← Book details Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 14

Sashe 3

Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba karamin dauki ba dadi aka yi da Daada ba, kafin ta barta tahowa Germany, sai da shugabar makarantar su ta zo har gida da kanta ta same ta, ta roketa ta kuma kwantar mata da hankali, ta gaya mata yara irin jikanyar ta ba'a wasa da talent din su, irin su ake nema don a farfado da harkar kiwon lafiya a Najeriya, sannan karatun da zata yi (Otorhinolaryngology) babu mai irin shi a fadin Najeriya a wancan lokacin, tayi wa jikanyarta addua ta bita da fatan alkhairi ta bar ta taje, ita kuma zata kula da rayuwar ta acan, akwai kanwarta dake aure a kasar.

Sannan ne Daada ta hakura, amma tace abu na halin rai da tsufa, ko a ina ta samu damar yin aure tayi, koda wanene, in dai musulmi ne, babba ko yaro, in dai zai rike maraicin ta, sabida bata da tabbacin zata dawo ta sameta a raye.

Don haka ne da jirgi ya kusa kifar dasu tafi kowa nadamar wannan tahowa, da ta yi hakuri ta yi zamanta bayan Daada, akan gadon bonon ta, da wannan ajali ya dauketa ne a bayan Daada cikin kwanciyar hankali.

Don ta san mutum baya tsallake ajalin sa, saidai inda ajalin kowa yake ne daban.

Suna saukowa daga jirgi ta hau raba idanu, abokan tafiyar ta duk sun kama gaban su, taimakon da Allah yayi mata tana da adireshin jami'ar data zo da duk wasu muhimman takardunta a tare da ita.

"RAHINA OMAR!

RAHINAH OMAR!!

RAHINAH OMAR!!!"
Taji an kira sunan ta daga baya, da sauri ta juya don ganin mai kwala mata kira haka, nan da nan ta gane shi, shine agent wanda aka turo daga Embassy yayi musu jagora a komai har su gama registration dinsu.

Kuma tana da hoton sa.

Sannan principal tace shi zai kaita wajen kanwarta Dr.

Laura wadda lakcara ce anan Cologne take aure.

Gara ta zauna gidan ta madadin zaman (students hall of residence).

Murmushi ya subuce mata, data hango abokan tafiyar ta tare da shi, suka rankaya cikin babbar mota suka wuce cikin gari.

Sunan ya cigaba da wata irin amsa-kuwwa a kwanyar sa, ba tare da sun ankara da shi ba, sabida a lokacin ya basu baya ".......Raheenah Omar.......".

Ya ji amsa-kuwwar wannan suna har cikin bargon sa.

Kamar yadda har zuwa yanzu yake jin ta cukuikuiye a jikin sa.

Surar ta bazata taba gushewa daga idanun sa ba, domin bai taba ganin kyakkyawar surar data manne a ruhin sa irin tata ba, sannan innocentlooks dake cikin fararen idanun ta wani sign ne daya makale a zuciyar sa.
****
FIRST ENCOUNTER (HADUWAR FARKO)
The Cologne Public Library" babban dakin karatu ne na jami'ar Cologne wanda yake lamushe dubunnan dalibai komai yawan su, yawanci daliban anan suke assignments din su, kuma idan kazo a matsayin sabon dalibi dole ne kayi register da Labirare, a matsayin ta na sabuwar daliba mai yin registration yau ta shigo labirare tunda wuri, bata kai ga tarewa gidan kanwar principal ba ta zauna tare da abokan tafiyarta a (hall of residence) har zuwa sanda zata kammala da registration.

Bayan ta kammala abinda ya kawo ta ta juya zata fita, accidently ta bugi mutum wanda ya juya baya yake jera littatafan Encyclopaedia Britannica a bookshelves na library din.

Littafan hannunsa suka fadi kasa.

Da sauri ta sunkuya tana tsince masa, ta mika masa cikin cewa "i'm sorry......." sorry din ta makale a makoshin ta sakamakon ganin makwabcin ta na jirgi.

Wanda ta sulalewa.

Ga dukkan alamu ma'aikacin library din ne.

A very handsome figure din data zauna mata a rai sati biyu da suka wuce, ko na kwana daya bata fasa tuna shi ba.

"You?"
Ya fada yana nuna ta da dan yatsa.

"...... matsoraciya mai tsoron mutuwa" ya sake fadi cikin harshen hausa.

Murmushi ta yi tayi gaba tana fadin "wa ke son ta?

Da jirgin nan ya kifa da ni Dada na ma mutuwa zata yi".

Dariya yayi ya bi bayan ta har kofar labirare.

"Daga wane gari kika zo?" Bata san meyasa ta samu kanta da kantara masa karya ba tace "Benue" kallon mamaki yayi mata don ko kusa bata yi kama da kabilu ba, face zallar fulani, bafullatana cikakkiya, ita kuwa ta fadi hakan ne sabida Dada ta ce mata never trust a stranger.

Sai yayi tunanin watakila zama ne ko aiki ya kai su zaman Benue din.

Bai cika ta da tambaya ba, suka yi sallama ta wuce ya wuce, amma da ya koma dakin sa na accomodation din dalibai sai ya kasa zaune ya kasa tsaye.

Ta yi masa karan -tsaye a zuciya a kan dalilin da bai sani ba.

A kuma yadda ya lura bata da wayau, wayau na fahimtar abubuwa muhimmai irin wanda ya samu kansa akan ta, bai taba tunanin aure nan kusa ba, amma yau ji yayi in bai mallaki yarinyar nan ba bazai iya rayuwa ba.

