Sashe 4
Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ranar data kwana biyar a gadon asibiti, cikin dare ta farka yana sallah, ta hada kai da gwiwa tayi kukan ta ta koshi, yana jin ta har ya gama nafilfilin sa ya juyo don ya kara bata baki.
Sai gani yayi ta mike, ta dauki mayafin ta ta yafa, tana shirin barin dakin.
Yayi maza ya sha gaban ta "Rahina ina zuwa?
Likita bai sallame ki ba tukunna, ya ce sai gobe, kiyi hakuri ki kwanta ki kara nutsuwa zuwa gobe, ni da kaina zan maida ke gidan ku".
Cikin kuka ta ce "Najeriya zan koma na fasa karatun, passport dina zan je in dauko a gidan aunty Laura, dama sun tsane ni, a dole nake zaune a gidan, bazan iya rayuwa babu Daada ba, don Allah.....don Allah ka fadawa hukumar makaranta na koma gida".
Wani matsanacin tausayin ta ne ya kama shi, yace "Rahinah in kin bar karatun ki, kuma babu Dada, kin koma gida, menene madafarki a gaba?
Gara ki karbi reality na cewa Dada ta rasu, ki tsaya ki gina future din ki, wanda ya riga ya mutu baya dawowa, kiyi hakuri zuwa gobe likita ya sallameki in raka ki gidan Antin ki, in kuma san gidan naku don yanzu ni Yayanki ne wanda bazai bari ki ragaita a rayuwa ba".
Da haka ya samu ya kalallameta, da tausasan lafuza, har ta yarda ta koma gado ta zauna.
Saidai yadda suka ga rana haka suka ga dare.
Kowanne abinda yake sakawa a ransa daban ne.
Ga Habibu, tunani yake wannan dama ce Allah ya bashi ta auren Rahinah cikin sauki, tunda bata da gatan da zai zame masa cikas, ba sai ya wahalar da kansa wajen neman soyayyar ta ba.
Raheenah kuwa tunanin ta irin zaman data fuskanta ana yi a gidan anty Laura ne; zama na kafirci da rashin tuna dokokin ubangiji, ta tsani zaman gidan don dai bata da yadda zata yi ne, sabida basu da kirki ko kadan, Anty Laura tana da wani Da Yasir fitinanne mai ruwan 'yan iska, wanda ta gama gane take-takensa na banza da wofi a kanta, don haka tunda ta yi sati a gidan ta fahimci zaman gidan bazai yiwu mata ba domin 'ya'yan anty Laura ko sallah basa yi.
Yanzu tunanin ta shine taje ta kwashe kayanta ta dauki passport din ta ta koma makaranta da zama yadda ta fara tun farko.
Tunda Habib ya ce komawar ta gida ba amfani.
Gari na wayewa likita ya sallame su, suka fito tare zuwa bakin titi, ya tare musu taxi suka hau zuwa gidan Dr.
Laura wanda ba shi da nisa da makarantar su.
Cikin halin ko'in 'kula Dr.
Laura ke tambayar ta inda ta tafi har kwana biyar, bayan an gaya mata kakarta ta rasu, shi kuma wannan saurayin ina ta samo shi?" Kamala da kwarjinin Habib yasa ta kasa ci masa mutunci yadda tayi niyya, a take ya kara fahimtar cewa dan sauran gatan da yake tunanin tana dashi a kasar ma babu, wannan matar da gani ba jinin ta bace ba.
Nan yayi mata bayanin daga asibiti suke, ya gaya mata duk halin da Rahina ta kasance, ga mamakin sa sai ta kyabe baki, "don tsohuwa ta mutu ne kike neman kashe kanki?
Ai kawai yarinya ki zauna kiyi rayuwa mai 'yanci a Jamus ki tarawa kanki ilmi da dukiya, kin ganni nan tun da na bar Africa na huta da wahala, aure kuwa na yi ya kai goma, yarannan da kike gani duk uban su daban, bana daukar bakin cikin namiji, in kika samu kwalin Cologne kin gama tsallakewa, ki tsaya kiyi karatu ki nemi rayuwar 'yanci kawai".
Rahina ta saki baki tana kallon ta, Shikuma Habib tsoron matar ne ya kama shi, ya tabbata barin ta da Rahinah hatsari ne babba, don haka ya yi gaggawar cewa shi yana son auren Rahina, a bashi auren ta.
Aunt
y Laura tace "ai ba 'ya ta bace, ba kuma 'yar uwata bace, student din yayata ce kawai, don haka zan mata magana, in ta amince kuma kanada sana'ar da zaka rike ta ko gobe zan wakilta muji na ya daura muku aure".
Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba, domin principal cewa tayi Dada ta bar mata wasiyyar idan Rahina ta samu miji musulmi, wanda zai rike maraicin ta ayi mata aure shine babban kwanciyar hankalin ta a kabarin ta.
Dr.
Laura tace "ai gashi kam ta samu, har da tabon sallah a goshin sa karewa, kuma ga yadda na lura yana son ta sosai, zan gaya wa baban Nihal ya zama waliyyinta ranar jumaa a daura musu aure".
Baban Nihal mijin Anty Laura da Dr.
Sayed suka zaunar da Raheena suna nuna mata amfanin tayi aure shine martaba da kwanciyar hankalin ta, Rahina ta kasa musa musu sai kuka, daga Sayed ya dinga lallashin ta, daga bisani suka daura auren a masallacin Cologne bayan an idar da sallahr jumaah, akan sadakin da Dr.
Sayed ya biya masa in Euros.
