← Book details Me Ya Jamin New Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Me Ya Jamin New Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata baƙar kunya ce ta kama Anam tayi ƙasa da kanta cikin tsananin jin kunya sumsum ta fice Alh Ma'aru yana mata dariya yana cewa “Anam badai kunya ba Hajiya kin bawa yar dakin naki kunya" itadai ƙasa ta sauka taci gaba da taya Mama Yabi aikin da takeyi suna gaf da gamawa Aliyu da Alh Ma'aru suka fito sukayi musu adawo lfy sannan sukaci gaba da ayyukansu basu suka gama ba sai bayan Magrib Anam ta shige ɗakin Mama Yabi tayi alwala tayi sallah ta miƙe a katifa Mama Yabi ce ta shigo masu da abinci ta tashi sukaci suna taba hirar su ta ƴa da uwar suna dariya can Anam ta haɗe rai ta koma kalar tausayi Mama ta dubeta tace tunda kika zo na fahimci damuwa a yanayinki meye ne yake faruwa?" Ƙwalƙwal tayi da ido tace “Allah mama na gaji da masifar Hajiya Salma kullum saita zageki ta zagi ubana da banma sanshi ba ga ƴaƴanta rashin kunya babu kwaɓa kamar ƴaƴan Allah bani musamman Farooq da Muwaddat ji suke kamar zasu iya cin abinci akaina"

Jinjina kai Mama Yabi tayi ta zubawa ƴartata ido tare da sauke numfashi tace “zuwa yanzu ya kamata ace kin saba da waɗannan ƙananun abubuwan Anam ya mutum zaiyi da yanda Ubangiji ya tsara masa rayuwarsa ne saidai ya gode masa kawai in yaƙi kuma ya godewa azabarsa don Allah ki koyi haƙuri da yanayin rayuwa komai zai wucce insha Allahu watarana sai kiga labari kike badawa"
Bata da wata sauran kalma data rage da zatayima Mama bayani ta fahimceta dole tasata yin shiru ta kwanta itadai da Dad zai taimaketa kamar yanda ya furta ya dawo da ita gurin Granny tabbas da taji daɗi sosai. Bayan sunyi sallar Isha wani aikin suka dauko ita da Mamanta sukeyin komai cike da kulawa da juna har suka gama wajen 11:30 suka nufi ɗakin Mama suka kwanta sunata yan hirarrakinsu mama tana faɗa mata so takeyi idan lkcn hutunta yayi zataje Gashua ta kwana biyu rabonta da gida Yobe shekara huɗu kenan kallonta Anam tayi tace “amma meye zai hana mu tafi tare Mama nima inason naje naga dangina"

Dafa kanta mama tayi tace “to banda abinki Kharimatu ai zakije ne kinsan yanayin aikina da naki ba ɗaya bane kedai kije kiyita hqr da halin iyayen gdanki watarana zai zama tarihi kinji" ɗaga kai tayi ta fara addu'ar kwanciya bacci badon taso hukuncin na Mama ba sai don ba halinta bane jayayya da mahaifiyarta da wannan bacci ya ɗauke ta da asuba kuwa suka shiga zarafin aikin abincin birthday duk da cewar an bayar da kwangilar wani amma yanayin yanda suke d yawan masifa gasu da ɗabbaƙa bidi'a yasa gidan ya cika ke kya dauka bikin aure sukeyi ko suna Anam Bata samu kantaba sai huɗu da yammaci tun safe dake Allah ya hore mata lfyr aiki kamar engine tayi wankanta ta ɗauki wata lashinta da Umaimah ta bata tasa riga ce doguwa saiya kasance sun fito mata da asalin surar ta da ƙuruciyarta abinka da chocolate color oily skin sai milk ɗin less ɗin yayi mugun haskata tayi kyau na ban mamaki ta fita ta nufi sashin Granny ta sameta ita da Alh Mahdi wa gurin Alh Ma'aru ta rusuna ta gaida shi ya amsa mata da sakin fuska Granny tace.

