← Book details Matar Police Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 19

Sashe 15

Matar Police Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Chan dai jikin Jidda ya fara Duran ruwa taga yarinya ba ta da niyar farkawa, chakulkulu ta fara ma ta ta na, "Wallahi Ku saketa na Fada ma Ku Ku saketa in ba haka ba kakata za ta tsine ma Ku."

Ashe daman yarinya iskancine tana jin an fara chakulkulu ta fara motsawa.

Da guji Jidda ta bar wajen sai da zanin ta ya fadi akasa tsabar gudu wai ajanune Ke bin ta abaya.

Ita ko Amira ban da dariya ba abin da ta ke...

Haka Jidda ta koma gida, ba zani, Iya na ga ni ta fara salati da sallallami, "Ni kuluwa na shiga hamsin ya na ganki tsirara?"

Jidda ta gwalalo ido, "Aljanu na gudunwa shine su ka zaremin zanin ni ban ma San ya fadi ba sai da muka koma aji."

Iya ta kyalkyale da dariya, "Ke ki ka San shakiyancin da ki ka yi dai, Babanki ma ya dawo tashi muje."

________Bayan kwana biyu.

Tun ranar da KHALEEL ya rankwashi Jidda bai kara zuwa gidan ba ko ince ba su kara haduwa ba sai yau da yake weekend ne kuma bai da aiki a office, Hajara ya dauko daga wajen salon kasancewar motar ta ta sa mi matsala, hakan ya sa shi cewa ta rakashi ya gaida Mama kan su wuce gida da kamar ba za ta yarda ba, da kyar dai ta yarda su ka shiga.

Ya na shiga ya Tarar Mama na fama da Jidda ta tsefe kan ta ta ki yarda fir, wai ai satin kitson biyu kuma sai ya yi wata kan ta tsefe.

Da shigarsu Tsawa KHALEEL ya ma ta, nan take Jidda ta fara fitsari awajen tana kuka, Iya na ganin Jidda na kuka itama ta fara, da sauri ta tashi ta shige daki ta kwaso kayansu ahargitse ma ta kulle azaninta, kuka ta ke bilhakki da gaskiya,ga kaya aka da ta daura ta fito ta na, "ke kina mata shima ya zo ya na mata ni na gama lura da Ku in ba kashemin ita kukayi ba bazaku taba jin dadi ba, yau zan bar ma Ku gidannan daga ni har ita sai Ku ta yi," in ta yi magana daya biyo sai goge majina da saman zani, ana kara kakkalo wani hawayen.

Janyo Jidda ta yi tana , "Muje."

Daga Mama har KHALEEL summan tsaye su kaj awajen har ma sun ka sa motsi bare magana.

Hajara kuwa Jan gefe ta yi tana danna wayarta hankali kwance.

Suna fita sai ga Baba ya shigo Mama ta kirashi awaya, da ya ke bai yi ni sa ba.

Ko kallonsa Iya ba tai ba ita dai yau sai sun koma kauye.

Jidda kuwa ta ji dadin zaman birni har ga Allah bata son komawa.

*SHIN YA KUKE GANI? YA DACE ACE JIDDA DA IYA SU KOMA KAUYE, KO KUWA ZAMAN BIRNIN DAI ZAI FI??? MAJORITY CARRY D BOTH*

Urs Xayyeesherth
[11/26, 10:03 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

26November2020

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 32/33_*

😂 *ARADU KAMAR AN TOFE LITTAFIN NAN YAWANCIN FANS DIN SA OUT OF 100% , 80% MA SU SUNA AISHA NE😂 ABIN DA MAMAKI FA TAKWARORINA NE MASOYA, WANNAM FEJIN SADAUKARWA NE GAREKI NAMESY AYSHA SHU'AIB, TARE DA AYSHATUL-HUMAERA, DA KE MA AISHA🤣DA AYSHER🤣BAN MA SAN YANDA ZAN BANBANTAKU BA WALLE😂KAWAI DA MA DUK WATA MAI SUNA AISHA INA YIN KU IRIN SOSAI DINNAN🥰🥰*

****************
************
******************

😂😂 *NA LURA MASOYAN DOMPOL KON BA SA SO TA KOMA KAUYE, DAMAN GWADA KU NAI AI ZAMAN BIRNI YA ZAMA DOLE GA JIDDA, TUNATARWA DAI FREE PAGES NA DAF DA KAREWA DAN HAKA DUK WADDA TA SHIRYA SIYA TA MIN MAGANA*

Baba ya durkusa gaban Iya ya na, "Dan Allah ki yi hakuri ko me aka mi ki daga yau basa a kara ba,in sha Allah, ki ya fe ma na."

Iya ta ce, "To ban da fitsara da iskanci ga ta tsarkin yan tsafta za ta addabarmin diya wai sai tai kitso, ana dole ne? Na ga ita kan ta lokacin da ta aureka a yar gajarta ta ke, ga kai kaman hammatar yan iska, ai ko gwanda jiddan ma ta gajemu tai gashi sak kamar na yan indiya, shine ake bakin ciki ko, hnmm za asha mamaki fa agidannan."

Mama ta karaso" Hajiya Dan Allah ki yafemin na tuba, bazan kara ma ta magana akan komai ba."

Iya ta kada kai tare da fadin, "Yoo ina ma kika ganmu bare ki kara tursasata yin wani abun, na Fada ma Ku fa ba abin da zai hanani barin gidannan Yau."

Daga Mama har Baba ba su San sanda hawaye ya fara zubowa daga idanunsu ba, mussaman Baba da ya San Iyah za ta Iya rabuwa da kowa ma indai akan Jidda ne.

