Sashe 1
Nahuce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Default Paragraph Font
Normal Table
No List
0Header Char_5f1393c6-6765-44ef-a9fe-0f57a1f14a3f
header
page number
0Footer Char_2ea6b853-1889-438e-b2af-3d95d47bb2c3
footer
(Daga Fushina)
Littafin
Sumayyah Abdulkadir
[email protected]
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafi ga kawata Fati Nahuche, godiya mai dimbin yawa gareki uwar Salma bisa gudummuwar ki yayin rubuta wannan littafi.
GARGADI
BAN YARDA A KARANTA WANNAN LITTAFI A KOWACCE KAFA TA SADARWA BA KO COPYING DINSA A YANAR GIZO KO KARANTAWA A YOUTUBE BA TARE DA IZNINA BA, YIN HAKAN KARYA DOKA NE KUMA ABIN TUHUMA DAGA LAUYANA BARR.
SADIQ RUFAI WALI.
TUKUICI NE
Ga duk makaranta littafaina, wadanda na sani da wadanda ban sani ba.
SHIMFIDA
ZAMFARA STATE, NAJERIYA
amma lis, a wata ranar Lahadi, wadda tayi daidai da shida ga watan Yuli, ta shekarar alif dari tara da casa'in da tara da misalin karfe biyar na yamma, majalisarsamarin unguwar Kofar Jange ta hadu, ta cika ta batse cikin birnin ZAMFARAN Najeriya.
Opposite wannan majalisa ta samari wani gida ne da za'a iya kira ginin masu kudin da, koko a ce 'yan bokon da, wanda aka yi wa renovation daidai da zamani, gida ne mai asali da tsohon tarihi a unguwar ta (Kofar Jange) da yayi fice sakamakon kasancewar mamallakin sa tsohon dan boko kuma dan siyasa da aka dama dashi a gwamnatin Zamfara tun daga state har federal.
Ita wannan unguwa KOFAR JANGE unguwa ce mai tsohon tarihi wadda ta samar da jiga-jigan 'yan boko da masu fada aji a jihar Zamfara.
A dalilin maigidan tsohon dan siyasa ne wanda ya kare rayuwar sa cikin hidimar al'umma.
Wadanda suka gudanar da siyasar su ta gaskiya da rikon amana tun duniya na kwance, lokacin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar.
Duk wani Bazamfare ya kwana ya tashi da sanin tarihin gidan Alhaji Mustapha Bilyamin Nahuche.
"GIDAN NAHUCHE!"
Shine lakabin da ake kiran wannan gida a garin Zamfara.
A saman gidan ma an rubuta hakan cikin rubutu na ruwan gwal.
Gida ne mara tarin iyali domin matar aure daya ce tal tayi rayuwa a cikin sa ba tare da kishiya ba; su biyu ne kadai 'ya'yan gidan a wajen marigayi mahaifin su Hon.
Mustapha Bilyamin da mahaifiyar su Hajiya Kaltume (Hajiyar Nahuche).
Wannan zama da samarin nan suka yi ba na komai bane na jiran isowar sa ne, shi kadai ran sa dan Nahuche jikan Nahuche.... da suke matukar kauna, ya kuma zame musu role-model wato mutum abun koyi a halayya da dabi'a, da kuma yadda yake gudanar da kafatanin tsarin rayuwar sa, bi ma'ana, shi mutum ne da suka yiwa kyakkyawar shaida ta saukin kai da girmama matasa; ga sukuni Allah ya bashi, ga tarin kuruciya da zuzzurfan ilmi amma babu ashararanci ko kankani a tare da shi.
Bai gaji mahaifin sa ba ta fuskar siyasa, amma ya gaje shi ta fuskar ilmin boko, shi kawai dan boko ne mai ci da gumin, biron sa.
Tun safe suke zaune, har zuwa yanzu da rana ta tasamma faduwa, suna da labarin ya shigo Zamfara a safiyar yau yana gidan sa na GRA, kuma duk ranar da ya shigo matasa da masu neman aiki na unguwar su sun warke, shi ba dan siyasa bane (business tycoon) ne mai kishin matasan yankin sa, sannan mai connections a birnin Tarayyah, suna da tabbacin dole zai zo ya gaida mahaifiyar sa Hajiya Kaltume komai dare, ba zai kwana cikin Zamfara ba, ba tare da ya zo ya ganta da tilon Dan sa ba.
