← Book details Matar Police Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 19

Sashe 11

Matar Police Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Jidda ta sauko ta bude flask din ta na ganin abinci jallop din shinkafa ce taji nama da kifi akalla mutane biyu zuwa uku za su ci su koshi.

Jidda ta fara ci tana, "Iya kice fa ta kawo mi ki naki abincin ke ma kin San yunwa na ke ji, wannan ma da kyar ya isheni."

Iya ta ce, "ai kinga irin matsalar da na ke jiye ma na kenan anzo abincin ma ba za a ba mu ishasshe ba sai an mana rowa, maza zainabu in za a Iya atashi adafamin nawa abincin yanzu in kuma da sauran na Ibrahim ki ba ni shi ya nemi wani abincin."

Mama ta ce, "Iya ki kalli abincin da ke cikin flask dinnan fa? Wallahi ko namiji ma da kyar za asamu mai Iya cinye abincin nan bare wannan yarinyar."

Iya ta rikye baki , "Abu yanzu ni ki ke fadawa maganar nan iye? E sabida ke kin saba da yiwa 'ya'ya mugunta ai ba za ki ba su abinci ishasshe ba to ni ba na haka kinga abincin nan? To tas Jidda za ta kare shi kuma atanadan ma ta na anjima ma."

Iya na jin sallamar Alhaji Ibrahim ta fara kukan munafurci, "Zainabu yanzu ni zaki ce ba zaki bawa abinci agidannan ba? Ni za ki hana abincin da 'Dana ya fita ya nemo, ni za ki ciwa zarafi, daman nasan ni ba so na kike ba daman ai da kina da dama da tuni kin illatani."

Mama tsayawa ta yi kawai ta ma rasa abin cewa, Iya sai da ta tabbatar baba ya ji komai kan ya na shigowa ta kara fashewa da kuka.

Tsawa Baba ya yiwa Mama tare da fadin, "Wannan wani irin iskancine? Mahaifiyar tawa za ki bari da yunwa da ace ta ki ce ni zan mata haka ko ko? Ke za ki mata haka? Kin nunamin cewa mahaifiyata ba komai ba CE awajenki ko."

Durkusa wa Mama ta yi ta ce, "Ayi hakuri akasi aka samu, bara na dauko abincin."

Dauko abincin Baba ta yi ta ajiye wa Iya agabanta dagowan da zatayi sai hawaye, Jidda na ganin hawayen nan ta kyakyalle da dariya, "Hhhh Katuwa na kuka."

Da sauri Mama ta bar falon, Mariya ma ta bi sahun bayanta ta na kuka.

Iya ta ce, "Munafukan banza munafukan wofi mu har agaya mana munafurci mu da mu ke namu akasan rafin maliya ma da gangun kifaye, an koyawa 'ya ma munafurci kai wannan lamari dole in gyara ma Ku zama agidannan."

Baba ya ce, "Adai kara hakuri Hajiya ki ci abincin sai ki yi wanka Kiyi sallah."

Iya ta ce, "Sallar dai ko? Ai naga na yi wanka da safe kan mu tawo ko ance ma ni ma agwagwace kamar waccer MATAR ta ka? To bazan ba kuma ba mai sani dole, ba gwanda ni ba ma ina wankan sau daya arana mahaifinka kan ya bar duniya sai ya yi wata bai sa ruwa ajikin shi ba, wani lokacin da dambe zan je in fadawa kakanka ya zo ya taimaka a mishi da girmanshi."

Jidda ta kyalkyale da dariya, "Ashe su kaka dai antaba Kazan ta."

Iya ta ce, 'Sosai ma Yo ai Wannan kadan ma kikaji."

Baba ya San In Iya ta fara zuba ba kakkautawa hakan ya sa shi gaggawan fadin, "To adai yi hakuri, ni bara na shiga masallaci in kun gama in gyara dakin tin jiya kuma nasa ankai kayan da kukazo da su."

Iya ta na sharban loma ta ce, "To to Masha Allah."

Da sauri Baba ya fice afalon ba inda ya fara nufa sai Dakin Mama wadda suna zaune da Mariya ban da kuka ba abin da suke.

Da sallamarshi ya shiga ya ce, "Farincikina, dole ki yi hakuri, ban da wata mafutar da ta wuce wannan, ke kan ki kinsan halin Hajiya tunda ma bare yanzu da tsufa ya kamata, magaifiyata ce dole mu yi hakuri da ita mussaman akan Jidda da ba wanda ta bari ni kai na ma da na ke danta ba ta barni ba, bare ke da kike matata, yi mata biyayya ya zama dole agareni ko da ba na so Indai ba zarce ka'idar musulunci ba ya wajaba akaina, dawo da su gidannan ba karamin jahadi bare Wanda ke da kanki ki ka kara karfafamin gwiwa domin inganta rayuwar 'yar mu, kin ga kuwa hakuri tare da kau da kai akan lamarinsu ya zame ma na dole, mussaman Jidda sai munyi kokarin janta ajiki, Mariya ina so daga yau ko fita za kiyi kunayi tare, kan asan makarantar da za a sata."

Mama ta share hawaye ta na fadin, "Ni lamarin Hajiya ba ya da muna ko kadan wallahi, damuwata Jidda ne da bata daukeni abakin komai ba illa wadda ta tsana abin nan na min zafi wallahi, inda wadda na Ke so aduniya bayan Jidda ne wallahi, ita ce 'ya ta karshe wadda na daura buri na duk a kan ta Amman kaddara ta shiga tsakanin mu ."

