← Book details Me Ya Jamin New Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 19

Sashe 11

Me Ya Jamin New Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da dare ne wayar tayi ta ring ta janyota ganin sunansa akan sensor yasa gabanta faɗuwa haka dai tai ƙarfin halin ɗagawa baijata da doguwar mgn ba tambayarta kawai yayi taci abincin tace eh ya kashe, tun daga wannan ranar ya zamewa Aliyu farilla kullum sai yazo gdan ya ganta kafin ya fita aiki wataran idan ya dawo ko kuma yace abashi ita zasuje unguwa ran Mama bayaso saidai bazata iya ce masa a'a ba shida matarsa Granny cema me ƙoƙarin hanawa to itama dole tanada iyaka musamman da yaje yayi mata daɗin baki ya kasheta da kalamai shikenan tayi muƙus a gdan ma idan yazo sai ya kira Anam ɗin sashin Granny ya lallaɓeta da yaudararrun kalamansa ya samu nutsuwa da ita tun tanaƙi har ta saduda.
Satin Salma uku a Niger ta dawo 9ja a lkcn shirye²n bikin yayi nisa sosai don har kayan amarya ankai sabon gdan daya gina mata komai Abba ne yayi mata tarkacensu ne na barebari kawai sukayi kayansu duk akaje aka jere a gdan ana jiran sati yazo akai amarya ɗakin mijinta.

Cikin kwanakin da aketa shirye²n shagalin bikin ne kuma ɗif ya ɗauke ƙafarsa a gdan nasu babu wanda ya kawo wani abu kowa yabar abin a cewa hidima ce tayi masa yawa Anam ce kawai jikinta yayi sanyi ganin ko waya ya daina kiranta ana saura kwanaki biyu bikin har an fara shagalin biki ana saura kwana uku bikin suka ɗunguma ita da Mama suka koma Guru acan zaaje a ɗaukota ranar da zasu tafin ne ta kira shi a waya kira uku bai ɗaga ba sai a na huɗu ya ɗaga yace ta fito harabar gdan yana jiranta.
Ta zari mayafinta ta fito da zaƙuwa saboda sun kwana biyu basu haɗu ba tun daga nesa ya kafeta da idanunsa kallon kusan faɗuwa yasata daƙyar ta iso gareshi har zuwa lkcn ita yake kallo ta tsugunna tace “Ina yini" numfashi ya sauke ya cire hularsa ya shafa sumarsa yace “kina lfy kinjini shiru amma baki nemeni ba" ƙasa ta sakeyi da kanta cikin kunya tace “nayi tunanin hidima ce ta ɓoyeka" murmushi yayi yace “daba ita ce bafa?" Nuni yayi mata da ta miƙe ta tashi tsaye tana wasa da zara²n yatsunta ya kwantar da kansa jikin mota yace “Granny ce tayimin tsakani dake shiyasa na ƙaurace miki"

Da sauri ta kalleshi ya ɗaga hannunsa ya ɗora daidai goshinsa yace “amma kiyi hƙr nasan zuciyarki ta ayyana miki wasu abubuwan ko? Am kamar me dame ta ayyana miki nasan dai tace miki Aliyu ya gujeki ya daina kiranki ya daina zuwa inda kike, bayan haka sai me?" Dariya tayi da ta bayyana kyawawan Haƙoranta ya zubanta idanu yana murmushi yace “naso ayi komai anan a gama Abba yace a'a saidai ayi a garinku okey ki kasance cikin aminci kiyimin tanadin Pure honey da zaki shayar dani a daren angwancina" turo baki tayi tace “meye ma ya rage bayan komai ka kwashe....." Rufe mata baki yayi yace “Aa bari faɗa ban ɗauki komai ba kawai rage zafi nayi za dai ɗauka zanci na ƙoshi ranar da su Granny bazaa sanyamin idanu ba.

