Sashe 11
Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yafendo tace "in kin ga wannan naman da ake cusawa cikin fulawa ki sayo min, irin wanda kika kawo min wancan zuwan naki makaranta" tayi dariya tace "bakin Yafendon mu akwai son cin dadi, zan kawo miki shawarma, nima yau ita nake son ci".
Da haka suka yi sallama ta daga wayar ta ta kira Yohana direba.
Suna tafe akan titi tana nazarin wani practical da zasu yi cikin ipad dinta, tayi shigarta islamically cikin abaya ruwan makuba da mayafinta kirar kasar Oman, cikin ta ya fito sosai yayi toro don ta shiga wata na bakwai.
Sake-sake take a ranta ko yaya haihuwa take?
Is it painful?
Shikuma raino da breast feeding ya suke?
Kamar amsa ga tambayarta dan cikin ta yayi wani uban juyi da yasa saida tasa hannu ta dafe shi, tana mai addu'ar Allah ya raba su lafiya.
Ta nunawa Yohana inda zai ajiyeta, wato parking lot na Cologne Public Library.
Ta bude kofa ta fito a hankali tana taku irin na masu ciki, ta shiga library din da kafar dama domin kuwa shima shigowar sa kenan.
Kamar kullum yana cikin kayan sa na hausawan usul jamfa da wando na farin boyel, amma yau bai sa hula ba, ya tara suma mai yawa akansa ta yadda farin gilashin da ya sanya ya nitse cikin gashin kansa.
Yana zaune a kujerar sa cikin wani dan cabin na glass inda yake kula da bangaren ajiyar littafai masu muhimmanci (reserve section) ya ga wucewar ta amma ita bata lura da shi ba, kuma gabadaya ta manta a wajen da yake aiki kenan.
Taje ta zabo littatafan da take bukata, amma bata samu guda biyu ba an ce suna reserve section.
Ta tako a hankali zuwa reserve din, ya juya baya yana fuskantar allon kwamfutar dake gaban sa, kwarai ya ga sanda ta taho, kuma ta taho ne tare da bugun zuciyar sa.
Ta kara wani itin kyau da sulbin fata tabbacin tana cikin kwanciyar hankali, sabanin shi da rayuwar sa ta jirkice bakidaya tun shigowar ta cikin ta.
Rahinah muguwa ce mai son kanta da la'akari da maslahar kanta kadai.
Idan wani barin na zuciyar sa ya so kare ta, wani baya mata uzuri cewa yake bata da hujjar kin koma maka...... tunda ka ce zaka canza zuwa yadda take so.
Babu wani bangare na zuciyar sa dake yarda wai Rahinah bata son sa.....tana amfani da kalmar ne don biyan bukatar kanta.
"Hi, can you please check these for me?
-Diagnosis in Otorhinolaryngology
-New Aspects of Fundamental Problems of Laryngology and Otology
Pediatric Otorhinolaryngology....Scott-Brown's Otorhino....." sauran maganar ta makale gabadaya a makoshin ta sakamakon juyowar sa gabadaya.
Saura kadan numfashin ta ya bar gangar jikin ta sabida wani mummunan kallo da Habib ya jefa mata.
Dadi da cewa bata tsammaci ganin sa ba a daidai wannan lokacin.
Sannan dadewar da ta yi bata ganshi ba ya dada haifar mata da faduwar gaban.
Tayi kokarin maida numfashinta amma ya gagara isa huhunta.
Daga sanda ya taso daga mazaunin sa zuwa isowar sa gabanta Rahina bata farfado daga suman tsayen data yi ba.
Haka kama hannun ta da yayi suka bar cikin library din bata iya ta kwaci kanta ba.
Saboda gabadaya bakin ta ya mutu ta kasa saita kanta a gabansa, ta kasa kuma yin kowacce irin hobbasa ta kwace hannun ta daga cikin nasa.
A sanin ta da shi dai bashi da mota, amma ya bude bayan wata mota opel-astra ya sanya ta ciki ya rufe harda mukulli.
Ya zagaya ta barin mazaunin sa ya zauna kuma ya tashi motar da wani irin mahaukacin gudu, bata raba daya biyun yau tata ta kare.
Don ta san Habibu akan ta wani mahaukaci-mahaukaci yake komawa.
Har kofar flat dinsa ya shiga da motar, ya kashe ta sannan ya dube ta da idanun da suka kada, suka kuma sanya hantar cikinta kadawa.
"Ki fita mu je, magana kawai zamu yi in mayar dake inda na dauko ki".
Rahinah ta soma hawaye, tace "babu inda zani, nida shiga wannan gudan sai dai akai gawata""ko?
Zaki shiga ne kuma da ran ki da lafiyar ki, ko ta tsiya ko ta arziki, kina sane da cewa har yanzu matsayin matata kike?"
Wani karfin zuciya ne ya zo mata, ta ce "wallahi ko ka bude min na fita, ko nayi maka ihun da zaka fada hannun hukuma, nace bana yi, bana so kuma bana auren dole ne?"
Ya kwantar da kai akan sitiyari yana kallon ta, masifa take yi tun karfin ta amma zakin muryarta kamar busar sarewa yake jin sa a kunnuwan sa.
Haka mace mai cikin take komawa?
Danya sharaf?
Komai fresh?
Idanuwan sa har wani kanakancewa suka yi suna dubanta da siga mai nuna bukatuwar miji zuwa ga matar sa......
"You can scream.... (kina iya yin ihun) amma ki sani nima inada nawa 'yancin da musulunci ya bani, kuma zan tabbatar miki shi yanzu".
Ya karasa maganr ta hanyar kamota da karfin gaske ya rungume ta, tana mutsu-mutsun kwatar kanta.
