← Book details Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Kaltume tayi shiru, kafin tace "menene tsakanin ku?

Habibu bana son kwashe-kwashen bariki, ka maida hankali ka gama abinda ya kai ka ka dawo gida, ka auri 'yar uwar ka cikin rufin asiri, matan nan na kasar waje duk yawancin su kyal kyal banza be (kyau ba hali).

Ba ana aure don kyawu bane ana duba asali (nasaba) da nagarta.

Nikuma shine abinda nake bukata a matar auren ka, wanda duk 'yar uwar ka Shafa'atu ta hada.

Idan kuma arziki ka hango a jikin ta wannan na Allah ne, rabon bawa kuwa zai tadda shi har inda yake".

"Hajiya ta maganar bazata yiwu ta waya ba, amma na yi alkawarin duk ranar dana dawo gida gabadaya zan gaya miki duk abinda ya faru.

Ina fatan a ranar kiyi min uzuri ki karbi hanzari na".

Haj.

Kaltume bata ce komai ba, bayan "Allah ya bamu mafita ta alkahairi".

And so
it was.....addu'ar uwa bata faduwa kasa banza, domin ya samu mafita a cikin addu'ar ta, ta karfin zuciya (courage) da karbar rayuwa a duk yadda ta zo masa.
****
Gidan Ambasadan Najeriya a kasar Jamus babban gida ne (family house) mai dauke da matar aure daya Nene Bilki da yaranta biyar maza hudu da mace daya Safeenah.

Itace babba sai kannen ta hudu 'yan maza; Safwan dan ajin karshe a sakandire, sai Abbas mai bi masa yana aji hudu, Suhaim da Ahlan sune kanana 'yan firamare a gidan.

Kenan Safinah ita ce kadai tsararta a gidan duk da cewa ta bata a kalla shekaru biyu, shekarun ta 21, tana mataki na uku a jami'ar Goethe University, Frankfurt.

Nigerian Embassy yana Frankfurt, daga Frankfurt zuwa Cologne tafiyar mota na awa biyu ne, wato 118 miles ko 180km.

Amma haka Ambasada yasa kullum ake dauko Raheenah a motar gidan sa zuwa makaranta, in an sauke su Safwan itama a kaita har Cologne, karfe 6 azo a dauketa.

Zaman ta da iyalin Ambasada Shehu kadaran-kadahan, rayuwa ce ta ba ruwan kowa da kowa kuma kowa yana da abin yi da zarar gari ya waye, daga nan kowa zai kama gabansa wajen neman ilmi masu aiki su tafi aiki, wato Nene da Daddy, yaran duk a kai su makaranta kuma sai yamma suke dawowa a tare, idan direba ya fara dauko Raheenah sai ya zo ya dauki wadanda ke cikin gari, Frankfurt.

Akwai mahaifiyar Ambasada a gidan da suke kira Yafendo, kusan da ita jinin Raheenah ya fi haduwa duka gidan, sabida tana da halaye da dabi'u irin na Dadar ta.

Su murza goro a magogi, kadin auduga, yawan girki, sannan bata cin girkin kowa ita take dafa abun ta na gargajiya, kullum in ta dawo makaranta tana son hira dakin Yafendo take tafiya, in kuma tana da karatu ko assignment to tana dakin ta.

Safeenah jinin su bai hadu ba sam, saboda ta faya kishi, yadda take ita kadai mace a gaban iyayenta rana daya Daddy ya kawo wata tsarar ta ya ajiye musu a gida don kawai yana uban 'yan Najeriya a Jamus.

Gaisuwa kadai ke shiga tsakanin su da Safeenah, dakunansu na kallon na juna amma ba mai shiga harkar kowa, ita kam Nene akwai faram-faram kamar mijin ta, tana aiki a Frankfurt Airport.

Amma bata jan baki a jiki, sama-sama dai, kowa yayi zaman kansa.

Babban abokin ta a gidan kam auta Ahlan ne, da suke yawan haduwa a dakin Yafendo.

