← Book details Matar Police Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 19

Sashe 8

Matar Police Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jidda ta ce,"Mu ma din Wallahi ba Wanda ya isa ya dakemu ai inko ya dakemu aradu yau sai ya cire wannan bujen wandon na shi batare da ya sani ba. "

Suna cikin hakan kuwa Maman buje ya ce, "Ah Amarya Lantana har andawo makaranta ne? To ma za shige aji ki barni da wa'innan shirmammun."

Lantana ta tashi ta shige aji, sai ga Zainab ta zo.

Zainab wata yarinyace sa'ar Jidda Amman kwata-kwata ba sa jituwa da Jidda, mussaman Zainab yadda ta ke nuna ma su gadara ai ita budurwa Malam buje ce, hakan ya sa ta zuwa makaranta a duk lokacin da ta so domin tasan ba dukan letti ake ma ta ba, ita kuwa Jidda kullum abin na tsaya ma ta arai ta dauki alwashin wataran sai ta yi maganin Zainab, Abu daya ke ba ta tsoro tasan ba ta da karfi kar azo ita ba ta daka adaketa.

Kallon Zainab ya tsaya yi yana wayancewa kan ya ce,"Ah'ah Zainabu yau an makara kenan? Ya akayi hakan ya faru Dan nasan ba halinki ba ne."

Marairaicewa Zainab ta yi ta ce, "Wallahi Malam cikina ke ciwo shiyasa Yanzu ma da kyar na tawo."

Daga ma ta gira ya yi kan ya ce, "Ayya sannu to maza huce ki shige aji."

Jidda ta yi kwafa.

Ta na fadi aranta yau insha Allah ko ma miye zai faru sai na yi maganin yarinyar nan.

Murmushi ta yi da ya baiyana afili.

Sannan Malam buje ya fara doka.

A na zuwa kan Jidda ta tsere aguje sai da suka zagaya makarantar nan kaf kan Jidda ta tsaya kan lokacin ma ya gaji, Dan mugunta kuwa sai da ya ma ta bulala daya.

Shige wa aji ta yi ta na ma sa gwalo, "Ai ko ba komai dai wani ya ji ajikin shi, hhh mallam mai buje kawai."

Tunda Jidda ta shiga ban da tunanin abin da za tayiwa Zainab ba abin da ta ke, ai ko sai lokacin Break ya yi, da sauri cikin yatsine Zainab ta ta so za ta huce Gaban Jidda da gangan ta ta ke wa Jidda kafa.

Karaf Jidda ta tashi nan ta ke ta wanke ta da mari, Zainab ta ce, "Kambu ni ki Ka Mara? Ni sa'arkice."

Ganin Jidda ta ga Zainab ba ta da niyar ramawa ya sa ta cigaba da dokanta ta na, "Eh din andake ki din ni sa'arkice da zaki takana ki huce kamar kin taka dutse ko hakuri ba za ki ban ba."

Kamar ta sami jaka dukanta kawai ta ke ta inda ta so.

Zainab kuwa raguwa tuni anfara kuka hawaye da majina ne kadai ke gangarowa daga fuskarta.

Ita ko da taga tana kuka nan ta ke karfi da kwarin gwiwa ya kara zuwa ma ta, tana dukan tana, "Yara sai shegen raini ai daga yau na ga wadda zaki karawa rashin kunya, gwanda ma ki kiyayeni ke kin San karfi na kowa? Ko shi mallam bujen ma kawai ina raga mi shi ne Amman in kuka kai ni makura sai na ma Ku targade akumatu Wallahi."

Dakyar Ko aka kira Malam buje ya kwaci Zainab a hannun Jidda.

Urs Xayyeesherth
[11/15, 4:03 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: https://chat.whatsapp.com/KZgI9wMaXS23wEuzgd0ntQ

_*Group di na na zallan mata ne Dan Allah kar namijin da ya shiga, sannan in kin San bakya SHARHI ke ma karki shiga*_

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 18/19_*

****************
************
******************

Jidda sai nishi ake ana wage baki adole yau ta yi duka abin da ba asaba ba.

Zainab kuwa baki ya mutu ko Ido ba ta so su hada da Jidda domin tasan yau ta maku, ko ina Jidda ta samu kawai dabga ta ke ita ko ajikinta.

A na tashi su ka nufi gidan Lantana.

Suna zuwa lantana da dauko kwanan garar da aka kawo ma ta ta ce, "Yauwa Jidda ina shinkafa za a dafa?

Jidda ta daga mata gira, " Eh ma na shinkafar nan ma ta turawa kuwa. "

Lantana ta ce,"To yanzu indo ki kunna ma na wutar ni sai in yi dakan kayan miyan."

Aiko da kyar wuta ta kunnu, kayan miya kuwa andaka su fatso fatso.

Lanata ta ce,"Jidda mun gama."

Tashi Jidda ta yi ta na ya mutsa fuska, "Yauwa dauko robar manjan afara zubawa, ki dauko waccer katuwar tukunyar, wadda ta fi kowacce girma fa."

Jiki na Rawa Lantana ta dauko ta mikawa Jidda.

Da Jidda ta fara zuba manjan nan sai da ya yi Rabin galan din kar ta bari, "Gashi nan, kin San Anaso manja ya ji sosai shinkafar ta yi ja ta fi kyau, yauwa dibomim ruwa cikin karamin bokitin nan."

Ko bari manjan ma ya soyu ba ayi ba aka zabga uban ruwa acikin tukunya, kan nan aka sa fatso-fatson kayan miya.