Ya manta da abinda ya kawo shi karatu ne kuma a yanzu ne ya fara masters din sa, ya samu part time job da labirare don ya taimaki kansa, kasancewar kudin da PTDF take basu ko kusa baya isar sa sabida tsadar studentaccomodation.

A yau da ya sake haduwa da Raheeenah, sai ya tuna cewa ashe shima namiji ne, ashe yana da bukatar mahadin rayuwa duka shekarun nan biyar da ya kwashe a Jamus, ashe bai taba haduwa da wadda zuciyar sa zata aminta bane, shiyasa bai taba son aure ba, sai akan Rahinah.

Wadda ganin shi da ita bai fi a kirga ba.

Gabadaya ya rikice ya birkice ya rasa inda zai sa kan sa.

Aure kawai yake so yayi kuma ba da kowa ba sai Rahinah Omar.

Yana da Ubangida limamin masallacin musulmai na jami'ar Colgne wanda ke karatun doctorate, mutumin kasar Maghrib ne, shine ya samar masa aikin da yake yi a library yanzu, duk da albashin ba mai yawa bane amma bai nemi komai ya rasa ba, har ya bar cikin jami'a ya kama private gida karami a wajen makaranta.

Rigimar son aure data shige shi a yanzu harda kuruciya domin kuwa abinda bai sani ba infatuation ke damun sa akan Raheenah ba soyayya ba.

Kyawun ta ne ya riba ce shi.

He just wants to have her as a spouse at the age of 27 a lokacin da ya kamata ace karatun sa ne a gaban sa ba mace ba.

Ga Hajiyar sa ta dade da samar masa mata a kauyen su, Nahuche.

Wadda take matukar so, don 'yar kanin baban sa ne.

Jira take ya kammala masters ya dawo ayi musu aure.

Amma haduwar sa da Raheenah ta rikita shi ta hargitsa shi, gabadaya ya rasa lissafin sa, bai taba tunanin yin zina a rayuwar shi ba duk da cewa ita tafi komai arha a Cologne, amma ji yake kamar zai iya raping Raheeenah in bata yarda ta aure shi ba, laifin da ya san zai iya kai shi ga hukuncin kisa a kasar turai, ji yake in bai yi aure da Rahinah ba a daidai wannan lokacin zai iya rasa ransa, al'amarin da ya kawo shi gaban ubangidansa at a smart pace (afujajan) yana neman mafita.

Dr.

Sayyed ya dube shi sosai bayan ya gama jin damuwar sa, da yake malamin Psychology ne a take ya gama fahimtar halin da Habib yake ciki (infatuation/lust), yace masa "ita yarinyar tana son ka, kuma ta amince zata aure ka?

Annabi SAW yayi umarni da ayi wa samari aure a lokacin da suka bukaci hakan, in ba haka ba barna bazata gushe ba a doron kasa.

Don haka in ta amince ni zan daura muku aure (ba tareda tunanin abinda zai biyo baya ba)".

Cikin rauni Habib yace "ni ko dosarta da zancen bazan iya ba, i'm sure ba abinda ya kawo ta kenan ba, she's very naive and innocent, ni kuma zan iya cutar da ita idan ta ki yarda ta aure ni, i just want to marry her...... or rape her.....in ba haka ba Dr mutuwa zan yi.

Na yarda bayan dayan wannan in kare behind bars!".

Dr.

Sayed ya gama gane inda Habib ke fuskanta, infatuation ne mai tsanani ya kama shi ba soyayya ba, yace "ba zaka mutu ba insha Allahu, kuma bazaka aikata zina ba har karshen rayuwar ka, sannan bazaka je kurkuku akan laifin fyade ba, kaje ka gwada sa'ar ka, in har ta amince ni kuma zan yi kasadar daura muku aure, ai karatu baya hana aure".

Tun daga lokacin yake tunanin ta inda zai bullo mata, sun sha haduwa a wurare daban daban musamman labirare data ke yawan zuwa.

Amma kwarjininta ya hana ya tunkare ta.

Until that fateful day.....da ya ga an daukota ranga-ranga a sume an yi asibitin jami'ar Cologne da ita a ambulance.

Abokan karatun ta sun tabbatar wa da likita cewa basu san me aka gaya mata a waya ba, ana cikin lecture ta ansa waya sai gani su kayi ta zuba kara ta zube a wurin a sume.

Ya makale a asibitin nan a kofar dakin da aka shiga da ita, ya ki matsawa ko nan da can, lokacin da likitoci suka yi nasarar dawo da numfashin ta shi suka ce ya zauna tare da ita kasancewar duk abokan karatun ta sun koma makaranta.

Sun dauka shima coursemate din ta ne.

Tana bude ido da sunan DADA ta bude baki.....tana kuka tana fulatanci, fulatancin da bai san me take fadi ba, a karshe ya tsinci kalmar hausa. ...

Dada ni da ke shike nan?

Dada kema kin tafi kin bar ni ba uwa ba uba a kasar da bani da kowa?

Dada kin kyauta min kenan?

Meyasa baki ce mutuwar ta dauke mu tare ba?

Me yasa baki jira na zama Otorhinolaryngologist ba na saya miki gida mai kyau da mota?"
Ta soma zabura tana fizge karin ruwan ta, da sauri ya rike ta ya kuma danna kararrawar kiran likitoci suka zo suka zurmuqa mata allurar barci.

Kwana uku cif Rahina na cikin wannan halin na tsananin firgita da dimuwar rasa Kakarta.

Ko na minti daya Habib bai bar asibitin nan ba, da nasiha da banbaki da janyo ayoyin Al'qurani masu tabbatar da kowanne mai rai mamaci ne "kullu nafsin za'iqatul maut" Habib ya samu ta soma dawowa hayyacin ta.
Chapter 3 · 0% Book details