Karfe nawa zai zo ne basu sani ba, in kuma zasu kwana dakon zuwan sa bazasu gaji ba, dalilin zaman su kenan a majalisar kofar gidan Hajiya Kaltume Nahuche.
Hira suke irin ta samari masu jini a jika masu burin da babu ranar cika shi; duka burin su dai shine su zama kamar sa a komai; a ilmi, a dabi'a, a halayya, a kasuwanci, a taimakon al'umma, a irin motocin da yake hawa, a irin simplelife-style din sa, a farin jini.....a kyawun sura a komai da komai.
A cewar su dai, yana daga cikin masu sa'a a rayuwa in ka dauke gwaurantakar sa da bata dada shi da kasa ba.
Abin kamar hadin baki rediyon hannun daya daga cikin su ta soma kwararo muryar sashen Hausa na BBC (British Broadcasting Corporation) cikin shirin su mai taken: "DOMIN MATASA....."
Mai gabatarwa yayi sallama sannan ya ambaci sunan bakon mako, wanda ya sanya samarin baki daya sakin ihu cikin hargagi irin na samari harda masu mikewa suna daga juna.
Shiri ne da sukeyi duk karshen sati wato ranar Lahadi domin tattaunawa da talentedbusiness tycoons masu jini a jika irin "HABIBU NAHUCHE....".
Domin karfafawa matasa wajen neman na kai da neman ilmi.
Mai gabatarwa, AbdulHadi Taheer, wakilin BBC a jihar Zamfara, ya ce "Assalamu alaykum masu sauraren muryar Hausa ta BBC, a yau muna tafe ne tare da "NAHUCHE", in nace Nahuche ina nufin HABIB, MUSTAPHA BILYAMIN NAHUCHE.......
The propriator of NAHUCHE HOTELS & NAHUCHE GROUP OF HOTELS.
Barka da zuwa wannan fili Engnr.
Nahuche, matasan Zamfara na son sanin takaitaccen tarihin ka?".
Zuzzurfar muryar sa kasaitacciya ta mazan da suka hantse cikin ilmin addini dana zamani ta kwararo sallama da Bazamfariyar accent din sa, wadda banbancin ta da sakkwatanci kadan ne.....
"Assalamu alaykum, sunana Habibu Mustapha Nahuche, ni Bazamfare ne gaba da baya, nayi karatun firamare da sakandire duka a kauyen Nahuche kafin mahaifi na ya dawo birni a dalilin neman ilmi da neman abinci.
Bayan kammala karatuna na sakandire na samu scholarship daga (Petroleum Technology Development Fund) da aka fi sani da PTDF zuwa kasar Germany, na karanci 'Hotels Administration' daga jami'ar Cologne, Germany.
Nayi digiri na biyu duk a Cologne akan fanni guda.
Na dawo gida a shekara ta 2000 na fara aiki da babban hotel din Najeriya na wancan lokacin (Nicon Noga) inda na rike manyan mukamai acan, daga baya na fara ginin hotel dina na farko a garin mu wato Zamfara, daga nan ne abubuwa suka mike har aka samar da NAHUCHE GROUP OF HOTELS a manyan jihohi na wannan kasa tamu mai albarka.
Na taba aure, inada yaro".
Abdulhadi Tahier yayi murmushi yace "masu sauraro zasu so su samu karin haske akan kalmar "na taba aure" domin kalma ce mai harshen damo, har yanzu da auren ko babu?"
Wani kasaitaccen murmushi ya saki, wani abu ya soki zuciyar sa, a lokacin da bafullatanar fuskarta ta gilma masa kamar walkiya, "ta yaya zai mantata da lokutan kwanaki bakwai?" A hankali kuma cikin karayar murya na tasowar wani tsohon miki yace.
"Duk yadda anka fassara ta, daidai ne!".
