Sashe 10
Matar Police Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Iya ta galla mi shi harara ta ce, "Kwajiyemin zumudi ai a bari dai inyi sallama da yan gari ko? Dan haka sai gobe, in ka ga za ka Iya kwana to in kuma bazaka Iya ba ka tafi mu zo da kan mu."
Alhaji Ibrahim ya yi saurin fadin, "A'a Iya zan ma jira Ku ai ba matsala."
Nan fa tinda Jidda ta fice agidannan ban da bazawa agari za su koma birni ba abin da ta ke fadi agari kowa na jin hakan za su yi Hamdala aransu domin Allah ya ta ba su ka kaikyayin da ke addabarsu.
Lantana da Indo kuwa kuka su ke hakkun domin ji su ke kamar za arabasu da farinciknsu, Jidda ta ce, "Ku dalla Ku daina kuka zanna zuwa ina dubaku fa in kawo ma Ku kayan birini, kayan abincin dadi har ma da na sawa kunji, Yauwa Lantana Ku zo ma muje ayi tsokanar karshe."
Indo ta ce, "Nikam dai fa ba na so ki tafi ga bikina fa watan gobe ni ko irin kwalliyar Da kikewa Lantana ba ki taba min ba."
Jidda ta ce, "Dalla chan ai zan zo zan fadawa Babana ya kawoni, ni dai damuwata yanzu mu yi tsokanar karshe kinga gobe da safe za mu tafi."
Lantana ta ce, "To ko dai kasuwa za mu shiga ne?"
"dilla can kin manta yanzu ke matar Aure ce in mu ka shiga kasuwa ummaru zai gan mu fa kuma kin San za ayi Fada."
Lantana ta ce, "umm Shikenan to Yanzu ina za mu je?"
Jidda ta ce, "Yauwa muje gonar Malam bala mai kan tabarya hhhhhh wayyo Wallahi goshin mutumin nan dariya ya ke ba ni."
Indo ta kyalyale da dariya, "Ai Wallahi ni goshin sa ma kadai na ke son ja fa."
Lantana ta ce, "Ai ko mu rufawa kan mu asiri Dan naji Ummaru na cewa ciwon hauka ya kama Malam balan fa in akaje gonarshi bugu ya ke."
Jidda ta ce, "Ku ji ma fa sallah ake kira in ban koma gida Yanzu ba Baba zai min Fada kin San yazo, gobe da safe kan mu tafi sai kuzo gidan kunji."
Lantana ta ce, "To Shikenan."
Indo ta ce, "to muje in raka kan na wuce gidan."
Su ka tashi sai da Indo ta raka Jidda gida kuwa kan ta tafi, Jidda na shiga gida.
"Mama tun da kika ci abinci fa kike fice agidan nan sai Yanzu." Cewar Alhaji Ibrahim.
Jidda ta shagwabe fuska, "Umm Baba fa na je sallama da Kawaye na ne."
Gudun kar ya takura Iya ta tunzura ya sa shi fadin, "Allah dai kyauta to."
Iya ta ce, "Ameen Uban kanzagi."
Jidda ta ce, "Iya ina shinkafar kince ita zaki dafa da daddare."
Iya ta ce, "Yoo gatanan ki diba na bar mi ki atukunya."
Sai da Jidda ta makare cikin roba kan ta zauna ta cinye tas, Baba kawai tsayawa ya yi kallon ikon Allah ba halin magana, mamaki ya ke da irin ci na Jidda.
****Washe gari da sanyi Safiya Iya ta fara tattara kayan su harda su tukwane.
Baba ya ce, "Iya akwai komai na girki agidan ba sai kin dauka ba."
Harararshi ta yi Tare da fadin, "Ni to zan tafi da nawa ina fadama ba abin da zan bari agidannan gwandama ka ji ehee kalan mu je ana raina mu akan abincin Da Jidda za ta ci? Bar ni na tafi da komai nawa."
Haka Baba ya yi shiru ya zubawa sarautar Allah ido.
Jidda ma ko ta na nan tana hada tarikicenta.
Sai da suka kwashe komai kaf su ka yi wanka, ganin baba ya sa Jidda yin wanka ba musu.
Sun fito za su tafi Iya ta ce, "Ayya mai gari nasan zai yi kewarmu ka bi da mu ta gunshi mu ma sa sallama."
Mai gari na ganin Jidda da Iya sai da gabanshi ya fadi ya ce, "Hajiya Iya ba dai wani laifin aka ma Ku ba."
Dariya Iya ta yi ta ce, "Aa fa maigari sallama na zo yi ma za mu koma birni da zama."
Wata irin ajiyar zuciya maigari ya yi wadda sai da ta bayyana azahiri.
Ya ce, "Ayya Yanzu dai za Ku tafi ku bar mu kenan Amman da Jidda zaki tafi?"
Iya ta ce, "Eh Wallahi tausayinka kawai na ke na tafiyar nan ta mu shiyasa na zo ma sallama."
Wani irin dadi maigari yaji aranshi fal farinciki azahiri kuwa kukan munafurci ya fara kakalowa, "Ai Wallahi ko ni ne abin tausayi nasan kaf garin nan sai ya yi rashin ki, Allah sarki Hajiya Iyatu kamar in bi Ku Wallahi."
Nan ta ke ma Iya ta fara kuka ta na goge majina da bakin zani ta ce, "Allah sarki Anya ma zan Iya tafiyar nan ko ni kam na fasa tun da dai ka ke kuka."