Abinci ba matsala bane a gidan, duk abinda kake so akwai a kicin in bazaka ci wanda kuku ya girka ba.

You are free to cook.

Wannan sune sabon family din da Rahinah Omar ta tsinci kanta cikin su.

Tana kuma jin dadin zama dasu da dukkan zuciyar ta, musanman halayen su na rashin sa ido.

Kowa a gidan goal-oriented ne.
****
Tayi sallama a dakin Yafendo, ta sameta tana kadin auduga, Yafendo tayi mata murmushi ta ce "har an dawo?

To ga kwadon rama nan na ajiye miki, duk sanda muka je gida nake yo guzurin abuta busashshiya mai yawa in aje, in naji kwadayi in jika abata ta sha kuli kuli shikenan".

Ji tayi wani mugun yawu ya tsinke mata, tsabar how eager ta zama ga cin ramar, ta ja kwanon da sauri ta soma aikawa cikin ta.

Yafendo tace "bani labarin ki mana jikata?

Iyayen ki 'yan wane gari ne?"
"Iyayena 'yan Girei ne Yafendo, amma ban taba ganin su ba sai a hoto, sunan Babana Malam Omar Modibbo, mahaifiyata Bingel ake ce mata bansan sunan ta na gaskiya ba, duk sun rasu ina karama a hannun kakata na girma, a sani na ita zan iya kira iyaye na saboda ban san dadin kowa ba sai nata".

Yafendo tace cikin mamaki "Girei ta Adamawa?" Tace "nan fa""mun taba zama ci rani a garin nida miji na kasancewar sana'ar kiwon shanu yayi, gari ne mai dadin zama, yaya sunan Kakar ki?

Don akwai Umaru Modibbo dana sani a garin mai mukamin Sarkin Fulanin Girei aboki ne ga Baban Ambasada domin yana sayen shanu wajen sa".

Cikin tsananin faduwar gaba Rahinah ta ce "har yanzu 'yan uwan sa suna Girei?""Eh toh bana ce ba, tunda mu zaman dan lokaci muka yi a garin, mun san shi a matsayin sarkin Fulanin Girei, amma yaya sunan Kakar taki?""Sunan mu daya, Rahinatu, sunanta aka sanya min.

Ana kiranta Dada""ai ko dai sune wadanda na sani, ita Dada tana sayar da daudawa da man shanu kuma na kan saya a wajenta, kuma a lokacin da na santa ba Umaru ne kawai dan ta ba, tana da wasu yayan biyu, ta taba gaya mun Daya yana Kaduna da iyalin sa tunda ya tai karatu birni ta rasa shi, daya ta mutu wajen haihuwar Farko, amma dai na san in aka je Girei zaa samu cikakken bayani a kan su tunda sarkin Fulani ba boyayye bane, to amma kin ce a garin Adamawa kika girma, su kuwa a Girei na san su" da sauri Rahina ta mike tana fadin bari in nemo miki hoton Dada ki tabbatar min idan ita ce don Allah Yafendo""wannan abu mai sauki?

Idanun nan nawa duk yawan shekaru da tsufa ras suke.

Ba abinda bana ganewa" kafin ta rufe baki Raheenah ta fita a dakin.

Ta jima tana bincike a cikin kayan ta, ta hargitsa komai na dakin ta, kafin ta samo hoton su ita da Dada tun tana karama, tsabar dadewar hoton ma na farar kala ne.

Ta dawo ta kawowa Yafendo, gabanta na wani irin faduwa da fargabar abinda Yafendo zata ce.

Tsohuwar ta kura ma hoton ido, kafin tace.

"Wannan Rahin ce, tabbas Rahin ce babar Ummaru,,,," Rahina ta saka kuka tace "don Allah ki kai ni garin in nemi dangina, Dada bata taba gaya min komai a kan su ba, banda cewa da tayi iyaye ne sun mutu, itama daga baya ta rasu.

Nikadai ce bani da kowa a duniya.....".