Jidda ta ce, "Yauwa yanzu ba bare magi guda ashirin azuba, ba zamu sa gishiri ba Dan yan gayu ba sa gishiri a abinci, Yauwa Indo in kin zuba magani ki rufe ruwan ya tafaso kan azuba shinkafar,Lantana ki Auno ma na mudu Daya."

Lantana ta ce, "To, kiji fa har abincin ya fara kamshi."

Jidda ta ce,"Ai kadan ma kenan sai ma mun gama dafawa zakiga yadda zatayi."

Jidda ta karbi shinkafar,Indo ta ce, "Laa Jidda ba Wanke ba fa?"

Jidda ta galla ma ta harara "ni banson rashin kunya to bara Awanke din ba wayace miki yan birni na wanke shinka? To yasin rage dadin ta ake in an wanke Dan haka ba wankewan da za ayi haka za asa."

Lantana ta ce, "Laa Jidda kaman fa naga su Inna Sai sun cire datti kan ma ake dafawan."

Jidda ta yi tsaki , "To ai sai ku yi tunda ni zaku koyama girkin in kukayi wasa Wallahi sai in tafi in bar ma Ku girkin nan danma kunci sa'a ina farinciki yau na Zane zainabu Amman da wallahi ba wadda zan koyawa girkinma."

Lantana ta ce, "Aa ki yi hakuri Jidda ni nama tuna fa haka kawai Inna ke sawa na ta ba ji ma tana cewa In anwanke shinkafa gardinta ake rage wa ."

"eh mana ba ki ga ba wanke taliya ba? Ai shiyasa ita tafi dadi."cewar Jidda.

Indo ta wage ba ki, " Au ahe hakane."

Jidda ta bude tukunya, "Oh ga hutar naci fa Amman ruwan nan ya ki tafasa, Indo za ki cigaba da fifitawa nikam nagaji wallahi."

Chan Jidda ta Kara budewa ruwan bai tafasa ba, tsaki ta yi ta ce, "Wallahi haka za azuba sa tafaso tare ma, tin da dai ya fara zafi ai Shikenan ta ma fi sauri, ni dama nasani ai da tin dazu da aka zuba ruwan na sa shinkafar atare."
Lantana ta ce, "Wallahi kuwa."

Zuba shinkafar ta yi sannan ta dunga juyawa da ludayi, "Bara na ji ko maganin dai ya ji, ta dandana , " Kai Indo salam Wallahi kara bare guda goma muji."

Da sauri indo ta kara bare maganin aka zuba.

Jidda ta dandana, "Ah yauwa Yanzu kam ya ji magi arufe ke kuma Lanatan kan girkin ya karasa kije kiyi kwaskwarima in mi ki kwalli ki sa kayan nan na sallanki."

Lantana ta ce, "Yauwa na ma tuni haka gwaggo ta ce min ina ado."

Jidda ta ce, "Eh ma na."

Nan fa Lantana ta yi kwaskwarima aka caccaba ma ta fuska.

"Kai Lantana ya naga kinaso ki fini kyau ne aradu daga yau bazan kara mi ki kwalliya ba." Cewar Jidda.

Lantana ta ce, "Tab nikam ai nasan ko me zanyi baxan kamoki kyau ba."

Jidda ta ce, "Allah to ba ni mudubin nan ma in kara ganin Dompol di na."

Kallon kanta ta ke tana wani yatsina fuska, da wani harare harare ta na daga gira.

"Gaskiyarki ne Lantana Gaskiya ni mai kyau ce, kyau iyaka kyau ysn ko makiyi Dompol kon ta zarce kowa, Laaa Indo dubamin abincin nan ki gani."

Indo tana dubawa ta ce, "Laaa Wallahi ta fara yi kin ga ta fara kwoyaye Asama fa."

Jidda ta ta so tana, "Yauwa yanzun nan zai karasa tinda ki ka kwayayen ai shine tafasan daman bara na Kara dandanawa inji."

Ta na dandanawa, "Wooo Gaskiya yau abincin nan fa zai ta fi da mutane."

Lantana ta ce, "ai ko daga jin kamshin ma."

Lantana an zauna an harde kafa daya kan daya.

Jidda ta ce, "Indo Kamar fa yamma ta Farayi jeki mokotannan ki jiyo ma na karfe nawa ne?"

Indo ta ce, "To."

Jidda aka cigaba da juya abinci kamar an sami masa.

Indo ta shigo , "wai karfe uku."

Jidda ta ce, "Tab Gaskiya Lokaci ya kure, bara abincin nan ya karasa yanzu za mu huce gida."

Lantana ta ce, "Amman kwa tsaya kuci ai ko Ku tafi da shi ko?"

Jidda ta ce, "Aa mu kam yadai yi ai na bakine gobe maci dumame ni yunwa ma nakeji zanje in ci tuwo na agida."

Lantana ta ce, "To shikenan."

Jidda ta kara dubawa, shinkafa tana nan ta yi tsumburun-burun, kana juyawa kana jin karar kasa, ga ruwa kamar gwate, abin dai ba kyan gani.

Jidda ta ce, "Yauwa ya ma yi daga gani, Yanzu ki dauko kwanuka ki zuba ma su ni kam mun tafi sai goben."

Jidda na isa gida tq bajewa Iya ta na jin yunwa ai ko sandaren dumamen tuwonta malmala uku nan ta ke ta cinye kan ta fara bayani, "Ashe daman ina da karfi na ke bari ake rainani Daga yau wallahi dukan yara zan nayi in suka kawomin raini, ai yau na yi maganin Zainabu."

Iya ta ce, "Iye karki cemin wannan zainabun mai fantekar fuska."
Chapter 8 · 0% Book details