← Book details Me Ya Jamin New Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 19

Sashe 3

Me Ya Jamin New Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da gudu ya ƙara so kanta ya ɗagota gabaɗaya jini ya wanke mata fuska yace “subhanallahi Salma bakida hankali ne wasa fa takewa ƴarki shine zaki ture ta har kiji mata ciwo haka kefa kika dameni naje na ɗaukota yara sun dameki dama abinda kika shirya yi mata kenan?"
Yana mgn yana tare jinin da hannunsa inda ita kuma Anam taketa jijjiga kanta daya ɗaure da wani mugun ciwo, taɓe baki Salma tayi tace “to ko zaka rama matane Aliyu naga alamun kaji ciwon kaima a jikinka" kallon Salman yayi rashin lkcn bata amsa yasashi kama hannun Anam yace “Sannu Kharimatu tashi muje ayi miki dressing na gurin" miƙewa tayi tana layi saboda ba ƙaramin jini ta zubar ba motar yaja a mugun guje suka fice daga gdan suka nufi wani asibitin kuɗi a cikin unguwar ta Yankaba tasha wahala kafin su zare kwalbar sukayi dressing gurin likitan ya dubesa yace “zatayita fama da ciwon kai dole ta rinƙa samun hutu" jinjina kai yayi ya biya su suka fito har yanzu kuka takeyi bawai na zafin ciwon bane a'a tunawa da tayi cewa da mahaifinta yana raye qila duk da haka bata rinƙa faruwa da itaba.

Sau ɗaya yace mata sannu har sukaje gda wani abin mamaki Salma Bata gyara gurin da jinin ya zuba ba balle ta gyara parlourn Suna shiga Anam ta ɗauki tsintsiya zata share parlourn ya dakatar da ita yace “kije ki kwanta kawai" aje tsintsiyar tayi ta nufi ɗakinta ta kwanta nandanan kuwa zazzaɓi ya rufeta me zafin gaske a daren taci wahalar zazzaɓin batayi tunanin zatakai safe ba hakanan dai ta rinƙa addu'o'in da suka sawwaƙa a bakinta har zuwa wayewar gari da safe da wuri ta tashi domin shirya yaran zuwa makaranta ta kamasu tayi musu wanka tanayi tana duba breakfast ɗin data ɗora harta gama ta haɗa masu gdan basu sauko ba ta zauna tana rawar sanyi tana bama yaran abinci zazzaɓi na ƙara ƙarfi sanyin A.C na haɗa ta ita ba abin ta kasheba matar gdan ta nakasata.
Gama sallamar yaran tayi takaisu ga driver ya tafi makaranta dasu hadda jannat dake itama ansata juma'a ne bata zuwa ta dawo a wahalce ta rinƙa gyara gdan ta kusa gama parlourn taji sun sauko ta durƙusa cikin ladabi ta gaishesu Salma ta ɗauke kai sai Aliyu ne yace “ya jikin...." Kafin ta bashi amsa yaga yanda take rawar sanyi yace “ko zazzaɓi kikeyi ne?" Ɗaga masa kai tayi ya matsa ya taɓa jikinta yaji zafi zau ya dubi Salma yace “ki ɗauki key na motarki ki tafi zan Kaita asibiti" wani malolon baƙin ciki ne ya cika zuciyar Salma ta kuwa taso masa da cewa “haba Aliyu wannan ai wulaƙanci ne akan wannan ƙazamar talakan zakace naje nayi driving bayan kasan banason......."

Ɗaga mata hannu yayi ya dubi Anam yace “Ɗauko hijjab ɗinki Kharimatu" da sauri ta miƙe domin shiga ta ɗauko hijjab ɗin jiri ya ɗebeta ji kakeyi tik ta zube a ƙasa ya isa da gudu ya ɗagota ya fice da ita yasata a mota suka fita suna zuwa aka bata gado tsoron kira yake ya faɗa yasan masifar Granny Indai tasan dalili to ba Salma ba shi kansa ya kaɗe har ganyensa.
Ganin lkc na tafiya gashi yanada taro 9:30am yasashi yin shahadar kiran wayar Mama Yabi ta ɗaga suka gaisa ya faɗa mata abinda ke faruwa aikam ta ruɗe tace “bansan yaushe Kharimatu zatayi hankali ba kawai saboda sakarci taje zata illata kanta ganinan"
Ajiyar zuciya yayi ganin ya ɗorata ta ɗoru yaci gaba da zama gurin Anam tare da zubanta ido yanda take kwance da drip a hannunta baccin wahala ya ɗauketa kanta sanye da hula fuskarta wasai ga ɗaurin dressing ɗin da akayi mata jiya a hankali ya gangaro zuwa gangar jikinta yana ƙare mata kallo tunda yake baitaɓa tsayawa ya ƙarewa Anam kallo ba sai Yau Nazeer abokinsa yana yawan faɗa masa wato Aliyu babyn nan ta gdanka Anam tana matuƙar burgeni ɓoyayyen kyaunta yana ruɗani bantaɓa gajiya da kallonta ba nikam da zan samu dama zanso abani wannan yarinya matsayin mata nasan zanji daɗin hakan" taɓe baki yayi ya miƙe yana ƙare mata kallo yace “kai kasan wani ɓoyayyen kyau Nazeer Ni bayyananne na sani".......

_Zaku iya samun damar cigaba da karanta wannan littafi kan ₦300 kacal tura ta acc 0255526235 Gtbank ko kati MTN ta whattsAp number 09013718241_

*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?