“Ƴar nema kinzo ki tumurmusani ɗin ne?" Dariya tayi tace “haba My Kakus ƴar tsohuwa yaushe rabonki da tausa irin tawa me daɗi saboda daɗinta fah kikece mata tausar Tailand" kama ƙafarta tayi tana matsawa a hankali Alh Mahdi ya tashi yace “Hajiya Iya tunda kin samu ƴar hira bari naje gurin yaran can da suka cika mana gda da kiɗa kamar ƴaƴan yahudawa"
Fita yayi Hajiya Iya da Anam sukaci gaba da hirarsu Hajiya Iya na korarta ita kuma ta nace taƙi tafiya saida tace “zakici kunnen Uwaki bari na kira miki Mala'ikinki Haidar ai yana gdan naga zuwanshi da iyalinshi ƙila na samu salama kajini da ƴa ƴar kusun uwa tanata murɗemin yatsa......"
Wata ƙara Hajiya Iya ta saki daidai lkcn da Aliyu ya shigo tayi caraf tace “yawwa Haidaruruwa kaɗamin wannan ja'irar yarinyar gurɗemin yatsu take neman yi" kafin ma ya waiwayo kanta tayi wuf ta shige ɗakin Hajiya Iya tana cewa “Granny kefa kikace nayi miki shikenan tunda bakiso bari na gyara miki ɗakinki na jera miki kayanki a wardrobe"

Bata kula da hararar da Aliyun ke watsa mata ba shi yarasa meye tashi batazo ɗaya da yarinyar ba yanda ta nufi ɗakin tana kaɗa jiki yayi mugun ƙular dashi a haukansa gani yake donshi takeyi wanda ita batasan ma da hakan ba tunda bata taɓa samun mai faɗi mata ba. Tana jiyo hirarsu da Granny yau ma kamar kullum Ƙorafi takeyi masa shi yaƙi gaba kullum kaganshi kamar haɗowar hadari bayada fara'a baya da rahama a fuskarsa inda shi kuma yace “nikam Granny kinsamin ido da yawa duk duniya kece kike cemin na ragu kona ƙaru ke kuma ba iya yimin maganin matsala ta zakiyi ba"........
Sunata hirarsu da zolayar juna yanata dariya abinda kullum yake bawa Anam mamaki ko a gdansa ita zata iya rantsewa bata taɓa ganinsa yana dariya ba kullum fuskarsa kamar ta bijimin sa amma Indai ya haɗu da Granny yanzu zakijishi yana ɓaɓɓaka dariya, taɓe baki tayi a ranta tace “miskilin banza da baya iya control na gdansa a fili kuma amsa kiran da Granny take mata tayi ta fito tana goge fuskarta da tsumma ta rusuna tace “gani Kaka" nuna mata kitchen tayi tace “wannan kitifaffen ubangidan naki zaki haɗowa abinci yace anan zaici"
Miƙewa tayi ta nufi kitchen ɗin yana latsa wayar hannunsa ta haɗo sinasir da miyarsa da taji tantaƙwashi da man shanu ta dauko masa lemu me sanyi da ruwa ta jero masa ta nufo inda yake gabanta na faɗuwa ko a gda bata ƙaunar kai masa abinci saboda baayi masa gwaninta.
Tsugunnawa tayi a gabansa mayafin jikinta ya zame daga kanta dake me yauƙi ne ya sauka ƙasa bisa rashin saa rigar irin me buɗaɗɗen wuyan nan ce tudun dukiyar fulaninta duk a waje suke hakan yayi daidai da ɗagowarsa da nufin yi mata masifar daya saba tsautsayi yasa idonsa ya caki ƙirjinta da batama lura da mayafin ya zame ba ya zubawa wannan abu me matuƙar ɗaukar hankalinsa a jikin mace idanu kamar wanda ya warke daga ciwon makanta, hakan yayi daidai da ɗagowarta da nufin neman izinin tashi domin ta gama haɗa masa kawai ta mayar da idanunta a ƙirjinta taga abinda ya shagala da kallo. Ta kuwa firgita ainun a razane ta wawuro mayafinta ta rufe jikinta ko ina na jikinta ya ɗauki rawa tasan yau ta shiga uku har shida gaban shida har tara ma ta shiga.

