Sashe 13
Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maza kwarara jikin ki Rahinah mu gangara asibiti, ga Habib nan yana nan ya zo sai ya kaimu tunda direba bai dawo ba har yanzu."
Tsananin halin da take ciki, shi ya hanata yin musun tafiya asibiti tare da Habibu kuma a cikin motarsa.
Daga ita sai Nene a baya tana shafa mata kanta da bayan ta tana yi mata addu'a yayin da shi yake tuki cikin wani mawuyacin hali.
Ji yake da zai iya da ya karba mata nakudar, kanar yadda ya zamo silar wahalar ta daga zuwa karatu.
Sun samu ganin Dr.
Saliha Widad wato likitar data ke gani itace on duty, nan da nan ta karbeta akan gadon tura marasa lafiya daga hannun Habibu da ya sunkotota gabadaya daga cikin mota zuwa cikin reception.
Dr.
Saliha ta duba ta tabbatar haihuwa ce gadan-gadan sai ta fito tana kiran sa.
Ta tambayi Nene shine mijin Rahinah?
Nene ta gyada kai ba tareda ta ce komai ba, yayin da likitar tace "kazo ka tsaya tare da ita, ka ga yadda dan ka/'yar ka zai iso duniya".
Habibu ya hada kai da bango yana ce mata "a'ah..." tayi murmushi tace "ashe raggo ne baban baby, Rahinah ta fika juriya.
C'mmon ka biyo ni nace".
Ya juya yana kallon Nene sai ta gyada mai kai, don bata so a tsaya ana tone-tone.
Ai har yanzu tana cikin zummar auren sa.
Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, haka ya daga kafa ya bi bayan Saliha Widad.
****
"Dada!"
Kawai take kira hadi da sunan Allah,ta yi gumi kashirban, kanta na bisa cinyoyin Habibu gashin kanta ya bazu jikin sa.
Ya rike hannayen ta cikin nasa, ita take nakudar amma ya fi ta hada gumi, jikin sa har kyarma yake.
Dr.
Saliha na fadi tayi nishi baby ya kusan isowa.
Da ta daddage ta saki nishin kuwa sai gashi ya fado tare da mabiyar sa.
Ya kuma canyara kuka a hannun Dr.
Saliha wadda bakin ta ya kasa rufo, shekarar ta kusan goma tana karbar haihuwa amma bata taba ganin haihuwar katon baby black beauty irin na Rahinah ba.
Saidai bai dauko komai nata ba har duhun fatar sa na mahaifin sa ne.
Aka gyarata, aka gyara wajen haihuwar, aka dau baby ana gogewa da man zaitoon aka shirya shi tsaf cikin kayan sanyi, aka nannadeshi a shawul sannan aka kawo mata shi saitin kanta.
Sai a lokacin ta soma dawowa hayyacin ta ta kuma ji kamar a jikin mutum take kwance.
Tana so ta kalli fuskar babyn amma tana son ganin wanda ya baje mata jiki ta kanannade akai ta haihu haka.
A hankali ta daga kanta, sai idanun ta cikin na Habibu, wanda hakan ya haifar mata da matsananciyar faduwar gaba.
Kafin ta soma yunkurin tashi ta kuma fashe da kuka.
"Amma Dr.
Widad kin cuce ni......" ta fada cikin kuka sosai, kamar Dr.
Na jin harshen nata, tayi Allah ya isa da fillanci, tayi da hausa, tayi da German, tayi davduk yaren data iya.
Duk akan Dr.
Widad data shigo mata da Habibu dakin haihuwa.
Nene tana ta bata baki kan ta yi hakuri.
Shikuwa ya harde hannuwa a kirji yana kallon ta da wani irin murmushin SO.
In da a ce zai iya, zai iya ciro zuciyar dake kirjin sa ya bata a halin yanzu don kawai ya nuna mata dimbin godiyar sa da soyayyar sa gareta.
Bisa bashi farin cikin da wani a duniya bai taba bashi ba.
Bisa maida shi UBA, bisa bashi precious gem din da kudi ko mulki basu isa su bawa dan adam ba.
Dr.
Ta mika mata Babyn bayan ta gama kukan bakin ciki ta share hawayen ta, da sauri ta karbe shi tana kallo.
Ba shiri ta daga ido ta dubi Habibu.
Yaro kamar Ubansa yayi khaki ya tofar.
Ya lumshe mata lumsassun idanun sa ya kuma daga mata girar sa daya, "eh dani yake kama ba da ke ba, kamar ya san ba kya son uban sa".
Ta gatsina baki ta cigaba da kallon babyn tana tazbihi a zuciyar ta.
Wata irin kauna ta da da mahaifi na keta ruhin ta da zuciyar ta.
Her only relative, her only blood!
Ta yaya bazata so shi sama da komai a duniya ba?
Bata yi aune ba ta ji Habib ya kashe su da hoto da camerar wayar sa.
Hararar sa tayi, duk wani abu da zai bakan ta mata ya san shi, yanzun ma Nene na bada baya ya matso gabanta, "wai sabida kin haihu gabana kike wannan kukan?
Yo wane dare ne jemage bai gani ba?
Bani Da na nan in ji dumin sa, kin wani kama shi kin kankame kamar ke kadai kika yi nakudarsa".
Ya mika hannu, ta yi maza ta janye dan ta.
"Ba zaka dauke shi ba!"
Ya saki baki yana kallon ta da mamaki, Nene ta shigo jin sautun kukan ta, tace "lafiya?
Ki bashi yaron mana ya yi masa khutbah?""Nene bazan bashi ba, da na ne nikadai, ba ruwan shi da mu ba ruwan mu da shi" Nene tace "Rahinah kin san abinda kike fada kuwa?
Mahaifin sa ne fa?