~Paid book~

Oum Hairan

7-8

Kiciɓis sukayi da Mama a ƙofar shiga ɗakin suka gaisa ta shige ciki ta zubawa ƴartata ido cike da tausayi ƙarasawa tayi gabanta ta riƙo hannunta daidai lkcn data buɗe idonta tace mata “sannu Kharimatu ashe haka tsautsayi ya faru dake kema kin cika gaugawa ki rinƙa bin abubuwa a hankali kinji" lumshe idonta tayi tanajin ɗacin abinda ya faru da ita a ranta Aliyu ya shigo da sallamarsa a ƙasan maqoshi ya ajiye ruwa da magunguna yace da Mama “tunda kinzo zanje office inada Meeting zuwa tara da rabi" kuɗi ya zaro ya ajiye a gefen gadon tayi masa gdy ya fice a ɗakin batare dako inda Anam take ya kalla ba.
Bayan fitarsa Mama ta haɗa mata shayi me kauri da madarar daya kawo ta zauna tana bata tanaci daƙyar abincin ɗaci yakeyi mata a baki hakadai ta rinƙa turawa harta ƙoshi jefi² suke yar hirarsu da Mama Anam ta kasa jurewa ta faɗawa Mama asalin abinda yaji mata ciwo har ya haifar mata da zazzaɓin sosai Mama taji babu daɗi amma a fili sai tace “babu komai akwai Allah da talaka da mai arziƙi duka wanda yayi su son abinsa yakeyi saboda haka komai yayi farko zaiyi ƙarshe"

Ba haka Anam tasoba domin zuwa lkcn hƙrnta da zama a gdan Salma ya ƙare burinta kawai barin gdan saidai batada wata hanya ta barin gdan dole saida shahalewar Mama, yini sukayi a asibitin da yamma Aliyu ya dawo shida Granny tanata zubawa Anam sannu likitan yazo ya sallameta yayi Hamdala domin bayaso asirinsu ya tonu yafiso ayi a lulluɓe mgnr ɗebe kayan sukayi suka zuba a mota bayan sun shiga Granny tace “Ali wannan yarinyar gda zata wucce gurin uwarta idan ta warke ta dawo wannan kasaltacciyar matar taka me shegen son jiki ba ƙyaleta zatayi ta warke ba"
Bayason jan maganar dole ya amince saboda gudun tujarar Granny suka wucce Ɗan ladi nab Sidi zuciyar Mama da Anam wasai suna zuwa ya zubesu ya juya ya nufi gdansa. A falon ya tarar da Salma taci uwar kwalliya ta harɗe tana kallo tanacin donnut ya dubi yaran yagansu da kayan islamiyya yace “ya haka Salma gobe babu makaranta ne?" Ɗagowa tayi tace “kayan naji suna tsamin gumi shine nabarsu idan kun dawo waccen yarinyar ta wanke" jinjina kai yayi lallai Salma batada imani wato wadda aka sallamo a asibiti take tsammanin tayi mata wanki lallai Granny tanada hangen nesa.

Samansa ya haye yayi wanka ya fito ya zauna a dinning ya buɗe abinci ya faraci baici na kirki ba ya miƙe ya nufi waje ya zauna a kujerun dake cikin flowers na gdan yana duba jarida
Bai koma cikin gdan ba sai bayan yayi sallah Magrib da isha sannan ya shiga ya nufi saman ya shiga ɗakinsa ya sake watsa ruwa ya kwanta shiru yana jiran Salma har dare ya tsala yaja tsaki ya juya lamarin Salma ta fannin kula da shimfiɗarsa yana bashi tsoro kullum ita cikin uzuri take yau aiki gobe ciwon mara jibi zubar jini idan bataga damaba sai su shafe satittika a haka babu ruwanta shikuma ga miskilanci Indai bata kawo kanta ba ya daina kiranta.
Wayewar garin ta shirya tsaf tana mita ta shirya yaran suka fice suka tafi aiki sukuma yaran aka wucce dasu makaranta a mota take tambayarsa wai meye ya hana Anam dawowa? A gajarce yace “ganin dama" daga haka tayi masa shiru shima yayi mata ya ajeta a ma'aikatarsu ya wucce Campanynsu.

Kwanakin da Anam tayi tare da Mahaifiyarta abin gwanin daɗi ji takeyi kamar karta koma.
Ranar data cika sati tana ɗakin Granny sunata shirmensu Suka tsinkayo sallamar Aliyu saida gabanta ya faɗi ya shigo ɗakin idanunsa na kanta hakanan ya riski kansa da wata muguwar faɗuwar gaba lkcn da ya sauke idanunsa akanta cikin sati gudan da baya ganinta sai yaga gabaɗaya ta canza masa tayi wani haske fuskarta tayi fiyau da ita, janye gashinta tayi daga hannun Granny da take daure matashi tana ranƙwashinta tana cewa “ni banda tsiya Allah yayi miki yalwar suma ki rinƙa neman lalatata da shirme idan tayi fushi ta kaɗe ai naga da uwar da zakiyawa mijin da kishiyar gwalli"
Turo baki tayi tace “tabdi lallai ma Granny nikam ki dainamin fatan kishiya wlh ko sunan banson ji" ba Granny ba hatta Aliyu saida ya zare tabarau ɗin idanunsa ya kalleta tayi ƙasa da kai ganin irin kallon da yakeyi mata yasata jan mayafinta ta fice sumsum har taje bakin ƙofa yace “ki shirya zamu tafi gdan babu kowa Salma ta tafi Ziyarar aiki Sokoto sai yara"
Chapter 3 · 0% Book details