Sashe 4
Me Ya Jamin New Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amsawa tayi cikin ladabi duk da bataso hakan ba amma ya zatayi ta fice ta nufi cikin ta ishe Hajiya Muniba a parlour tayi mata sannu da gda ta amsa mata a yatsine ta wucce ta tarar Mama hatta haɗe mata kayanta dauka kawai tayi tana hawaye ta fita daidai lkcn da yake fitowa a sashin Granny ya shiga gdan bai jima ba ya fito ya shiga motar itama ta shiga suka wucce.
Yaran sai murna sukeyi ta dawo itakuma tana ƙunci sarai Aliyu ya lura bataso dawowar ba daga yanayinta baisan dalili ba duk sai yaji ya tsargi kansa da takura mata to amma ya zaiyi zaman gda daga shi sai yara bazai yiwu ba itakuma Salma yanayin aikinta yana yawan sasu yawo.
Kayanta ta ɗauka ta shige ciki yabita da kallo shi kansa baisan meye yake kallo a jikinta ba amma tabbas yasani ba tun yau ba wani abu yana burgeshi game da yarinyar a hankali batare daya sani ba ya kira sunanta taja ta tsaya cikin fargaba tare da juyowa shikansa baisan dalilin kiran ba yace “am ki dafamin coffee ki kawomin ɗakina" saida taji wani ras da yace ɗakinsa domin a tarihin zamanta na gdan batajin ta taɓa shiga ɗakinsa yananan bai bata dama ba har marinta saida yayi akan aikenta ma da Salma takeyi tun lkcn ta daina gigin zuwar masa ɗaki........
_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi kan ₦300 kacal tura ta acc 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta whattsAp number 09013718241_
*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?
Paid book
Oum Hairan
9-10
Shiga tayi ta aje kayan ta fito ta nufi kitchen yaran suka biyo ta musamman Farooq yana ce mata “nifa yunwa nake ji daddy indomie kawai ya bamu" jinjina kai tayi ta kunnan kan Gas biyu ɗaya ta doransa coffee ɗaya ta ɗora abinci ta riga gama dafa masa coffee ɗin ta ɗauka ta nufi ɗakin nasa ta ƙwanƙwasa yana zaune ya zuba uban tagumi baisan abinda zuciyarsa take shirin aikatawa ba amma tabbas tana tunzurashi ya aikata wani abu saidai shi kansa yanajin faɗuwar gaba idan ya tuna abin mai wahalar yuwuwa ne bayan haka ma zuciyarsa kamar ba adala bace a cikin sati guda tunanin nan ya fara bijiro masa wanda ya ɗarsu domin nemawa yaransa mafita shin tayaya ma Anam zata amince da wannan shirin nasa? In itan ta amince mahaifiyarta da mahaifansa zasu yarda? Musamman ma Hajiya Muniba.
Ya jinjina wannan lamari yafi a ƙirga kafin ya ankare da taɓa ƙofar da akeyi yabata izinin shigowa ta buɗe ta shigo da sallama a bakinta amma kanta a ƙasa yake ta ajiye masa flat ɗin data jero kofunan ta miƙe zata fita yace “am bakiji ba...." Tsayawa tayi tare da juyowa ta koma ta tsugunna tace “Na'am" zubanta ido yayi ya kuma kasa cewa da ita komi har saida ta gaji tace “Abinci na ɗorawa su Farooq zai iya ƙonewa"
Numfashi ya sauke ya bata izinin tashi ta miƙe ta fita ta koma kitchen ɗin ta tace shinkafar data ɗora ta zuba musu miyar data dumama ta ɗauka suka fito Parlourn tana bawa jannat Muwaddat da Farooq sunaci yanda yaran sukecin abincin zai tabbatar maka da gaske yunwa sukeji.
Sunci abincin sosai ta gyara gurin ta jasu ɗakinsu ta kwantar dasu bayan tayi musu wanka itama tayi tayi sallar Magrib da isha da bata samu tayi ba ta kwanta a cikinsu tana rungume da Jannat tayi musu Addu'a bacci ya ɗaukesu dukkansu.
Fitowa yayi domin duba yaran ya buɗe ɗakin ya shiga tare da kai hannu ya kunna glub gabansa ya fadi ganinta kwance tsakiyar yaran ya daɗe tsaye yana kallonta luguden zuciyarsa na ƙaruwa a kallo na zahiri baya hango wani abu dake burgeshi ga Anam Amma ya fahimci zuciyarsa ta jima da sanya masa wasu alamomi masu neman fassara.
Juyawa yayi ya fice zucciyar tasa cike da tunanin ta inda zai fara aikinsa tabbas lkc yayi da ya kamata ya samawa yarinyar yanci wanda ya farajin ɗarsuwar dacewar sa daga tausayi, ya ɓata dogon lkc yana tunanin rikicin da yake shirin ɓallowa kansa da Anam Amma zuciyarsa taƙi karaya a ƙarshe wayarsa ya ɗauka ya turawa abokinsa Nazeer cewar gobe su haɗu a office yanason su tattauna. Hakance ta faru washegarin kamar yanda Anam ta tashi da wuri haka shima ya tashi lkcn daya fito tana kitchen tana haɗa abin karin safe tana goye da Jannat da tayima wanka ta juyo ta ganshi tsaye a ƙofar kitchen ɗin ta sunkuyar da kanta tare da gaisheshi cikin ladabi ya amsata yace “ina sauri ne" daga kai tayi tare da ɗaukar kayan data gama dasu takai dinning ta dawo ta gyara kitchen ɗin ta shirya yaran ta miƙawa driver su ya tafi kaisu makaranta hakan yabata damar sake kwanciya.