Yau na ji karfin hali wai barawo da sallama.
Ki bashi yaron nan kafin raina ya baci akan hakan".
Rahinah ta saka kuka sannan ta mika masa yaron.
Ya karbeshi da wata irin kulawa tamkar ya maida shi cikin sa.
Yayi masa khutbah da sunan da ya zaba masa wato sunan mahaifin Manzo SAW.
Ya tauna dabino (ajwa) ya sanya masa a baki, yaron ya hau motsa dan bakin sa gwanin sha'awa, Habib bai san lokacin da wasu irin zafafan hawaye suka zubo masa ba.
Ya rungume yaron a kirjin sa.
A haka Ambasada ya shigo ya same su.
Safinah ta biyo bayan sa dauke da kwandon abinci.
Ya yi wa Habib da Rahinah "congratulations" sannan ya karbi yaron yayi masa addu'a.
Washegari aka sallame su.
Suka koma gida.
Tun daga ranar Habib yake zarya, sayo banza sayo hopi, duk don ya farantawa Rahinah.
Amma ina!
Zuciyarta ta riga ta kekashe akan Habibu, babu wani repenting da zai yi ya burge ta.
Babban tashin haankalin sa shine Rahinah ta gama iddah, gashi yayi alkawarin bazai maida ita ba da amincewa da yardarta ba, shima Ambasada bazai taba amincewa ba yayi forcing din ta akan abinda ta nuna ta gama bashi baya.
Tsayin watanni uku tana shayar da Abdallah kasancewar suna cikin hutun summer.
Ta saba da yaron sosai, bata barci sai yana kan kirjin ta, har fargabar komawa makaranta take, don ta san dole zai koma haunnun mai raino.
Ita kam ba wanda take jin zata iya baiwa dan ta ya rike mata yadda take ji da abun ta.
Ko Habibu bata bari ya dauke shi sai in Ambasada yana gidan yayi mata jan ido.
Gabadaya Habibu Nahuche ya gama susucewa, ya fita hayyacin sa don zuwa yanzu ya tabbatar da ya rasa Rahinah.
Lokacin da suka koma hutu Nene tace zata samar mata mai raino, amma Rahinah ta fito fili tace da Nene zata yi deferring karatun ta zuwa shekara ta gaba don ta samu damar kulawa da Abdallah.
Da bashi cikakken lokacin ta a lokacin da yafi bukatar hakan.
Nene da Ambasada na jinjina soyayyar Rahinah ga dan ta, amma a zuciyar su suna tausaya mata.
Don sun san irin wannan kaunar sai ka samu a karshe iyayen da 'ya'yan basa rayuwa tare.
Kaunar tata tayi yawa kuma silence din Habibu na nufin wani abu.
Yafi watanni uku bai kara takowa inda suke ba tun wani wulakanci da Rahinah tayi masa, inda tace idan ba ita ce autar mata ba, kuma ba daga kanta an daina haifar mata ba, sannan shi ba maye bane to ya fita hanyar ta ya je ya nemi wani gantalallen auren amma ba nata ba, tun daga ranar bai kara takowa ba, amma sakon shigar kudi basa yankewa a tsakanin su.
A wannan watan da ake ciki ya kammala rubutun proposal din sa, ya karbi shaidar kammala masters din sa, aka yi musu convocation na graduating.
A ranar da ya karbi kwalin sa ya hada komai nasa don barin kasar Jamus.
In bai yi kuskure ba yau ne Abdallah ya cika shekara daya da haihuwa kuma yana gudun sa ko'ina.
Don daga baya ya kan je ganin sa amma iyakar sa falon saukar bakin Ambasada, a kawo masa yaron suyi soyayyar su ta uba da da, ya bashi sayayyar da ya yo masa, ya tafi ya bar shi yana kukan sai ya bi shi.
Sun yi wani irin sabo wanda in zaka ga sanda zasu rabu sai zuciyar ka ta motsa, ka kuma tambayi kan ka shin ita Rahina wace irin zuciya gareta?
Anya ma tana da tsokar zuciya a cikin kirjin ta?
A wani zuwa da yayi ganin Abdallah, ba tareda sanin ta ba ya fice da shi a mota, tun safe har yamma, a ranar Rahinah har dan karamin hauka ta yi, Nene na kwantar mata da hankali tana gaya mata bazai ki dawo mata da dan ta ba tunda nono yake sha.
Yafendo kam haushin Rahinah ta koma ji sabida rashin kawaicin ta akan yaron, tace ita bata taba ganin mara kunyar bafullatana irin Rahinah ba, rashin kunyar tata shahararriya ce kuma a kan dan fari, inji Yafendo.
Idan ta kaita bango kuma ta ce "kinibabbiya, sanda tasa Uban sa a daki yayi mata cikin sa ai bata ce masa rowar sa zata yi masa ba idan sun haife shi, in da gaske take son yaron ta koma gidan ubansa mana?
Dukkansu basu san inda Habib ya kai Abdallah ya kuma dawo dashi ba.
Rahinah kamar ta shide da Abdallah ya dawo don murna. ****
Yayi sallama a falon Ambasada Shehu, shi kuma ya amsa cikin sakin fuska da mutuntawa kamar yadda suka saba a kowacce haduwar su.
Har kasa ya tsugunna ya gaishe shi.
Shikuma ya soma yi masa fada akan irin ramar da yake yi, da kyar idan yana cin abinci yadda ya kamata.
Ya ce "shi mace bata isa tasa shi a wannan halin ba, don dukkansu daga karkataccen hakarkari aka halicce su.
Yana da tabbacin Rahinah zata huce watarana kuma da kanta zata nemeshi ta nemi dawowa dakin ta.
Haihuwa a tsakani ba wasa bace.