← Book details Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 14

Sashe 2

Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ma kamar kullum ya fito yana takun nan nasa majestically, cikin farin danyen Voyel mara nauyi dan shafal, dinkin jikin sa (very simple) wanda aka yi shi dan siriri da farin zare, sai da ya baiwa kowannen su hannu daya bayan daya babu gazawa cikin far'a da sakin fuska, sannan ya kawo ihsanin da ya saba yi musu a dunkule yayi musu, addu'a iri-iri Habibu ya sha ta, bai tsaya sosai ba ya wuce kai tsaye zuwa cikin gidan iyayen sa.

Mahaifin Habibu Alhaji Mustapha Bilyamin Nahuche tsohon dan siyasa ne wanda ya rike manyan mukaman siyasa a jihar Zamfara a lokacin rayuwar sa, yayi dan majalisar dattijai mai wakiltar Zamfara ta kudu, yayi sanatan Zamfara ta kudu, yayi shugaban karamar hukumar su wato Bungudu wadda garin Nahuche ke karkashin ta.

Ya rasu ya bar matar aure daya da 'ya'ya biyu mace da namiji.

Itace aunty Badiyya Nahuche, wadda ke aure a garin Kaduna, tanada yara hudu, sannan shi Habib, dake binta, daga kansu Allah bai kara baiwa Haj Kaltume haihuwa ba.

Da sallama ya shiga falon Hajiyarsa, tana kishingide akan tumtum, ta kunna rediyo tana sauraron hirar da ake yi da shi.

Shigowar sa tayi daidai da karewar shirin.

Ta kashe rediyon tana mai shimfida masa karamin center carpet, bakin ta dauke da murmushi, fadi take.

"Habibu bazaka bari ka kwanta ka huta zuwa gobe sannan ka shigo ba?

Ka taho tun daga Lagos?

Ka san dai tunda samarin nan suka ganka ba bari zasu yi ka huta ba".

Murmushi yayi yana zama akan shimfidar data yi masa, idanun sa cike da kewar ta, da ganin su zaka san akwai shaquwa da kauna ta musamman bayan ta iyaye da Allah ya riga ya assasa, cikin nutsuwa irin tasa ya sunkuya ya gaisheta, sannan yace "bana taba gajiya dasu Hajiyar mu.

They are part of me (su rabin jiki na ne), nima shekarun baya ai kamar su din nake; matashi mai buri.

Ina Abdallah?"
Hajiya Kaltume ta nisa, sannan ta ce "Badiyya ta tafi dashi Kaduna hutu, amma gobe insha Allah nace a kawo shi don ku gaisa, kafin ka tafi Makurdi din da ka ce zaka wuce daga nan.

Anya Habibu ina amfanin a dinga yamadidi da kai a kafafen yada labarai ana fadin baka da aure sai kace wani dan siyasa?

Shin ita ta kara tuna ka a duka wadannan shekarun nan ko bata san inda kake ba da dan ta?

In tana da niyyar cigaba da rayuwa da kai ai da tuni ta nemeka.

Tunda na tabbata ta san inda ka ke.

Kai ne baka san inda take ba.

Kai din a yanzu kuma fitacce ne kuma sananne a kasar Najeriya, bai yuwuwa ace bata san da wanzuwar ka ba koda a kafafen yada labarai ne.

Idan har tana da muradin sake rayuwa da kai.

Mata na duniya babu irin wadanda iyayen su basa kawo min, babu 'yar wanda bazaka aura ba Habibu, ka hakura da yarinyar nan...... ka hakura da ita bisa umarni na!".

Hajiya Kaltume bata ankara da cewa hawaye ne ke zuba daga idon sa ba.....sai da ta kai karshen maganar ta.

A fili ta furta
"Yaa Salamu sallim!"
Domin al'amarin Habib da uwar dan sa yafi karfin tunanin ta.

A duk lokacin da ta takura masa da zancen aure karshenta kenan, yayi mata hawaye.