Juyawa tayi zatabar gurin yayi saurin riƙota ya haɗata da jikinsa yace “Da banida wani uzuri tare zamu tafi amma babu komai saura ƙiris" haka ya rinƙa yi mata kalami duk ya kashe mata jiki kafin yace “kinsan me" girgiza masa kai tayi ya matso kusa da ita sosai yace “ina sonki...." Kwasa tayi da gudu tana waiwayensa tana dariya shima yanayi mata dariya baibar gdan ba saida yaga tashin motarsu.
Suna ɗagawa juna hannu cike da shauƙin juna har sukayi nisa sannan ya hƙr tunda motarsu ta tashi yaji gabansa na faɗuwa jikinsa duk ya mutu hakanan ya tsinci kansa cikin kewarta daƙyar yaja motarsa ya nufi gdanta da yasa aketa shiryawa ya zauna a falon ya zubawa manyan hotunan su idanu tsayin lkc ya shagala da kallon hotunan daya sanya akayi musu manya ya kafesu a falon kyawunta sihirtacce ba kowa yake gane tana da kyau ba sai wanda yasan asalin sirrin kyau shi kansa a farko idan Nazeer yana yaba kyawunta musawa yakeyi sai yanzu ya gaskata itaɗin kyakkyawace ta kwatance musamman cikin watanni biyun nan daya gyarata da manya mayuka oily skin nata sai wani ɗaukar idanu sukeyi.

Wayarsa ce ta katse masa tunanin Second wife ya gani a rubuce saman sensor na wayar ya ɗauka da sauri tare da lumshe idanu ya kara a kunnensa kafin yayi mgn yaji hayaniya ta cika masa kunne ya miƙe da sauri tare da cewa “Khamilu ina Kharimatun...." A ɗaya ɓangaren akace “mal ka nutsu mun tsinci wannan wayar ne a cikin wata jaka Allah yasa babu security so muna dubawa sai mukaga wannan number ansa Zaujhnoor shiyasa muka kiraka....." Katseshi yayi da cewa naji malam ina matata kardai kacemin hatsari sukayi ida drivern ina Mama?" Wani ne ya karɓi wayar yace “bazamu tantance komai ba amma dai an ɗaukesu ankasu asibitin Dutse saboda yafi kusa da inda sukayi accident ɗin so ana buƙatar makusantans......"
Bai gama sauraron wayar ba ya fice da gudu ya shiga mota ya fice a gdan cikin tashin hankali shidai bazaice ga yanda akayi yaje Dutse ba sai ganinsa yayi a cikin asibitin yana zuwa ya tarar da Alh Ma'aru a asibitin lkcn suna emergency ana ƙoƙarin ceto rayuwarsu abu da ƙarar kwana an samu nasarar samun rayuwar kowa amma banda ta Mama Yabi Allah ya karɓi rayuwarta a wannan hatsari inda Khamilu ya samu karaya huɗu Ita kuwa Anam doguwar suma da Ɓarin cikin da babu wanda yasan dashi ta samu sai karaya ɗaya a ƙafa.

*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: *MYJ29-30 Oum Hairan* Littafina na kuɗi kada ki karanta min baki biya ba don Allah idan kinaso ki biya ta 0255526235 Gtbank ko ki turo hoton katin 300 ta wannan number 09013718241 saiki tura evidance of payment ta number dai ko VTU ta 09031307566

Tashin hankali da ɗimuwar da Aliyu ya kasance a ciki ba kaɗan bace daƙyar da rarrashi Abba yasashi ya nutsu tare da nuna masa hƙr shi ya kama da dauriya saboda Anam a gurinsa kawai ya rage zata samu nutsuwa idan shi bai nutsu ba taya ita zata nutsu?
Da wannan kalaman ya ɗan samu salamar zuci ya zubawa amaryar tasa ido da take cikin halin suma sosai yaji takaicin suɓcewar cikin nasa duk da kasancewar baisan sashi ba a ransa yake raya da yanzu yaransa sun kusa zama huɗu fah rashi biyu sukayi ga rashin surukarsa ga rashin cikinsa, a haka Su Mal Datti kakan Anam sukazo aka tafi da gawar Mama zuwa Kano don tafi kusa domin a sutura ta Aliyu baije ba haka ya wanzu a asibitin sai yammaci liss komai ya ɗan tsagaita sukayi transfer ɗin petiant ɗin zuwa asibitin Mal Aminu Kano aka ɗebe su a Embulance zuwa Kano Granny ke jinyan Anam cike da tausayi da jin ƙai tana tuna kalaman yarinyar a mafi yawan lokuta idan anyi zancen mutuwa takance mata.

