← Book details Me Ya Jamin New Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 19

Sashe 1

Me Ya Jamin New Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?

Fauziyya Tasiu Umar
(Oum Hairan)

1-2

Tsugunne a bayan gdan wata matashiyar budurwa ce yar sha shidda zuwa sha bakwai baƙa me matsakaicin tsaho da ɓoyayyen kyau take wankin kayan yara na makaranta tanata rawar sanyi da alamun yanayin hunturun yana kaɗa duk dama Dole ne ya shigeta duba da ko arziƙin rigar sanyi bata samu ba, wani yaro ne qarami da bazai wucce shekara bakwai ba ya fito daga wata ƙofa alamu sun nuna itane ƙofar da zata sadaka da asalin gdan.
Hankalinta nakan wankin da takeyi bata ankare sa tahowar yaron ba saiji tayi ya watsa mata ruwan sanyi a jikinta ta zabura da sauri ta miqe cikin kiɗima take duban yaron idanunta ya kawo ruwa tace “Farook ni ka watsawa ruwa a wannan sanyin ko?" Murgiɗa mata baki yayi yace “an watsa miki ɗin talaka almajira kawai Momy tace kizo ki haɗa mana break in kinƙi kuma ta zaneki"
A sanyaye ta saki aikin da takeyi tana daga rigarta data manne a jikinta ta nufi ƙofar parlourn ta shiga da sallama babu kowa a parlourn sai Muwaddat da jannat ta dubesu dukkansu babu wanda ya samu arziƙin ko wankin idanu ta matsa ta dauki Irfan daketa miƙo mata hannu tana masa murmushi tace “yarinyana ko Pampers baa cire miki ba bari nayi muku wanka sai nabaku abinci Isiya yakaiku makaranta ko?" Ta Faɗi da sigar tambayar yaran Muwaddat ta zunguro baki gaba tace “aa nidai Aunty Anam ki bamu abinci tukunna da yunwa muka tashi"

Saukowar masu gdan ne yasata haɗa nutsuwarta ta durƙusa cikin ladabi tace “barka da fitowa yallabai Hajiya Barka da asuba" baiko kalleta ba yasa kai ya fice a falon Hajiya Salma ce ma ta harareta tace “kinanan kina sakarcin naki na tsiya zaki makarar min da yara ko duba ko Pampers baki cirewa jannat ba saboda ke kin zama mara mutunci to ki makarar dasu sai hankalinki ya kwanta jaka kawai....."
Kalmar ƙarshen ta bugeta sosai ta sunkuyar dakai hakan bai mawa Hajiya Salma ba saida ta saukenta ƙusa a tsakiyar kanta ta rintse idanu hawaye nabin kuncinta inda sabo zuwa yanzu ya kamata ace ta saba da izayar gdannan tunda kusan a cikinta ta rayu tun tana shekara biyar suke tare da mahaifiyarta a wannan gda duk da kasancewar ba'a asalin wannan gidan suke ba mahaifiyarta tana gdansu Aliyu wato mamallakin gdan tanayima iyayensa aiki lkcn da Aliyu yayi aure ne matarsa ta matsa tanason yar aiki shine aka kawo ta gdan nasa matsayin yar aikin gdan yanzu shekara takwas kenan tana aiki a gdan a gabanta duk aka haifi waɗannan yaran Umar Farooq Muwaddat da jannat amma har yanzu yanci yaqi zuwan mata daga megidan har matar gdan har yaran gdan babu wanda take samun sauqi ta gurinsa har garama Salma wani lkcn takan jata suyi hira idan yan mutumcin na kusa.

Ɗaukar yaran tayi suka nufi dakinsu tayi musu wanka tasa musu uniform ta fito ta haɗa musu break ɗin sukaci Farooq nata barna shida Muwaddat babu wanda ta isa hanawa yanzun uwarsu tana dawowa su kitsa mata ƙarya da gaskiya ta hau ta zauna ta zage ubanta daya mutu tun batasan kanta ba ta zage uwarta data qare rayuwarta a bauta don rufa mata asiri sannan idan bai isar mata ba ta gama ta da dukan mutuwa wannan yasa take takatsantsan da lamarin gdan.
Daƙyar Allah ya taimaketa suka gama ta goya Jannat suka fito ta bawa Isiya lunch box ɗin yaran suka shiga Mota itakuma ta lulluɓe jannat ta koma ta karasa wankin ta shanya ta shiga ta fara gyaran gdan ɗakin Aliyu ne kawai bata shiga ba saboda yayi mata ƙwaƙƙwaran kashedi akan shigar masa ɗaki tun yana gda ko anan ɗinma da Salma taso sakar mata gyaran ɗakin da ita da Salman yacima mutumci dole tasa ta hqr take gyara masa idan ta dawo daga aikinta.

Tana kammalawa da parlourn ta nufi ɗakinta ta gyara ta kwantar da jannat tayi wanka tasa wata jemammiyar atamfarta domin Salma ta hanata Sanya kaya masu kyau kullum kaganta cikin tsumma zaka ishe da hijjab a jikinta batasan dalilin wannan doka ba.
Sai biyu ta shiga kitchen ta manta bata tambayi masu gdan abinda zasu ci ba ta ɗauki wayarta ta kira number Hajiya Salma saida ta katse ta sake kira sannan ta ɗaga cikin masifa tace “wai Anam ke wacce irin wawuya ce ina aiki zaki dameni...." Cikin ladabi tace “kiyi hqr Hajiya mantawa nayi ban tambaye ki abinda za'a girka muku ba....." Da masifa tace dalla Malama bansani ba ni zaki tambaya bazaki tambayi su Farooq ba to ki girka ubanki....." Qit ta kashe wayar Anam ta tsaye sororo da waya a hannunta tanajin ciwon yanda Hajiya Salma batajin nauyin zaginta yanzu daga tambaya sai cin mutumci?
A saluɓe ta nufi kitchen tana tunanin abinda zata girka lumshe manyan idanunta tayi dabara ta faɗo mata tasan Aliyu yanason tuwon shinkafa miyar taushe aikuwa nandanan ta fita tabawa driver sautun kayan taushe wanda babu a gdan ta koma ta ɗora tuwonta ta malmaleshi a leda ta fara tafasa namanta isasshe tasa masa kayan ƙamshi nandanan ta haɗa komanta sannan taja da baya tayi farfesun naman kaji da yaji Attahiru ta jere musu a dinning ta dauko man shanu soyayye ta narka takai musu dinning ɗin.