Don bai da abin cewa.

Shin wacece wannan uwar Abdallah haka?

Kuma me ta taka da har ta mallake zuciyar namijin duniya irin dan ta Habibu Nahuche???
****
ABUJA, NAJERIYA
(Cikin Gidajen Likitoci na National Hospital
9:30 am).
a kashe rediyon a hankali, zuciyar ta na wani irinragaita, tana daga cikin wadanda suka fara aikawa BBC sakon appreciation din su ga wannan shiri na musamman.

Abubuwa masu yawa da suka gabata a birnin Cologne din Jamani shekaru GOMA a baya na gilma mata.

Wannan ita ce kaddarar su, da har gobe ba wanda ya san ta.

Kuma kaddarar data hana ta AURE shekaru goma bayan rabuwar su.

Kaddarar data maida rayuwar ta duhu didim; farin ciki bai kara gudana a cikin ta ba; "Kaddarar auren kwana bakwai".

Ta dauki hoton karamin kyakkyawan yaron mai kama da ubansa a komai tana kallo, hawaye na sauka akan fararen sumul-sumul din kundukukinta.

Ta san yanzu ya girma, watakila aji hudu na firamare.

Cikin kowanne hali dai ta san zai kula da shi.

Damuwar ta ba akan kulawar da zai samu bane domin hakika Habib Nahuche zai kula da dan sa har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa.

Damuwar ta akan yadda har gobe ta kasa kallon kowanne namiji da idanun sigar aure, kowa ya zo sai ta ga bai kai shi ba, ko farcen kafar sa bai kama ba, koda kuwa ya fi shi komai na rayuwa.

Duk da cewa ta san shi ne kawai a matsayin dalibin jami'ar Cologne ba'a matsayin sa na yanzun ba (mamallakin Nahuche Hotels) amma tana bibiye da duk wani fadi-tashin sa na rayuwa daga ranar da ya yi kidnapping Dan su.

Dalilin bibiyar ne bata sani ba har yau, tunda ita tace bata son sa.

Farin jini kam har bata san irin nata ba, manema ba irin wadanda Allah bai bata ba, kuma burin Dada shine tayi aure tun kafin Allah ya dau ranta, amma har gobe ta kasa kallon kan sauran maza da gashi sai dan mutanen Nahuche.

The one that took away her pride na diya mace.

Wanda ta tabbatar zuwa yanzu ya manta da ita, a irin shuhurar da Allah yayi masa cikin shekaru goma kacal da rabuwar su.

Bata san hawaye take ba.

Sai da ta ji dandanon gishiri a bakin ta.

Hawayen da ta tabbatar bazata daina zubar dasu ba har zuwa karshen rayuwar ta.

Idan har rayuwa bata koma yadda take a baya ba; with him by her side.

"Auren Wucin Gadi".

"Auren kwanaki bakwai kacal".

Wadanda abubuwan da suka wakana cikin su sun fi tsayin na shekaru bakwai.

Wanda ya samar da kaddarar Dan da ke a tsakani, Dan da silar zuwan sa duniya ne yayi connecting komai, ya hada zukata ya kuma raba su cikin kwanaki bakwai.

Jami'ar Cologne din Jamus ita ce tushe, mafari, ginshiki na dukkan walagigin rayuwar data samu kanta.

Plus rashin cikakken gata da ya baibayeta a lokacin.

Shekaru goma a baya, suka soma tariyo kansu a idanun ta, tamkar a majigi.
*****
(FARKON LABARIN)
SHEKARU GOMA A BAYA
aga cikin bututun maganar cikin jirgin Boeing745 wanda ya tashi zuwa kasar Jamus a yau daga filin jirgin saman Murtala Mohammed dake Lagos, bututun sadar da sako na gaggawa ya karade kunnen fasinjoji, "jirgi yana cikin hatsari, jirgin mu yana watangaririya, hazo ya lullube sararin samaniya gabadaya, direbobi sun rasa direction din su, a sabili da haka muke shawartar a sanya rigar hatsari, don komai na iya faruwa, sannan ta soma bayanin (how to escape a plane crash) cikin gaggawar magana.