Abdulhadi Tahier bai ja tambayar da nisa ba don ya fahimci ya gama amsa ta.
Sai ya dauko maqasudin tattaunawar, wanda shine abinda suke so matasa su amfana da shi.
"Ko menene sirrin da ke karkashin nasarori da habakar 'Nahuche Hotels' akan sauran gidajen saukar baki da muke dasu a kasar Najeriya?"
Bai bata lokaci ba ya amsa.
"Excellent Service Delivery!"
"Shin ina ne NAHUCHE?
Domin banda Zamfarawa, ba kowa ya san garin 'Nahuche' da ake kiran ka da ita ba, wadda har ta boye asalin sunanka na yanka?
A yanzun ana maganar kasarmu Najeriya ne in general da babu babban birnin da baka da Hotel, kana da masu kallon ka as a role-model suke kuma son jin wasu daga boyayyun sirrikan rayuwar ka".
"Nahuche karamin kauye ne a karamar hukumar Bungudu.
Ainahin garin Nahuche gari ne dadadde, garin ne da mutanen garin hausawa ne.
Mutanen garin bakake ne sid.
A wata shekara garin ya hadu da musibar hare-hare daga wasu garuruwan.
An addabi garin da yaqi har suka rasa yadda za suyi.
Ana cikin wannan halin ha
ulin, sai wani shahararren mayaqi Ya zo daga Katsina, cikin kabilar Rumawa.
Rumawa kuma ka san fulani ne kyawawan gaske.
Wannan shahararren mayakin tafiya ta biyo da shi ta cikin garin Nahuche, sai Kekun Nahuche (sunan ainihin sarautar Nahuche kenan) Ya roki wannan mayakin da ya taimaka masu kan hare-haren da su ke fama da su.
Har yayyi mashi alkawarin idan har yacci wannan yaqin to zai bashshi rabin kassar shi da kuma sarautar Uban Dawakin Nahuche.
Aka yi yaqi, kuma aka samu cin nasara, shi kuma Kekun Nahuche bai manta da alkawarin da ya dauka ba, ya ba wannan mutumin sarautar Uban Dawaki (saboda ko da yazo a kan Doki yazo) ya kuma bashi rabin kasar shi Nahuche, shi kuma ya koma Katsina ya zo da iyalin shi suka ci gaba da zaman lafiya da mutanen garin, da Keku da Uban Dawaki sune ainahin sarautun da ke Nahuche kuma kowanne na mulki individually.
Har yanzu akwai rabe-rabe akan sunan wannan Bakatsinen amma mafi yawanci sun ce sunan shi Juli (sunan fulani ne).
Juli ya sa
ya 'yan shi sun yi makaranta, ciki har da kakanninmu, my grandfather (Bilyamin Nahuche) yana daga cikin dattijan wannan gari".
"Madallah da wannan kyakkyawan bayani na tarihi akan garin Nahuche, a karshe wane sako gare ka ga matasa masu burin zama manyan (business figures) irin ka a Najeriya?
Wannan karon da murmushi ya amsa.
"Su duba organizational theory of business, kafin kafa kowanne irin kasuwanci.
Gaskiya, rangwame da rikon amana shine sirrin nasarar kasuwanci, kada a raina riba komai kankantarta.
A zama kullum cikin tunanin sababbin hanyoyin habaka kasuwanci a zamanance (technological innovation).
Abu na karshe shine mai cin muguwar riba, baya taba nasara a kasuwanci kuma dukiyar sa bata albarka".
Samarin nan banda ihu ba abinda suke yi lokacin da shirin ya kare, muryar shi kadai tsuma samarin Zamfara take yi, kaunar da suke mishi ba 'yar kadan bace.
Da a ce shi mai bin ra'ayin wasu ne ba ra'ayin rikau ba, da ya dade da shiga siyasa "........Allah ya taimaki Nahuche.......Allah ka bar mana Nahuche......." kawai suke ambato cikin hargowa.
Daidai lokacin da motar baka wuluk kirar PORSCHE ta sulmiyo ta shigo layin kamar yadda suka yi tsammani.
Suke kuma dakon jira.
Dan sardidin matashi da shi.
Habibu Nahuche.