari Nene ta rakata anti-natal da suke zuwa duk sati, likita ta dubata sosai ta kuma ce baby is breach sai an gyara masa kwanciya.
Haka ta daure aka gyara sannan ta karasa duba ta, tace tanaso tayi mata alfarmar zuwa dakin haihuwa tare da mijin ta, sabida suna so mata su dinga haihuwa akan idanun mazajen su, domin neman karin kauna da soyayya, jin kai da tausayi a garesu.
Gashi bata taba ganin ta ta zo tare da shi ba.
Rahina dai bata ce komai ba, sai Nene ce ta ce baya kasar ne, amma in ya dawo kafin ta haihu da shi za'a shigo labour room.
Rahinah ta daga 'yan idanun ta taba kallon Nene kamar tace da ita akan me za ki mata karya!
Mun rabu, short and simple.
Sai ta tuna abinda Ambasada ya taba gaya musu cewa saki ba karamin abu bane a kasar jamus, and it should be abiding by German law.
Don haka rufe zancen da Nene tayi kawai shine daidai.
Watanni biyu a gaba, ta shiga watan haihuwa, ta kuma gama shekarar farko ta karatun ta.
Wato tsayin semester biyu.
A haka take zuwa zana jarrabawa da tsohon ciki har ta kammala da kyakkyawan sakamako.
Ambasada ya baiwa Nene kudi yace ta saya mata duk abinda zata bukata na haihuwa ba ruwansa da abinda Habibu zai bayar.
A daren ranar ne kuma sai ga tarin akwatuna shaqe da sitturun jarirai unisex daga Habibu Nahuche.
Hatta pampas da feeding bottle sai da ya sayawa dan sa, amma ita ko tsinke bai saka da sunan ta ba.
Wannan ya sosa mata rai ba don tana son abin hannun sa ba, a'a yadda ya nuna yafi son abinda zata haifa yanzu akan ta shine abinda ya sosa zuciyar ta.
"To a kan me?"
Zuciyar ta tambaya.
"A kan dalilin da nima ban sani ba!" Ta amsawa kanta a fili.
****
EDD dinta saura kwana biyar rannan da daddare suna zaune a dakin Yafendo suna cin tuwo taji damshi-damshi daga kasan jikin ta.
Bata kawo komai ba sabida sabida bata ji ciwon komai ba.
An ce mata kuma ciwo ake ji mai tsanani.
Amma ba'a dauki wani dogon lokaci ba ta soma 'yan mutsu-mutsun da ya ja hankalin Yafendo kanta.
"Yar nan lafiya kike yanka gumi haka?" Tayi yake tace "bakomai fa Yafendo, zafi kawai nake ji" Yafendo ta gyada kai ba don ta harda ba suka cigaba da hira.
Safeenah ta shigo ta gaida Yakumbo, sannan ta dubi Rahinah tace "Nene ta ce kina da bako a falon Daddy........" amma kafin ta kai karshen maganar ta sai gani suka yi tana shure-shure.
Yafendo tace "Aha!
Ni na san abun ne ya zo, kika yi mirsisi ke ga jaruma.
Ke Safeentu kira Nenen ku ki gaya mata haihuwa ta zo a kawomin reza".
Safeenah ta zaro ido sannan ta fita a guje, kada taje ayi haihuwar a gabanta.
Nene ta fado dakin da gudunta, tace "Yafendo wace irin Reza?
Ki rufa min asiri in mutu maza su kai ni, ba'a kasar mu muke ba inda ake haihuwar gida.