Da sauri mai gari ya share hawayen tare da Jan majina ya durkusa gabanta tare da fadin, "aa ba za ayi haka ba nikam na hakura Wallahi na yafe mu je ma in rakaku."
Maigari ya kalli ya Fada ya ce, "Maza Ku hanzarto mu raka Hajiya Iyatu."
Haduwa sukayi duka suka nufi hanyar rakiyar Su Jidda, Lantana da Indo sai kuka ake za arabu da Aminiya.
Jidda ko sai washe baki ta ke tana, "Lantana karki damu in kin haihu ai zan zo suna da bikin Indo."
A haka dai har su ka isa Motar sai da maigari ya tabbatar andaina hango motar su Jidda kan ya ce, "Alhamdulillah Nagode wa Allah, Allah raka ta ki gona yanzu ba ni ba jin batun mutuwa."
Jidda da Iya kuwa tunda suka shiga mota ban da barci ba abin da su ke sai da aka kusa isa garin kano su ka farka.
Kamar jira Jidda ta ke asauka ta na fita ta fara tsalle-tsalle ki cibis ta bangaje wani Matashin saurayi.
Ko juyawa ta kalle shi ba tai ba bare ta bashi hakuri.
Hakan ya sa shi saurin shan gabanta tare da kwalla ma ta wani hamshakin mari, ya cigaba da tafiyar shi.
Kuka ta fara ta na, "Allah ya i San min wallahi mugu kawai azzaalumi mai kan tabar...
Urs Xayyeesherth
[11/19, 2:08 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
°°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°
16November
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝
__________________________________________________________
_We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_
_*LABARI DA RUBUTAWA*_
_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_
_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
1- _BABU RUWAN SO_
2- _KUCHAKAR KISHIYA_
3- _WASA DA SO_
4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_
5- _JAMEEL (Nafseen)_
6- _KWADAYI 2020_
AND NOW *MATAR POLICE*
_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
*_FREE PAGE 23/24_*
_*Free pages na daf na karewa wa inda ba su biya ba su hanzarto domin biya tare da samun cigaba akan lokaci*_
****************
************
******************
Tabarya, kuma sai Allah ya sa ka min."
Ta na ta tsine-tsine dawowa ya yi, ya tsaya ya kare ma ta kwallo da kyau jikin shi ya ba shi cewa wannan yar uwar shi ce, duk da kasancewar bai San ta ba kuma bai taba ganinta ba sai yau, tsanarta ya ji kawai ya shiga ranshi nan ta ke domin in akwai Abin da KHALEEL ya tsana bai wuce rashin kunya ba,bayan ya gama kare ma ta kallo, wani hamshakin tsaki ya yi sannan ya ya juya da niyar tafiya.
Ita ko Jidda kan ta akatsa ko kallon fuskarshi ma ba tai ba bare tasan waye har sai da taji takun tafiyarshi na barin wajen kan ta murguda baki tare da dogon tsaki kan ta ce, "Aikin banza duk da ban ga fuskarka Amman zan ganeka da wannan zoben hannun na ka, kuma wallahi sai na rama Marin da ka min, mugu kawai duk gida anbi antara mugaye kawai, kuma duk sai na gyara ma Ku zama."
Iya ce karaso tana fadin, "Jidda wai ina ki ke ne? Daga zuwa naji kin fara un-uni kar dai wani ne ya ta ba min ke?"
Jidda ta ce, "Wani ne fa wai Dan natakashi ba da Sanina ba shine ya mareni, kuma fa ni ban sani ba."
Iya ta ce, "Lallai ma suna so daga yau in fara tsine ma su kenan ko? Gida duk anbi antara azababbu mugaye agida to wallahi ba zata sabu ba."
Mama da Mariya sun fara jin kwaroroton Iya hakan ya sa su saurin fitowa.
Mama ta durkusa , "Ina kwana Hajiya."
Kau da kan ta gefe tai tare da amsawa kamar me shan magani.
Mariya ta ce, "Ah Hajiyar mu an iso kowa sai ya San da zuwanki."
Iya ta ce, "Ba dole ba daga zuwa har an taba min abar so na."
Mama ta ce, "Iya Kiyi hakuri yanzu dai mu shiga ciki."
Iya ta ja Jidda su ka yi gaba fuuu.
Mama ta tsaya ta na fadin, "To Allah ga mu gareka, Allah ne kadai ya San yadda zaman gidannan zai kasance."
Mariya ta ce, "Mama Kiyi hakuri ai anyi mai wuyar tunda suka Yarda su ka dawo komai zai yi dai-dai."
Mama ta ce, "to mu shiga kar wani abun ya biyo baya ni ban San ma waye yadaketa ba tunda dai duk antafi makaranta, Uncle ma ya na kasuwa KHALEEL ne kadai ya fita yanzu." Ta na maganar har su ka shige ciki.
Iya zaune akasan kafet Jidda kuwa ta Dane kan kujera ta na kwance ga kafa duk datti kamar an kwato ta daga filin dambe.
Kawar da kai Mama ta yi kawai daga baya kuma wani tunani ya zo ma ta tace, "Jidda ko gaisuwa ba bu? Ko ba ki ganni ba ne?"
Jidda ta murguda baki tare da fadin, "Ni ai bakyasona ni bazan gaisheki din ba ni ke ba mamana ba ne, Kaka ta fi sona tinda ita bata dukana."
Dan takaici Mama ba ta Iya kara fadin uffan ba, sai zuwa ta dauko abinci da tayi.
Ajiye ma su foodflask din tayi gaban su sannan ta dauko flat da cokali.