← Book details Matar Police Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 19

Sashe 3

Matar Police Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Ku fara shiga kasuwa, wajen wani mai goriba Jidda ta tsaya tana kifta mi shi ido.

Abin ka da Dan karkara anga yan mata mai kwalliyar yan birni tuni ya birkice sai kallonta kawai ya ke.

Ita kuwa Jidda kara wani rankwashewa ta ke tana, "Gaskiya Gorubar nan za ta yi zaki fa, bara in fara dandana Wannan muji."

Daya ta dauka ta fara ci ta ce, "Kai Gaskiya da zaki sosai Indo, lantana kuma ku zo Ku zabi na Ku."

Da sauri su ka karaso su ka dauko daddaya ita ko Jidda ban da Wanda ke hannunta sai da ta kara diban manya guda uku.

Nan fa Mai Goriba hankali shi ya fara dawowa seti ya ce, "To Yan mata kudin fa."

Jidda ta kyakyale da dariya kan ta ce, "Kudi kuma? Ai ka kalli rabonka, tinda ka kwalla min Ido ai ba a banza za ka kalli kwalliyar Dompol kon ba."

Mai goroba ya ce, "Dan Allah Ku ba ni kudin ba nawa ba ne na ajiya ne fa."

Da ido Jidda ta yi ma su Indo magana sannan afili ta ce, "Ku je gun IYA Ku karbomin kudin in bawa Wannan mayyen."

Su ka tafi abin su.
Ita ko ta kara dumbuzan guda biyu ya zama shida kan ta zura aguje, ba abin ya bita ba azo a kwamushe sauran kawai hawaye ya fara ya na, "Allah ya isa Wallahi ni dai ban yafe ba , Wannan yarinya akwai mugunta Allah zai sakamin."

Jidda da su Indo ko na labe ban da dariya ba abinda su ke yi mi shi.

Jidda ta ce, "yauwa Ku zo muyi gaba abin mu saura Addu'Ah Dan na jima ban sha ba wallahi."

Sai ga Umaru na washe baki ya ga masoyiyarsa da kawayenta, da sauri ya karaso garesu shi da abokinsa Adam.

Lantana sai wani fari ake da ido anga masoyi.

Ta na saurin domin karasawa garesu, Jiddatu tai ma ta wata tsaya, "Dalla chan ki tsaya ya karaso wawiya kawai Ki ja ma sa aji mana haka yan matan birni su ke, na alama yau in mu ka koma gida sai na koya mi ki soyayya yadda naji yayata na yi intana waya."

Lantana dai ba da son ranta ba ta tsaya har su Ummaru su ka karaso.

Ummaru ya ce, "Ah Su Jiddatu manya kenan Yau anshigo gari, ." kawar da kai Jidda ta yi ta na, "Eh fa munzo gaisuwa ne."

Lantana ta ce, "Wato shine jiya ka ki zuwa ko?"

Ummaru ya ce, "Haba Lantana kema kin San dai anfara shirye-shiryen bikin mu dole sai na kara dagewa da noma."

Adam ya ja Ummaru gefe, "Kai nikam dai fa ina son Wannan Jiddar nan ta min wallahi gashi yanayin ta na yan birni."

Ummaru ya kama baki, "tab wai Jiddatu ka ke nufi ko Indo? Ai in fada ma kaf kauyen nan ba Wanda ta ke kulawa, Amman gwada sa'ar ka dai."

Su dawo
Adam ya ce, "Jidda Dan Allah ko za mu iya magana?"

Da Murmushinta ta Amsa da Eh suka ja gefe.

Adam na Sosa Kai ya ke fadin, "a Gaskiya kin min matukar kyau tinda nake akarkarar nan ban taba ganin mai kyau kamar ki ba."

Wani irin dadi Jidda ke ji har cikin ranta kara kallon kanta ta ke tana wani fari da Ido harda juyawa irin ya ma kara ganinta da kyau sosai.

Ya cigaba da fadin, "da ya ke kinsan ni natafi birni Neman kudi Yanzu ma maganar auren Ummaru ne yadawo Dani, Dan Allah ko zaki so ni Wallahi ni dai na mutu aso da kaunarka."

Tini ran Jidda ya baci ba abinda ta tsana fiye da mutum ya ce ma ta wai yana sonta, can kuma sai ta kyalkyale da dariya ta ce, "Amman kaban kunya na aza kawai zakata yabon kyau na ne sai ka bige da wai ka na sona? To ahir din ka ni ko mai maigarin garin nan ma bai isa ya ce ya na sona ba bare kai, kagan ni nan ni Jiddatu kyau iya ka kyau to ka kiyayeni da Wannan rashin kunyar ta ka, yara ba ko kunya wai ka na so na?"

Tsalle tai ta Zungure ma sa kai tai ta ce, "Dama wasa kaje kayi ya fi ma danni in yaro ya karamin Zane shi zan wallahi."

Adam kawai tsayawa yayi yana kallonta domin agirme dai yasan ya ba Jidda shekara goma ko fi ma Amman har ta na zungure mi shi kai.

Tsaki tai ganin ya tsaya kallonta ta ce, "Ke Lantana Soyayyar nan ta isa haka anfa zuwa siyan Addu'ahn ma sai wani makon Yanzu yunwa na Ke ji muje gida."

Sallama Lantana ta yiwa Ummaru shi ko Adam ya yi suman tsaye.

A komawa Indo ce ta Goya Jidda har gida suna shiga ta baje," IYA ina tuwona ni wallahi yunwa nakeji in banci ba ina ganin mutuwa zan yi."