*********
Duban juna sukeyi da Nazeer kowa yana sauke numfashi inda Nazeer yake goge zuffa ya ɗago cikin tsananin mamakin abokin nasa yace “ƴar aikin gdanka kakeji kanaso kuma so na aure? To ya kuma zakayi da masifaffiyar matarka me baƙin kishin masifa?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya aje biron da yake wasa dashi a hannunsa yace “abinda nakasa samun amsarsa kenan am ni Ina ganin idan harsu Hajiya sun amince bazai zama matsala ba asanya rana gajeriys cikin sirri zanyi ƙoƙarin nema mata gida ƙarami nasata a ciki kafin komai ya daidaita bansan meye yake damun mata ba sun gaza ta ɓangarori da dama na auratayya amma daga lkcn da namiji yayi niyyar ɗauko musu wacce zata tayasu sai suyi tsalle suce basusan zancen ba duba dai Nazeer kaga rayuwar gdana nasani duk da cewar Salma Bata cikin matan da zaayima tambarin ƙazanta Amma fah da taimakon Anam kullum kaje gdannan Anam Bata tsaye bata zaune itace kula da yara gda da masu gda to inda zata iya ɗaukar wannan aikin meye yasa bazan gayyato ta tazo ta tayamu rayuwar har abada ba? Am Bama wannan ba Nazeer duk da cewar Ni bana cikin jinsi na maza masu takura ko yawan buqata hasali ma ta wannan fannin inada rauni amma fah a hakan duk lkcn dana buƙaci Salma sai ta kawomin uzuri kuma fah duk da haka cewa takeyi Ni ragone"
Shafa ƙeya Nazeer yayi yace “hakane
saidai kasan tunanin mata ya bambanta da namu sukan a ɓangarensu wannan babban abin kunya ne zaka aikata tabbas za'ayi surutu Bama iyakar surutu ba harda abinda yafi surutu to amma dake ka shirya saika fita da qwanjinka idan rabone sai kaga ka dauka"
Miƙewa sukayi tare suka fita sun jima jikin mota suna ƙara tattaunawa sannan sukayi musabaha suka rabu kowa ya shiga motarsa lkcn da yaje gda bai iske kowa ba a parlour ɗakinsa ya shiga ya cire kayansa ya watsa ruwa ya sanya jallabiya ya sauko ƙasan ɗakin Anam ya nufa ya ƙwanƙwasa ta miƙe a gyaran wardrobe ɗin da takeyi ta buɗe yana tsaye da cup a hannunsa ya zubanta idanunsa masu kama da wanda kejin bacci ta sunkuya cikin nutsuwa tace “barka da dawowa" lumshe idonsa yayi yanajin muryarta na ratsa sassan jikinsa yace “ina yaran nan?" Sunkuyar dakai tayi tace “dake juma'a ce Zeeze tazo ta ɗaukesu wai Aunty Salma tace tazo ta ɗaukesu suyi weekend acan"
Jinjina kai yayi yace “ina buƙatar abinci" yana faɗin haka yayi gaba ta koma ciki ta ɗauka hijjab ɗinta ta fito ta shiga kitchen ta haɗo masa abincin ta kawo masa ta miƙe zata tafi yace “bakiji ba" tsayawa tayi yace “ki haɗa kizo ki zauna inason mgn dake ne" dawowa tayi ta zauna ta fara haɗa masa a zahiri zakace wayar hannunsa yake kallo amma Anam ya zubawa idanu yana nazarinta sanyin yanayinta yafi komai burgeshi a ƴan kwanakin nan mika masa flat ɗin tayi cikin natsuwa yasa hannu ya karba tare da saukowa ƙasa ya zauna ya tanƙwashe ƙafarsa yanacin abincin yana satar kallonta, duk ta tsargu so take ya sallameta ta tafi gashi taga alamun bashi da niyyar bata izinin tafiya.
“Ranar da naje ɗaukoki a gda naji kinyi mgn lkcn da Granny take Miki faɗan gyara gashi kince ta daina yi miki fatan kishiya ko zan iya sanin dalilinki?"
Kanta na ƙasa ta ɗago ta sake sunkuyar dakai bazata iya jurewa irin kallon da yakeyi mata ba hakan yasa duk ta takura
Alamu yaga na bazatayi mgn ba yasashi cewa “ok amma zaki iya auren me mata?" Ɗagowa tayi da mugun sauri tare da girgiza masa kai ba tare da ta san tana girgiza masan ba kafeta yayi da idanunsa cike da faduwar gaba yace “why?" Maimakon ta bashi amsa sai kawai yaga ta fara share hawaye ya sake zubanta ido yace “talk me mana" ƙasa tayi da idanunta tace “ni kawai banaso ne saboda bazan iya fitina da tashin hankali ba kuma...kuma...." Shiru tayi
Tana qorarin haɗiye mgnr yace “kuma me?" Sake jan zuciya tayi tace “idan bakada galihu Gara ka samu mijinka kai ɗaya kada kaje ka shiga inda za'a ke maka gori" da sauri ya dubeta yace “gorin me?" Shiru tayi masa alamun tagaji da tambayar yayi murmushi ya matso gabanta yakai hannunsa kamar zai kamo nata tayi saurin janyewa cike da tsoro kawar da hannunsa yayi yace “yanzu idan ya kasance wani mutum me daraja da yasan ƙimarki yasan mutuncinki ya fito yace yanason aurenki sai ya kasance yanada mata da yara amma yace bazai hadaku gda ɗaya ba zai ware miki mazauninki daban shin zaki iya amincewa da hakan ko har yanzu baki gamsu ba?"