Sashe 10
Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba ciki ba ko 'ya'ya goma ne suka bayyana tsakani zan baka abin ka, yadda bana son ka haka bana maraba da duk abinda ya fito daga jikin ka...."
"Rahinatu!"
Ambasada ya kira ta sounding fatherly, "banda cin fuska ga wanda ya girme miki, balle mijin auren ki, wanda har yanzu kike cikin zummar auren sa, har sai idan kin haihu bai ce ya mayar dake ba.
Tunda baki amincewa komen ba shikenan, amma ki janye munanan kalaman da kika yi masa".
Tana kuka sosai, kukan kaddarar da ta sameta, tace "ka yi hakuri Daddy na maida kalamai na, amma har abada bazan koma masa ba".
"Shikenan zance ya kare, shima cewa yayi ai in kin amince.
Kinga kuwa yasa tagociya kenan ga maganarsa.
Don haka ki kwantar da hankalin ki kina hannun Daddyn ki, har Allah ya sauke ki lafiya".
Ya juya ga Habib, wanda tuni ya mike tsaye ya zuba hannayen sa cikin aljihun caftan din shi yana nufin barin dakin don in ya cigaba da zama zuciyar sa na iya fashewa ko tayi bindiga, a yiwa uwarsa da 'yar uwar sa asara!
Ya gama saduda Rahinah bata son shi, kuma har abada bazata so shi ba, tunda rabon bazata da Allah ya kaddara a tsakanin su bai sa ta so shi din ba.
Ya sha jin ance mace na fara son mijinta ne daga lokacin da rabo ya gifta a tsakanin su.
Wanda ke nufin ita Rahinah is exceptional and extraordinary daga sauran mata.......
"Daga wannan watan zaka dinga raba albashinka biyu kana bata rabi don ciyarwa har sai ta sauka.
Ba don bazan iya daukar dawainiyar su ba sai don in baka damar ka ta uba da addini ya baka.
Ka kuma koyi daukar responsibility na iyali tun daga yanzu".
Kansa a kasa idanunsa sun kada sun yi jazir yace babu damuwa insha Allahu.
A turamin account number din ta".
"Kana iya tafiya Habibu, Allah yayi muku albarka, yasa hakan shi ya fi alkhairi tsakanin ku".
Hawayen da yake ta rikewa ne suka kwace masa, ya juya kadan ya dubi Rahinah wadda ke kallon bayansa a lokacin, suka kuma hada ido, ji tayi zuciyarta na son karyewa (rauni irin na diya mace) amma ta amince wannan shine decision mai kyau ga rayuwar ta.
Sai ta maida idanunta ta lumshe su a hankali.
Tana sauke ajiyar zuciya.
Shikuma yasa kai ya fita daga dakin, babu ko waiwaye.
Kamar yadda yake ji a ransa bazai kara waiwayar RAHINAH OMAR a rayuwar sa ba.
****
Sai da ta kwashe kwanaki bakwai kafin ta samu karfin jikin ta, kuzarin jikin ta ya dawo ko ba duka ba.
Har tana jin zata iya zuwa makaranta a gobe monday.
Tana canza kayanta na barci zata kwanta Nene tayi sallama a dakin.
"Rahinatu kin yi barci ne?""Yanzu dai nake shiri Nene""to zo mu yi magana irin ta uwa da 'ya" tayi murmushi, don Nene ta canza mata bakidaya tundaga samun cikin ta, sosai take janta a jiki yanzu, tana tausaya mata, domin gani take tayi kankanta da haihuwa kashin jikin ta kamar bai gama kwari ba.
Sabida bata da manyan barage.
Ta zauna daidai kafar Nene Bilki ita kuma tana daga saman gadon ta, tace "Rahinah meyasa bazaki koma gidan mijin ki ba?
Yaron nan ya bani tausayi sosai, da gani yana bukatar ki cikin rayuwar sa.
Can you be open to me?
Inaso in san meye matsalar ku?
A matsayina na uwa zan iya bada shawara".
Rahinah ta sunkuyar da kai, tana tuno irin rashin tausayi da rashin soyayyar da Habib ya gwada mata, kullum tana ji a littafai cewa aure abu ne na soyayya, miji tarairayar matarsa yake yana bi da ita ta hanyar da bazata cutu a shimfida ba, amma Habib Nahuche a wannan fannin sai dai a kira shi NOVICE.
Don haka bata ga amfanin zama dashi ba gara tayi rayuwarta single.
Amma ta yaya zata iya gayawa Nene haka bata ga rashin kunyarta ba?
Ita a ina tasan yadda ake rayuwar aure tunda ba taba yi tayi ba!
She's just comparing and imagining.
Don haka ta ga gara ta rike sirrin auren ta a zuciyarta, shi ciki ba anyi shi don cin tuwo ne kadai ba.
Ta soma tunanin abinda ya kamata ta gayawa Nene, don ita duk wata shawara in dai akan ta komawa Habib ne to bata bukatar ta.
"I don't love him Nene!"
Ta fada tana hawaye.
"Sabida bai aure ni cikin mutunci da daraja ba, ya sameni a arha da yawa.
Cigaba da zama dashi zai iya janyomin psychological depression".
"Allah ya sawwake" inji Nene Bilki, amma daga nan zuwa ki haihu ki nutsu ki fahimci zuciyar ki.
Maiyiwuwa wani bacin rai ya sanya miki wanda ya lullube soyayyar.
Bazan takura sai naji ba don tsakanin mace da mijinta sai Allah da ya halicce su.
Amma shi AURE is not all about love my dear.....so many cirmustances na sanya mu zaman aure.