Iya ta fito, "Ina kan ki fita ki ka karya Jiddatu malmala uku fa kika cinye, wai Dan Allah ina zaki kai ci ne? Ni naga ta kai na Ke gashi ba kiga ba Amman sai bala'inci."

Harararta Jidda ta fara yi, "Ai dadinta ma Dai Babana Ke kawo abincin nan bare amin gori."

Iya ta ajiye mata tuwon masara miyar kuka malmala daya.

Jidda na gani ta kurma ihu kambu, "Dan Wannan tuwon Wallahi ni ya min kadan ki karamin."

Iya ta ce, "Saura fa malmala biyu ne kadai kuma kinsan yau har rana daman nayi mana."

Jidda kawai ta fashe da kuka ta na rikye ciki, "Wayyo Iya za ta kasheni da yunwa, wayyo cikina shikenan shikenan zan mutu da yunwa."

Kuka ta Ke tana bori tare da suruntai.

Kan kace miye iya ta diri mata tukunyar tuwon gabanta.

Tana gani ta tashi tana share hawaye ta ce, "Indo Ku tafi gida sai na gama cin abinci kwa dawo."

Fita kawai su ka yi domin sun San koda sun zauna Jidda ba sammusu tuwon nan za ta yi ba.

Fara cin tuwon nan tai ba kwakkwotawa kai kace bata taba cin abinci ba cikin dakiku kadan Jidda ta cinye manyan malmalayen tuwo guda uku.

Tana cinyewa ta ce, "IYAtuna Dan Allah ki daura ma na wani abincin kan anjima kin San cikina da jin yunwa."

Urs Xayyeesherth
[11/13, 1:57 PM] Xayyeesherth: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._
__________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*_FREE PAGE 7/8_*

****************
************
******************

Su ka tintsire da dariya , "Iya Taji kunji min Fitinanniya wato kina sane da labarin jummala mai Jinnun karya."

Jidda ta ce, "Eh mana ai nikam ma Yau dole ki kara bani labari domin kare kai na ko wataran ma za akara hakan."

Iya ta tabe baki , "Ja'ira kawai ai ina ganinki nasan cewa wannan iya shegenki ne kawai."

Jiddatu ta ce, "umm nikam dai Wallahi yunwa na ke ji Iya."

Iya ta ce, "Aiko ban ko daura sanwa ba na fito kenan aka sanar dani halin da kike ciki."

Nan take Jiddatu ta baje awajen tana bori, "Ni Wallahi yunwa nake ji kuma mutuwa zanyi in banci abincin nan ba, wayyo hanjin cikina suna magana wallahi Iya kinji ko magana suke Wallahi Yunwa nakeji kaman cikin zai fashe hanjin su fito."

Iya ta dafa hannu aka ta na fadin, "ki rufamin asiri Jidda karki mutu wallahi in kika mutu bin ki zan yi ko mahaifinki ban mai son da na ke yi mi ki ba kiyi hakuri kinji ki bawa hanjin cikinki hakuri yanzu zan dafa miki taliyar birni (indomie) ko Leda biyu ai ya isheki ko?" Iyatu na maganar ta na goge guntun hawayenta.

Jiddatu ta gyara zama ta na, "Yauwa sun tsaya ma yanzu ki dafamin ko da Leda uku dai zanyi maneji dashi kin San tsutsar cikin nan nawa da hanjin kwashewa su ke, kuma ki daina kuka bazan mutu ba kinji mutuwa ma tare zamuyi."

Jiki na rawa Iya ta tashi ta na shekan majina ta ji yar lelenta na maganar mutuwa tuni ta dafa ma ta indomie.

Tana gamawa kuwa Jiddatu ta langwabe sai da Iya ta bata abaki.

Da daddare Iyatu zaune da Jiddatu tare da su indo da lantana anzo hirar dare.

Jiddatu ta tintsire da dariya, "Wayyo Allah na Wallahi yau Baku ga maigari ba harda fitsari fa, lokacin da ya cire rawanin shi saura kiri in sa dare sai na wayance da ihu."

Indo ta ce, "Haka Baffa ya zo yana fadawa Inna ai wallahi na so ma ina wajen daman gashi mugu aj gwanda da ki ka mishi hakan ma."

Lantana ta ce, "Hhhh wayaga mai gari na fitsari f
Indon nan ya yi zuru-zuru kamar magarya."

Jiddatu ce ta katse su, "Ai Wallahi da ace ya sa andakeni ko? Daga shi har mai hukuncin sai na rama in nemo wannan abin kaikayin in sa ma su ajiki."

Iyatu ta ce, "Ai ko ba Ku da wayo irin namu na yan da kinga ai ni naso ma ki bari ya Dan tabaki kan daga baya ki tsere kinga daga nan zamu hada ma su damurmurar Dana sani."

Jiddatu ta shekye da dariya, "Kai Amman dai Allah shiryaki Iyatuna Wallahi kin San salon mugunta da ace azamanin fir'auna ki ka zo dole Ku sasanta.".

Iya ta gyatsine fuska kinci gidanku sai dai Wannan masifaffiyar uwartaki Amman ba ni ba."

Jiddatu ta fara hararar Iya, "Ni dai wannan ba Uwata ba ce bayan ma ba ta so na, yauwa Iyatuna kawo kudin tsiren ma nasan yanzu Mallam Audi ya fito."

Iya ta lalubo gefen zaninta ta Ciro wata fatakakkiyar naira Dari ta ce, "Gashinan ki ce mishi acikamin kulli kuma gashasshe mai zafi za abani."
Chapter 3 · 0% Book details