Yafendo ta kamata ta rike tace "daina kuka 'yar nan, insha Allahu da kaina zan kai ki har garin Girei, kuma zan sa Ambasada yayi bincike mai yawa idan mun je gida, duk shekara muke zuwa ganin gida, yanzu bamu jima da dawowa ba amma da zarar zamu je har da ke zamu tafi, ki kwantar da hankalin ki, kinsan 'yan bokon nan ba abinda basa iya bincikowa".

Da haka ta samu ta lallashi Rahinah, suka yi sallama ta koma daki cike da zullumi.

A daren bata yi wani isashshen barci ba sabida taraddadi da ya cika ranta, ashe tana da rabon ganin wanda zai ce ya san wani nata ma bayan Dada?

Excitement ya cika zuciyar ta, ta dokantu shekara ta zagayo ta bi iyalin gidannan Najeriya.

Washegari da safe ta yi shirin makaranta, ta hada tea a dining din kitchen zata sha, kawai sai taji zuciyarta na tashi kuma ba abinda take so sai ramar Yafendo.

Da sauri ta suri jakar ta ta nufi dakin Yafendo.

Ta idar da sallahr walha kenan, ta shigo dakin kamar an jefo ta, "Yafendo don Allah don annabi ki sammin rama da kuli, in ban ci ba yanzun nan mutuwa zan yi".

Yafendo ta katse lazimin ta jin abinda Rahinah ke cewa, kafin kuma ta bata amsa ta hau daddaga shirgin Yafendo tana neman Ramar, Yafendo tace "Rama da safiyar nan 'yar nan?

Ki tafi makaranta kafin ki dawo zan kwada miki, yanzu ki nemi ruwan dumi ki zuba a cikin ki""na hada na kasa sha, tashin zuciya bambita yake sa ni, don Allah ki taimakeni".

Da sauri Yafendo ta dauko ramar, tace "jona ruwan dumi a butar can" cikin minti biyar tayi mata kwadon ta bata.

Nan ta hau ci ba kakkkautawa hannu baka hannu kwarya.

Yafendo tana ta mamaki a ranta, anya lafiyar ta?

Data dawo daga makaranta ma kai tsaye dakin Yafendo ta zarto.

"Na kwaso yunwa Yafendo, zan samu kwadin ramar ki?' Kawai sai ta ga Yafendo ta zaro kwano a rufe ta mika mata, already ta kwada tun kafin ta dawo".

"Allah ya kara nisan kwana Yafendo nagode" ta soma ci a urunce.

Yayin da Yafendo ta tsura mata ido.

Ta koma dakin ta ta sunce zata yi wanka, amma sai ta bige da kallon kan ta a mudubi, a take ta hango wasu bakin sauyuka a halittar jikin ta.

Abinda ya fi daukar hankalin ta shine karuwar girman kirjinta sosai, sannan tayi wani irin fari dau!

Kamar babu jini a jikin ta.

Rahinah bata damu ba ta cigaba da wankanta tana fadin mutum na kara girma ai dole kirjin sa ma ya kara girma.

Tana fitowa Ahlan ya shigo da gudu, "Aunty Rahina Nene tace wai yau baki ci abinci ba ko lafiya?" Ta ce "Ahlan ka gayawa Nene wallahi kwanan nan ban iya cin komai sai RAMA".

Ba jimawa sai ga Nenen da kanta, tayi sallama ta shigo, tace "Rahinah me kika ce a gaya min?

Ban gane hausar Ahlan ba, Jamusanci ya masa yawa" nan ta maimaita mata.

Tace "ke a ina kika ga Ramar?""Wajen Yafendo, tana da ita mai yawa" Mami ta tsura mata ido, a take ta hango sauyukan data ke son gani.

Tace "Rahinah kina yin period kuwa?" Kanta tsaye ta amsa "ai ni rabo na da shi har na manta, amma kin san i'm too busy to notice that ba don kin fada ba".
Chapter 8 · 0% Book details