Janyota tai suka cigaba da tafiya ta na hama min masifa, KHALEEL da ya tsaya kallon ikon Allah ne ya yi saurin shan gabansu.

Shima durkusawa Ya yi kamar yadda Baba ya yi, "Hajiya Dan Allah ki yi hakuri, ba za akara takurawa Jidda ba, ai ni na za ta ma kitson kan na ta ya kai shekara ne ba a tsefe ba, da nasan sati biyu ne ma ko magana bazan yi ba."

KHALEEL na magana hanjin cikin Iyahtu na motsawa domin duk a tsorace ta ke gudun kar ya dauko bindiga ya ce zai harbeta cikin sauri ta ke fadin, "Yawwa Dan Albarka daman nasan da ka sani ai bazaka tabamin jikalle ba ko? To Yanzu dai ina bakazo da bindiga ba?"

KHALEEL ya fahimci tsoron bindiga karara afuskar Iyah hakan ya sa shi fadin, "Aa Amman na barta amota ko in dauko mi ki ne?"

Ta na ji ya ce ta na mota ta yi wata irin ajiyar zuciya da ya kai karshen maganar kuwa
Wani irin zaro ido Iyah tai tare da fadin, "A'a A'a Dan Allah ka bar ta ni inna ganta ai suma zan, na yarda za mu koma Amman fa kama Mamanku magana in ta kara tabamin 'ya Wallahi sai taga baje kolin iskanci agidannan, in mu ka fita ba ma zamu koma kauyen ba duniya zamu shiga."

KHALEEL ya ce, "Ba ma za ayi hakan ba insha Allah."

Mika hannu ya yi zai karbi daurin kayan, Hajiya Iyah ta ce, "O'o bar ni inshiga da kayana."

Jan Jidda tai su ka koma ciki, ta na shiga ta ga Hajara zaune ban da danna wayarta ba abin da ta ke Iyah ta kalleta tare gyatsine baki, "To fa wannan mai zubin tabaryar daga ina?"

Jidda ta kyakyalle da dariya su ka shige dakin su .

Mama da Baba suna ta yiwa KHALEEL godiya domin sun San in ba dan KHALEEL ba yau ba Wanda ya isa ya hana Jidda da Iyah barin gidannan.

Murmushi kawai KHALEEL ya yi ya na, "Bara na je na kira Hajara mu tafi nasan ta gaji da jirana yanzu."

Suna shiga Mota Hajara ta fara banbamin masifa," in ban da wulakanci ka tafi ka bar ni zaune kamar ka Shanya wake?"

KHALEEL ya ce, "Am So Sorry Madam baki ga case din da ya tashi ba ne, yakamata in tsaya in gyara tunda har da ni aka bata."

Hajara ta ce, "ai shisshiginka ya ja ma, to ma wai wannan yarinyar daga ina? Ga shi ma na ga kaman kuna kama duk da dai ban wani tsaya kallonta ba."

KHALEEL ya ce, "Hmm kanwata Autar Mama."

Tsaki Hajara ta yi, "Ka ji da shi dai in ma Matar ka ce."

Dagowa KHALEEL ya yi ya kalleta, "Haba Hajara mai zan yi da kanwata kuma? Kanwar ma Jidda, Allah ya sawake Wallahi kin chuceni ma, ko da wata ce awaje banjin zan Iya kara mi ki kishiya bare wannan yar shilar me nasama ya ci bare ya ba na kasa."

Dariya Hajara ta yi, "Yoo waya sani Abu aduhu Ai sa an laluba akan San na kwarai,hhhhhh ni ko ma zan so ace an baka wannan yar shilar ko na huta."

KHALEEL ya ba ta rai, "Stop it, Sweety ba na son irin wannan wasan kin fi kowa sani tam."

Duk kasancewar KHALEEL ya san wasa Hajara ta ke Amman ran shi ya matukar baci tun da ta dangan ta shi da Jidda kuma ma amatsayin ma ta, tsanar Jidda ne karara ya shiga ran shi, jima ya ke kwata-kwata ba ya son kara ganinta domin ya tsani yarinyar maganar ta ma inda hali bai son akara a inda ya ke.

1wk ltr

Jidda zaune afalo ban da tsalle-tsalle ba abin da ta ke yi, Hamza ne ya shigo da Sallamarsa da gudu ta je ta rungumesa , "Oyo yo Yayana."

Mamaki Hamza ya yi ganin Jidda agidan na su.

"Ah Jidda yaushe Ku ka zo?"cewar Hamza.

Jidda ta ce, " Tab ai mun jima tun kwanaki fa har ma Baba ya sani makaranta, Yawwa Yaya Hamza ka dawo Dan Allah za ka goyani?

Hamza ya rikye baki, "Kin gan ki Yanzu ai kin zama katuwa inna goyaki Mama za ta yi Fada, kin ga ma fa yunwa na ke ji, ya na ji gidan shiru, ina Anty Mariya da Mama?"

Jidda ta ce, "Anty Mariya ta je rabon ankon bikinta kuma ta ki tafiya da ni, Mama da Kaka kuma kowa ya na dakinsa."

Hamza ya ce, "Owk shikenan Yanzu dai bara na Je nai wanka na yi alwala, inna yi sallah ma gaisa."

Hamza na shiga daki Uncle ne ya shigo da sallamarshi, ko kallonsa Jidda ba ta yi ba, domin ta tsani mutum nan haka kawai batare da tasan dalili ba.

Ya ce, "Jidda ina Mariya."

Murguda ma shi baki ta yi, "Ta tafi anguwa nima ban sani ba ma."
Chapter 15 · 0% Book details