Abinda ya gigita fasinjoji, ya firgita mata da yara, masu kuka na yi, masu salati na yi, bata san sanda ta kankame mutumin dake gefenta ba tana rusar kuka.

"Ina da gyatuma, da Allah da ni kadai ta dogara, dama sai da tace min kada in taho karatun nan, don ba lallai mu sake ganawa ba, don Allah don annabi ka taimaka min kada in mutu, in koma wajen Daada".

Za'a iya cewa shikadai ne bai razana a cikin jirgin ba, da ganin yarinyar ta gama tsurewa, kokari yake yasa mata rigar hadari amma ta bi ta cukuikuiye shi gabadaya.

Ta kankameshi kamar ta samu uwar ta.

Duk da cikin tashin hankali suke sai da yaji wani iri a cikin jikin sa da ruhin sa.

Da karfi ya yakice ta,
"Hey!

Relax, are you not a Moslem?

Kiyi addu'a, ki cika ni insa miki rigar kubuta daga hadarin jirgi".

Ya soma ambaton "innalillahi wainna ilaihi raji'oun......" a fili har itama ta kama eventually.

Cikin ikon Allah ba'a yi minti talatin ba kuma komai ya daidaita.

Hazo ya yaye, jirgi ya daidaita akan hanyar shi, ba jimawa suka sauka a birnin Cologne, Germany.

Kunyar abinda ta aikata kuma ta zo ta lullubeta, ta kasa sake hada ido da shi, ta nemi hanya ta sulale abin ta, cikin nasihohin Daada kafin ta taho har da cewa kada ta yarda jikin ta ya rabi na kowanne namiji haramun ne in ba mijin auren ta ba, yau ba raba ba kadai ta kankame namijin da bata san daga inda yake ba, tana tafe tana waige-waigen neman abokan tafiyar ta.

Bafulatanar Adamawa ce kyakkyawar gaske, doguwa sambaleliya, siririya, shekarunta sha tara da haihuwa, tana cikin dalibai masu hazaka da gwamnatin jihar Adamawa ta zaba tayi sponsoring karatun su na likita zuwa kasar Jamus akan likitancin fidar kunne, hanci da wuya (ENT surgeon) wadanda sunyi karanci a Nijeriya, specialization din su shi ake kira (Otorhinolaryngology).

Ta tashi ba tare da iyayen ta ba, sun mutu tun tana kankanuwa, a hannun kakarta Daada wadda ta haifi mahaifin ta ta tashi, don haka duk wani wayo irin na yaran da suka tashi gaban iyaye bata da shi, goyon kaka ce ziryan, mai tarin yarinta, wauta da shagwaba, amma a fannin karatu zaqaqura ce.

Daada ita tasa ta a makaranta, hazakarta tun tana karama daban ce data sauran tsararrakin ta.

Bata san kowa ba a danginta sai Dada, Dada ce kawar ta, uwar ta uban ta komai nata.

Hazaqarta ce ta sayo mata kauna a gun malamanta, bayan kammala sakandire wadda ta gwamnati ce, tafi kowa cin WAEC da NECO, B2 guda biyar rus, da A1 a biology, physics, chemistry da lissafi, wannan yasa hukumar makarantar ta bada sunanta a gurbin sukolaship na dalibai biyu masu hazaka 'ya'yan marasa karfi da gwamnatin jiha ta basu.

Komai za'a yi musu, sannan za'a dinga basu alawus na cin abinci, har su gama karatunsu a Jamus wanda zai dauke su tsawon shekaru biyar zuwa bakwai har specialization din da a ka tura su su yi.

A karshen kowacce shekara zasu zo gida su yi hutu su koma.
Chapter 2 · 0% Book details