Shige daki ta zauna tana game da rakani kashinta jin motar masu gdanne yasata miƙewa ta fito tana riqe da hannun jannat sanye da ƙaton hijjab ɗinta caraf bisa tsautsayi idanunta ya fada cikin na Aliyu tayi saurin janyewa ta rusuna tayi musu Barka da dawowa ya amsa a shaƙe ya buɗe baki yace “hajiya tace kije can gobe Umaimah zatayi birthday akwai ayyuka acan"
Ajiyar zuciya tayi ko banza ta huta da masifar Salmah ta kwana biyu miƙewa tayi ta koma ɗakinta ta haɗa kayanta a yar ƙaramar akwatu ta dauko ta fito ta canza kaya tasa mayafi har sunyi wanka sun dawo dinning ɗin sunacin abinci ta rusuna tace “na shirya zan tafi" dubanta Salmah tayi tace “kwana uku zakiyi ki dawo" jinjina kai tayi Ta miƙe Aliyu dake satar kallonta yace “ki jirani a waje ganinan"

Jinjina kai tayi ta fita ta tsaya jikin motar ya ɗauki sama da 30 minutes sannan ya fito fuskarsa a murtuke ya buɗe motar ya shiga ya zauna ta buɗe gdan baya zata shiga yace “kinsan dake ni drivern babanki ne shiyasa zaki zauna a baya na tuqaki" bataso ake taɓa mata iyaye yanzun zuciyarta take karyewa ta juya jiki a mace ta shiga motar ya figa a guje ya fice daga gdan suka nufi Danladi na Sidi inda family house dinsu Aliyu yake suna zuwa ta buɗe motar ta fice yabi bayanta da kallo da mugun faduwar gaba ganin yanda take motsa jikinta.
Lumshe idanunsa yayi abin yayi masa dadin gani mamaki ya cikasa yaushe yarinyar ta girma haka har ta haɗa kayan ruwa haka? Saurin jan tsaki yayi yana kawar da tunanin ya fito a motar ya nufi cikin gdan a parlourn Ƙasa ya ishe su ita da Mamanta ta kama mata suna morping yana da hotuna Mama ce taga shigowarsa ta rusuna da girmamawa ta gaisheshi ya amsa kamar yanda yake amsawa da gadara ya haye sama Anam ta taɓe baki tace “kamar wani namijin ƙwarai a gda sai yanda akayi dashi" daƙuwa Mama Yabi ta watsa mata tace malafar ubaki ƴar nema koma mene ai yayi miki rana dalilin zaman gdansa gashinan kema ƴar Sakandire ɗin nan da yara sukeyi kin samu kinyi ta kuɗi to ubaki zakice da Haidar?"

Bata kuma cewa komai ba Umaimah ta fito da wata ƙawarta tana ganinta tace “yawwa Anam ki shiga ɗakina ki gyaramin ki shiryamin wardrobe ɗina kayan sun hargitse" amsawa tayi da to cikin ladabi ta nufi saman tayi sallama Hajiya Muniba tana zaune hakimce a parlourn gaban Anam ya fadi.
Ta rusuna ta gaisheta ta amsa mata a wulaqance tace “lfy" cikin in...Ina tace “Hajiya Umaimah ce tace nazo na gyara mata ɗakinta" jinjina kai tayi ta nuna mata hanya ta miƙe taci uwar ɗammara da mayafin ta nufi ɗakin na Umaimah ta soma gyarawa bayan ta gama ta fito har yanzu suna zaune a parlourn sabanin ɗazu yanzu harda Granny ta ƙwama uban glass tana ganinta sukayi murmushi a tare tace “ƴar nema jikar na samu kinje kin ɓuya luf abinki Haidar ya boyeki baku Abuja baku Kano zonan naji fatar ki ko tayi laushi"
Dariya tayi da tasa fararen haƙoranta da suka jeru reras da kyakkyawar wushiyar suka bayyana dimple ɗinta ya lotsa tace “Granny tawa bari nazo nayi miki tausar Tailand" Alh Ma'aru dake gefe yayi murmushi yace “Anam ta Granny nifa Ina tunanin Granny zan dawowa dake su Aliyu sa nemi wata" riƙe baki Granny tayi tace “hooooo Ni Mairamu rufamin asiri da wannan ƴar ƙaniyar ɗiyar tun tana mitsitsiyarta ma azaba take ganamin balle yanzu dubi yanda take wani haɓaka kamar amsawa tsiro taki yo dubi iyayen nonuwa da ɗuwaiwaka idan ta zauneni ai saidai na farka a kabari"

_whattsAp number 09013718241_

*Oum Hairan*
[11/6, 7:22 PM] Oum Hairan&Affan: ME YA JAMIN?

Fauziyya Tasiu Umar
(Oum Hairan)

3-4
Chapter 1 · 0% Book details