Ni kinga so nake Saffenah ta samu mijin amma Allah bai bata ba, shikuwa Habibu har cikin kwayan idanun sa na hango SO mai yawa, wanda nake da yaqinin da zaki hakura ku koma zai isheku rabawa ku duka, ya yalwaci zuciyar kowannen ku.
Yanzu mu bar maganar kome, mu yi ta karatun ki.
Kinga dai position din jikin ki na da dana yanzu ba daya bane, ba zaki jure wannan zirga-zirgar tsakanin Frankfurt da Cologne ba.
Don haka na kawo shawara me zai hana ki nemi iznin accessing lectures dinki online?
In yaso lokacin jarabawa sai kije ki rubuta, doctor yace kina bukatar hutu sosai.
In yaso in kika haihu sai ki cigaba yadda kike yi".
Rahina bata so ya zamo cewa kowacce shawara da Nene ta kawo bata dauki ko daya ba, banda haka da ta gaya mata......gara ta cigaba da zirga-zirga yadda cikin zai jijjigu ya bare.
Cikin da bata maraba da shi ko kadan cikin rayuwar ta.
"To shikenan Nene, insha Allah zan rubuta application na neman iznin hakan, sai a karbo takardar asibitin" Nene tace "hakan dai ya fi".
"Sai maganar abinci, duk abinda kika je shi kike so, shi zuciyar ki ta kwanta da shi, kada kiyi kauron baki ki gayamin, nikuma insha Allahu zan dafa miki muddin ina gida, in ma bana nan ga Yafendo, kada ki dinga zama ke kadai idan ba karatu kike ba".
"Nagode, nagode Nene, Allah yayi muku sakayya da alkhairi, yadda kuka dubi maraici na Allah ya dubi haular ku a bayan ku".
****
Sati uku kenan tana karatun ta conveniently online.
Natsuwa ta soma shigar ta yadda ya kamata.
Tunda bata ganin Habibu A.
Bilyamin Nahuche bata da bacin rai, kuma bata da damuwa.
Ciki dai har mantawa take yana makale a jikin ta, in banda mugun kwadayi da yake sa ta, kamar ta cinye Nene da Yafendo sabida dafa min kaza, dafa min kaza.
To haka rayuwa take, komai lalacewar zamani baka rasa mutane na kwarai masu zuciyar taimako saboda Allah, iyalin Ambasada Shehu Bichi, ba abinda zata ce dasu sai addua da fatan Alkhairi.
Hutun farko na summer mutanen gidan duka zasu je Paris, amma Ambasada yace banda ita da Yafendo, su zauna suyi kadin auduga a gida, ta sha jarabawa tana bukatar zaman waje daya ta nutsu, don su kam in sun tafi sai sun kwashe sati hudu suna yawo.
Sun tashi ranar lahadi, gidan ya rage daga ita sai Yafendo, don haka ta lokewa tsohuwar, ba hirar data ke so su yi sai ta garin Girei da mutanen cikin sa.
Duk yadda Yafendo ke son ta nusar da ita gara ta koma gidan ta taga gara ta kyaleta, tana cikin walwala da farin ciki a gaban nasu, kamar bacin ranta shine ace ta koma gidan Habibu Nahuche.
Ita kuma haka kawai yaron ya shiga ranta, yana da wata irin Charisma da ba duka maza Allah ya mallakawa ba.
Zuwan sa biyu gaida Daddy suna haduwa da Yafendon a falon saukar bakin Daddy, tayi ta zolayar sa wai biko yake zuwa a inda ba'a son sa.
Shikuma baya shiru ramawa yake yi, yace yanada kamar ta me zai yi da wata Rahinah?
Shi Yafendo ta ishe shi rayuwar duniya.
Ya zo ne ya ji lafiyar dan sa a wurin Daddy he's not here for RAHINAH!
Bata jima da dawowa daga dakin Yafendo ba ta ga wayar ta na haske, alamar shigowar sako text.
Ta dauka ta duba sai taga cewa alert ne na kudi Euros
3000.
Daga Habibu Aminu Nahuche.
Ya cika alkawari na farko da Daddy yasa shi ya dauka na ciyar da ita har sai ta haihu.
Bata san ya aka yi ya aka yi ba kawai ta ji kwalla ta cika idanun ta.
****
Rayuwa ta cigaba da gudana yadda suka tsara ta, sai dai kuma sau tari ta kan zo wa dan adam da sauye-sauye; abin nufi, cikin ta na girma ra'ayin ta na canzawa akan sa.
From negative to positive.
A kullum ta ji shi yana wutsilniya sai ta ji gabanta ya fadi, sannan kauna irin ta UWA ta soma kanannade ta ba tareda ta yi shawara da ita ba.
Bata son uban cikin, amma tana jin zata iya yin komai don tsira da wannan dan na cikin ta.
Shi kadai ne ya rage wanda zata kalla ta kira jinin ta, tunda har gobe bata da wanda zata kira nata a gefen ta.
Ta yi sallama a dakin Yafendo, ta sameta tana murza goge a magogi tana hambudawa, Yafendo tace "yau tun safe ban ji motsin ki ba, inji dai lafiya kuka tashi?" Ta zauna gefen Yafendon, tace "lafiya na tashi Yafendo ina wani group discussion ne da 'yan class din mu via zoom.
Sai yanzu muka gama kuma dole yau zan shiga makaranta akwai littafan da zan karbo a library".
Yafendo tace "a wannan yanayin da kike 'yar nan?
Zaki niki hanya ki bar gari zuwa makarantar nan taku mai nisa?" Tayi murmushi ta dora hannunta akan na Yafendo tace "kada ki damu tawan, ina jin karfin jikina sosai, kuma direba zan kira mu tafi tare".