Kudi tsababa masu yawa duk don ya taimaka ta amshi auren domin ta kafe kai da fata bayan daurin auren tace bata so, duk da convincing din ta da Dr.
Sayed ya bata lokaci yayi, har mari ta sha a wajen anty Laura tace "ubanki ya ce ki kwaso min shi?
Ba tare na gan ku ba?
To in baki son shi sai dai ki bar min gida na, ko ki auri Yasir ya sha cocaine dinsa ya lakadaki ba ruwa na".
Ta debi kudin sadakin ta watsa mata, tace "kije ki hada kayan ki da daddare zasu zo su tafi dake, Allah ya gani ni taimakon ki na yi, don nasan in bakiyi auren bama karshenta ki zama international prostitute.
A Jamus kike yarinya ba a Najeriya ba".
Tana kuka tana komai Anty Laura dasu Nihal suka loda mata kayan ta a bayan taxi din da Habib ya zo a ciki, kamar dama zaman ta tare dasu ya takura musu don dai basu da yadda zasu yi da ita ne.
Tunda suka shigo motar take kuka, kuka tukuru tamkar zata fidda rayuwarta.
Wannan wace irin rayuwa ce?
Daga ganin mutum bata san komai a kan shi ba, don kawai musulmi ne kuma ya zo daga kasarta sai a aura mata?
Kawai don an ga bata da gata?
Ita bata ce lallai sai ta zauna da Dr.
Laura ba ta so ta koma hostel kawai tunda ko ta koma Najeriya babu Dada wajen wa zata je?
Tunda ta taso bata san kowa nata ba sai Dada, daga dangin uwa har na uba, ta rayu karkashin kulawar tsohuwa Dada a shekarun rayuwarta bakidaya.
Yau ga rayuwar da rashin gatan Dada ya jefa ta a ciki; auren mutumin da bata sani ba, bata san asalin sa ba, bata san halayen sa ba, bata san manufar sa a kanta ba.
Just haduwar kan hanya wadda bazata iya bada shaidar komai a kan sa ba, wannan taimako nasa ya zame mata masifa, duk yadda aka yi yana da target dinsa a kanta, amma in ba haka ba ta yaya daga ganin ta bai san asalin ta ba zai zabe ta ta zama matar auren sa?
Ko da take goyon kaka, tana da hankalin ta.
Bazata taba barin shi ya gurbata mata rayuwa ba.
Ta soma yi mishi kallon mutumin kirki tun daga haduwar su ta farko, amma ashe ba haka bane yana da mission dinsa da yake son cikawa a kanta.
Zata bashi mamaki, zata nuna mishi ka bar raina allura....karfe ce, komai kankantar ta.
Wannan take hakkin dan adam ne, a aure shi babu cikakkiyar yarda da amincewar sa.
Tana da damar da zata kai su ga hukuma daga su har anty Laura, amma bazata yi hakan ba, sabida ko yaya dukkan su sun taimaketa a Jamus.
Kuma Dr.
Sayed yayi iya kokarin sa wajen convincing din ta.
Amma ta gama kudurta mafita, mafitar da zata nemawa kanta ta kwatarwa kanta 'yanci.....
"Bazata taba bari ya samu access din keta mata haddi ba, in ma kwadayin hakan ne yasa shi auren ta da gaggawa haka.
Har sai ya gaji ya bata 'yancin ta na dalibtaka wanda shine abinda ya kawo ta Jamus ba auren sa ba".
*****
Kugin karshe da motar tayi, a kofar flat din Habibu ne, wanda ke shiyyar Klettenberg.
Shi ya bude mata kofa da kansa ya kuma rungumota barin jikin sa.
Ji tayi kamar ya dala mata wuta, amma haka ta daure ta cije ta shiga gidan tana hawaye.
Dr.
Sayed ya biyo bayansu har falon gidan, ya zauna yayi musu nasiha sosai, yace su taru su rufawa juna asiri su zauna lafiya, duk wata matsala da suke da ita su sameshi, shi uba ne a garesu, kuma Raheenah ta kwantar da hankalin ta Habib mai son ta ne, bai aureta da wata manufa ba sai bisa son cika sunnar Ma'aiki SAW.
Da wannan yayi musu doguwar addua'a sannan ya tafi, bayan Habib ya taka masa ya rufe gidan ya dawo.
A inda ya barta anan ya sameta, amma ta yaye lullubin fuskarta tana yi masa wani irin kallo, kallo irin na kamar ka ga makiyin ka, koko abunda zai cutar da kai.
Da gaske zuciyar ta da dan kankanin tunanin ta basu bashi kowanne matsayi ba, face na mai mugun nufi a kanta.
Ya zauna dab da ita, har tana iya jin kamshin turarensa Carolina Herrera (Men).
Da sauri ta matsa ta ja baya, sannan ta nuna shi da dan yatsa ta soma magana cikin hawaye.
"Allah ya fi ka!
Duk abinda kake nufi da ni Allah ya fi ka".
Cikin madaukakin mamaki yake kallon ta, baki sake, ya ce "Rahinah are you alright?""A'a a haukace nake, kawai daga ganin mace akan hanya baka san ko wcece ba sai kasa power ka aureta?
Sabida ka fahimci bani da gata ko?
Shiyasa ban cancanci ka nemi soyayyata ba, ka nemi dangi na ka aure ni cikin mutunci, ka taimaka min inyi abinda ya kawo ni sai kawai kayi min kutse a rayuwa ka raba ni da burika na?
Ni na ce maka na zo Jamus don in yi aure ne?"
Habib yayi mata wani irin kallo, domin ji yayi ya muzanta a gaban ta, yarinya tamkar mai gani har hanji!