Baba ya ce, "Ki daina fadin hakan insha Allah komai zai huce, Yauwa dazu na ga KHALEEL da mu ka iso Allah ya sa dai lafiya ko?"

Mama ta ce, "Hmm to za ace Lafiyar kenan, matsalar dai ta Hajara ce, har yanzu ita fa bata shirya haihuwa ba gashi shi kuma ya kasa hakuri da son 'ya'ya, kuma shi ya na sonta ba zai iya ma ta kishiya ba, na rasa ta inda zan fuskantowa lamarin."

Baba ya ce, "Yanzu irin case din da ake ta fama da su kenan wallahi Allah dai ya kyauta bara na je sallah, kuma kuyi sannan Ku koma falon kar abarsu su kadai."

Urs Xayyeesherth
[11/19, 2:08 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

18 November

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 25_*

****************
************
******************

Washe gari.

Jidda da Mariya zaune afalo Mariya na chatting, sai ga sallama.

KHALEEL ne ya shiga cikin Uniform din sa na Police Rai abace ya zauna yana, "Mariya ina Mamane?"

Mariya ta dago ta kalle shi tare da fadin, "Ah Yaya Khalil kai ne? Ai ko Yanzu Uncle ya fita, Mama kuma tana dakinta."

Kallon agogon hannunsa ya yi cike da takaici ya ce, "Owk wato ba zai Iya jirana gaba ai ya kyauta bara na je na sami Mama daman ni gun ta na zo."

Jidda ko tana gaban TV kallon Tom and Jerry ban da kyakyala dariya ba abin da ta ke.

Wuce wa Khalil ya zo yi kwatsam ya taka igiyar TV ya dauke.

Tsaki Jidda ta yi tana, "Wannan ai Iskanci ne kawai mutum ya na kallo anzo an kashe, Allah ya isana wajen da aka tsallake ban ga ni ba."

Mariya ta ce, "Ke Jidda miye haka ba ki da kunya ko?"

Murguda mata baki Jidda tai ta ce, "To ni waya ce ya ta ba min kallo na."

Kamar zai yi gaba ya dawo baya ya kare ma ta kallo ya tuna da abin da ya hadu su ajiya tsaki ya yi tare da karasowa gaban ta, bakinta ya riko da hannunsa ya na, "Ke ba ki da kunya ko? Ko dai makauniyace ke? Wawiya kazamiya kawai, ki fita a idona Tin ka saki agaba."

Jidda na kokarin yin kuka ya kara bige bakin ya na, "Ni ban ma San me ya kawo wannan sharar gidannan ba, Mariya anya ko wannan ba yar tsutuwa Mama ta jajibo ma na ba ko?"

Mariya ta kyakyalle da dariya Yaya Khalil adai yi hakuri abar ta haka in ka shiga ka tambayi Mama.

Tsaki ya yi ya sake ta tare da tashi domin tafiya.

Da gudu Jidda ta mikye tana, "An Fada din wallahi Allah ya isan min mugu mai kan mangoro bakin gwanda kawai gatun banza da wofi kuma kai ne kazami ba dai ni ba."

Abin ya matukar bawa KHALEEL haushi tafiya ya yi kawai ba tare da ya waigo ba.

Ya na shiga ya sami Mama ta sa Qur'ani agaba tana karatu.

Sallamarsa ce ta katseta ta amsa tare da kokarin rufewa, "Ah KHALEEL har ka iso anji asibitin an cire ko?"

Cike da takaici Khalil ya ce, "Ina fa Mama ni kam na hakura kawai duk sanda taso ganin 'ya'yan ta je acire."

Mama ta ce, "To shikenan Amman ya naga ranka abace ko wani abun ne kuma?"

KHALEEL ya numfasa kan ya ce, "Wata yarinyace wallahi, wai ma wacece ne yarinyar nan tin jiya fa zan fita ta takeni ni ko na maketa."

Mama ta yi tsaki kan ta ce, "Jidda ce wallahi, ni nasan ba mai aikata wannan lamari sai ita."

Khalil ya ce, " Jidda dai Auta Mama? Kar kice Min itace ta zama Mara kunya haka?"

Mama ta ce, "Hmm ka manta ne kai kafi kowa sanin damuwata bai huce halin da Jidda ke ciki ba, gashi andawo da itan ma ni naga kamar abun karuwa ya ke, Yanzu za ta yi abu ka yi magana Hajiya Iya ta fara tsine ma ka."

KHALEEL ya ce, "Ai ko ni Wallahi Indai zan zo gidannan to sai na gyarama Jidda zama daga ita ma har ita Hajiya Iyan."

Mama ta yi murmushi ta ce, "Khalil ai da ka taba Jidda gwanda ka rufama kan ka asiri ka taba koma waye, yau ka ga Hamza na School, Uncle kuma ba ya zama tunda Alhaji ya fara tafiye- tafiyen nan wace makaranta ka ke ganin yadace akayi ta duk da tafara a kauye dai Amman yakamata amaidata baya kasan karatun chan da nan ba daya ba ne bare bana jin cewa ma ta na wani kokartawa."

KHALEEL ya ce, "Zan sa aduba ko ta su Ameera ne asata."

Mama ta ce, "yauwa hakan ma ya fi."
Chapter 11 · 0% Book details