Yace "Rahinah ki dubi Allah ki tausaya mun......my life is shattered without you.
Ko me kike so zan miki, ko me kike so zan zama.
Nayi alkawarin fin Romeo iya soyayya.
One more last chance.... ko don albarkar dana dake karkashin marar ki.
Rahinah ko a lahira wani kan ci albarkacin wani.
In kika barni gabadaya bazan iya kara aure ba.
Zan yi ta zama da dan ki ne yana debe min kewar ki har karshen rayuwata......".
Rahinah ta ga cewa hargagin ta ko cika bakin ta bai kwatar ta hannun Habibu a yau, he's ready to face anything don ganin ya kusance ta a yau, wanda hakan na nufin maida hannun agogo baya.
Tun farko ita wane tsautsayi ya kawo ta library bayan ta san anan yake?
Ta soma kuka tana rokon sa "don Allah ka amida ni inda ka dauko ni, kaga bani da lafiya, bazan iya wannan abun ba zan mutu, da na ma zai mutu, wallahi nayi alkawarin zan saurareka da duk abinda ka zo da shi amma bayan na haihu....".
Habib ya sassauta rikon da yayi mata, shima bazai so wani abu ya samu dan sa ba, dan da yake jin duk duniya ba abinda yake so kamar sa in ka dauke Haj.
Kaltume.
"Kin yi alkawari zaki saurare ni in kin haihu?"
Ya tambaya in a subdued voice.
Da sauri ta gyada kai, ba don ta yarda ta yi alkawarin a karkashin zuciyarta ba, fatan ta ta rabu da Habib lafiya ba tareda ya maida ita gidan nan nasa ba, data yi alkawarin ita da shi sai dai a kawo gawar ta.
Sai jin Habibu tayi yana dauke hawayen fuskarta da halshen sa, wani al'amari tamkar electrical shocking ya bakunce ta.
Ashe ba a iya nan zai tsaya ba?
Al'amarin da ya biyo baya mai tsauri da nauyi ne da ya shallake tunanin ta.
He began to kiss her passionately wani abu da bai taba faruwa tsakanin su ba.
Ko ya manta a inda suke, ko kuma ita ta manta cewa sakakkiya ce a wurin sa.
Wani incident da ya dauki tsayin mintuna masu yawa da bazai taba gogewa daga kwakwalwar Rahinah Omar ba.
Ya kuma goge tabon abubuwa masu yawa da suka samu muhalli tuntuni akan Habibu Nahuche a zuciyar ta.....
Wayarta ce ta dauki tsuwwa....kira ake akai-akai.
Da sauri ta ja baya.... tana wani irin hararar sa tamkar idanun ta sa fado kasa.
Habibu ya shafa kai, yana kallon ta da dukkan kauna da soyayya na zuciyar sa, idanun sa har shigewa ciki suke sabida azabar soyayya.
Shi kadai ya san azabar da yake dandana.
Komai ya dawo masa sabo, ji yake tamkar bai taba kusantar Rahinah ba sai a wannan lokacin.
Amma ya san ko shi maye ne Rahinah bazata sake bashi wannan da
mar ba, idan har ba ya ya yi yaqin kwatowa kansa soyayya ba.
"Nene!"
Sunan da ya bayyana akan screen din kenan.
Gabanta yayi wani irin faduwa.
Me ta aikata?
Me take aikatawa rayuwar ta?
Dadin bakin namiji ne zai sa ta gurbata kyakkyawan ginin data faro?
Ya su Nene zasu ji in suka ji tana tare da Habib ne a kofar gidan sa cikin motar sa ba tasu ba?
Bayan ba yadda basu yi da ita ba kan ta koma masa amma tace a'ah?
Me yasa ta yarda ta biyo shi?
Shin idan Nene ko Ambasada suka san tana tareda Habibu ba zasu zargeta da raina musu hankali ba?
Da wani irin zafin nama ta bude murfin motar ta fice, Allah ya so ta ya saki lock din, ta leko ta window tace cikin muryar kuka.
"Allah ya isa taba ni da kayi, Allah ya saka min!".
Habib Nahuce.
Bai san sanda dariya ta kwace masa ba duk da halin da yake ciki.
Yace "Allah ya saka mana tare Rahinatu!
Akwai mugu a duniya irin ki?
Kin ci albarkacin Baby na, na rantse da sai kin kunshi wani sabon cikin a yau kin haifo su tare sun zama biyu.......".
Bata tsaya sauraron mugayen kalamansa ba masu kama da sabon Allah a kunnuwan ta ta nufi titi da mugun sauri tana tare taxi.
Yohana sai ganin ta yayi taxi ta sauketa a gefen sa, ita da tace library zata shiga ta karbo littafi ta fito.
In ya kirga daidai ta kwashe akwalla awanni biyu kenan.
Ba wannan ne ya bashi mamaki ba sai yadda ta bude motar ta afko kamar wadda aka biyo.
"Are you okey Madame?"
Ya tambaya calmly.
"I'm okey Yohana let's go, kada ka tsaya a ko'ina sai mun isa Frankfurt".
"Is someone following us?
So that i report to police?"
"A'a babu mai bin mu, kaidai ka tafi da sauri ka bar harabar wajen nan".
Ya ja motar suka bar wajen yana cewa "alright Madame, but kowanne karamin abu ki dinga gaggawar sanar da police".
Ita dai tace masa ta ji.
Sun yi nisa sosai wayar ta ta sake kara, tayi ajiyar zuciya sai yanzu ta fara samun nutsuwa data tabbatar sun fita daga shiyyar birnin Cologne.
Sun kama hanyar da zata kai su Frankfurt.
Da ta duba sai ta ga 10 missed calls daga Nene.