[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?

Fauziyya Tasiu Umar
(Oum Hairan)

5-6

Cikin kiɗima ta ja da baya ta zube a ƙasa tayi knile down tace “kayima girman Allah da darajar Hajiya da Alh kayi hqr wlh tallahi bansan ya zame b......" Ɗaganta hannu yayi ya haɗiye kunyarsa cikin ƙara ji yace “tashi kibani guri mara sanin ciwon kai wato ke nan har kinkai budurwar da zaki rinƙa tallan jikinki a kwararo toni ko jiki zai burgeni me zanyi da wannan baƙar fatar taki wawuya dake bagidajiya"
Itadai Anam har tuntuɓe takeyi saboda sauri sukayi kicibis da Granny ta riƙota da sauri tana cewa “ke marainiyar Allah nutsu kama kanki meye yayi zafi da wannan firgici haka me Haidar ɗin yayi miki?" Toshe bakinta tayi domin batada kalmar magana ta janye ta kwasa a mugun guje ta nufi bayan gdan saida ta fakaici ido sannan ta shiga gdan ta shige ɗakin Mama Yabi cikin Sa'a itanma batanan ta kwanta tana mayar da numfashi tare da yima Allah gdy daya kuɓutar da ita daga cin duka gurinsa tananan kwance har aka gama birthday ɗin kowa ya watse saida ta tabbatar da tafiyar Aliyu da Salma sannan ta fito suka shiga gyaran gdan basu gama ba saida dare ya shiga suka ƙarasa suka kwanta .

Washegari ma aikin ne dasu Hajiya Muniba irin matan nan ne da baayi musu gwaninta komai kayi baka iyaba su gyara nan tace ba hakaba su gyara nan tace a'a daƙyar Allah ya basu ikon gamawa itama wannan rana sunji a jikinsu dan ko abinci basu samu damar ci ba sai Magrib suna cikin cin abincin Umaimah ta shigo ta dubeta tace “Ya Aliyu yace kije ku tafi gobe Monday sunada aiki" wani abu ya tokare mata maƙoshi abincin data zuba a bakinta yaƙi haɗiyuwa a ranta tace “shikenan shi bawa bashi da hutu bashi da ƴanci a rayuwarsa?
Mama ce ta taɓa ta tace “ki tashi karkiyi laifi Haidar ba wuya bane fusatashi" miƙewa tayi sarai tasan halinsa ko kayanta bata ɗauka ba ta fita yana zaune cikin mota ta nufi motar gabanta na faɗuwa da kuma matsananciyar kunyarsa ta isa ta buɗe ta shiga bata ko samu arziƙin kallo ba ya gama wayarsa yatada motar suka tafi har sukaje gdan bai tanka mata ba yana parking ta fita yabi bayanta da kallo tare da taɓe baki.
Turus taja ta tsaya saboda ganin yanda parlourn yayi kaca² yaran duk sun ɓatashi da gudu Jannat ta nufota ta ɗauke ta tana juyawa da ita tanayi mata dariya yarinyar ma na dariya daidai lkcn da Salma ta fito Anam bataji tahowarta ba kawai sukayi karo aikuwa ta angajeta bisa tsautsayi ta faɗa kan cup ɗin glass ɗin ɗaya fashe a parlourn aikuwa ta fasa ƙara saboda nitsewar da kwalbar tayi a goshinta jini yayi wata irin tsartuwa ya fallatsa har jikin Aliyu dake tsaye tun lkcn da Anam keyima Jannat wasa.
Chapter 2 · 0% Book details