Granny nidai fatan da nakeyi kada mutuwa ta ɗauke min Mama tabarni nikaɗai ina Gantali a duniya wlh duk ranar dana buɗi ido naga babu Mamana a gefena tabbas idan nima ajalina bai rigaya ba to kuwa sai an rinƙa haɗamin da addu'a domin tsaf zan iya zaucewa"
Hawaye ta ɗauke a idanunta yau ga ranar da take tsoron zuwa ta iso babu mama Yabi mutuniyar kirki da duniya bata ɗaɗsta da ƙasa ba gashi abin yazo mata a daidai lkcn da tafi buƙatarta fiye da komai, Granny ta Jima tana alhinin wannan rashi kafin ta tashi ta nemi makwanci ta kwanta haka suka wanzu a asibitin wajen kwana huɗu sannan Anam ta fara dawowa hayyacinta.

Ta fara buɗe idonta tana me ambaton sunan Allah a hankali ta fara sauke idanunta kan mutanen dake zagaye da ita ta jima idanunta akan Aliyu da shima ya kafeta da idonsa da suke cikin farin glass a nutse ta ɗaga hannunta ta miƙa masa ya kama hannun nata ta yunƙura alamu sun nuna masa tashi takeson yi ya ta rintse idanunta tanajin azaba da zugi a hannun nata daya karye ta saki wata yar siririyar ƙara data sanyashi kallonta ta buɗe idonta da hawaye ke ƙoƙarin gangarowa a hankali cikin muryar tausayi yace mata “Sannu" daga masa kai tayi tana kallon Granny da taketa matsar hawaye a kasalce tace “Granny meye ya kawo mu nan ina Mama...."

Ƙasa taga Granny tayi da kanta yayinda Aliyu ya fice daga ɗakin da sauri, dukkansu tabisu da kallon rashin fahimta tanabin hannunta da kallo ta zuro ƙafafunta ƙasa ta tashi tsaye tana layi ta nufi Granny ta Kama hannunta tace “Idan zan iya tuna wani abu kamar hatsari mukayi ko Granny please ki faɗa min ina Mama inje inganta ince dai ita bataji ciwo ba?" Rungumeta Granny tayi da Muryar kuka tace “kiyi hƙr Kharimatu duk abinda da Ubangiji ya zartas akan bawa shine daidai tabbas mutuwa batada daɗi musamman ta iyaye Kharimatu muna tayaki alhinin rashin salihar mahaifiyarki Ubangiji yasa lahirarta tafi duniyarta...."
Tun kafin Granny ta ida rufe bakinta sabuwar tashin hankali tayi wankan tsarki ta samu gurbi a ilahirin sassan jikin Anam ta rinƙa kallon Granny kanta na juyawa tana ganin abubuwa hurhuɗu kafin kace meye wannan ta sake zubewa a ƙasa luuuuuu.
Daidai lkcn da Aliyu da likitan suke shigowa suka nufota a guje Aliyu ya tallafota yana kiran sunanta amma ina babu alamun zatayi motsi, ɗagowa yayi ya dubi Granny yace “Fada mata kikayi ko?" Share hawayenta tayi tace “To Gadanga meye amfanin ɓoye mata abinda dole zata sani?" Shiru yayi cike da jin takaicin abinda Granny ta aikata ya ɗagata ya ɗorata a gadon ya kwantar da ita likitan yayi yan aikace²nsa ya fita daidai lkcn da Momy ta shigo asibitin suka gaisa da Granny ta tambayeta me jiki ta bata lbrn farkawar ta Hajiya Muniba ta jinjina kai tace “Insha Allahu zata tashi rashin Mahaifiya da ciwo saidai Allah ya bamu ikon yi musu addu'a"
Chapter 11 · 0% Book details